chapter 1
NOOR-UR -RAHMAN.
Noor !!Noor!!
Noor
Gidan uban wa kika shige inata faman kiranki kinajina kikayi shiru,.
Kaman a mafarki taji anyi watsi da kayan kan miror dinta ,
A zabure ta mike tazuba masa kyawawan idanunta wadanda bacci bai gama sakar su ba '
Dan kwalinta ta jawo ta daura tareda saukowa daga kan gadon jikinta na bari ganin yanayin da yake wanda tasan bakaramin aikinsa bane ya bata kashi ,
Bakinta na karkarwa tace yaya nas Allah banji shigowar ka ba kainane yake ciwo sosai shiyasa nadan kwanta kuma bansan lokacin da bacci ya daukeni ba "
Da sauran mayen da bai gama sakinsa ba yace "dan ubanki baki duba lokaci ba hala karfe goma sha biyu na dare baccin me zakiyi ban shigo gidaba?
KO kin manta na gargadeki akanyin bacci kafin nayi koda kuwa zan kai gobene a waje ,hala dukan dana miki da safe bai isheki ba "
Gadan gadan yayo kanta tareda cire belt din dake jikinsa yafara zabga mata ,tun sautin kukanta na fita har ya daina sabida tsabagen wahalar da take ji na dukan nasa,saida yayi mata lilis kafun ya tsalaketa ya shige bandaki yana fito ".
A hankali ta mike da kar ta bar dakin tana share hawaye ,
Da ace duka na kisa to da tuni dukan yaya nas ya kaita har lahira domin ranaku daidaikune baya tashinta da duka sannan zaiyyi wuya yashigo gida bai dake taba musamman idan yana cikin maye '.
Kitchen ta Shiga adaddafe ta dauko warmers na abincin da Already tagama hada masa ,
A gaban kujera three seater ta jerasu domin tasan halinsa yanzu zai ci ubanta idan ta jera masa kan dining ,
Bayan ta gama aje masa komai da yake bukatane ta dauko remote din tv ta aje a gefen kulolin dan yanzun yafito bai gansu ba jikinta zai iya gaya mata "
Kaman an jefosa kuwa haka ya fito daga bedroom din yana zazzare idanu ,
Sanye yake cikin grey din singlet da boxers wanda ga dukkan alamu ya watsa ruwane kafun yasaka su"
Aladarsa kenan ,"duk lokacin da ya shigo gida cikin maye zai shiga yasakar ma kansa ruwan sanyine ko abin zai dan sakesa ,wani lokacin kuma idan rikakun yan iskan na kansa zaibi gadone yana tsaminsa wanda hakan ba karamin damunta yake ba musamman idan yanema muamalan auratayya da ita wanda dole take bada kai bori ya hau domin idan ta tsaya taurin kai ita keda shan wahala .
Kallonta yayi tareda yamutsa fuska ,a dan tsorace tace yaya nas ga abincin ka and i cooked your favorite,batareda ya tankataba ya karaso gareta tareda ball da warmers din wanda saida abincin ciki ya zube ,da yatsa ya fara nunata tareda fadin"dan ubanki ni zaki ajema abinci a kasa nida gidana ?
Kin rainani kwana biyunan noor wanda inatunanin kwana biyu baki samun isashen duka to kinsan Allah idan kika kara mun irin haka na lahira sai ya fiki jin dadi kuma yanzu ki tashi kije ki dafa mun wani abincin"
A take wasu zafafan hawaye suka sauko mata sabida ta tabbata da ace a table din ta aje masa same abunda zai faruke nan ,babu ranar da zatayi abu ta birgeshi ko ya yaba mata,. ita kullum a ba dai dai take ba,
Share hawayenta tayi tareda kwashe kayan da ta zubar tayi kitchen,
Koda ta fito goge gurin bata tarar dashi ba dan haka cikin tsanaki tagoge gurin tsaf kana ta koma dora masa wani sanwan duk da irin bacci dake idanunta "
Duk inda zaije bayajin dadi idan har ba abincinta ya dawo yaci ba sabida noor badaganan ba wajen iya sarrafa abinci dan haka wani lokacin zai gayyato abokansa yan iska yasaka ta dafa musu abinci suzo suci su bama wandon su iska .
Bayan ta gama girkinne ta shiga dakin domin sanar dashi ta gama,kwance tagansa kan gado yana video call da ire iren yan matansa wanda idan da sabo ta riga ta saba ganin haka bata katse shiba ta fita domin bashi gurin dan muddin ta katseshi zata gane Allah dayane "
Bayan kamar minti talatin sai gashi yafito yanata fadi shi a dole isasse "
Bai nemi ta zuba masa abincin ba wanda hakan yayi mata dadi ainun ,
Saida ya kammala yayi gyatsa kafun yamike tareda mata alamun ta biyosa daki,bata yi musu ba ta miki kamar wata jela ta bisa dakin dan a yanzu dai she have got enough of Dukan sa na ranar .
