14
On the authority of Abu Dhar Jundub bin Junadah, and Muadh bin Jabal that the messenger of Allah said : "Fear Allah wherever you are, and follow up a bad deed with a good one and it will wipe it out, and behave well towards people." Tirmithi narrated the Hadith and said it was fine, and in another version, said ture and fine.
******
Ranar ƙin dillanci...
Rayuwa yana kaima Xobaederh karo yadda takeso, duk wani ƙaramin chance data samu tana kasancewa tareda Yusuf, harsun saba kuma sun ƙware sosai wajen ɓuya.
Koda ta tafi makaranta idan Lubna ta fita zai mata waya akan ta dawo gida domin su ha'ince ta. Yanzu kam zuciyar su ya bushe da saɓon Allah.
Ainau tana ankare dasu, abin kam yana bala'in ɓata mata rai. Yanzu yar karama da ita tunani yayi mata yawa. Magana ma zaka tsinta sau nawa tayi a rana.
Bata wuce 'uhm' ko 'uhm uhm' yanzu komai nata ya koma sanya sanya kamar babu laka jikinta. Lubna babu yadda batayi ba ta faɗa mata meke damunta amma tayi shiru.
Koda yake itama Lubna tana ganin ittifaki, yanzu zaman gidanta ya gundureta. Xobaederh ta bala'in rainata kamar kishiyarta kokuma tsaran wasanta.
Sai aikin dataga dama takeyi, idan kuma tana jin gari burus takeyi a ɗaki taƙi fitowa, kuma idan an gama abinci dole ta zuba san ranta.
Gata dama tanada bala'in zuri kamar ba mace ba, abinci takeci sosai babu kama hannun yaro. Yusuf kuma babu kunya idanu balle tsoron Allah, zama yakeyi da Xobaederh a falo suyita kwasan hira abinsu.
Ba zasuyi mu'amala ba ta fannin jiki amma kam sun sake jikinsu, kuma haka za'a rinka aikace aikace bazai ce mata taje tayi ba, Ainau zatazo tana goge goge illa ce mata yake ta bari idan Xobaederh ta tashi saita dawo.
Ainau bata fasa bin iyayenta da azkar, addu'a shine jigon rayuwa kuma duk daren daɗewa Allah saiya fitar ma kowa hakkinsa.
Kuma ko ba'a fitar mata da hakkinta ba tasan cewa a lahira yana jiranta, haka ta fawwala ma Allah komai.
Batun gayama Lubna kuma meke faruwa cikin gidanta bata sake gigin yiba tunda taci labta, ta bari ta gannin ma idonta, kuma gafa signs kala kala amma sam Lubna bata gani.
Ko zuwanka gidan na farko ne zaka gane amma banda Lubna, ita komai daidai take gani tsakanin zamanta kewan su, infact ko Yusuf yana mamakin yadda bata ɗago komai ba, 'Oho naci bulus wallahi' Yake faɗa cikin ransa.
***
Yau akwai wani taron tallafa ma mata yan mata da kuma zaurawa wanda Hajia Zainab Aminu Zailani da kuma Hajia Lubna Yusuf suka jagoranta.
Taro ne wanda ya ƙunsa guntun seminar sai kuma a ƙaddamar dasu keken dinki, na saƙa, na weaving da kuma na design duk kuma kyauta za'a bada.
Asabar ne so yara duk sun tafi hadda tun 8am, tunda asuba da Ainau ta tashi da cutar malaria, balle abinka da genotype na AA wantu malaria salama alaikum.
Da farko bataso zuwa amma daddynta ya watseta tas akan bayasan wasa da karatu, idan karatun boko ne koma meke damunta zata tafi amma dayake islamiya shine ci baya.
Anan ya rinka sababi inda yake shiga banan yake fita ba, itama Lubna dukda taji jikin Ainau yayi rau kamar garwashe bata musa zancen Yusuf ba.
Ta tashi da kanta ta mika mata uniform ta saka, ko wanka batayi ba saboda sanyin datake ji, anan dai aka bata paracetamol tasha idan yaso bayan ta dawo sai aje koda Maryam pharmacy ne a siyan mata magani.
Driver ya kaisu a motar Yusuf sabida yace shi baijin fita waje, ita kuma Lubna ta tafi wajen taron ta da wuri domin su gama shiri, sam bata shiri da African time.
***
Xobaederh tana ankare da duk abinda Yusuf keyi, watau shima jaraban ta matso shi kenan. Yau kwana uku kenan basu samu wani Freedom ba mai tsawo.
Gida yana watsewa taje da kanta ta hada masu breakfast na wainar kwai, plantain sai sap na acha. Tare sukaci hankali kwance kamar ma'aurata.
