2

Abu Hurairah (May Allah be pleased with him) reported: The Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "When a man dies, his deeds come to an end except for three things: Sadaqah Jariyah (ceaseless charity); a knowledge which is beneficial, or a virtuous decendant who prays for him (for the deceased)."[Muslim].

******

"Alhaji kana tunanin Yusuf zai kawo ƙuri'a kuwa? Gaskiya inaso ka duba other candidates kafin ayi tafiya nan dashi" Sameer Cizo ya faɗa cikin damuwa. Kafama ma A2Z ido yayi yana jiran yaji irin amsar da zai bashi. Ya cika yayi fam kawai dannewa yakeyi saboda Yusuf bai wani goge ba a siyasa.

"Kwarai kuwa, Yusuf shine perfect candidate sabida yanada gaskiya da riƙon amana wanda ba kasafai ake samun irinsu ba" A2Z yace yana karkaɗa kafa sannan ya kurba Maltina. Kuma ya ɗaga ma Cizo gira irin ya yarda dashi

"Amma... Toh shikenan" Sameer yaso magana saiya fasa. Yabar ma cikinsa komai ya fawwala ma Allah. Cizo shine Chief of Staff ko ace personal assistant na Alhaji Aminu. Yasan shi sosai kuma yanzu sunyi shekara 10 tare.

Sun haɗu tun lokacin Alhaji yana aiki a Ministry of Finance a inda ya zama Director a Abuja kafin A2Z yayi retire yanzu yanada kamfanin sa na A2Z Investment dake Ali Akilu road.

Suna cikin magana ne sai wata ta dumfaro su, sanye take cikin jallabiya mai hula kuma ta saka a saman kanta, sai kuma School bag din Hp goye a bayanta. Kafanta kuma takalmi ne na kwabɗeɗan boots irin mai nauyin nan. Kuma ya wuce ƙaurinta sosai.

Dukda dare ne bai hanata dampara tabarau tabkeke ba akan idonta, sannu a hankali taje wajen.

Zuwa tayi ta zauna akan couch 1 seater inda suke, kafa ta daura akan daya tana karkaɗawa. Saita dauki Maltina ta bude, yanda tayi abun cikin gareje saida yayi kumfa ya soma zuba.

"Shit" ta faɗa sannan ta sauke kafarta kasa, duk abinda takeyi su Cizo da A2Z suna kallonta irin kallon Ikon Allah saboda har yanzu fuska yana rufe da hula.

A hankali ta zame hular saita kallesu tana murmushi, anan ne Cizo yayi ajiyar zuciya tareda kallon A2Z, sai yace "Itace wannan"

Sannan ya kalleta yace, "Ke meye haka zaki shigo mana like you own the place"

Murmushin ƙeta tayi sannan tace, "Looks like it"

Kallonta A2Z yayi kafin yace, "Bangane ba? Kana nufin wannan yar figikan itace takeso ta tada mana zaune tsaye?" yace yana watsa mata harara, tunda ya raina shekarunta

"wayo na yafi karfin shekaruna" tace masa tana murmushi, saita mayar da hankalinta kan TV dake manne a bango yana aiki amma babu murya. Remote dake gefen wajen ta ɗauko ta ƙara murya kaɗan tana kallon Network News na NTA tunda har tara yayi.

"Sameer zan samu matsala dakai idan kana kawo min confused yara, har tanada guts da zan haɗa mata meeting cikin dare bazata iya ganina ba ido yana ganin ido koh?" Yace ma Cizo, shikam ɓarin leɓe ya somayi saboda har A2Z ya harzuka.

"Nifa bance dole kayi business dani ba, kana ganina haka koh? I'm a freelance writer, bana ƙarkashin kowa. Abinda naga dama nake yi so the highest bidder zan bashi labarin" tace ma A2Z cikin yanayin ko in kula

Miƙewa tsaye tayi saita fito da wasu envelopes mai ƙunshe da hotuna ta watsar kan table, anan idon kowa yabi hoton. Nan fuskan A2Z yayi la'asar. Kusan ace duka rayuwarsa ne takeda hoton, kuma abin zai kawo masa barazana wajen cin zaɓe nan gaba.

