10
Narrated Anas, The Prophet (pbuh) said, "The real patience is at the first stroke of a calamity."(Sahih Bukhari)
Mu'awiyah (May Allah be pleased with him) reported: The Messenger of Allah said, "When Allah wishes good for someone, He bestows upon him the understanding of Deen."[Al-Bukhari and Muslim].
******
After some weeks...
Kafan Sameer ya warke yanzu, bawai sosai ba saidai yana dogara sanda ya taka zuwa inda yakeso. Duk ɗawainiyan da Nimra tayi masa ta ƙara ƙima idonsa.
Koda aka sallame shi tareda ita sukaje gidansa domin tayi fixing komai yadda ya dace. Kuma da kanta ta siya crouches mai biyu wanda zai rinka ɗingisawa.
Sannan ta siyan mashi abinci ɗanye wanda za'a rinka dafa mashi tareda samu dattijuwa wanda zata rinka girki da gyaran gida.
Shi dai nashi baifi ya saka TV a gaba yayita kallon Super Sport ko ESPN ba, kokuma tashar waka kamar su MTV Base ko Soundcity yanayi yana busa sholisho wanda sana'arsa ne tareda recovery at the same time.
Yan kwanakin nan yakan dingisa yaje Guest house saboda zaman gida ya soma isarsa, koda yaje komai baya ganewa abinka na 'yan boko.
Nimra ta riga tayi cataloguing kowane file yadda ya dace kuma harkan campaign akeyi na yan makaranta ba wanda yaso yayi lokacin ba me jiɓanta yan daba da ta' adda.
Batun Ess kuwa abu yazo mashi ya tafi Australia domin ya ƙaro ilimi na kiwonsa. Faduwa yazo daidai da zama ne wajen Nimra, dukda bai faɗa mata sanda zai dawo ba, kawai tana kyautata zaton cewa kafin nan tayi ram dasu A2Z tama bar garin wajen witness protection.
Rabuwarta dashi yazo mata yadda take baƙuta, babu hargitsi ko tashen hankula.
Xobaederh with the X kam tura yakai bango, Yusuf yana azkar da kyau kuma cikin Ikon Allah bata samun galaba akansa. Duk wani farmaki data keso takai masa bata cin nasara.
Gashi saboda campaign yayi resigning wajen aiki domin yayi siyasa gadan gadan, yawan lokuta da yakeyi a gida yanzu yafina da.
Lubna da sauran yaran suna bala'in jin daɗin wannan abun, banda dai Ainau. A da chan Ainau da Xobaederh ko ba'a ce suna shiri ba za'a iya cewa akwai kyakkyawan fahimta tsakanin su.
Amma yanzu kam banda girma da mutunci babu abinda ke haɗa Ainau da ita.
Ita ba jahila bace kuma sau da dama ana masu wa'azi akan barin jikinka ma wani ya gani. Yanzu tana Js2 zata 3 kuma tuni sauran yan set dinta sun fara tara samari.
Dayake ma ita yar ficika ce ƙyau ƙyau kila itama da wani ya ƙyasata, so tasan yadda yan mata ke yi idan sunga mazajen da suke so.
Bawai tana taya Mommy ɗinta kishi bane, tana san idan za'a yi komai ayi shi cikin tsari. Bataso san duniya yakai mutum ga halaka.
Zina mugun abu ne dake gurɓanar da al'umma. Allah ya la'ance masu yinta kuma babu haufi Xobaederh niyyarta kenan. Tasan cewa za'ayi tashin duniyar tsuntsaye idan aka kawo maganar auren Xobaederh da babanta.
Saidai shime mafi alheri ma kowa, koba komai basu haifa shegu wanda za'a danganta da ita... Wannan kenan
***
Akwai wasu gang din kidnappers, sun dade suna cima Nigeria tuwo a kwarya saboda kwarewansu, abun nasu har dupty govnor sun Taba sacewa da kuma minister of Works wanda itama yar Kaduna ne.
Sufa kafin su sacee mutum sai sun tabbatar kudinsu xe fito. Saboda basa kisa, wannan bayama cikin slogan dinsu thou bama wanda ya Taba musu gardama.
Har yau an kasa kama su kuwa, babu yanda ba'ayi ba amma abin ya faskara. Yan sanda sunyi ittilafi cewa dole akwai wani acikinsu wanda yakeda kaifin basira yasa suke komai cikin dabara beyond expectations.