****
Asubar fari ta farka domin yin sallah kana ta hada masa karin kumallo dan 6:30 yake tafiya aiki kuma bai daukan excuse na latti idan tayi'
Wanka tafarayi domin tsarkake jikinta kana ta yi sallah,sosai ta kaima Allah kukanta tareda rokan ya cireta cikin wannan kangin rayuwar auren da take ,
Dubanta ta mayar gareshi taga yanata baccinsa kaman wanda ya mutu ,tsaki tayi tareda tashi a gun tana Allah wadai da halayya irinta yaya nas ,jitake kaman ta gudu ta bar mishi gidan amma ta wani bangaren idan ta tuna maganar mahaifinta da yace mata muddin ta yarda tayi abunda nasir zaiyyi Allah wadai da ita to bazai taba yafe mataba"
Bayan tagama hada masa karin kumallone ta koma kan kujera ta dauko quran tafara karantawa a hankali dan shine maganin kowace masifa sannan indai tana karantasa takanji sassauci a cikin zuciyarta ,
Cikin shigarsa ta suit ya fito kaman duka kenan wanda ba karamin kyansa da haibarsa bace ta kara bayyana a kayan "
Cikeda ladabi ta gaishe sa ,batayi tsammanin zai amsataba amma ga mamakinta taji ya amsa wanda rabonta da jin ya amsa gaisuwarta tun tana amarya ,
Bai jata da dogon maganaba ya hau kan dining yafara karyawa ,
Kallonta yayi yace "ke kin karya "
Aa "tabasa amsa a takaice "
Maiyasa "?
Da mamaki ta kallesa kafun tace so nake kagama tukunna,
Bai sakecewa komai ba yacigaba da cin abincinsa wanda bai daukesa minti talatinba ya dauka jakarsa ta zuwa aiki ya fice a gidan "
Ajiyar zuciyatayi tana kara jinjina dabiun yaya nas wanda bata saniba shin dama yana dasune ko kuma bayan auransune ya ara ya yafa "
*****************************************
Alhaji mukhtar dala baban dan kasuwane dake zaune a cikin garin kano da matarsa hajia maryam da yaransu uku"
Muhammadu auwal shine baban dansu wanda yake da shekara ashirin da tara sai mai bi masa Noorurrahman mai shekara ashirin da biyu sai yar kanwarsu mahnaz mai shekara goma sha bakwai,
Alhaji mukhtar yakasance mutum ne shi mai tsaurin ra'ayi wanda idan yace abu bakine to koda kuwa ba baki bane dole a bakinan zai zauna ,
Inda Allah yake abunsa sai ya saba hali tsakaninsa da matarsa hajiya maryam domin ita ta kasance mutumce mai sanyin hali da jan yaranta ajiki domin jin damuwarsu "
Sai da takai gwaro ta kai mari kafun ya sassauta wani abun gameda yaransa har yakan dan jasu a jiki suyi hira .
Sosai yaso muhammadu auwal ya gajeshi ta hanyar kasuwancinsa amma yakiya domin shi ya kudiri niyar yayi karatu mai zurfi wanda mahaifiyarsa tayi ruwa tayi tsaki mahaifinsa ya tsaya masa har yayi karatu mai kyau inda Alhamdulilahi burinsa ya cika nazama shahararen dan jarida "
Noor kuwa koda ta gama secondary school fafur ya kafe akan cewa bazata cigaba da karatuba domin a cewarsa aurene kawai yadace da mace musamman ma mace kaman noor mai kyan fuska dana jiki.
Tayi kuka ta gode Allah ,babu irin rokan da batayiwa mahaifin nataba akan ya taimaka mata tayi koda diplomane amma yace ina ai aure kawai shine last choice dinta wanda bata isa ta hana yayi mataba domin dama tun kafin tagama makaranta ya gama maganar da tilon dan uwansa Alhaji umar da gidansa ke jikin nasa magana akan hadata da babban dansa nasir "
Tunda yafara maganar take kuka wanda hakan baisaka yaji tausayintaba ya janye kudirinsa a take tausayin mahnaz dake daf da gama secondary yashigeta dan tasan itama irin footsteps dinta zata taka inyabarta tayi shekara biyun datayi kenan bayan kammala secondary dinta .
A sukurkuce tashiga dakin mahaifiyarta wadda tunda Alhaji muktar yafara maganar ta tashi ta bar masa gun,jikinta ta fada tana kuka ,
A hankali tafara shafa kanta tace "noor nasanki yarinyace mai biyyaya sannan mahaifinki bazai taba cutar dakeba bugu da kari naseer yaron kirkine inada yakinin bayan aurenku zai barki kicigaba da karatu sannan shi din dan uwankine duk yarda wani zai mutuntaki bai kaiga shi ba yanzu ki share hawayenki kinemi yardar Allah insha Allahu bazaki taba tabewaba.
Hawayenta ta goge jin maganar mahaifiyarta wanda a take wani kwanciyar hankali ya zuyarceta,
Daukan dukkan lamarinta tayi ta damkawa Allah mai komai mai kowa .
Chuchujay🖤
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top