"Kasani cewa Alhaji ina binka duk inda kake zuwa For the past 3 months, nasan cewa duk safe kana fita strolling kai kaɗai wajen karfe shida kuma kullum kana gaisawa da wani almajiri. Saidai kuma abin mamaki shi ne bayan kun gaisa zai saka hannunsa cikin aljihu ba cikin robon baransa ba kamar yadda ya saba"

"Tun ban lura ba har nazo na gane ba gaisawa kukeyi ba, illa kana miƙa masa wani abune wanda yake adanawa"

"Abin mamaki wai ace da safe ya fita bara? ba kai kaɗai ba har wasu manya manyan motoci suma suna tsayawa amma ba'a ganin fuskansu" Daga nan taja dogon numfashi, sukam su A2Z baki ya mutu. Sannan ta cigaba da magana

"Almajirin ne wanda baifi shekara tara ba yake zuwa ta window ɗin motan ya karba shima ya saka a aljihunsa"

"Nasan cewa kuma kana duba gidajen marayu duk karfe goma na safe kafin ka cigaba da sauran aikin ka, sannan kuma kana wani secret Phone call daga karfe sha biyu na rana zuwa karfe ɗaya"

"sannan nasan cewa kana zuwa...."

"Ke karamar mara kunya, naji kina bina sai me?" Yace ransa duk a ɓace tareda zare mata ido, kana kuma ganin jijiyan fuskansa duk ya tashi

Bazawaran dariya tayi saita soma magana, "Ai ban kai wajen ba, nasan favorite abincin ka, color dinka, matarka, yaronka, komai daka keyi ina laɓe."

Wasu hotuna ta soma barbazawa kan tabur, tana duƙe tana kallon wasu daga ciki saita soma nunawa.

" Na kasa gane dangantar ka da Wannan almajiri, sai kuma duk dare bayan iyalanka sun kwanta kana biyawa wani gida....... " anan ta karkare tana kallonsu.

Shikam cizo dayake zamada A2Z baima san da wannan abu ba, nan ya sake baki hangangan yana jimami. A2Z kuma zufa ke keto masa.

"Ina ruwanki?" A2Z yace.

"Chill babu fah, karka sha na damu dakai ne ko wani abu. Kamar yanda na faɗa da farko. Idan nayi rubutu ina sayar ma highest bidder ne."

Tashi tsaye tayi tana tattara hotunan ta, cikin kota kula ta ci gaba da magana," Title din takardan shine 'Expose on Arewa politicians' so bakai kaɗai ba, harsu opponents ɗinka na sauran party inada abubuwa akansu"

"Meyasa kika zo wajena dashi, yazan tabbatar da cewa baki kai masu wannan zancen ba kafin kizo wajena" ya tambaya cikin tuhuma yana kuma so ya karance yanayinta.

"Saboda hankalina yafi kwanciya dakai, i have more trust in you akan kayi ruling garin nan. Saidai kuma nima inada abinda nake buƙata daga wajenka" tace da guntun dariya a leɓanta

Sannan kuma ta soma magana gira a ɗage, "You are not stupid kayi tunanin cewa haka kurum zan kawo maka wannan abun ba tareda nawa ribar ba"

"Name kenan?" yace saiya watsa mata dara daran idonsa masu kamada kwai

"inaso na shiga, ina so nima na zama wani abu a garin Kaduna, ina so nasan me kakeyi" tace masa ido kur cikin nasa. Bai cire nasa ba ya soma magana, "Cizo bamu waje"

Nan cizo ya tashi ya tafi, sai A2Z yaci kwalarta, shaka yakai mata kamar zai zare mata rai daga jikinta. "Ke dan ubanki kinsan dawa kike magana kuwa?" ya faɗa da karfin gaske

"Exactly shine tambayar da nake ma kaina, waye asalin A2Z? Inaso nasan deepest secret ɗinka, bawai perfect gentleman da kowa keso a gari ba, Alhaji Aminu Zailani nakeso na sani kuma ina kan batu na, inaso na shiga koma me kakayi, inaso nasan sirrin dayasa duka yan Kaduna suke tsoron ka"

"Babu abinda ya shafe ki, this is no child's play. Kuma idan kikayi wasa zansa a salwantar dake da duk......"
Bai gama ba ta katse shi tareda fisge kanta daga riƙonsa, itama zare masa ido tayi.