Hakane kam,cikin bin ciki da kwarewa irin na Abu Dhar an gano cewa sunar shugabansu bai wuce "Gamji" ba. Ana masa laƙabi da Gamji namijin zaki an buga an barka. Saidai ba asan waye wannan ba.
shine gang leader na kidnappers. tun a seconndry Gamji is very stubborn, mini terrorist kakaji kuma fuskanshi Sam yanayin salihai ne, shine shaye shaye, sata, dukan malamai, zuwa da bindiga aji, daga karshe aka koreshi tunda ya zama annoba.
A haka babanshi ya yanke shawara akan yakai shi makaranta da ake saka kangararru wanda suka buwaye bil'adam. Tofah anan angulu ta koma asalin gidanta na tsamiya domin shine silar sa na fara sace ɗan adam.
A yanxu xekai shekara biyar zuwa shida yana harkan. Mutane dayawa ne a karkashin shi harda wanda suka haifeshi, sannan jinsi da kabilu duk an gwamatsu. Gashi da Ka ganshi kaga yaro. Saidai dangerous, yana da basira sosai Kuma yana amfani da kwalkwawa shiyasa har yau an kasa kama shi.
Ko mutum daya baa Taba kamawa a group dinsu ba. Suna balain alfahari dashi, Yasa ma suka masa laƙabi da Gamji mazajen Dawa, duk haukar kura tana ganinku saita natsu, girman banza girman giwa saboda ka kace mata tsara... Wannan kenan
***
Yau babban rana ne ma 'Yan wadata family watau initiation day. Ranar da za'a shiga da sabbin masu wanka da jini.
Sunada Polygraph watau lie detector machine da suke amfani dashi wajen tambaya. Tanan suke gane masu karya da masu shirin ha' intan su.
Idan sun kamaka da jininka zasuyi wanka ranar, a yau za'a saka maza uku da mata biyar.
Wajen karfe takwas na safe, A2Z yana zaune a falonsa yana nishaɗi. Shayi yake sha a babban falonsa, dayake bai fita ba saboda amarya zainab ta haihu kuma sun saka mashi Izzudeenie.
Tun a masallaci da asuba akayi huɗuba inda yaro yaci sunarsa, shifa bashida matsala wajen saka ma yara suna. Ko a haka sunar Zainab ta zaɓa kuma shi ya saka, no questions asked.
Shi a ganinsa he has more children than he needs, gashi duk sunar danginsa wanda ya kamata yayi masu kara duk yayi. Musamman ma uwarshi mai Suna Hajara.
Mai jego tana daga gefensa suna zantawa, Hajia Zainab watau matarsa babba ta shigo. Asali ma ita takeda tuwo yau.
Zama tayi sukayi gaisuwan mutunci sannan ta karɓa Izz, dama pampers ake saka mashi duk ta hada tanayi, sannan kuma suna zantawa jefi jefi.
Mata mai sanin ya kamata, ko a haka idan Zainab ta fita ita mai riƙe mata shine, koda yake sau nawa kuma, kusan duka yaran gidan a hannunta suka tashi.
Gyara murya tayi tana magana ƙasa ƙasa, "Alhaji dama alfarma nakeso na tambaya wajenka"
Ajiye kofin shayi yayi wanda yake kurɓa saiya mayar da hankalinsa wajenta, "Uhm hum inaji"
"Dama yanzu da safen nan naga text message daga Unicef akan zasuyi 2 days workshop Abuja, shine nakeso da izinin ka sai naje"
Kallonta ya soma yi, ita kam zuciya sai bugu uku uku, addu'a takeyi Allah ya ɗaurata akanshi. Tunani yakeyi murna fal ransa, faduwa tazo mashi daidai da zama, tunda dama ɗakinta yake zai tafi initiation ɗinsa hankali kwance.
"Okay babu damuwa, Allah ya taimaka"
"Amin summa amin" Anty Zainab tace
"Amin" Hajia tace, sannan ta kara "Dama kuma ina so na tafi da Lubna, kaga wannan abun zai ƙara mana soyayyar mutane"
"Wallahi kinyi dabara, nima da bana jego aida na fita wallahi" Anty Zainab tace.
"Toh ki kira Lubna ɗin sai ta tambaya nata mijin, idan ya yarda sai ku tafi koh" A2Z yace.
