13
It was narrated from Abdullah bin Amr that the Prophet said: "Do not marry women for their beauty for it may lead to their doom. Do not marry them for their wealth, for it may lead them to fall into sin. Rather, marry them for her religion. A black slave woman with piercings who is religious is better." (Da'if)
It was narrated from Ibn Abbas that the Messenger of Allah said: "A widow has more right (to decide) concerning herself than her guardian, and a virgin should be consulted". It was said: "O Messenger of Allah, a virgin may be too shy to speak." He said: "Her consent is her silence." (sahih)
"There is no prayer after the morning prayer till the sun rises, and there is no prayer after the 'Asr prayer till the sun sets." #Hadith
******
Please ina ƙara rokan ku da babban murya ku rinka kokarin yin comments line by line kuna karfafa min gwiwa kamar yadda nima nake daɗa maku
Tafiya takeyi cikin rangaji, kana ganinta kasan tasha wahala sosai. Duk idanunta ya firfito kamar kwai saboda tsabaragen yunwa.
Haka Abu Dhar yace mata tayi, sun samu wani leads na ƙungiyar Gamji. Ance da yammaci wasu daga cikin su suna zama a wajen domin su huta.
Shine akace ta rinka zuwa ko zata samu tasan wani abu akansu, rabon dataci wani abin kirki kwana uku kenan sabida yunwa da wahala ya nuna a jikinta.
Sanye take da riga da zani, sai wani tsohon mayafi wanda ta kare jikinta, sannan kuma ga wani yar leda mai kalan ganye inda ta saka komatsanta.
Maza da mata ne ke cikin filin shakatawa, duk kowa abinda ke gabansa yakeyi. Tana tafe tana tangal tangal sai wani mota yazo wucewa sukayi karon rago dashi.
Runtse ido tayi saita faɗi kasa, wani zafi mara misaltuwa taji ya soma bin dukan wani sasan na jikinta, tana kwance wanwar a kasa sai ya fito daga motarsa.
Salati yakeyi sosai cikin tashin hankali, mutanen dake gefe wasu na kallo wasu kuma sun basar, masu kallo daga inda suke suka soma tofa albarkacin bakinsu suna tsine ma almajiran watau laifinta suke gani.
Harda masu cewa da sune sai sun rinka kwada mata mari koda a sume suka iske ta, gobe almajiran duniya zasu shiga taitayinsu.
Zuwa yayi inda take ya tallabo ta, sam bai san wacece ita ba. Ita kuwa a hankali ta bude ido, amma kuma da sauri ta rufe idonta.
Kanta ne ya soma mata sara wani zafaffan ciwon kai ya fara addabanta, gashi kuma jini ya soma zuba ta saman goshinta, batasan waye ya bigeta bah kuma bazata iya tuna abinda ya faru gabanin haka bah.
Sake bude ido tayi ta kalle shi, wanda shi kam ya tallabo ta yana kokarin kawo mata agaji, "Zaki iya tashi tsaye?" ya tambaya.
Dakai ta amsa tareda daga kai kadan, bakinta yayi bushewa data tabbata bazata iya amfani dashi wajen magana ba.
Kokarin tashi tayi saita dan dafashi saboda kafanta, chapketa yayi kokarin yi cikin reflex ta matsa baya tareda cewa 'karka damu zan iya'
"Nimra!" yace cikin mamaki, fiƙi fiƙi da ido tayi tana murjewa a hankali, nan ta soma yi kamar taɓarɓa tana kallonsa alamar bata ganesa. Koda yake tabbas bata ganesa ba, bugun kan ya shafe kwakwalwarta da sunadarin tuna mutane.
Yana ganin yanayin ta saiya tausaya mata. Dama ya daɗe yana so ya gane dalilin dayasa ta ɓace ɓat a doran ƙasa.
Wani arniyan mota ne yazo gefensu ya faka, anan wani matashin saurayi da kuma kanzagansa suka fito cikin shiga na alfarma da kuma takama.
Idon kowa a kansu har ita kanta Nimra, ta juya sosai tana kallonsu dukda ba sanin su tayi ba balle ita kanta, sai kawai jiri ya ɗebeta ta zube sumammiya.
