1
'Uthman bin 'Affan (May Allah be pleased with him) reported: The Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "The best amongst you is the one who learns the Qur'an and teaches it."[Al-Bukhari].
It was narrated from 'Abdullah bin 'Amr that A man asked the Messenger of Allah [SAW]: "What quality of Islam is best?" He said: "To feed (the poor) and to say the Salam to whomever one knows and whomever one does not know." (Sahih)
******
Taken 'Bariki' bai wuce a bishi da garin kazo nazo ba, garin da akwai chuɗanya na al'adu da kuma addinai daban daban.
Kuma kusan kowane bariki ana samun ɗabi'u kamar su Cin hanci da rashawa, sace sace, shaye shaye, safaran mutane, damfara, tsaface tsaface, Cha Cha, kawaliyanci dadai sauran abubuwan da suka addabe dan adam suka hana shi sakat yayi barci ƙofa a bude.
Kaduna garin gwamna, centre of learning, gari mai mata mai naira koda meka zo an fika. Idan kudi kake taƙama dashi akwai wanda suka ninka tunanin ka. Idan kuma kyau ne akwai hunun ayn na duniya, in kuma karya ne ko iya bariki kazo wajen. Idan kuma addini ko karatu ne suma sun tara.
Inda ka tsaya anan wani ya ɗaura nasa, babban garine mai girman gari da kuma yawan al'umma. Babban goro kenan sai magogin ƙarfe.
Bariki kake ji wai lahiran makwaiɗata, kazo kana dariya ka tafi kana kuka. Wasu sukan ce Bariki alalen gero, idan baka iyaba saita kwaɓe maka. Kowa dai da yanda ya ɗauki nasa fassaran. Wasu ma sukance daga duniya sai Kaduna...
***
"Ɗus ɗus ɗus" takeji yana fita daga bayi, babu mamaki famfo ne bata rufe da kyau ba yake ɗiga. Wannan ɗigan da yake yi ba ƙaramin tada mata hankali yake ba.
Duk ɗigan ruwan kamar wani sara ne ake mata akai, gashi bata wani samu isarshen barci ba. Idanunta sunyi mitsil mitsil kamar basu wajen. Da jan jiki tana tangal tangal harda tuntuɓe ta ƙarasa bayin ta rufe da kyau.
Koda ta koma ɗaki bata samu ta rufe kanta da bargo ba saboda tsabaragen gajiya, haka tayi barci abinta.
Sanda ta sake farkawa daga barci. karfe 5'00am agogon bango ya nuna. Miƙa tayi a hankali sannan ta soma addu'a.
"Alhamdu lillaahil-lathee 'ahyaanaa ba'da maa 'amaatanaa wa'ilayhin-nushoor."
A yanayin barci ta miƙe tsaye tana tafe tareda ɗan tangal tangal saboda rashin isarshen barci. Banɗaki ta shiga ta kintsa sosai na wanka tareda ɗaura alwala.
Wani hijab dake ninke akan akwatunan ta ne ta ɗauko tareda darduma, anan ta shimfiɗa saita kabbara sallah. Rakatanil fijr tayi sannan ta soma azkar a tsanake, bayan nan saita kabbara sallar asuba.
Gyara gidan tayi tsaf komai ya zauna inda ya dace, sannan tabi gidan ta turaren wuta. Ita ma'abociyar tsabta ce kuma shine babban tambarinta. Bayan nan ta wuce kitchen domin ta dafa breakfast sannan shima ta kimsta.
Bata wasa da karin kumallo, "Breakfast is the most important meal" ta faɗa a fili sannan ta ɗaura ma kanta Indomie. Ta hadashi da kwai ɗaya saita saka masa su vegetables.
A kitchen ɗin taci cikin tukunyar sannan ta wanke shima.
Bayan awa ɗaya....
Tafe take sanye da takalmin hightop baki mai suede, da full confidence kana ganinta kasan cewa tasan makamin aikinta. Farin chiffon top ta saka mai kananan furanni sannan kuma an kawata wuyan da duwatsu masu kyan gani.
Saita haɗa da dogon bakin skirt tareda blazer baki, mutanen dake wajen duk kusan haka suma sukayi shiga. Shigar cooperate kamar yanda bature ya faɗa abinsa, Saidai maza su wando ne da kuma shirt.
Karfe takwas da minti biyu daidai agogon bango dake manne a Police Headquarters na independent way ya nuna. Mutane ne mazansu da matansu kowa yana harkan gabansa
Babban conference hall ne Oval shape, saidai kuma mutanen dake wajen basu su wuce goma sha biyar ba. Wajen yayi shiru kowa yana abinda yake gabansa.
Wasu daga cikin suna danna wayan hannunsu, wasu kuma Ipad. Kadan kuma daga ciki suna duba manual ɗin dake wajen.
Ita kuma tana sake duba presentation ɗin datayi jiya a cikin PC ɗinta. Komai sabo yake dawo mata. Ta tuna yanda aketa binta da tafi da murmushi. Lallai ka zama zakaran gwajin dafi yanada dadi.
"sorry I'm late" wani dattijo cikin kayan yan sanda na kalar ruwan bula da kuma baƙar wando yace, kai tsaye wajen allon rubutu yaje saiya soma.
