11

On the authority of Abu Dhar Jundub bin Junadah, and Muadh bin Jabal that the messenger of Allah said : "Fear Allah wherever you are, and follow up a bad deed with a good one and it will wipe it out, and behave well towards people." Tirmithi narrated the Hadith and said it was fine, and in another version, said ture and fine.

******

   Nimra gabanta yanata duka uku uku tun shigan wannan makon, zulumi fal ranta akan abinda yake shirin faruwa. Sam ta kasa samun natsuwa.

    Komai ɗar ɗar takeyi kawai tana daurewa ne, ita yanzu batada wani buri daya wuce kafin a sakata ta kamasu a gama komai.

    A ranar da abin zai wakana, taje nan Ex minister's quaters na Rabah Road domin ta motsa jiki, ta gefen Filin Shinning Diamond tayi duk tsalle tsallenta.

  Ya kamata tayi training sabida gudun ɓacin rana, bayan nan saita koma gida domin tayi abinda ta saba watau Boxing.

   Bayi ta wuce kai tsaye bayan nan domin tayi zufa sosai, sanda ta fito har wajen 8:30am. Bazata campaign office da wuri ba sabida yau ana sunar haihuwan Yaron A2Z.

    Kamar yadda tayi wancan karan ta masallaci ta bada sallahu, haka ma wannan karon tayi kafin ranar, inda suka haɗu suka sake haɗuwa.

    Anan ta bashi location da lokacin da aka bata na inda zata, tace masa tana neman back up amma kuma baifi na mutum ɗaya ko biyu ba.

    Ta gama shirinta tsaf cikin kayan alfarma, tana zaune tana duba wasu takardu saiga Farhan yaron Mommy ya shigo wai ana kiranta.

    Kallabi ta jawo saita riƙe masa hannu suka tafi. A hanya suka haɗu da Ummu Hani kanwar Xobaederh. Tana ganin Nimra tayi saurin garke kofa tareda ma wani sallama alamar rashin gaskiya.

    "Ina kwana Anty Nimra" tace a ladabce, dama tanada hankali sosai, bazaka ma haɗasu da Xobaederh bah.

    "Lafia lau Ummu, ba kyasan shigo min hira" tace da fara'a. Ita kuma Ummu murmushi tayi sabida batada abin cewa

   Tare suka jera har falon, Mommy ne da Daddy suna zaune akan 3 seater. Sauran yara wasu na daga ƙasa.

   Sallama sukayi sai suka shiga, daga Mommy har Daddy da fara'a suka amsa.

    "Nimra dama nace kizo muyi breakfast ne" Daddy yace

   Sinna kai Nimra tayi saboda abin yayi mata zuwan bazata, Ummu ne ta tashi tareda ledar data shigo dashi. Babban gwangwani ne na madarar Nido wanda taje kanti ta siyo.

   Da taimakon Nimra suka gama jera komai kan dinning, "Shine tun safe baki kirani nazo anyi girkin dani ba" Nimra tayima Ummu korafi.

   "Wallahi Anty bansan da zancen ba"

   Sap na Acha ne da kosai aka soya masu sannan kuma akwai roguwan tsire wanda aka siya jiya.

   Koda gidan Abu Dhar taje bata taɓa hawa kan dining ba, infact wai cin abinci cikin dangi yau ta soma. Dukda basu haɗa jini ba karamcinsu baya misaltuwa.

    Ta samu comfort dasu sosai, saidai tana tunanin yadda zata faɗa masu cikin yau ko gobe zata tafi. Dole a canza mata gari bayan ta gama assignment din saboda tsaro amma ba tsoro ba.

   Da kanta ta kwashe kwanuka sannan ta wuce kitchen ta wanke tas, sun hanata amma bataji ba. Daga nan ta masu godiya saita koma nata gidan.

   A lokacin goma ya wuce, harta ɗauko laptop tana kallon 'The Mountain Between Us" wani sabon American film. Mintuna arba' in da fara kallon saita tuna ya kamata ta soma tattara komatsanta waje daya.

   Nan ta kwashe duk su International passport ɗinta dasu Identity card saisu Atm.

     12am...

    Tsaye take a wajen titin Dandali na Malali village, a daidaita sahu ta hau ya kaita wajen kamar yadda A2Z ya umurta.

    Tana tsaye sai A2Z yayi mata text akan ta koma gida an fasa, nan ta soma dube dube ko wani laifin tayi. Haka ta samu cikin Ikon Allah ta hau achaba.