Da Murna Ammi ta tashi harda kusan tuntube saboda zata tafi ɗaki ta ɗauko wayanta, wannan abu akwai manyan mata sosai wanda ya kamata su fara hulda dasu.... Wannan kenan!
***
Ana zaune ana kalaci a falo, pancake ne wanda yasha madara da syrup suke ɓasga. Sai kuma shayin Ahmad Tea lemon, so babu amfanin saka madara.
Abin kuma yazo daidai makon bara su Ainau sukayi hutu dasu Amra duka, su kuma yanzu Xobaederh kallo ya koma sama tunda babu shirin komawa School.
ASUU kungiyar kare hakkin malamai sun tafi yajin aikin wanda basu saka ranar dawowa ba, yanzu dai haka tana nan zaman daram dam dam.
Duk suna zaune a falon ana cin abinci, Ainau ce ta tashi ta zuba ma Yusuf Guda uku a plate saita saka masa grapes tareda syrup domin ya ƙayatu.
"Hajia Ainau iyayen kauɗi, mai miya da gudan shanu" Anty Lubna ta zolayeta tana murmushi.
"Mummy kice kema bakiji dadin ganin abin a haka ba?" tace ma Lubna.
"Banji ba" tace tana dariya.
"Anty Aynarh dan Allah nima kiyi min irin na Daddy" khadija tace, "Pleaseeee" ta sake maimaitawa.
Haka kuwa akayi, nan Ainau tayima kannenta tareda kanta, shidai Sadeeq sarkin wasa baima san wainar da ake toyawa ba tunda ya duƙufa yana buga Endless Run a iPad ɗin Lubna.
Xobaederh ce ta fito sanye da riga shara Shara irin light chiffon wanda zai baiyana kalar inner wears ɗinta. Bata saka vest ba tunda dama da gangan tayi.
Duk bra ɗinta acuci pink yana bayyanawa ta ciki, saita saka pencil skirt purple. Tana tafe ɗan dakyar kamar gurguwa saboda skirt ya matse ƙugu.
Amma "That's the point" take cewa, sannan tana tafe tana girgiza, bata saka kallabi ba tayi ponytail. Babu make up ɗinta na fama yau.
Sannu a hankali ta taka taje wajen, hankalinta yana kan Yusuf taga ko zai kalleta, amma ina sam baiyi ba. Itama Ainau daga ta kalle babanta saita kalle Anty ɗinta.
Duk gidan ita ce ta ɗago bakin zaren, wannan abin ya rikice mata. Sau da dama tana so ta gayama Mommy ɗinta tayi hankali da Xobaederh amma saita rasa me zata faɗa a takaice.
"Allahu mustan" take yawan faɗi.
Kiiiiiiiii Xobaederh ta fige kujera kamar zata cire masu kunnen, har saida Amra sarkin tsoro ta fashe da kuka kuma cikin reflex lubna ta zabga mata duka.
Xobaederh tayi da gangan ne ko Yusuf zai kalleta amma yayi burus da ita. Zama tayi sannan tace, "Anty Lubna ina kwana, ya kwana su Ainau"
"Lafia lau wallahi, ya kike?" Lubna tace da fara'anta. Ta lura yanzu nasu yazo ɗaya da xobaederh.
"Alhamdulillahi" kallon Yusuf tayi da murmushi tareda canza murya, "Uncle Yusuf ina kwana?"
"Lafia" ya amsa a dikilce
"Ina kwana Anty Xobaederh" Ainau tace, "Uhm" ta amsa.
Sunyi shiru bakajin motsin komai saina cokali, Xobaederh ne ta katse, "Uncle Yusuf yaushe ne IPhone 8 zai fito?"
"Bazan iya sani ba tunda bana aiki a wajen" ya gwasaleta. Duk abinda yake wakana a idon Lubna. Ta lura Xobaederh tana kokari da Yusuf.
Ta rasa inda ya samo tsautsauran ra'ayi, abin yana damunta kuma ba kaɗan ba. Bata san wulakanci tunda mutum ba abin a wulakanta bane.
Wayanta ne ya soma ruri, sunar Hajia Zainab ta gani. Nan da fara'a ta ɗauka. Anan ta sanar mata cewa akwai workshop na Unicef a Abuja kuma tanaso taje, tun kafin ta tambaya Yusuf ta amsa gayyatan.