Kafin yakai inda take ta dade tuni a kasa, haka ya cuncubeta yakai motarsa ta wajen baya ya saka saiya rufe, sannan ya koma ɓangaren gaba wajen tuƙi ya tafi.
Bai tsaya ko ina ba sai Al Madina Hospital, nan aka bata agaji na gaggawa, da aka tambaye sunarsa nan ya faɗa masu sunar shi Suhail Aminu Zailani.
Dayake zabe yayi ƙaramari kowa yasan sunar A2Z ake nufi, nan take aka soma bata komai daya dace ba tareda an nema police report ba kafin suna samun gwamnati a karba license dinsu a makon farko.
Anan gurin Doctor yayi masa bayani akan ce ta samu matsala a kwakwalwarta, saidai zai iya dawowa wajen gobe ko sati daya, kawai it depends on the patient.
***
Yusuf ne ke kai mari yakai gwauro cikin daki watau safa da marwa, babu abinda yake gani a idonsa sai Xobaederh. Duk ta cika mashi ido ta hanashi sakat.
Abinda yake fuskanta kenan kwana biyu, bayada wani sana'a sai tunanin ta. Sam yanzu ya daina gudunsa na fama ya wuni a majalisa.
Daga Lubna har Xobaederh murna fal ransu, kuma yana jin dadin yanda Xobaederh take sakan mashi jikinta yayita satan kallo. Koda yake kayan data saba sawa ne amma sai yanzu yake lura da fitsaran dake cikinsu.
Sam ba abin ka kalle mutum bane kayi alfahari dashi indai ba matarka bace. Kamar yadda ta saba tana kashe masa ido a dining tana masa salo, wannan karon daɗin abin yakeyi.
Da kuma kansa yakance ta kara masa abinci duk dan ta kasance wajensa. Ainau tana ankare dashi amma ta kasa explaining yanayin nan.
Yanzu kam tura takai bango wajen Yusuf, bawai kawai ya rinka kallon Xobaederh bane, yanaso ya kasance tareda ita ne. Yanda yake jinta babu abinda zai hanashi.
Ita kam aikin baya mata saurin datake bukata, tasha tana gama bashi maganin a ranar zai nemeta a shimfidan sa amma kuma salap.
Saida ta kira Malamin ta domin taji ba'asi, anan yace tayi hakuri shi aikinsa a hankali zai soma tasiri.
Kowa na zaune a falo suna kallon tashar WapTv in da ake program din 'This Life'
Ainau dai tana mayarda takardunta na Islamiya inda ta gama biyama Khadija Hadith ɗin 'Bugiyatul Muslim' lokaci yayi zasu tafi Islamiya ne.
Fitowa yayi daga dakinsa yana ƙunci, Amrah ce tazo zata hau jikinsa, da sauri yaja baya saiya soma magana.
"Karki sake ki hauni, duk jikina yana min ciwo" maida hankalinsa yayi wajen su Ainau, "Me kukeyi har yanzu baku wuce bah"
"Yanzu zamu saka uniform sai mu tafi" Ainau ta amsa tareda mikewa tsaye. Itama Khadija abinda takeyi kenan. Abubakar kam wasanshi yakeyi da Playstation dinsa.
"ranka ya dade banda Kaine?" Yusuf ya tambaya cikin izgili gira a harɗe
"Yanzu zan tashi Daddy" ya fada saiya mike.
Lubna dai bata gane kansa ba, kwana biyun nan ya fiye faɗa kamar dage. Sannan kuma fafur ya kaurace mata wajen zamanta kewan ma'aurata.
Kallon Lubna yayi, "Kin amso wannan takardar wajen Hajia Zainab kuwa?"
Sosa kai tayi tana dariyar borin kunya, "Aikam ban amsa bah"
"Yanzu dai tunda yara zasu fita saiki tashi kije ki karbo, idan yaso ki zauna a chan idan sun tashi saiki je ki biya ki dauko su"
"Wannan ma yayi, Xobaederh nasan zata luran min da gidan kafin nan" Lubna tace saita mike tsaye.