   Suma Su Abu Dhar suna daga chan nesa suna kallon ta, da suka lura cewa hanyar gisa ta nufa sai suka koma.

    Bata karya kwanar layinsu ba saiga sojoji sun tsaya kamar na check point, anan wani ya umurce ta akan ta shiga daya daga cikin motan wajen.

   Babu musu ta bisu tunda hukuma ne, tana shiga sai taga A2Z yana murmushi, sai yake fada mata dama sunaso susan babu wanda ya bita.

   Da farko sun zaci ana binta watau motarsu Abu Dhar amma dasuka ga batayi magana dasu ba kuma gashi hanya bai haɗasu ba.
  
   Sannu a hankali suka tafi chan inda bata sani ba saboda fuskanta a rufe.

   Da kansa gate ɗin ya buɗe wanda bakin kirin ne, Su wajen mota biyar wanda sukayi convoy suka hada dai Nimra tana ganin  ikon Allah

'Innaa lillaahi wa 'innaa 'ilayhi raaji'oon, Allaahumma'- ajirni fee museebatee wa 'akhliflee khayran minhaa' tayita faɗa cikin ranta' 

   A filin sukayi parking inda mutane daban daban suketa fitowa, da wanda suka rigata zuwa. Abin mamaki take gani sosai saboda mutanen data gani.

    Iyayen mutane wanda ake ganin ƙimarsu a gari, irin masu dattako da mutunci ne kuma ƙusoshin gwamnati.

    Bata sake mamaki ba sai dataga Bugun Abuja ta fito anata sara mata, daga gani itama babba ce a ƙungiyar.

    Nanfa mai ganga ya soma buguwa ta wani sautin mara misaltuwa, sai ga kabewa ya faɗo daga bishiya makeke dake filin wajen, wani  mutum ne ya faɗo kan abin daɓas saiya fashe.

   Nanfa ya hau bori sai jijiga yakeyi, itama Bugun Abuja kiɗan ya ɗebeta saita soma taku sannu sannu tana maƙale kafaɗa, gashi ta ɗaga hannaye sama kamar balbela.

   Wasu maza kamarsu Commissioner Of Information da Finance suma suka shiga filin rawar, A2Z dai rangaji yakeyi daga kai saboda rafanan basu kai kansa ba.

   A haka suka rinka yi har kowa ya soma kwasan rawa, banda addu'a babu abinda Nimra takeyi. Allah ne cikin ikonsa zai iya kubutar da ita daga wajen.

   Ko sauran mutanen da za'ayi initiating ɗinsu dan sanabe suka soma rawa tun rafanai basu hau kansu ba.

   Ana cikin haka sai aka katsaita domin ayi abinda ya kawosu gadan gadan. Bugun Abuja daga dukkan alamu ita ce babban a wajen.

    Canza kamanni tayi wannan karon in a more serious face, yanzu kam kamar ba ita ba. Duk wani murmushi da kirki da kake tunanin tanada shi yanzu duk ya ɓace.

     Daga kan Nimra za'a fara, tana zuwa gabanta sai suka soma kallon kallo, za'a iya cewa Bugun Abuja ta sandare ne. Ita kam Nimra har yanzu bata fasa addu'a ba.

    Kawai tunanin yadda zata bar nan wajen takeyi, balle kuma gashi su Abu Dhar basu san inda take ba. A ƙa'ida ya kamata ta yanka hannunta ta zuba jinin dake fita cikin wani ƙoƙo.

    Amma sam Bugun Abuja taƙi motsi, Nimra dai duk ta tsure babu irin addu'an da batayi harda na barci. Sai kawai Bugun Abuja ta kawar gefe ta soma kalle kowa.

   "Naji labarin cewa ana binciken wannan kungiyar"

  Damm gaban Nimra ya faɗi, babu haufi ta kawo kanta zuwa makisa, zufa ya soma keto mata duk ta ɗimanta.

    "Naji labarin suna dabda sanin abubuwa masu mahimmanci akan mu" ta faɗa tana tafiya.

   Kowa a wajen shiru yayi yana sauraro, zuwa tayi wajen wani mutum ta tsaya a gabansa, wukan dake hannunta ta luma masa cikin kirji.