"Daddyn mu zani Abuja da Hajia Zainab workshop, please ka barni naje" ta tambaya
"okay babu damuwa" saida ya amsa ya tuna baisan ranar dawowa ba. Da sauri ya zare ido sannan yace "Dawowan yaushe?"
"Gobe ne Daddyn mu, please bazaka ma lura bana nanba" ta jadadda masa.
Nan ranshi yayi mugun ɓaci, yanzu za'a barshi da wancan ƙedarar. Ainau ce tayi charap tace, "Saimu kwana wajen granny(Maman Xobaederh)"
"Hakan yayi kyau ku tafi duka kowa da kowa" Yusuf yace da murnar sa.
"Ah ah muyi zaman mu anan mana, kar muje mu takura ma Mommy, kunsan ance tanada hawan jini kwanaki" Xobaederh tace
"Eh hakane fah, kuyi zaman ku anan" Lubna tace tareda miƙewa zuwa ɗakinta domin ta haɗa kayanta.
***
Xobaederh haba haba da Lubna takeyi, ita ta tayata ma ninke kaya tareda ɗaukan mata extra dress incase zasu sake kwana. Karamcin yasaka Lubna jin daɗi.
Saida ta bata 2k domin tayi amfani dashi, anan ta gode mata domin har booth takai mata akwati. Tana tafe tana ɗaga mata hannu harta bar haraban gidan.
Direct Chemist Xobaederh ta wuce domin ta siya kayan maye.
"Wehdone Anty Dan Allah bana samun barci isarshe shine nake neman abubuwan da zai sakani. I think inada insomnia"
Nan mai shago ta takarta mata magani kala kala da yadda zata shasu, da kudin Lubna ta biya saita fita.
Wani shago taje na provision ta siya 5 alive wanda zata haɗa mashi dashi. Balle dama Uncle Yusuf yana san abin.
"Yau za'ayi bidiri" ta faɗa tana fito... Haka ta faɗa sanda ta koma ɗakinta.
Normal activities ɗinta tayi, da rana ta dafa masu spaghetti mai hanta da vegetables, sannan duk yaran tayi faram faram dasu bata wulakanta ba.
Yau tanajin kanta kamar ma itace uwarsu kuma Yusuf ne angonta. Harta scolar tayi nasu kayan Yusuf a washing machine dana Amra dana Sadeeq. Banda dai na Lubna.
Su kuma su Anty Lubna ana birnin tarayya, tasan cewa tabar gidanta in good hands, da chan Ainau ke komai amma yanzu zuwan Xobaederh zata rage mata aikin, tabbas ita alheri ce.
***
Wajen Maghrib Lubna tace ma Yusuf ya dawo gida domin kada abar yara su kaɗai, sannan kuma da kanta wajen 7:30pm ta kira tayi magana da kowa harta Xobaederh.
Ba'a dafa dinner ba, Yusuf ya siyan masu gurguwan kan hanya watau kaza, sannan kuma an haɗa da shawarma na classy burgers.
Ya siyan masu Sadeeq da Amra Ribena na gora, sai Khadija aka siyan mata Cway. Ainau kuma dama Chi exotic ne sai Smoove ma Xobaederh, as expected 5 alive ma kanshi.
Da sauri Xobaederh ta amsa kayan ta kai kitchen domin ta saka masu a plate tareda rabawa, sannan kuma ta faki ido ta canza zuwa wanda ta siya ta watsa magani suka narke.
Murna fal ranta, babu wanda yasan da abinda ke ranta sai Allah, yau hakkonta zai cinma ruwa. Zata samu Yusuf hankali kwance.
Duk noke noken dayake yi tasan duk barazana ne, tana fara sarrafa shi zai bari bori ya hau.
Sunata cin abinci Sunata hira, ita batayi masa shishigi ba saboda anjima sai yanda taga dama.
Yara sunyi barci ta taimaka masa sunyi fitsari tareda kwantar dasu, itama Xobaederh sallama tayi ta koma ɗaki. Ainau da taga komai ya tafi daidai saita tafi itama.
Shi dai ya lura idonsa yayi nauyi ga barci na rashin dalili, haka dai ya kashe kayan kallon ya tafi ɗakinsa, baiyi tunanin saka key ba tunda ba ɗabi'ansa bane.