***
Gidansa na Wurno Road ya kaita kai tsaye, tun bayan rabuwarsu ya koma chan Unguwar kanawa amma suma sunce basusan inda take ba.
Dama yar haya ce kuma ta tafi, duk tsoffin number ɗinta ya nema, switch off yake riska alamar an kashe. Tunani kala kala yakeyi kila kinsa yasa ta gudu bataso ta hada alaka dashi.
Yanzu dai yana cikin murna saboda zata murmure a wajensa har ta warke, anan zata gane cewa shine soul mate dinta. Saidai kuma mamakin irin shiganta yakeyi.
Wani zuciyar yake faɗa masa kila karayan arziki ya kamata ne, nan tausayinta ya diran masa a cikin zuciya. Tabbas daka ganta kaga abin tausayi.
Inna watau yar tsohuwar dake masa aiki ya gani a tsakar gida tana kwashe shanyar tsumma, Dattijuwa wanda take masa su gyaran gida da sauransu. Saidai ba anan take kwana ba.
7am to 6pm takeyi saita koma Katuru Road inda gidan jikanta yake wanda take zama dasu.
"Sannu da zuwa Alhaji" tace saita karasa wajen Nimra tana tayashi dafa ta.
"Yauwa Inna sannu da aiki"
Sun soma tafiya sai yace, "ban sani bane na bugeta da motana, yanzu zata soma zama damu kafin ta murmure, ki sakata a dayan dakin ita da kayanta"
"Ba damuwa Alhaji Allah ya kyautata tsautsayi da asara a gaba"
Shi saiya koma domin ya samo masu abinci wanda zasu ci, Isa Kaita ya koma inda ya sayi su fruits, snacks da drinks sai kuma wani Pharmacy domin siyan maganin da Dr yace a siya
Harya kama hanya saiya tuna Nimra bata dace da irin munanan kayan ba, wani Boutique ya shiga ya kwaso mata su abaya da dogayen riguna yan madaidaita guda biyar, sannan da atamfa guda biyu wanda nan gaba zai kaima tailor.
Shi dama haka yake, yanada bala'in sanin ya kamata, sai kuma ya siyan mata ready made hijab dogon na sallah. Bai kasafa ba saida ya biya cosmetics shop ya siya mayuka dasu toiletries haka.
Sanda ya shiga dakin zaune ya ganta tana wasa da yatsanta, dukta rame ta canza fasali, alwashi ya dauka a ransa saiya canza mata rayuwa ya fitar da ita daga wani kunci datake ciki.
"Nimra sannu koh" kallonsa tayi kamar batasan meyake magana bah.
Murmushi yayi mata saiya zauna dan nesa da ita, "Sunanki ne Nimra ai koko baki gane abinda nake cewa ne"
Sake kallonsa tayi sai tayi murmushi, "Ina gane me kake fadi mana, kuma na lura cewa kamar kasan ni, amma sunana ba Nimra bah kuma ban sanka bah"
"okay karki damu, banda hanzari. A hankali zaki gane wanene ni kuma komai zai daidaita maki"
Ajiye kayan daya siyo yayi akan gadon saiya tafi ya barta, a bakin kofa ya tsaya saiya juya, "Tunda bakisan na rinka kiranki Nimra menene kike tunanin sunarki?"
"Rumaysa" tace masa sincerely
"Wow Rumaysa! I like it better" yace cikin shauki
Sam bai yarda da sunar ba, amma kawai domin zaman lafiya ya hakura, Lalle wata sa'iin idan mutum ya mance da abubuwa yana samun dan tabun hankali. Tabbas ta soma samun hauka.
Kowa yasanta da Nimra saboda duk campaign na babanshi itace ja gaba.
Daga dayan bangaren kam, Abu Dhar yaune zatayi mashi magana akan ko ta samu taga mutanen Gamji ko akasin haka. Waya yana hannunsa yanata jiran ta kirasa amma shiru.
Nan ya yanke jiki ya tafi inda take ko zai ganta, ko basuyi magana ba yasan cewa tana kan aikinta, babu ita babu dalilin ta.
Saiya fara tambaya ko an ganta, sabida ya bata sadaka da dari biyar bata bashi canji ba ta gudu.