   Nan ya faɗi shame shame jini yana malala, Ashe shima daga wani Division na yan sanda yake aiki a kansu ba'a sani ba

     Kallon kowa tayi saita ce, "Kowa yayi handling business ɗinsa, saina neme ku" saita wuce, abinda take nufi kowa ya kashe wanda ya kawo.

   A2Z yana feeling wani connection da Nimra wanda bazai iya kasheta ba, ita dai Bugun Abuja zuwa tayi wajen motarta ta shiga saita ware.

   Suma sauran haka suka rinka shiga cikin nasu suna tafiya, suna cikin mota aka sake rufe mata fuska har cikin gari, daga nan suka tafi direct guest house.

   Anan A2Z ya kalle Nimra wanda batace komai ba tun daga gidan, shiru sukayi sosai wanda a lokacin har 3:20am. Gyara zama yayi sosai saiya ce, "Yarinya kin debo ruwan dafa kanki"

   Kallon takaici tayi masa, ita yanzu batasan yanda zatayi ba. Daga nan bata san faith ɗinta ba. Babu haufi idan babu batun kama yan Wadata bazata cigaba da aiki tareda A2Z ba.

   Kuma kowa yana yaba iya aikinta yasa aka bata wannan abu wanda a ganinsu ƙarami ne wajen ta. Amma kuma ta kwapsa, hawaye ya soma malalo mata daya bayan daya.

   Kuma tabbas zaman kaduna a yanzu ya gagareta, dole ta barshi kota raye ko a mace. Zuwa yayi ya zauna kujerar datake, hannunta ya rike ya soma murzawa.

    "Ki daina kuka, ance na kasheki. Amma banajin zan iya ba" yace. Wani takaice ya sake kamata, ji take kamar ta mike tsaye tace mashi he is under arrest. Amma kuma akan wani laifi?

  Idan tace yana tsafi ko wani abu, tsafi is a relative term kuma an illusion wanda idan babu sheda a hannu babu abinda hukuma zasu mashi. Watau kawai yanzu sunci bulus kenan.

   Dan bata tunanin zasu sake wani taro nan kusa balle a gansu a kama, kallon A2Z takeyi wani zuciya yanaso ya faɗa mashi asalin wacece ita.

   "Zan baki kudi ki bar gari, koda ba Nigeria ba kawai ki tafi banaso ki shiga matsala, kin taimakeni sosai inaso nima na rama ma kura aniyarta"

   Shiru tayi ta rasa me zatace, batasan ko taji haushinsa bane kokuma ta gode masa. Anan ya tashi ya tafi drawer ɗinsa ya ɗauko wrap din yan dubu guda bakwai ya miƙa mata.

   "Gashi nasan babu yawa amma zai taimaka maki kafin ki samu tudun dafawa" yace mata. Da kai ta amsa wanda tuntuni batace ko ufan ba.

   Gira ya ɗaga da kafaɗarsa saiya tafi, ita bata bar wajen ba saida asuba, kallon karshe tayima wajen sosai saita tafi, Allahu mustan... Wannan kenan!

***

Koda Ainau ta murɗa kofa ta shiga sai gabanta ya faɗi, Daddy ta gani da xobaederh cikin haramtaccen yanayi. Da gudu ta koma shi kuma Yusuf kwala mata kari yakeyi.

   Dakin Lubna ta shiga saita garke kofa, "Ina bazai yiwu ba" ta rinka faɗa ma kanta.

   Kayan shi yayi maza ya saka domin yabita yayi mata bayani, a duniya idan za'a ce masa anama namiji fyaɗe bazai yarda ba. Wannan bashida maraba dashi.

   Wai yau shine wata yar ficika ta yaudare shi haka, "Kaidin mata yanada yawa" ya ayyana a ransa

   Ita kuma gogar babu abinda ya shalleta, zuwa tayi ta saka kayanta a tsanake, ko overall ɗin bata saka ba saidai ta riƙe a hannunta tana tafe kamar tayi abin arziki.

   Komawa ɗaki tayi murna fal ranta ta samu Yusuf, gashi kuma wani tururin sanshi daya sake mamayeta. Taji dadin kasancewa dashi kuma tana fatan ta sake samun irin haka.

   Ainau zaman dirshan tayi a kasa tanata rizga kuka, tun datake shekara kusan 13 bata taba ganin abu mai muni kamar yauba. Kuma abin mamaki ya kamata Mommy ɗinta ta lura kafin yanzu.

   "Ainau Dan Allah ki buɗe kofa muyi magana, ki bari kiji daga bakina" Yusuf yace daga kofa.

