chapter 10

Noorurrahman✔

Tunda farhana suka sauketa a bakin gate din makarantan gabanta ke dukan uku uku, tsoranta Allah tsoranta abunda zataje ta tarar a cikin makarantan "
Mutane tagani a bakin wani board akafe suna surutai ,gabanta bai sake yankewa ba saida ta tambayi wani security abunda suke a gurin ya shaida mata an kafe result ne da kuma sunan wadanda aka kora'

Wata mumunar faduwa gabanta yayi dataji ya ambaci wadanda aka kora ,
DA sarsarfa ta karasa gurin batareda wani tunaniba ta ratsa cikin mutanen tana neman ko tana cikin yan kora "
Wani matashine dayaga gaba dayanta ba a nutse take bane ya Matso kusa da ita "
Menene admission number dinki ,
Fada masa tayi batareda ta kallesa ba ita dai burinta bai wuce ace babu sunanta ba"

A tsanake yafara dubawa yanasan ya ganota, yayi hakan yayi wajen sau uku amma babu ita babu alamunta ,kallansa ya maido gareta ,
Level nawa kike."

One ta bashi amsa "

Kamar tace kowa ya juyo ya kalleta take kuma suka hau dariya "
wani makakin bakin cikine ya tsaya mata dan last abunda ta tsana shine Dariya ta tsani ita ba mahaukaciya ba a dinga mata dariya "

Matashin da ya taimaka ne yayi musu magana"
Haba menene kuma abun dariya "
Wata budurwa da tafi kowa darawa tace haba saleem yazakace kar muyi dariya bayan abun dariyarne ya faru ,level one fa mutanen da suka fara lectures jiya mai hadinsu da duba jarabawa"_
Batareda ya kulata ba ya kalli noor "muje ko"

Babu musu ta bishi dan zata iya saka kuka yarda bakin ciki ya tokare mata makoshi.

Hanyar dept dinsu ta nufa tana jin haushin kanta da abin da ya faru.

Saleem ne ya katse mata shirun ta ta hanyar mika mata goran ruwa,
Karba tayi tana masa godia.
"
Nasan banida hurumin magana amma nakasa shiru ,
Jiya kuka fara lectures mai ya kaiki duba jarabawa kuma"

Runtse idanu tayi jin wata kunya ta dirar mata dan sai yanzu abunda tayi yake kara dawo mata ,

"Nayi abunda yakamata ayi expelling dina so dana tambayi security yace mun harda yan kora i couldn't hold my self "

Mai yasa zaayi expelling dinki daga fara zuwa makarantarki jiya"

Its a long story ,
Anyways
Thank you for having my back earlier,I will forever be great full "
Fara tafiya tayi dan last thing abunda take bukata shine hulda da mutane cikin makarantar kar ma ace maza"

How can you be great full when you don't even know my name "
God "
Shine abunda ta fada cikin ranta so take alakar ta tsaya anan inda ta soma"

Saleem Dikko ,
Banking and finance ,3rd year"

Murmushi tamasa kafin tace "
Noorurrahman "
Batareda ta sake jin ta bakinsa ba tabar gurin"

Lokacin data shiga aji dalibai ta tarar suna ta surutai group group"
Chan baya ta samu ta zauna ,wayanta ta dauko ta kunna kira'ar minshawi cikin suratul imran ,earpiece ta saka tafara saurara cikin nutsuwa,
.jitayi an dafa mata kafada ,
Bude lumsashun idanunta tayi ta dorasu akan wadda ta dafata "

Udaysah ce"
Ajiyan zuciya tayi "
Noor about jiya kiyi hakuri dan Allah i dont know what comes over me "
Kinsan ..

Bata bari ta karasaba ta tashi ta fice a ajin dan muddin tayi magana to mai zafi ce zata fito abakinta"

Office din sir fayyaz ta nufa dole taje tayi wani abu "
Ta Yanke shawarar bashi hakuri ko dan karatunsu"

Bakin office din ta tsaya tana tunanin mai ma zatayi "_
Pepper spray ta dauko a jakarta lokacin da idea ya fado mata ,kasan idanunta ta fesa ,take sukayi ja wani radadi ya ziyarcesu ,lokaci daya hawaye suka fara zuba dan azabar zafin pepper spray din"_
Gyara kanta tayi ta tataro dukan kwarin gwiwarta kafun tayi knocking "