Daga masu mashi dariya sai masu tsine mata, harda masu cewa ai yasa basa bada sadaka tunda abin ya koma iya shege.
Haka ya gama za gayawa babu wanda yakeda sani akanta, Allah Must'an ya faɗa a fili saiya wuce
***
Xobaederh ta gama fesa wanka tana shafa Anty Lubna tazo tayi mata sallama akan zata fita, ta dafa jollof rice and chicken sai onion sauce.
Ba wannan yake gabanta ba, yau saita samu Yusuf domin kam ta bala'in gajiya da jiransa yazo wajenta.
Lubna bata kai wajen motaba da yara Yusuf ya nufa dakin Xobaederh, ko tsoro kada wani ya dawo ya gansa baiyi ba, tura takai bango a wajensa.
A hankali ya tura saiya shiga ciki, gabansa yana duka alamar rashin gaskiya amma bai fasa ba.
Zaune ya ganta daga ita sai towel, murna fal ranta mara misaltuwa, tasan meya kawoshi. Mallam ne ya ingiza matashi kamar yadda ta bukata.
"My Yusuf" tace da sanyin murya tana kashe masa ido.
"Abinda nakeji maki a raina bai dace ba, wannan abin kunya muke aikatawa amma na rasa sanin dalilin dayasa na kasa barin irin tunanin" yace kasa kasa amma kuma tanaji
Tasowa tayi taje dab dashi, fuskanshi ta tallabo wanda yayi kokarin hanata amma saida tayi, "Muna san juna ne, kuma banga dalilin dayasa kake nokewa ba. Kaddara ne yazo mana ka riga auren Anty Lubna kafin ni. Amma ai bai hana cewa bazamu faranta ma juna raiba"
Kallonta yayi kawai, yanaso ya tafi amma ya kasa, ruhinsa baya wajen nan kawai gangar jikinsa ne, kamar wani abu ke rikasa tsam. Gashi yana ganin yau idan bai aikata alfasha da ita ba bazai samu sukuni bah.
"Ina sanka Yusuf kuma nasan kana sona, yanzu babu kowa cikin gidan nan, nasan kana tsoron Anty ne amma bata nan.
Babu wanda zai ganmu. Why not mu faranta ma juna rai"
"Hakane babu mai ganin mu" yace mata
Fadawa jikinsa tayi cikin murna, shikam saiya rufe kofa ya biye mata
***
A kwana a hantse sai kyakkyawa, Nimra ta soma murmurewa. Har yau bata tuna wani abu tsakanin ta da Suhail ba ko rayuwarta na Nimra.
Saidai yadda yake faranta mata tana masa, yana mutunta a matsayinta na ya mace, baya daukar dama wai tana zaune gidansa yace zai kawo mata wargi.
Yau zasu fita waje taga gari tun zuwanta na farko kenan, daya daga cikin abayanta peach ta saka. Ya karba jikinta kamar dan ita akayi.
Gashi the old Nimra is back, tayi make-up tareda saka pink lipstick kamar yadda take bala'in san abin.
Sai kuma ta saka nerd glasses wanda ya ƙayata mata fuskanta.
Sunje Daraja plaza domin suyi siyayya, Abu Dhar yazo wucewa yaga kamar Nimra. Anan yayi reverse ya dawo wajen. Ta gefe ya tsaya ya kafa mata ido amma bai karasa wajenta bah.
"Yaya Abu Dhar" tace tana kokarin karasawa, mamaki yakeyi meyasa Nimra zata je kusa dashi.
"Yaya Abu Dhar yaushe rabon dana ganka?" tace cikin fara'a
Baikai ga amsawa bah saiga Suhail ya karasa wajen gira a tamke, "Nimra me kikeyi a wajen nan, sorry i mean Rumaysa"
"Wannan wani Yayana ne haka, he is the closest thing i have to a family, sunarsa Abu Dhar" ta amsa cikin fara'a.
"Ita tace maka sunarta Rumaysa?" Abu Dhar yayi tambaya cikin damuwa.
