17

Fargaba ya mamaye Ummu hani, tana fara wasi wa si akan abinda zuciyar ta ke raya mata. Kada dai X da Uncle Yusuf. Da sauri ta kawar ta tunanin, tasan ko ana ha maza ha mata bazai ci amanar Anty Lubna ba haka.

   Shi kuma daga ɗaki yace ma X ta tashi ta koma dakinta, kafin a gansu. Bata soba ta saka night robe din Lubna tana gunguni. Shine ya soma fita, ganin Ummu yayi a falo, fuska a murtuke saiya soma magana,

"Zo ki siyo jakan ruwa a wancan shagon"

Taso tace mashi akwai ruwa wajen leda hudu amma taga yau yana cikin ra'ayi. Mikewa tayi ta tafi. Bayan nan sai X ta fito tana karkade karkade ta wuce. Bandaki ta shiga tayi wanka, tana fitowa saiga Ummu hani.

"Xobaederh tun dazu nake neman ki, ina kika je ?"

"Gidan maman walida, makwabtar su Anty... In fact inama ruwan ki" saita watsa mata harara.

Sum sum Umma tayi saita fice, dakin Lubna taje tunda taga Yusuf ya koma dakinsa. Gyara gadon tayi tareda canza bedsheets saita zauna.

Kwanaki sunata tafiya har Ainau ta samu sauki, yanzu haka ana shirin sallamar tane. Ita kuma ta kafe cewa bazata koma gidansu ba, anyi anyi amma ta nace. Mommy ne ta sameta ita kadai take mata tambaya.

  Anan tace mata ita batajin dadin zama da Xobaederh, ita kuma bazata iya sake hada inuwa daya da ita ba. Bata dai gaya mata zancen su da babanta ba, ta lura ba abinda hankali zai dauka bane. Fatan ta a gansu da ido cikin ido.

An gama hada mata kayanta zasu tafi, Mommy ne tace ta shiga motarta. Sannan ta umurta Yusuf da Lubna suje gida gasu nan zuwa. Sanda aka yanka kwanar gidan Lubna Ainau ta soma hawaye. Bakin ciki mara misaltuwa take ji.

Bata ce komai ba suka shiga, koda suka shiga sai ga X da irin mugayen shigan ta. Rabin kirjinta a waje ga kayan ya bala'in matseta. Salati Mommy ta somayi tana kallon kowa data lura X ba shirin saka mayafi takeyi ba.

"Lubna kika yarda? Wannan wani irin sakarci ne kamar baki gani?"

Lubna sinna kai tayi, bata sake cewa ba. Ita ma taga wautan ta a wajen. Shi kuma Yusuf saiya dauke kai.

"Keh Xobaederh maza kije ki canza kayan nan, kona saɓa maki wallahi"

Rai baiso ba X ta tafi daki tana tura baki, boyfriend jacket tasa ta dawo. Dukda haka kana ganin kirjin. Mommy tafasa kawai takeyi ta rasa meke mata dadi. Dole Ainau taji bataso ta zauna a gidan ubanta. Amma yau komai ya faru ya kare.

Bayan an zauna an sha hira kadan, ita Umma ta gama haɗa kayanta harta fito dashi. Sai Mommy ta kalle X tace mata saura ita.

"Mommy ban gane ba? Ina ce ance na dawo nan?"

"Dole ki dawo tunda gidan ubanki ne"

"Amma Daddy yace na zauna"

"Kuma nace ki shirya ko kici na jaki"

Hankalin X yayi mugun tashi, amma ko a haka bai kai na Yusuf ba. Shine ya soma magana cikin ko in kula.

"Mommy ban tare numfashin kiba, amma ai Xobaederh bata takura ma kowa... Ko Lubna?" saiya kalle Lubna ta mara mashi baya. Kauda kai tayi ta share shi.

"Still banga laifin datayi ba da zata tafi... Kawai nawa ra'ayin kenan"

Mommy bata tanka shiba, kawai a ranta tace ai dole yaso ta zauna koba komai ana bashi free show yayita kallo.

"Xobaederh kije ki hado kayanki, wallahi zan dake ki kinji na rantse"

X bata mike ba illa kuka data fashe dashi, "Anty Dan Allah ki bata hakuri"

"Kawai tunda Mommy tayi magana ki bita, Kinga yanzu ma Ainau tana jinya... Zata so ta huta sosai a dakin zaman falo bai kamace taba"

"Anty wallahi zan rinka kwanan falo"

Mommy ne da kanta taje dakin, taga akwatunan tuni ta soma zubawa, kiran Ainau tayi wanda dakyar take takawa amma kuma sai jindadi takeyi. Anan ta rinka nuna mata kayan X suna sawa a jaka. Bata gama kwasan duka ba tace idan Ainau taji sauki a hankali ta rinka sawa a jaka sai a bama Driver yakai masu.

