3
Yahya related to me from Malik from Abu'z-Zinad from al-Araj from Abu Hurayra that the Messenger of Allah, may Allah bless him and grant him peace, said, "Beware of suspicion. Suspicion is the most untrue speech. Do not spy and do not eavesdrop. Do not compete with each other and do not envy each other and do not hate each other and do not shun each other. Be slaves of Allah, brothers." (Malik Muwatta)
******
Nimra kai tsaye motarta ta shiga, this is the beginning of a new era, ta jaddada ma kanta. Kafin ta tada motar ta sake ƙarema wajen kallo. Thou ba ta fara zuwa ba tunda tana maƙale tana bibiyansa.
Tasan cewa A2Z dirty politician ne, amma a haka shi ƙaramin alhaki ne a madadin sauran abokan harkansa.
Koda Arc Yusuf Jere ya koma gida ya tarar da matarsa Lubna tana zaune akan kujera tana jiransa. Anty Lubna ma'abociyar kwalliya ce danko saida ta tsatso cikin daren kamar ma zuwa biki, tasan da meeting ɗin kuma bayan Maghrib ta rakashi wajen motarsa sabida zumuɗi.
Tunda A2Z yace akwai meeting ranta ya soma mata wani iri, bawai tashin hankali take fuskanta ba, irin good anxiety ke ɗawainiya da ita, kawai burinta bai wuce ya dawo masu da labari mai daɗin jiba.
A2Z ya kasance political godfather, kuma idan ya sama siyasarka albarka shikenan ka nare.
Arc Yusuf Jere yana taɓa siyasa jefi jefi, bawai ya taɓa fitowa takaran zaɓe bane. Kawai yana mara ma wanda suka fito ne baya sannan kuma cikin haka har aka bashi riƙon kwaryan Chairman na Kaduna North Local Government.
Lubna da sauri ta ƙarasa inda yake tana murmushi, dama kallon Zeeworld takeyi. Bata bari ya zauna ba ta samo jero masa magana.
"Well!!! meyace?" ta faɗa cikin zumuɗi
Murmushi yayi bai amsata ba tukun, saida ya zauna sannan ya kalleta. "cewa yayi wai yana son na zama deputy dinsa idan yaci primary election"
Daka tsalle tayi cikin murna ta soma tiƙa rawa, a shekara talatin da shida rawa ba abin kunya bane wajenta kuma zata iyayi ko gaban waye ba Yusuf kawai ba. Ita bawai za'a ce batada kunya ba amma abubuwa da dama bat shakkan yinsa, " Wow naji dadi sosai wallahi, ina fatan ka amsa masa koh" tace
"Nace masa zanyi shawara" ya amsa cikin yanayin da ko Lubna ta kasa fassarawa
"Shawara name kuma? Deputy Governor ai abin sone, wannan abin shine burin kowa. Gaskiya da safe zaka kirashi ka ce masa ka amince kafin ya bama wani post din" ta jaddada masa kafin ya jawo masu salalan tsiya
"Toh amma siyasa ba abu bane mai sauki, akwai challenges da yawa..." ya faɗa cikin damuwa. Shi dama Yusif baya san duk wani abun takura da zai sakashi ciwon kai
"Nifa ban yarda ba, dole ka amince tunda dai sun yaba da hankalinka. Haba Yusuf duk abinda nayi maka a baya bazaka faranta min da wannan ba(Haka take masa gori kusan kullum) Jibeni fah, na aureka sanda bakada ko sisi kuma na haifan maka yara har guda hudu" ta karasa maganar tana kukan munafuncin data saba idan tana neman biyan buƙata. Kuma tasan cewa baya ƙaunar kuka.
Tabbas Lubna ta masa halarci a baya, ta kasance mace ajin farko ce na bugun billboard. Amma ta aureshi bashida ko sisi ta watsar da ma neman aurenta masu ƙunban susa. Saidai kuma politics is a dirty game wanda baya tunanin zai iya.
Zuwa tayi kujerar dayake zaune ta zauna itama, rike masa hannu tayi tana murzawa a hankali cikin kulawa saita cigaba da kuka, "Dan Allah ka amince, koba komai zamu taimake yan uwa da abokan arziki, kaga wannan yiwa kaine tunda ladar mu yana wajen Allah.
Da lallami da daɗin bakin ta samu harya yarda, murna fal ranta zata shigo gari ta kuma shiga sahun manyan matan kaduna, yanzu idan Allah ya taimaka masu zata zama the number 2 woman a kaduna state.
***
wajen 3:30am A2Z ya koma gida, siɗaɗawa yayi ya koma ɓangaren sa babu wanda yasan fitarsa ko shigansa sai Maigadi.
Baiyi barci ba saida yayi wanka ya saka jallabiya yabi sasa na yaransa da matansa yaga duk suna kwance, matansa guda huɗu da yara ashirin da tara.