   Bata kulashi ba, ita tasan karya zai mata amma bazata saurare shiba, tana nan har Mommy ɗinta ta dawo ta fada mata komai.

   Suna haka ne Amra da Sadeeq aka samo rigima, dadin abin Ainau tayi masu shayi faɗan bread sukeyi. Anan Yusuf yaje domin yaji dasu.

   Komai ya chushe mashi, baisan inda zai ajiye tunani ba. A duniya bai taɓa jin kunyar abu ba kamar yadda Ainau ta ganshi a yau. Da ace ƙasa zai buɗe ya haɗiye shi ya fi mashi sauki da wannan ɗiban albarka data gani.

    Haka yaje yanata lallaba su, ita kuma Xobaederh an tsala wanka za'a sallah kamar na walha. Gwara ita, shikam yama mance da sallah.

    Ga kuma kanshi na mashi ciwon gaske, duniya a kwance zaiso ya huta ma ranshi ne, amma inaa. Baya tunanin nanda kwana biyu zai iya rantsawa.

     Lubna hankali ya tashi, da tana ma magana da Ainau, yanzu kam har Ainau bata samu. Haka ta tattara komatsan ta tabar birnin tarayya.

   Gabanta faduwa yaketa yi, tabbas anyi mutuwa ne yasa aketa ɓoye mata. "Innalillahi wa inna ilayhi rajiun" take faɗi

   Xobaederh ta fito murmushi ƙarara fuskanta, kanne mashi ido tayi. Shikam harara ya watsa mata.

    "Zakici ubanki wallahi" ya faɗa kasa kasa wanda ita kadai ta fahimta.

   Bata ko damu ba illa ƙarasawa wajen, zama tayi kafa daya kan daya saita fito da wayanta, cikin rashin kunya tana wani jijiga ta soma magana, "Yusuf ɗina" tace tana murmushi.

   Kamar garwashin wuta yaji abin cikin jikinshi, ya tsaneta kuma tsana mara misaltuwa.

    "Yusuf dina fushi kake dani? Dan Allah karka min haka"

    "Ki tattara kayanki ki tafi tun kafin Lubna ta dawo kici bura ubanki" yace a hasalce

   "Baby naga wajen zama, babu inda zani" tace tareda murguda masa baki tana masa gwalo

    "Bakisan waye niba, kawai kina jin labarina ne" yace a fusace. Dataga da gaske yakeyi saita shiga gallery. Nuna masa hotunan tayi tana murmushi.

    "Me kake tunanin cewa zai faru idan Anty Lubna taga wannan, infact kokuma Babana balle uwa uba na nuna a duniya. Kaidai siyasa saidai a TV" tace cikin ƙeta tareda yin Dab

    Kallonta yayi yana jimami, shi kuma nashi jarabawan kenan. Haduwa da wannan mara imani. Sam ya raina shekarunta.

   Ita tashi tayi tana tafiya ta wuce dinning domin ta haɗa ma kanta shayi mai uban kauri. Shi kuma bai sake magana ba, haka su Amra suka gama cin abinci saiya wuce daki.

    Anan yayi wanka shima yayi sallar wanda kamar na walha ne, gashi baisan mai Ainau zatayi ba. Fatan shi ya samu yayi mata magana kafin Lubna.

    Wajen 12 Lubna ta diro cikin gidan, su Khadija ranar banda bilayi a falo daga kan tiles zuwa kan kujera babu halin shiga ɗaki.

    Xobaederh tana ɗaki tanata barci, itama Ainau barci yayi gaba da ita a bakin kofa, Yusuf dai kansa kawai ciwo yake ya jingina a gefen gado.

   Abubuwa dayawa kawai ke masa yawo, daga sama yaji Muryan Lubna tana magana, ita kuma tana kokarin shiga ɗakinta amma ta kasa.

    "Yaushe kika dawo?" yace cikin tsoro.

    "Shigowana kenan" ta amsa tareda Ƙarasawa wajen sa. Ganin idonsa datayi yayi ja yasa mata tsoro.

    "Yusuf lafia? Meke damunka ? Wani bashida lafia ne?" ta jera masa

   Rike mata hannu yayi, "Lafia lau muje ki shiga daki"
  
  Ta tura sai taji a rufe, kallon Yusuf tayi sai tace, "Lafia ina Ainau?"

