16
***
"Ashe ta farka" Lubna tace tareda karasawa wajen Ainau. Ita ma Mommy abinda tayi kenan. Xobaederh na daga gefe tana gunguni ranta yana bala'in ɓaci. Taji haushin yadda aka cin mata mutunci gaban Lubna.
A hankali Ainau ta bude ido ta kalle Mommy, sai ta soma magana "please ki tafi dani gidan ki dan Allah idan za'a sallame ni"
Lubna ne ta chapke da sauri.
"Karki damu Ainau indai akan rashin zamana a gida ne ya kusan kaiwa karshe, kiyi hakuri zaki rinka ganina sosai harki warke"
Girgiza kai tayi alamar bata yarda ba, lallashi ake mata amma ta kafe. Sai Doctor ya shiga a lokacin, anan ya sake dubata inda yace zata kai wajen sati daya ko fiye, da farko Yusuf yana murna saboda zai samu lokaci da Xobaederh, sai kuma ya tuna cewa zata bar gidan su, bakin ciki ya soma dawainiya dashi.
Duk wani aikin wajen Mommy take tada Xobaederh tayi, ita ce zuba masu abinci, zuwa ta taro yan barka. Siyo ruwa da sauran su. Duk yadda bataso ta moru rannan an gurje ta. Yusuf yana bakin asibiti ya basu waje, kadan kadan yake zuwa dakin. Ainau kuma ras bakin ta bai mutu ba.
Su Abubakar basu san dawan da ake ciki, Ummu hani ta kula dasu yadda ya dace. Ta soya masu plantain da kwai, saita yi masu wanka. Sannan tayi shara, wanke wanke harda scholar a washing machine. Gidan fes ya canza fasali.
Da rana kuma tayi tuwan shinkafa da miyan agushi, sannan ta bama driver ya kai masu asibiti. Lubna tayi kwadayin zama da ita sosai amma kuma tasan ita take taya mommy hidima data dauketa.
Daddyn su Xobaederh ne yazo bayan la'asar, bayan ya gama gaisuwa sai Xobaederh ta soma mashi korafi wai Mommy tace ta tafi. Anan ta haɗa mashi karya da gaskiya sannan Malali yafi kusa da KASU kuma sunada yan ajinsu dayawa anan, wata sa in ana haɗuwa ayi tutorial.
Mommy dai bata yarda ba, tace idan dai Xobaederh zata koma saita fito da miji nanda sati uku. Yana cika babu kowa zata dawo gida. Bazata je ta takura ma masu aure ba bayan basuda wani ɗakuna dayawa.
Da sauri Xobaederh tace ta yarda, tasan cewa kafin nan zasu soma dabara da Yusuf. Idan ma zai tayata samun wanda zata aura ne sai bayan nan suyita haduwa abin su koma yayane shi yasani. Sai kuma Mustapha ya fado mata arai, tunani ta soma kota aure shi kawai ta huta da takura.
Da driver ya kai abincin dare wanda Ummu hani tayi, sai Xobaederh ta bishi domin ta gaji. Mommy bata hanata ba, ita dai Lubna shiru tayi. Ta rasa dalilin dayasa Xobaederh bata san barin gidan. Da ance ta bari hankalinta ya rinka tashi kenan, kuma da farko bataso zuwa ba. Kokuma yanzu Mommy batada dadin zama ne tsufa ya soma kamata.
Suna isa gida Xobaederh taga Ummu da yaran duka ana zaune a kasa, biya masu karatun da akayi masu takeyi na islamiya, ko kallon su batayi ba ta wuce tayi wanka. Jira takeyi taga Ummu hani ta tafi amma shiru ga takwas ya gota, tasan Lubna a chan zata kwana amma Yusuf zai dawo anjima.
"Ke bazaki shirya ki tafi ba sai dare yayi maki" Tace mata
"Anan zan kwana" ta amsa a ladabce, kallon hadarin kaji X tayi mata tana huci.
"Ban gane ba? Kin dawo nan kenan?"