Tunda suke basu samu sakewa ba kamar na yau, yara bazasu dawo ba sai sunyi azahar, Lubna kam batada lokacin dawowa saboda shi program din sai 11 za'a fara ba'a san ranar dawowa ba.
Ainau tana islamiya Mallam Okasha ya lura da yanayin ta, sai kwanciya takeyi kuma kasan bata jin daɗin jikinta. Anan ya bada naira dari a sakata akan napep domin a mayar da ita gidan.
Kowa yayi mata addu'a, da farko ma anata kiran Yusuf ne yazo daukarta amma yana tareda ƙedara baiji ba. Yasama kawai aka sakata a napep.
Yau Xobaederh abin nata ya girma, dakin kwanar Lubna taja Yusuf suje domin cin amana. Ainau kuma ta shiga cikin gidan kai tsaye bata kawo komai ranta ba.
Yanzu tana hankalta da shiga dakin daddynta kona Xobaederh kafin taga abinda yafi karfin idonta.
A sanyaye ta tura kofar dakin Mommynta, tanayi tana dafe bango sabida azabar ciwon kai. Wuta baro baro a cikin dakin...
"Innalillahi wa inna ilayhi rajiun" tace tareda aza hannayenta a saman kanta.
Nan ta fadi kasa rashe rashe, su kuma su Xobaederh wanda basuyi tsammanin kowa zai gansu ba ido ya raina fata. Da sauri suka soma tattara kayansu koma dai ace Yusuf ya tattara nasa ya karasa wajen Ainau dake kwance.
Tallabota yayi yace, "Baby dan Allah ki dawo hayacinki, wallahi aikin shedan ne" yace yana kuka.
Ita kam Xobaederh zuwa durowa tayi ta dauko night robe din Lubna ta saka tana wani zare masu ido.
"Ainau gaskiya kina shiga hurumin da banaki ba, haba wai yaushe zaki barni na rashe ne cikin lumana ba takura" tace tareda yin kwafa.
"Bakida hankali ne, maimakon ki samo ruwa kina ganin kamar suma tayi zaki kawo min shiririta"
Haka ta wuce bayin dake ɗakin ta debo ruwa cikin wani roba ta kawo masa, haka ya rinka shafawa a fuskan Ainau tareda tofa mata addu'a. Cikin Ikon Allah saita farfado.
Tana buɗe ido tayi arba da Yusuf saita mayar ta damste, hawaye ne ke malalo mata kawai, ita kadai tasan me take ji. Bata san inda zata saisaita tunanin ta ba, walau zazzabi kokuma abinda tagani suna aikatawa.
"Yanzu ya ake ciki ne? Zaki faɗa ma Lubna ne ko zaki rufa mana asirin da Allah ya rufe" Xobaederh tace tana jijiga. Bude ido Ainau tayi saita kalleta sannan ta sake rufewa.
"Dafa ke nakeyi? Karki kawo min iskanci karamar alhaki" ta sake faɗi cikin tsawa.
"Haba Xobaederh kiyi hakuri mana, bakiga yanayin datake bane?" Yusuf yace
"Ba wani maganar Hak'uri, gwara nasan ko zan soma tattara kayana ne saboda karyan matarka tanaji zatayi fatali dani" tace tareda murguda baki.
Bai kulata ba illa daga Ainau cak zai ajiye akan gado, da karfin jikinta ta tsala ihu alamar bataso ta kwanta a inda suka tashi. Tsaki Xobaederh tayi sai tace, "Munahuka, ke kika sani" haka ya dauka duvet ya shimfida mata a kasa saiya ajiyeta.
Ko wanka baiyi ba illa zura jallabiya ya wuce pharmacy domin siyan magani, dolen Ainau tasha maganin da kuma maltina.
***
Wajen la'asar sakaliya, Lubna da sauran yara sun dawo. Ainau tayi barci harta tashi kuma jikinta yayi sanyi. Yusuf ya siyo masu takeaway na abinci a Halims.
Xobaederh tayi zuciya bata samu ta sake sosai dashi ba, so batayi aikin komai ba. Da kanshi yayi wanke wanke kafin lubna ta ɗago.
Shi murnarsa daya shine Allah ya bashi yarinya mai hankali wanda zata rufa mashi asiri, yasan cewa his secret is safe with her.
Ainau da kanta take ɓare masu fruits ɗinda Lubna ta siyo, duk yanda Lubna ta hanata tace gwara ta mosta jikinta kafin ya rufeta tayi jinya da kyau.