"wallahi hatsari tayi shine akace tayi losing memory dinta, toh tun daga nan tace sunarta Rumaysa kuma karna kirata Nimra" Suhail ya amsa yana sosa kai
"Toh babu damuwa, ka bani Address dinka saina zo na dubata anjima, dama munata nemanta wallahi"
Shi Abu Dhar tsoro yakeyi kardai ta faɗa ma suhail asalin wacece ita.
WACECE NIMRA?
***
Sukam Bugun Abuja tuni ta saka trailers dinta a kasuwa, sau dama suna neman inda Nimra take amma babu ita babu dalilin ta.
Saboda wannan komatsan nata bata taɓa bi takaiba, batama san nata bane koda inna ta saka a durowa.
Ita tasha na yan gidan ne so bata bincika ba, kuma wayanta yana ciki amma a kashe.
Su Gamji sun kirata sun tura mata yatsan Blackberry wanda suka cizge. Anan ta sake samun tashin hankali.
Dole ta mike tsaye ta shiga neman kudi gadan gadan kafin taji a salansa yarta ta mutu. Duk yanda Blackberry ta watse Bugun Abuja tana bala'in santa kamar ranta.
Dama dan yatsanka baya ruɓewa ka yanke ka yar, balle kamar kumbo ne kamar karensa.
Gamji yanzu ya kama mutane biyar inda kudin idan anyi masa Total zai samu 2 billion naira, shifa ya soma gajiya da wannan sana'a.
Yasa da wannan kudin tareda sauran wanda ya tara zai sallama Boys dinsa saiya karata da sauran kudin wanda bashiba har yaransa idan ya samu a gaba zasu samu.
Ya lura Bugun Abuja tafi rainin wayo yasa ya soma gutsul gutsul da naman shamsiyya saboda ta gane how serious he is.
***
Xobaederh murna fal ranta, yau ta samu abinda takeso, shikam Yusuf banda dana sani babu abinda yake ɗawainiya dashi.
Kayanshi ya dauka ya saka ya tafi dakinsa inda yayi wanka, ita kam Xobaederh bata tashi ba kuma batada niyar tashi.
Asalima sake rufe kanta tayi da bargo tanata tunanin ta inda zata rinka samun ranaku kamar haka.
Anty Lubna har Sunje shida na yamma yayi sun dawo, falo babu kowa shi kuma Yusuf yana daki abin duniya yake masa yawo.
Bazai yiwu ba dole su samu yanda zasu rinka communicating da Xobaederh tareda samun inda zasu rinka haduwa, bawai yanasan yayi bane.
Kawai yana ganin idan bai kasance da ita ba kamar zai iya hauka kokuma ya rasa ransa, balle yanzu kuma kamar an kara ingiza shine. Saidai kuma still yana tausayin lubna kuma baiso ya rinka cin amanarta a gidanta
"Zubaidah kinyi abincin kuwa banji kamshi yana tashi bane?" Anty Lubna tace, ita kam Ainau shiga dakin tayi. Gabanta fadi yakeyi tana addu'a kada zarginta ya kasance gaskiya.
"Banyi bah" ta amsa
"Akan wani dalili?"
A fili Xobaederh taso tace saboda banga dama bane dan ubanki amma sai kuma tace, "Banjin dadin jikina ne"
Saita sake kwanciyar ta, Yusuf ya fito zashi bakin gate daga nan zai wuce Masjid. Ganinsu yayi a bakin dakin charko charko.
Tsoro fal ransa kada a kama shi, "Lafiya na ganku tsaye? Ya nema sani
" wai Anty ce ba lafia" Ainau tace tana taɓe baki
"Wai ne ma? Watau baki yarda da ita bane kenan?" Yusuf yace a hasalce.
Ita lubna bataga abin jin haushi ba, tabbas waine sabida lafiyanta lau kafin su fita.
"Tunda dai tace batada lafia ku kyale ta mana" Ya sake fadi. "Indai abinci danni akeyi zansha tea gwara ta huta" ya kara
"idan kai bazaka ciba yaranka fah, jibe Amrah shekaranta nawa? Lubna tace
" Ki daina shagwaba su, Amra ma zata iya shan tea, kokuma ayi indomie and egg shikenan hankali kwance" yace.