"Eh dazu na biya na dauko kayana har Anty ta dawo saina koma"
"Kutumar uba bazai yiwu ba, bazaa sha fate ranar sallah ba"
"Ke Xobaederh meye naki? Gidan nan naga da kyar aka barki kika dawo, sannan ni dakin Anty zan kwanan.. Meye matsalar ki dani?"
"Wallahi yanzu zan kalle ki da mari kika min rashin kunya, kinsan ni ba sa'ar ki bace"
Dama daukar Amra zatayi ta kai ɗaki domin ta fara gyangyadi, anan ta cigaba da abinda takeyi ta kyale X. Ummu hani bata samu matsala da Jamb ba, yanzu haka ta gama ABU Quantity Survey tana bautar ƙasa a ministry of works.
X taga fah da gaske a gidan zata zauna, kuma yanzu duk shirin abinda ta kulla bazai faru ba. Taso ta gwangwaje ne sosai. Bin Ummu tayi daki, "Dan ubanki ni zaki kyale ina maki magana?" saita janyo mata kallabi, har Ummu tayi zuciya saita kyale ta, kome take nema da ita bazata samu ba.
Da Xobaederh taga babu sarki sai Allah saita yi ma Yusuf text ya dawo maza maza. Duk daukan sa yasha su Amra ne, yana zuwa tana varenda tana kumfa.
"Da saninka aka ce Ummu zata tare gidan nan sai Anty ta dawo?"
"Abinda yasa kika kirani kenan?"
"Ka amsa ni mana?"
"Meyasa bakida hakuri ne? Wai ko tausayin matsalar da muke ciki bakya yi, kinsan cewa saboda ke Ainau take hannun Allah haka koh? Amma baki damu ba, kina ganin wani abu ya faru da ita Lubna bazata daure kiba"
Jikin x yayi la'asar amma ta dake, itama taga rashin kyautawan ta, "Ni dai gobe kace mata ta tafi" saita buga kafa ta wuce ciki.
Shima shiga yayi ya tafi nasa dakin, dama yaci dinner. Wanka ne daman baiyi ba, saiya shiga bayi yayi sannan ya fito ya kashe wuta tareda kulle kofa sai ya kwanta. A ranar bai nema X ba tunda yasan Ummu tana nan. Ita kuma X jiran take yace tazo amma taga shiru har 3 dare.
Tashi tayi cikin fushi taje dakin, yana barci yaji tana magana. Yaso ya basar amma ya fasa, "wai mena gama maki magana akan hakuri? Why aren't you smart? Kina ganin Ummu shine zaki shigan min daki... Ummu ba Ainau bane fah tsab zata tona. Ki bari mu samu wani hanyar mana"
Kallonsa tayi tana mamaki yadda ya soma mata gardama, ko dai asirin ya soma karyewa ne, koma menene yanzu zata gurin boka. Bataso ya rinka tunani idan ya jibance ta, abinda taga dama take so tayi. Marairaice wa tayi ta soma magana.
"Kayi hakuri my Yusuf, dama kudi nakeso ka bani ina da bukatar su"
"Nawa?"
"20k"
"Ki bari gobe zan baki"
Bata sake ce masa komai ba illa shafa mashi fuska saita tafi tana juya masa jiki, yadda takesan Malam na gangagre akwai arha kuma akwai aiki. Idan Yusuf yazo hannu zatayi bushasha lokacin.
***
Abu Dhar ya sake dawowa lokacin Suhail ya tafi gidan gona, anan ya kawo takardu sosai na Nimra. Tana kallo yanata fahimtar da ita, a hankali ta soma samun flash back na Bugun Abuja da yan mafia, A2Z dashi kansa Suhail din. Balle dama tana shan maganin regaining memories dinta.
Rannar sun wuni tare sunata aiki, Inna tsohuwa bayan ta gama aikace aikacen ta saita tafi saura su biyu. Shi Abu Dhar ya kasa natsuwa da dakin da Suhail ya garƙe da kwado. Kawai jikinsa bai bashi ba. Balle kuma ya tuna Suhail ya taba bacewa na shekara biyu, daya dawo kuma shine ya soma aikin kaji. Sam hankalin sa yaki kwantawa.