Xobaederh tunani kala kala takeyi akan yadda zata magance matsalar Ainau, duk duniya su uku ne suka san abin nan yana faruwa, watau ita sai Yusuf da Ainau.
Dole ta nema mafita saboda ta samu yadda zataci karenta babu babbaka. Bazai yiwu ta saida laptop dinta a banza ba sannan kuma ta saidai imaninta amma bata mora da kyau.
Yar karama yarinya ta zame mata ciwon idanu, dole ta tashi tsaye dan kam bazata barma Lubna Yusuf ɓagas ba.... Wannan kenan!
***
Haka Xobaederh barci ya ɗauketa batayi ko sallar maghrib ba, tana tashi an kusan isha sai faɗa takeyi wai an bar mata kofan daki a bude sauro ya shigo mata.
Haka tayita sababi har saida Lubna taji haushi ta bata dubu data akan taje kiosk ta siyo Baygon.
Wajen takwas da rabi ta farga wai ita bata san kan anguwar ba saidai alambaran Ainau taje. Lubna tana daki lokacin haka Yusuf ya tursasa Ainau akan taje.
Zura hijab jiki yana mata ciwo tayi saita fito, shagon wajen kusa dasu babu Baygon sai wasu kamfani, sanin kanta ne idan Xobaederh kanta ya motsa zata iya cewa ta mayar.
Sai kawai ta karasa gaba chan wani shago inda zata samu, isarta wajen keda wuya saita riske wasu matasa su uku suna shan taba.
Da azama tayi abinda ya kaita tabar wajen, tana tafe sai taji ana binta. A hankali saita lura sune suke binta.
"Ke yan mata minti daya" wani yace a cikinsu.
Bata tanka ba illa sake sauri tareda addu'a.
"Dan ubanki badake mukeyi ba, banza kuchaka har kin samu kamar mu muna maki magana kinyi banza damu" ya sake fadi
"Bar shegiya tsinanna danta samu mun kallan kandas din jikinta kamar kuli kuli zata kawo mana wargi" wani ya chapke.
Na ukun kam da baice komai ba, take sigarin hannunsa yayi a kasa saiya karasa inda take tafiya, kan kace kwabo ya fizge hijab dinta ta baya wanda ya sarketa ta kasa tafiya.
Nan tayi kokarin kwace kanta saiya kwada mata mari, maiya kaita tace mashi Allah ya isa. Aikam nan ya hurzuka ya soma zabga mata mari.
Ananfa ta rinka rokansu amma kamar tana ingiza sune, zuciyar su ta riga ta bushe kamar stock fish babu burbushin imani wajen su. "Dan Allah karku illanta ni, kuyi hakuri kuyi min rai dan san annabi" take faɗi tana zabga kuka. Amma kamar kana busa sarewa a kunnen bebe.
Nan su ukun suka rinka dimanta, balle da sukaga shaltos ba wani amfani zai masu ba, kuma babu handset a hannunta balle su fizge.
Sannan gata kwaila kashi da rai jijiya da wahala, numfashi sama sama takeyi dukta galabaita, babu kowa a hanyar balle a kawo mata agaji.
Jini ne ke malala ta baki ta hanci, sai wani ya zaro karamar wukan sa, "Yanzu in kun kasheni saiku zauna gadin duniya, inda zaku turani kuma watarana zaku zo" tace kasa ƙasa wanda dai zasu iya ji.
Nan ya rinka luma mata a ciki, wanda saida ta tsandara kara mai gigitarwa. Tunda take bata taɓa haduwa da azaba ba irin na yau. Haka ya sake luma mata wani yana surfa zagi.
"Dan ubanki har kin isa kiyi min gorin mutuwa, kina wani cewa zamuyi muma, shegiyar mai siffan yan wuta" yace saiya sake chaka mata.
Bai bari ba saida yayi mata sau takwas wanda shima abokansa ne suka rikesa, anan kuma suka gungurata cikin kwalbatin dake gefen wajen.
Lubna batasan Ainau ta fita ba, kawai taje tayi bismillah ta rufe kofa, shikuma Yusuf saboda wahalar dayasha yau yana daki yana gyangyadi.
Itama Xobaederh barci yayi gaba da ita, babu wanda ya lura cewa Ainau bata nan. A yau sun nuna Ainau batada wani amfani a wajen su kowa kawai harkan gabansa yakeyi.
Tana kwalbati cikin tabo tana numfashi sama sama, neman agaji takeyi amma babu wanda yasan tana wajen. Gashi jini ne yaketa kwararowa ta duka inda aka chaketa dashi.
Tana haka har Allah ya amsa abinsa.... Wannan kenan
#CodenameNimra
Fully DIMPLELATED.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top