'kamar goyon bayan Xobaederh yakeyi' Lubna tace cikin ranta.
Ita raini ne bataso, tun farko data gaya mata data dawo gida tayi aikinta idan yaso driver ya dauko yara, amma kawai tace mata batada lafiya gatsal cikin raini ne bazata lamunta.
Abin haushi har mijinta yana bin bayanta, bazai yiwu batada iko cikin gidanta ba. Sam baza'a sha fate ranar sallah ba.
Dole Xobaederh tasan yadda zata rinka yi inba haka ba to tana dab da komawa gidansu. Haka ta wuce Kitchen dab da maghrib zatayi girkin.
Jollof din tayi duk ranta yana ƙuna, bayan ta gama wajen isha batama samu tayi wanke wanke ba illa komawa daki saboda ana binta bashin sallah.
Xobaederh ta gani zaune akan kujera kamar matar gida, sanye take da English wears riga mai guntun hannu sai ɗamanmen skirt.
Kanta babu kallabi sai ta tamke gashin kanta kashi biyu, sannan ta zabga jan baki purple tana tauna chingam din orbit.
Latsa remote takeyi bata MTV base ko soundcity tana rera waka kamar music producer. Anty lubna kam sai zufa takeyi kamar mai aiki ta fito daga kitchen.
Baki hangangan a bude kamar fly over, mamaki takeyi wai mara lafiya kenan, "Ciwon kenan" tace a hasalce
"Well i got better" ta amsa cikin ko in kula.
"Nifa raini ne banso da iskanci, in kinsan bazaki tayani aiki ba meyasa baki fada minba"
"Nifa tsiyana dake Anty Lubna bakida dadin sha'ani, kiyita fada kamar karya. Abu baikai ya kawo ba saiki maida shi magana, yanzu ina raini anan dannayi ciwo" tace cikin rashin kunya
Lubna bataji da kyau ba, idan kunnenta ba karya yayi mata ba Zubaidah karya ta kirata dashi, mamaki kam fal wajen Ainau dan saida da rike baki tana jimami.
Kafin Lubna ta amsa sai Yusuf ya shigo, sallamarsa ya kaste su, yanda yaga kowa yasa yayi tambaya.
"Halan jikin nata ne?"
"wannan karan ba jikinta bane kawai har kwakwalwarta, dan kam ta haukace tayi tunanin ta zageni ta kuma cigaba da zama a gidana"
"Banfa zageta bah" tace cikin shagwaba
"Wallahi kin cema Mommy Karya" Ainau tace
"Nima naji" da Abubakar da Khadija sukace a tare.
"Dalla ku rufe ma mutane baki, tun kuna yara kun koya annamimanci" Yusuf ya tsawata masu
"karka hanasu, ai gaskiya suka faɗa kuma yau sai tabar min gidana, daga nan iskanci ke farawa tun yanzu kina zagina na tabbata Allah na tuba nan gaba zaki ce zaki fara kwana da mijina"
Kallon ke kisa sani Xobaederh tayi mata bata ce komai ba, jira takeyi taji me Yusuf zaice, tabbas yasan idan ya goya ma matarsa baya zata tona masa asiri. Dakewa yayi ya soma magana tsoro fal ransa
"Yanzu naji koma menene nasan akasi aka samu, Xobaederh kici girma ki bama Lubna hak'uri"
"Watau ita zataci girma kenan koh" Lubna tace a hasalce
"Yi hak'uri" tace tana tura baki daga nan ta wuce daki a fusace an cuceta. Tabbas dole ya tsawata ma matarsa tunda kamar yadda take mace ajin farko itama haka take, dole ta fita harkanta kokuma ta hanashi abinda idan bai samu ba bazai samu kwanciyar hankali.
"Yanzu Lubna kinji Kunya, ai Xobaederh kamar yarki take, bai kamata kuna sa'insa ba, inace ke kike so ta zauna" yace mata
"Yanzu kuma baniso" tace
"aikam babu abinda zakiyi yanzu, it's too late saboda Xobaederh taga wajen zama" yace saiya wuce dakinsa.... Wannan kenan!
#CODENAMENIMRA
Fully DIMPLELATED
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top