"Idan Suhail ya dawo kice masa kin soma tuna kanki, ina ne yaje sanda ya bace har na tsawon shekara biyu"
Nimra dakai ta amsa mashi, bata kawo komai ranta ba. Tadai san Suhail baya san magana akan past dinsa. Sannan kuma baya san alaka da yan gidansu. Tana ganin maybe yasan babansa dan mafia ne.
Wajen karfe uku Abu Dhar ya tafi, sannan yace zai sake dawowa gobe. Shi kuma wajen la'asar Suhail ya dawo. Suna zaune suna hira sai Nimra tayi masa tambaya kamar yadda Abu yace tayi.
"Bansan haka, bansan binciki" yace ransa a bace har jijiyan fuskan sa yana fitowa.
"Ba bincike bane, na soma tuna komai kuma inaso nasan duka story din... Is that to much to ask?" tace cikin tsiwa.
"Ina ruwan ki shine matsala na, rannan kin tambaya meke dakin chan yanzu kuma wannan... Me kike nufi? Ni mutumin banza ne kome?"
"Idan kace kai mutumin banza ne ni na isa nace a'a... Daga tambaya duk ka daga hankalin ka"
Saisaita kansa yayi, wannan maganar bai kai fushin dayake ba. Saidai idan yana boye wani abu. Shi dai baisan bincike ne a rayuwar sa kwata kwata. Wani paper ya gani ya leko kasan kujera, ashe sanda Abu Dhar yazo bai gama tattara komai ba. Yana daukowa yaga Nigeria Police, kallonta yayi yana tambaya da idan sa.
"Ohhh Da Yaya Abu yazo zai biya aiki, shine komai ya watse bai hada da wannan ba ashe"
"Dama dan sanda ne?"
"Eh mana kowa ya sani, shine Shahararren Inspector Abu Dhar"
Karkada kai yayi, yasan sunar saboda duk wanda yake Kaduna ya sani. Amma baisan fuskan shiba. Saiya soma tunani tunda Nimra ta gansa take masa tambaya da baya so. Baice komai ba ya wuce dakin daya ke kullewa.
Yana shiga ya rufe saiya dauki waya yana kira, "Ya batun kayan nan?... Yes yes yes.. Eh su... Ku boye su da kyau fah sabida akwai matsala nake ji"
Baisan ashe Nimra tana labe a bakin kofa ba, mamaki takeyi yadda taga rashin gaskiya karara a fuskan sa. Bataji meya ce ba amma ta san Suhail ba a yadda yazo masu bane, koko shima yana cikin mafia ne ?
***
Da safe Umma tayi ma yara breakfast dasu Lubna, ranar za'a koma makaranta. Driver yaje ajiye su sai ya kaima su Lubna abinci. X bata tashi fitowa ba sai 8:05. Rigar barcin ta fari tasa babu overall din. Duk tsammanin ta Ummu hani ta tafi aiki ne. A falo sukayi kicibis. Mirsisi tayi ta wuce dining.
Daidai lokacin saiga Yusuf ya fito, Ummu ta gaida shi a ladabce, saita wurga ma X hijab na hannun ta domin ta rufe. Ido yayi ma X ta karɓa karda Ummu ta gane. Haka tayi ranta bai soba. Saita gaida shi, shima yana amsawa cikin basarwa.
Daki X ta koma, a bakin kofa ta yarda hijab din tana cizan yatsa. Ummu ta shiga da sauri, "Allah ya so ki ina wajen da hijab" tace tana tayata jimami. Ita kuma watsa mata harara tayi, sai tace "Uhm"
"Tunda kinsan yana nan ki daina fita babu hijab"
X bata amsa ba tayi kwanciyar ta, Yusuf yana dining yana cin Abinci Ummu ta jira shi. Anan tace za'a kawo kudin cefane idan zata dawo saita biya kasuwa ta siya. Anan yayi mata transfer na 10k. Sai yayi ma X text akan ta tura account number domin ya bata nata. Murna tayi sosai yau zata gidan Malam.