"calm down, nasan me zaka ce, zaka salwantar da duk wanda nakeso koh? Well jokes on you sabida ni marainiya ce, a gidan raino na tashi tun ina wata shida aka tsince ni a bola. Banida wanda nake so wanda zaka firgitani dashi" Tace masa saita zauna da kyau sosai a couch

"My heart is very cold, na fuskanta abubuwa da dama tunda na tashi, banida wani happy memory. Zan iya cewa abinda na fuskanta bazaka iya rayuwa a rabinsa ba, Mace mai kamar maza kake gani saboda ni daban ce a sauran mata" ta karasa maganar da smug face

Kallonta yayi yana mamaki, yarinyar dududu bata wuce 25yrs a duniya ba, amma sai tsaurin rai da zafin nama kamar ba mace ba, tabbas batada hankali. Batasan me take faɗi ba. Bakin rijiya ba wajen wasan yara ba. Saidai kuma yasan matsalarta.

Ba mamaki kudi takeso, waya ya ɗauko ya kira Sameer saiya ƙarasa wajen da suke. Nan yayi masa ƙurmusu cikin kunne saiya je inda A2Z ya ajiye briefcase ɗinsa.

Kuɗaɗe ne a shirye daga yan 50 zuwa 1000 notes, nan ya ciro yan 100 guda biyar ya watsa mata.

Kallon kuɗin tayi sekeke bata bari ta taɓa ba, sannan ta kalle A2Z, "Karfa ka raina ni Mallam, kana tunanin kuɗinka nakeso. Nafi karfin chicken change ɗinka. Nayi rayuwa babu su kuma rashin su bazai hanani komai ba"

"yanzu me kikeso wajena? Ana cikin zaune zaki tada zaune tsaye. Takaran gwanna fah na fito, wutsiyan raƙumi yayi nesa da ƙasa wallahi"

"Look nasan baka yarda dani ba, nima haka bazan yarda da mutum ya fito min gatsal haka ba. Kawai ka sani cewa nima ina san Freedom ne. Inaso na zama wani abu tunda ba tallan kanwa nazo duniya ba. Kuma this world is a cruel world, dole saika samun wani gagarumin goyon baya kafin ka samu nasara"

"zamuyi disguise ace ina rubuta Memoir akan kane, yasa zan rinka binka ko'ina saboda nayi studying ɗinka, zai zama sirrin mu babu wanda zaiji asalin zancen"

Shiru yayi na wajen mintuna 5, daga ita har Cizo suna sauraren me yakeso yayi. Ajiyar zuciya yayi sai yace, "Okay fine, zan sakaki a trial basis. Dole ayi monitoring ɗinki asan komai naki. Kuma idan kika ha'ince ni nan take zan kashe banza"

Murmushi tayi tareda daka tsalle, Cizo shima yayi mamaki saboda A2Z bamai saurin yarda bane.

Shikam A2Z tarko ya ɗana mata, bata isa ta yaudare shiba. Ya rigata soma bariki saboda shi tsohon hannu ne. Yana tunanin hanyar da zaibi ya kasheta ne, tabbas bazata wuce 24hrs a duniya ba.

"Ya sunar ki?"

"A Girl has no name" tace cikin izgili

"ke bana wasa dake? Kokuma ki fice min anan wajen"

"Lets see.... Zaka iya kirana da NIMRA"

"Nimra! Nimra!!" Cizo ya maimaita a ransa, ya daɗe da Alhaji amma bai taɓa aminta da shiba. Tun kafin aje ko'ina na cinma burinsa har wata kuchaka zata maye gurbinsa.

Wannan damar shiya kamata a bashi, shine ya kamata ya shiga koma me A2Z keyi tunda shine shaƙiƙinsa amma an bata a cikin rana ɗaya, lallai bazai taɓa yarda ba tunda shima ba tallan kanwa yazo yi duniya ba.

Tarko shima zai ɗana mata ta tafi ta basu waje, haka kurum monkey work baboon no go come chop am.

Wurin yayi tsit sai karar TV, anata kallon suna yaƙe ma juna sirrin ciki sai hanji.

Anan tayi masu sallama ta kwashe hotunan ta saita ƙara wuta, wani murna mara misaltuwa taji. Bata san dalili ba amma wata sa'in ta lura tafiya slow akan aikin su.

Abinda 3 months ago aka basu yanzu ne ma ta soma samun aikin, wai a hakama ba shi bane target ɗinta. Target ɗinta bashida suna balle hoto.

Kawai ansan dashi a cikin duniya ne, bashida ma jinsi walau mace ne ko namiji.... Wannan kenan!!!










Please don't forget to comment and tell me your opinions from these 2 chapters.








DIMPLΣS


mention a user

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top