    "ki buga kila barci takeyi"

   Ainau tana barci taji Muryan Lubna daga sama, da sauri ta mike domin ta bude, me zata gani Daddy ɗinta ne  gefen wajen.

    "Ainau zo inaso na aikeki" yace mata.

    "Ina zuwa Daddy zan gaya ma Mommy abu ne"

    "ke bansan raini, zai aike ki shine kike so ki fada min abu. Uwaki dake da abinda zaki faɗa min. Bazan jiba" Lubna tace saita wuce ciki.

    Ran Ainau ƙuna yayi, amma fushi da Mommy dinta ba nata bane, wucewa tayi tabi sahun Yusuf har dakinsa.

   Sunyi shiru na kusan minti uku, "Gani Daddy" tace tana kuka.

   Da kyar ya iya cewa, "Kin tsane ni koh?"

   Bata amsa ba, kawai shesheka takeyi tana karkarwa, Daddy ɗinta yana burgeta sosai amma laifin sa na yau babba ne a zuciyar ta.

    "Nasan kin tsane ni, kuma kina jin haushina tareda abinda nayi. Kawai inaso kisan cewa wallahi banda laifi" yace harda guntun hawaye

    Shiru yayi ya rasa ta inda zai faɗa ma 13yrs child raping ɗinsa akayi, cikin kuka ta soma magana "Daddy karka damu, bazan faɗa ma Mommy ba because it's not my secret to tell. Kaida ita ne, amanar aurenta kaci ba nawa ba. Kawai ka roke gafara wajen Allah ne saboda a idonsa kayi"

   Idan Ainau ba yarsa bane, bazai yarda da shekarunta ba, jibe yanda take jero masa kalamai, "Daddy abu daya nakeso, banasan Anty ta cigaba da zama anan gidan"

   Tana faɗin haka saiga Lubna tazo, daga dukkan alamu taji abinda ya faru. "Akan wani dalili" lubna ta tambaya fuska a murtuke.

   Shiru sukayi su biyun suka rasa na cewa, "Akan wani dalili? Iye kuna jina kun bama banza ajiyarta"

    Ainau tana rawar baki tace, "Dama munyi faɗa ne da ita dazu..." bata gama magana ba Lubna ta haska mata mari.

     Nan Ainau ta rike fuska, "Lubna meye haka?" Yusuf yace, koda yake shima yana neman inda zai fada ma Ainau Xobaederh tana nan babu inda zata.

    Wayan charger na Flavour mai tsawo da kauri Lubna ta dauko, nanfa ta rinka auna ma Ainau. Ta lura yarinyar ta koya shika shikan rashin kunya, amma dole ta aika ma jiki manzansa wanda ke isar masa da sako

    A yau Ainau sai daji na mai danwake, watau yaji kenan.

   Yusuf yana shiga tsakani tana turjewa, gashi sai binta da zagi takeyi, "Dan ubanku daga tafiya kwana daya shi ne zaki ajiye tarbiyan ki, halan Zubaida tsaran wasan kine"

   Nanfa ta rinka zabga mata wanda da kyar Yusuf ya amsheta, dukda ba wata fara bace zakaga shedan duka jilinta domin ta wahala. Numfashi sama sama takeji tana kuka.

   Tunda take bata taba ganin tashin hankali irin wannan ba, tana hutawa sai Lubna kuma ta kai ma bakinta naushi, nanfa jini ya soma malala.

    "Lubna bakida hankali ne? Yarki zaki kashe?" Yusuf yace a fusace.

    "Yarinya tayi rashin kunya kada mu hukunta ta, ka ci gaba da kyale irin abin nan. Wata rana muna nan zata yanke ka da mari"

   Xobaederh hayaniya yana damunta kuma taji muryan Lubna, nan taje ta kashe kwarkwatan ido. Tana ganin Ainau ta tausaya mata dukda batasan laifin datayi ba saboda ta jibgo.

    "Xobaederh kiyi hakuri koba komai daga yau bazata sake maki rashin kunya ba" Lubna tace

   Murmushi kawai tayi bata gane kan zancen ba, "Kuma zaman nan gidan kina nan har auranki" ta ƙara cewa

   Murna fal ya mamaye Xobaederh, ta lura tanata samun komai cikin sauki. Koma wani munafunci Yusuf ya kulla taji dadinsa, kuma bature yayi karya da yace "You can't eat your cake and have it"  Wannan kenan!

   

   


#CodenameNimra






Fully DIMPLELATED
  

  

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top