Yana gama ci ya tafi, saiya sauke Ummu a unguwar sarki. Godiya tayi mashi sosai. Tana isa tace ma oganta dan Allah tana jinya satin. Dama sunada yawa masu bautar ƙasa sai aka daga mata kafa. Kasuwa central taje tayi cefane kayan miya dasu nama daidai duk abinda ake bukata.
Koda ta isa gida babu kowa, X ta tafi wajen boka. Girki tayi na abincin rana. Shinkafa da miya sai fresh fish. Da kanta taje domin taga Ainau. Har yanzu tana kwance kuma bata fara cin abinci mai nauyi ba. Shayi da kuma koko take sha. Su Lubna ne suke ci. Yusuf ma yana wajen, yana ganinta saiya ce bari yaje ya dawo.
Gida ya koma straight wajen X, amma yana zuwa sai yaga bata nan. Kiranta yayi a waya sai tace gata nan. Malam ya hada mata wani hayaƙi da zata rinka sawa da turaren wuta. Koda ta shiga tayi murna ganin su kadai ne, sai tace bari ta kunna masu turaren tukun. Bai musa taje tasa a burner ta dawo, abin yanata damunsa hayaƙi yana juya mashi kai amma babu yadda zaiyi. Bazai iya cewa ta kashe ba.
Ita kuma Ainau tana kwance amma addu'a take cikin ranta, yadda Yusuf ya fita tasan inda zashi, "la ila inna anta subhanaka inni kuntu minal zalimin" take yi kadan kadan abinda. Lokaci ya gota sai Umma ta ce bari taje kafin su Khadija su dawo daya ya kusa. Napep ta hau ta koma.
Daga tsakar gida taji turare, mamaki tayi saboda tasan X basa shiri da abin. Sannan ta sake mamaki ganin motar Yusuf a gida, kila yazo daukar wani abu ne. Bataga kowa a falo ba. Amma taga rigar X akan kujera. Dariya taji na Yusuf yana fita daga dakin Lubna. Zuwa tayi ta murda sai taji a rufe. Kwankwasawa tayi, "Uncle kana ciki ne"
Su kuma tunda sukaga an murda gabansu ya tsinke, saida sukaji Ummu hani saiya kwantar da hankali. Yanzu zata bar mashi gida idan batayi wasa ba.
X tana kwance bata ce komai ba, shine ya saka kayansa ya fita waje. Bai ce komai ya hada fuska yana kallon ta. Murmushi tayi, "dama nayi mamakin ganin kane"
"Me kike nufi banda ikon dawowa gida na?"
"A'a ba haka bane naga... Koda yake never mind.. Dama laptop dina zan dauka akwai abinda zan duba"
"Barci nakeyi... Ki bari anjima idan na tashi... Kinsan kwana biyu bana samun isarshen barci" saiya koma ya rufe kofa. X tana dariya tareda toshe bakinta. Abinda tayi burgeta yake. A duniya tana bala'in san yadda suke hawa gadon Lubna su ha'ince ta. Yafi mata komai dadi. Sannan ta gama tasa kayan Lubna. Lubna ta fita da komai amma saita nuna bata ba daga nan yake ba.
Jikin Ummu yayi sanyi ta rasa meyasa Yusuf yayi mata haka, kitchen taje ta zauna bataso tayi zaman falo su hadu. Sannan bataso taga X a dayan daki. Gaba daya zaman gidan ya isheta. Idan taje asibiti gobe zata roke Mommy akan ta barta ta koma gida idan yazo X ta lura da yaran ita kadai.
Sai kuma ta soma tunani me yake yi dakin Lubna, ranta ke kawo mata mugun zato sai tana kawarwa. Tunani take dalilin rigar X a falo... Saita mike taje dakinta domin ta duba. Wayam ta gani babu komai.... Wannan kenan!
#Nimra
#Ainakatiti ✨
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top