Aurensa kam yakai goma sha uku koma fiye da haka, shi bai taɓa zama ba tareda ya cika gidansa sun kai mata huɗu ba. Kuma shi duk meya haɗaku baya zuwa biko.
Idan rawan kanki yakai ki kika tafi yaji gidanku abu kuma ya wuce sati guda zai aiko maki da takardar saki, kuma cikin ƙanƙanin lokaci za'a maye gurbinki cikin giɗan.
Duka manyan yaransa iyayensu basa gidan, Hajia Zainab wanda ake cema Ammi ne take zaune dashi shekara ashirin da daya. Itace ta riƙe masa yaransa kuma tayi masu riƙon amana, tunda aka aureta bata taɓa fita da sunar yaji ba.
An kawo mata kishiyoyi amma ko ajikinta, wasu har suna haihuwa biyu kafin su tafi, kuma akwai wanda basu haihu ba. Ita kam Hajja Zainab tanada yara huɗu dashi, akwai Hajara, Aminu Jnr, Anisa, Adamu.
Rainon yaran baya damunta tunda akwai ɗakuna birjik kuma akwai masu aiki wanda suke kama komai, mostly nata bai wuce social interaction dasu ba tareda motherly love.
Bawai za'a ce batada san abin duniya bane, zagine ma ace mutum baya san kudi, ita dai tasan yanda take kashe kwaɗayinta. Kuma bakin ciki baya cikin ɗabi'unta.
Saidai baza'a rasata da nata halin ba tunda ɗan adam tara yake baikai goma ba.
Sai kuma matarsa ta biyu mai suna Hajia Hannatu, yanzu aurenta shekara bakwai kenan tanada yara biyu, Sakina da Suwaiba. Na uku Anty Khadija tanada yaro daya mai suna Jamil. Amaryan batada yaro amma tanada tsohon ciki
Shekarun yaransa daga shekara 35 zuwa wata biyu ne wanda Zainab amarya karshe data fita ta haifa.
Yanada jikoki guda tara daga wajen manyan yaransa, duk sunyi aure yanzu saura Suhail wanda kannensa ke ce masa "Yaya Ess" abokai kuma Ess gatsal suke faɗi. shekaran sa 29, itakam Hajia Zainab bata aurar da kowa ba, Hajara ko Hajjo kamar yanda aka fi kira ce take final year a Kasu.
Bayan A2Z ya gama zaga gidansa saiya koma ɓangaren sa, ba'a wani daɗeba aka kira sallah, anan ya tashi ya wuce Masjid saboda baya barin jam'i ya wuceshi.... Wannan kenan!
6am...
Yau A2Z ya wuce strolling sai dube dube yakeyi, yana tafe yana dangara sandarsa na alfarma wanda itace abin riƙewan sa idan yana tafiya shi kaɗai. Kokari yake ya gane proximity ɗin dake tsakanin sa da Nimra amma babu wani alamar ta.
Sai kuma zuciyarsa ya soma harbawa, kardai ace aljanna ce wanda ta badda kamanta tanama gefensa tana sinsina shi. Da sauri ya kawar da tunanin tareda ƙara kafa ya koma gida.
Ita kam tunda tayi proving point ɗinta bata bisa ba a ranar, wajen bakwai tana sanye da leggings da kuma tank top. Hannunta sanye yake da gloves ɗin boxing sannan tana tsaye gaban heavy bag na boxing a Varenda ɗinta.
Nan ta soma kicking ɗinsa da kafa tana kuma naushi da hannu, tanayi tana hutuwa gashi sai zufa takeyi. A duniya tanasan yin boxing saboda yana soothing mata stress. Sannan daga ɗaki wakar Imagine Dragons na 'Believer' ta saka a repeat yana tashi.
Idan tanayi tana samun natsuwa kuma tana tunani da kyau. Ko ba'a faɗa mata ba tasan cewa A2Z tarko ya ɗana mata, saidai ɗin itama she is not naive or stupid. Dole zata sake ɗaura danmara akan cinma burin ta.
Tanata tunani tana kawo scenario kala kala wanda A2Z zai iya amfani dashi ya cutar da ita, tasan cewa she is playing a dangerous game. Amma kuma ita ai daban ce, 'Normal' ba abu bane data sani. Duk rayuwanta a wahalce tayi shi.
Batada tsoro ko kaɗan kuma abubuwa basa firgitata da sauri, idan ta saka rai akan abu bata bari saita cinma burinta. Naci gareta kamar quda saidai a kasheta yasama aikinta na yar sanda yaje daidai da personality ɗinta.
Bayan minti kusan talatin tana abu ɗaya saita wuce bayi domin tayi wanka, gidanta dan madaici ne. One room apartment ne da falo sai bayi da kitchen guda daya daya.
Haya ta kama na wasu attijirai, su bawai sun bata gidan bane dansuna san kuɗin. Kawai saboda ita mace ce kuma ya kamata tana zaune karkashin wani koma yayane.