Anan yayi masu bayani akan darusan ranar tareda rufe seminar ɗin na 2017. Ɗakin ya kunsa kwararrun mutane ko ace Exquisite mutane wanda sunyi fintinkau a discipline ɗinsu. Kuma duk sunzo Kaduna ne daga jihohi daban daban.
Ballot box aka fito dashi wanda suka zaɓa inda zasuyi aikinsu, an basu sabon suna da kuma hannun jari wanda zaiyi matching new identity ɗinsu. Idan kuma aikin gwamnati ne zaije dashi sai a samo masu.
Ita dai ta zaba suna NIMRA KHALEEL sunar labarawa yanada dadi gashi it's easy kowa zai iya faɗi.
Wannan sabon Department aka bude cikin Police wanda saika samu deep clearance kafin kasan dashi. Infact bama kowa yasan da zamansa saboda koda kayi searching cikin database ɗinsu bazaka gani ba.
Sunarsa Nigerian Agency of Mavens Intelligence Research NAMIR, sanda Nimra taje submitting form ɗinta na sabon suna, sai supervisor dinsu yayi murmushi, koda yaushe saita nuna ita daban ce. Gashi duk wajen tafi kowa ƙuruciya.
yanzu Nimra zai iya zama Nigeria Intelligence of Mavens Research Agency. "Bravo" Yace mata saiya daga mata gira. Ita kam murmushi tayi sannan ta wuce. Tunda magana bai wani dameta ba saidai idan tana cikin character na Undercover.
Case ɗin da aka basu na tsoffin wanda suka addabe mutane ne, daga political corruption, sata, Mafia, Drug abuse, Human Trafficking etc gashi kuma polisawa sunata fafatawa amma sun kasa samun bakin zaren.
Kuma zai yiwu mutane wajen biyu ko uku koma fiye da haka daga divisions daban daban na jahar Kaduna suma suna kan case ɗin
Yasa aka gargaɗe su akan kada su yarda da kowa, every man for himself suyi abin cikin sirri ne har sai sun samo right target ɗinsu ko waninsa.... Wannan kenan?
***
3 months later...
8:00pm ne a A2Z Guest house, gidan hutawa ne na Alhaji Aminu Zailani kokuma A2Z kamar yanda aka fi saninsa dashi, tsohon dan siyasa ne a jihar Kaduna.
A falon mai ɗan girma kokuma ace shine wajen tare baƙi suke zaune, za'a iya kiransa da Common room ɗin wajen. Daga wajen bango wani wakeken hoto ne daga sama har ƙasa an maƙala na A2Z yana washe baki.
Sannan kuma akwai couch da kujerun roba birjik wasu an haɗa har guda biyu ma a waje ɗaya, a tsakiyar falon centre table ke wajen inda namane birjik cinyar rago wanda aka gasa sunaci.
Ga kuma fruits dayawa harsu Tufa da inibi a wajen, sannan sai katan ɗin Maltina da kuma roban ruwa suna sha. Su huɗu ke zaune a ɗakin kuma duk sun zauna kan kujera sai guda daya dake zaune kan sallaya yanata zuba.
"Ai bana Alhaji Adamu ya faɗa gwata! Ai ƙarya yake yaja dakai wallahi a garin kaduna" Yace tareda tura nama cikin bakinsa.
Shikam A2Z yaji daɗin abinda aka faɗa, nan ya soma karka ɗa kafansa yana wani mazurai, "Toh dama banda abinka Haladu aini na kece masa nesa ba kusa ba, kwarankwatsa tun Abuja yana Lagos"
"Sosai ma kuwa, naji labarin yayi oda na kantena(Container) guda 8 daga chena(China) an riƙe shegu" Haladu yace yana babbaka dariya.
Suma sauran biyu dariyar suka soma, dama indai Haladu yana wajen an rinka cin dariya kenan, qanshin gari kake gani mai shinshina kowane sabon abu daya faru. Kawai dai ka bashi abinci da ruwan sanyi.
Architect Yusuf Jere (Arc YJ) tareda Sameer Cizo. Suna zaune suma suna ci. Saida sukayi nat sannan A2Z ya gyara zama da kuma murya.
"Dama inaso ka mara min baya ne ka zama deputy ɗina a zaɓen dake gabatowa" ya faɗa tareda kallon Arc Yusuf
Fuskan Arc cikeda mamaki sanda A2Z yayi magana, saidai kuma yasan A2Z ba abokin wasan shi bane ta wajen kudi da shekaru. Kowa yasan yanada mutunci da kuma dattako.
"Zan iya zuwa nayi shawara?" yace a sanyaye cikin ladabi
"Sosai ma kuwa, shawara yanada bala'in amfani sabida abune wanda zai canza mana rayuwa da mutanen kaduna baki daya"
"Yauwa nagode Alhaji, bari sai mun sake haɗuwa"
Anan Arc Yusuf Jere ya miƙe tsaye tareda basu hannun, juyawa yayi ya nufa hanyar kofa.
A wajen shigowa suka ci karo da wata yarinya, nan suka sakan ma juna murmushi sai kowa ya kama gabansa... Wannan kenan!!!
DIMPLΣS
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top