Come in muryarsa ta bata umarni"
Budewa tayi tasa kai tashiga office din bakinta dauke da sallama"
Noor " taji an ambaci sunanta "
Kallann wanda ya kira sunanta tayi ,
Saleem ne
Yitayi kamar bata sanshi ba dan bataso ya bata mata shirinta "

zaka iya tafiya "
Fayyaz yabashi umarni"
.bamusu ya mike sanin halin sir fayyaz amma zuciyarsa fal tambayoyi ,lapia idanunta sukayi ja haka kuma mai akai mata haka take kuka"
Fita yayi yana juya tambayoyin da bashi da amsarsu "

Kara matsar kwalla tayi lokacin da salim ya fita daga office din,
"Sir nazo na baka hakuri akan abunda kanwata tayi maka,
Dago rinannun idanunta tayi ta kallesa "
Kara kallanta yayi yana mamakin yarda kasan idanunta sukayi ja "

Who are you ya tsinci kansa da fada"
Batai mamakin kasa ganetan da baiyyiba dan daga ganinsa dama zaiyyi wulakanci amma ya zatayi shes doing this for there future.

Sir sister na jiya mukazo ta ce  sai kabani hakuri ,
Dan Allah kayi hakuri sir bata da lapia ne tana da matsalan kaine da yake tashi a cikin 24 hours sau daya "
Kara matsar kwalla tayi "
Bansan ya akayiba sir tace na rakota zata karbi abu na sha'afa gaba daya kuma banyi tunanin komai ba na biyota ban kara ganin lapin kaina na barinta tazo nan dinba saida tafara maka rashin kunya na kasa tsayawane sabida na tsorata dan Allah sir kayi mana aikin gafara "

Sakar baki yayi yana mamakin yarda ta iya tsayawa yana kallonta tana kallonsa tana gillo masa wannan shegiyar karya wadda kai bazai dauka ba "

GeT OUT shine abunda ya iya fada "
Wani kukan karyar ta kara saka wa,
Dan Allah sir kayi mana afuwa daga yau bazata sake ba ,
Mun tuba idan iyayenmu sukaji wannan maganar laipina ne zai zama babba"

wani kyamarta da takaicintane ya ke shigarsa  a hankali ,a hankali,musamman dayaga taki daina gillo masa ta mazugal"
Buga desk dinsa yayi da karfi "
"I said Get out ,
Baki jini bane idan kika kara mun magana daya sai kin bar makarantar nan wallahi kifice mun a gani ko ran ki ya baci sosai"

Jin cikin maganarsa baa koresu ba yasa batareda damuwaba ta fice daga office din ,
Direct restroom ta nufa dan wanke fuskarta amma still effect din pepper spray din Nanan a kasan idanunta,badomin tanada wani lecture dinba da gida zata wuce ,

Tayi saa ba malami sai daliban dake ta hira kamar yarda ta tafi ta barsu,
Desk din da ta tashi taga udaysah na gurin a zaune har lokacin, baya ta samu ta zauna dan bata san sake kulata"

Ganin ta ware baya ta zauna yasa udaysah batayi zuciyaba ta sake zuwa gareta tunda itace tayi mata lapia"

Noor look "there is no point mu zauna muna fada kan abun nan ,nasan na miki ba daidai ba kuma na dauki laipina bai kamata nayi haka ba ,kiyi hakuri and trust me bazan taba yi ma malami haka ba im smartest than that, brother fayyaz yaya nane and abokin wasa nane amma still naji haushin abunda yayi miki kuma da kin tsaya har karshe da kin gane brother nane "

Wani dum gaban noor ya fadi lokacin da ta tuno muguwar karyar da tayi ma fayyaz"
Ya illahi"
Juyowa tayi tana facing udaysah "
Did you just said yayan kine "

Kada kai udaysah tayi "
Eh yaya nane da nake zaune a gidansu mahaifiyarsa sister din abuh nace "

Doka hannayenta biyu tayi akan desk ta dora kanta ,
Shikenan ita dai yau gaba daya da rashin saa tashigo cikin makarantar nan "
Kara tuno irin uwar karyar da ta shirya ma fayyaza tayi
Innalillahi what have I done.



*****
Kuyi hakuri da wannan
Nayi typing ya goge but nayi kokarin sake muku and im even exhausted to edit ".

Chu chu jay✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top