Koda yake garin waka sani waya sanka, hanya ma akayi mata kafin ta samu wajen. Bawai ma bazata iya zama ita kaɗai bane, kawai tayi disguise ne kafin ta jawo ma kanta surutai cikin gari.
Boys quarters dinsu suka ranta mata a inda take biya 120 thousand duk shekara, sannan kuma hanyar shiga daban saidai akwai ƙafamin gate wanda ya zamanta mahaɗa da gidan attajiran.
Cikin mintuna 20 ta gama wanka harta soma saka kaya, blue platted skirt ta saka mai igiyoyi wanda ake ma laƙabi da monkey jacket, saita saka fitted long sleeve baki da kuma bakun kallabi.
Fuska tabisa da powder sai jan baki nude color kamar bata saka komai ba, sannan saita saka kwallin kajol a idonta. Dama ita iyakacin kwalliyar ta kenan, ta ƙure a daka kenan ma fuskanta, saidai kuma idan character dinta ya bukaci daban.
Kyanta bana bugun billboard bane, saidai tanada haske. Amma kuma ba abin a zuzuta bane, ta gode ma Allah za'a ce tunda bazaka kusheta ba. Kuma batada gashi kwata kwata, fuskanta yana yana yin masu gashi amma idan ta buɗe maka zaka sha mamaki... Wannan kenan!
'Kululu' cikinta ya soma rawar shakiti bobo, yunwa ya soma addabatan amma kuma gas ɗinta ya kare. Da kuma saura kayan abincinta yayi ƙasa.
Haka ta dauki gas ɗin da niyar zuwa siyan wani anjima, maganar abinci kuwa Rich Bite taje domin ta saka wani abu a bakin salatin ta, kafin tayi mutuwar banza tunda bata shiri da yunwa at all.
Laptop ɗinta na Lenovo da charger ɗinsa ta saka a laptop bag ɗinta, saita dauki kuma handbag ɗinta tareda mukullin motarta. Nan ta fita tareda rufe gidan baki daya.
A yaune zata soma aiki tareda dan takaran gwamna na jam'iyan NDPP watau Nigerian Democratic People's Party. Ba wani bane illa Alhaji Aminu Zailani aka A2Z, wani washar takejj a ranta because she is optimistic about the future.
***
Shikam Cizo bayan yaje gida saiya soma kai mari yakai gwaro, ya kasa zama a waje ɗaya duk abin duniya yayi masa cinkoso, wucewa drawer ɗinsa yayi, key yayi amfani dashi ya bude saiya fito da bindigar sa. Kallonta yayi yana saka bullets. Yayi kwana biyu baiyi amfani da itaba kusan wata shida kenan.
Yana shafawa yana tunani idansa kuma ya canza kala, nan ya fitoda hodar Iblis yar ƙarama an naɗe a farin takarda. Zubawa yayi akan babban yatsansa ta baya saiya shaka da karfin gaske.
Nan kwakwalwarsa ya amsa mashi yaji yayi wani sama shedan kuma ya soma aikinsa gadan gadan, haɗuwar farko da zai sakeyi da Nimra zai rakata lahira. Wannan shine alkawarin daya ɗaukar ma kansa.
A2Z kam yau ya soke ziyarar dayakeyi gidan marayu, dama badan Allah yake zuwa saboda Campaign ne Zaɓe ya kusa, duk wani eye service yanzu ya kware akai. Shifa saiya shiga gidan gwamna na Sir Kashim Ibrahim House dake Kawo bara idan Allah ya Kaimu.
Ya riga yayi planning political life ɗinsa bazai bari Nimra tazo ta kawo masa cikas ba, yau ɗinnan zata mutu bazata wuce wannan rana na juma'a ba a duniya. Office ɗin wani amininsa daya bar gari zasuje anjima.
A Nagwamaste building last floor ne, baima bita kan Sameer ba. Shikam Sameer yanada shaƙiƙi cikin sauran boys ɗin Alhaji. Anan yaji labari cewa za'a meeting ba tareda shiba.
Zufa ya keto masa har tashi ta soma samunsa ana abu ba tareda shiba, Abokin A2Z da za'a ofis dinsa mai bala'in kuɗi ne kuma ya bada gudun mawa sosai na campaign.
Ran Sameer yayi mummunan ɓaci kuwa wai tun kafin ya zama gwamna yanaso ya watsar dashi. Siɗaɗa yayi yaje building ɗin.
Shikam Alhaji ya bada sallahu duk wanda ya shiga ciki a ingiza shi ta window ya faɗo ƙasa daga 10 storey building.
Sameer cizo ya hange Nimra tana tafiya cikin walwala ta nufa wajen. Nan ya rinka sauri saboda ya rigata shiga ciki. Idan yayi sa'an haka saiya ci ubanta da kyau idan sun haɗu, bazata tarwatsa masa abinda ya gina shekara da shekaru ba... Wannan kenan!!
Fully DIMPLELATED
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top