Janyo jakar tayi tazo falo, anan Hankalin X ya tashi. Rugawa tayi ta duka gaban mommy. Anan mommy tayi ajiyar zuciya.

"Wai ubanki kika ajiye ne da zaki wani damu? Koko dan ubanki Yusuf kike so ne?"

A razane X ta kalleta, shima Yusuf haka. Lubna kuma dariyan ƙeta tayi.

"Haba dai taso Yusuf! Kamar 'ya ta ce fa.... Wutsiyar rakumi yayi nesa da ƙasa mana... Kambu... Kila dai wani saurayin tayi a unguwa" tace tana dariya.

"Umma hani kai min kayanta cikin boot"

Da sauri tayi tana jin dadi, ita ma batasan zamanta gidan. Bayan nan ta dawo ta kwashe kayanta.

"Okay wuce muje" saita nuna mata hanyar kofa. Taso taki ta tursasa Yusuf amma kuma idan aka gane za'a raba su baki daya. Ita bawai samun Yusuf din bane kawai. A'a tana so ta rinka nuna ma Lubna bata isa ba cikin gidanta. Tana mata fitsara da diban albarka. Ta hanata jin dadin zaman gidan shine yafi mata dadi.

Yanzu kawai zasu rinka haduwa da Yusuf a hotel, amma kuma da tsada. Kudin da zasuyi amfani dashi dama kudin aka bata tana kashewa.

***
   A hankali Nimra take tuna abubuwan da suka faru da ita. Sannan shima Abu Dhar yana taimaka mata. Duk abinda sukeyi haka Suhail bai lura ba. Tun daga ranar kuma bata sake masa tambaya ba, shima bai sake nuna wani abin da za'a tambaya ba.

  Abu Dhar yaje gidansu Mommy da Nimra domin yayi masu bayani, anan yace an sace ta saboda yanayin aikin ta, sannan kuma sai tayi losing memory dinta. Itama ta tuna su kuma tasan sunada mutunci. Basu hakuri tayi suma sukayi mata jimami.

Komawa gidanta zatayi amma sai anyi wasu gyare gyare, Suhail baiso tafiyar ba shi kawai a daura masu aure ta tare. Tace masa yayi hakuri tukun. Taje wajen A2Z inda hankalin sa ya kwanta, shima ganin shirun ya daga masa hankali.

Wannan karan dataje Gamji Park bata saka kayan almajirai ba, da mutuncin ta taje tanata hutuna kamar tourist. Amma kuma tana yi tana daukar mutane dake wajen ne hoto. Harta gama zata tafi saita ga Suhail. Mamaki tayi yace wai yanada wani customer mai restaurants anan suke haduwa.

Bata kawo komai ba ranta shiya rage mata hanya, amma saida suka biya 9-11 suka shiya shawarma tukun sai suka wuce gida. Isar su keda wuya sai aka kira magrib. Bai shiga ba illa wucewa direct Masjid.

Kamar ana kiranta tace bari ta duba dakinsa na makulli, tunda gobe zata tafi tabar gidan. Dayake ta iya bude kowane key da cokali koda karfe. Haka tasa cokali mai yatsu a ramin tayita kici kici harya bude.

Ganin dakin wayam banda wani files haka a ajiye. Harta tafi saita dawo. Budewa tayi sai taga pictures din mutane kala kala. Tana kallo bata ganewa saiga hoton Blackberry. Sakin pictures din tayi da sauri ta soma matsawa baya.

"Nooo.... It can't be" tace tana girgiza kanta. Kardai ace Suhail shine agent din Gamji na cikin gari wanda ake da leads akansa. Maybe shi yasa take yawan ganinsa a Gamji Park. Idan yazo yaga mutane masu armashi yasa ayi kidnapping dinsu.

Dukawa tayi tana sake kallon abin da kyau, duk hotunan manyan mutane ne attajirai ko yaransu. Gana ma'aikata da suke aiki ma Gamji. Batadai ga hoton Gamji ba tunda dama ance babu wanda ya taba ganin sa.

Suhail ne ya shigo yana kallonta, haki ya soma kamar mayunwacin zaki. Da sauri ta mike tsaye zatayi magana. Amma naushi ya ɓurma mata a bakinta. Anan ta baje summanmiya.

***

"Oga kana ganin idan muka yi trading dinta ma freedom dinmu Abu Dhar zai yarda" daya daga cikin masu ma Gamji aiki ya fada.

"Me zai hana mana, yana bala'in ji da ita" Gamji yace.

Ita kuma Nimra tana wani daki an kulle ta da duck tape, ga kuma an rufe mata ido bata ganin komai. Kokarin tantance komai takeyi, sai ta tuna last tana dakin Suhail inda taga hoton Blackberry.

Yanzu haka tana ina ne? Gidan Suhail din kokuma wajen Gamji ita ma an tafi da ita? Wannan kenan!






Afuwan ba yawa.



#Nimra
#Ainakatiti ✨

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top