Tanajin an kashe wuta ta daka tsalle, bayi ta shiga ta feshe wanka. Sannan taje ta shafa maiyuka masu saka jiki santsi da taushi.
Wannan farin night gown daya fara ganinta a ciki ta dauko, sakawa tayi saita kwance gashiinta ya zuba mata a baya, sannan saita fesa turare.
Chewing-gum na orbit ta watsa biyu a baki saita fita, wani idan ya ganta kamar Anty Lubna ne zata dakin Yusuf.
Tura kofa tayi ta shiga, yanata barci baima san anayi ba. Nan ta kunna torchlight din wayanta ta kare mashi kallo, wani sanshi ke shigarta ba kadan ba.
Anan ma ta ɗaukeshi hotuna guda hudu yana barci, sannan sai ta hau kan gadon.
Cikin barci yaji ana shafa shi, sam ya mance da wata Xobaederh sai Lubna. Balle kuma jikinsa duk ya mutu gashi dama suna yanayi.
Anan ya biye ma Xobaederh, bata hanashi illa yi kamar matarsa na sunna. A yau tasamu Yusuf a matsayin ɗa namiji la'ada waje.
Koda wasa batayi dana sanin abinda tayi ba, bataga rashin kamancin abinda tayi ba. Illa farin ciki, half loaf is better than none ta jaddada ma kanta. Koda yake abinda yaja ma Xobaederh wannan mugun ɗabi'a baifi hulda da abokan banza ba.
Yusuf ne ɗa namiji data fara sani amma kuma idanta babu abinda bai gani ba. Ta kasance mace ce mai kallon hotunan da bidiyo na batsa, daga ita har kawayenta ba abin wuya bane dan sun kalla.
Da sun karba wayan mutum sunga irin hoton video ɗin basa damuwa su kunna suna kallon mace da namiji cikin haramtaccen yanayi. Yasa ta fitsare ma Yusuf tun fil azal.
A hakan ta samu tayi selfie bila a dadin wanda tuni barcin yafi karfinsa. Hotunan banza hoton ayi tirda shi tayi masu tare suna kwance. Irin dai yadda take gani a wayar wasu.
Bashi ya farkaba sai 8:30am, Xobaederh tana makale dashi sunata sharban barci. Batada buri daya wuce Lubna taganta a wannan yanayi koba komai ta kwashe bakin ciki zuciya ya buga ta mutu tabar mata shi.
Ainau koda taje ɗakin Xobaederh bata ganta ba sai tayi tsammanin tana bayi ne. Kitchen ta wuce domin tayi su wanke wanke tareda ɗaura ruwan karin kumallo.
Da Yusuf ya farka ya soma magana a gajiye, "Lubna yaushe kike dawo"
Anan Xobaederh ta farka tana murmushi, da sauri ya tureta yana kokarin tashi. Saiya lura da yanayinsa.
Haska mata mari yayi cikin zafin nama, "Ke dan ubanki me kika min? Uban me kika min?" saiya shaketa.
Kokarin kwace kanta tayi saita ce, "me nayi maka kokuma me mukayi. Karka raina min hankali Mallam"
Kawai sakinta yayi ya dafa kansa, tafasa kawai yakeyi ya rasa inda zai saita tunanin sa. Tabbas Xobaederh kanwar shedan ce, laifin meya mata da zata zalunce shi haka?
Ita kuma ƙedarar mirsisis tayi ta soma saka kayanta, kukan munafunci ta somayi, "Bansan meyasa kake denying komai ba, ni bana jin haushin kasancewa dakai shine kai zaka min haka, jiya fah har cewa kayi kanaso na" ta faɗa cikin shesheka.
Ainau tana tafe sannu a hankali zata ɗakin Yusuf, sai wayanta ya soma ruri. Fasawa tayi domin taga waye. Anan taga Lubna ne, cikin Azama ta kara a kunneta.
"Wai ina Daddyn dinki ne da Antyn ki duk basa daukar wayansu? Halan lafia ?" lubna tace damuwa fal ranta
"Mommy banga Daddy yauba, amma Anty tana bayi dazu. Bari naje na duba ɗakinsa yanzu"
Tafiya Ainau ke keyi, saidai kuma kafin takai kofan ɗakin gabanta yaji mummunan faɗuwa, hannu yana karkarwa ta murɗa. Mezata gani?????
#CodeNameNimra
Fully DIMPLELATED
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top