Twenty-two



Yahya related to me from Malik from Sumayy, the mawla of Abu Bakr ibn Abd ar-Rahman, from Abu Hurayra that the Messenger of Allah, may Allah bless him and grant him peace, said, "If people knew what was in the adhan and the first row of the prayer and could only draw lots for it, they would draw lots. And if they knew what was in doing dhuhr early, they would race each other to it. And if they knew what was in Isha and subh they will go to them even if they had to crawl”

**********


Cyprus

Tsuru tsuru yayi ya rasa meke masa dadi, baice komai illa kallon kasa cikin nadama. Tunanin shi bai wuce yanda suka san inda yake ba bcs yayi covering tracks ɗinshi daidai gwargwado.

Da Kai nakeyi, abinda kayi ka kyauta kenan?” IG ya faɗa. Daga Idonshi yayi suka haɗa da mahaifinsa amma saiya mayar kasa bcs kunyar kansa yakeyi.
Nifa bawai nazo nace maka ka bini bane, kawai nazo naga lafianka ne. Tunda dai bakasan ka zauna damu, saboda mahaifiyarka ta samu natsuwa akan ba saceka akayi ba kuma ba mutuwa kayi ba.” Yana kaiwa nan saiya juya ya tafi.

Da sauri Khattab yaje gaban Daddyn sa yana rok’on sa hannu biyu, IG ko kallonsa baiyi ba ya ture shi tareda cigaba da tafiya.

“Dan Allah Daddy kayi hakuri, wallahi k’uruciya ne. Please karka kyale ni.... Im really sorry”
Sekeke IG ya kalli Khattab tareda kwafa, “Kuruciya koh? Ka raina kanka bani ba. Wannan tozarci dame yayi kama? Wai ace dan ɓata suna shi ne kayi gaba abinka saboda ka tozarta ni akan ban isa ba”

Kaga duk bincike ɗinnan danakeyi Bawai saboda kai nayi ba, kaji ni da kyau saboda Matata nakeyi bcs dukta birkice kullum kuka. Mutane suka zauna babu yara balle ni don kace ka gaji dani

IG yake magana muryanshi zallan ɓacin rai ke tashi, shi kuma Khattab yana ɗuk’e a kasa yana kuka tareda rike masa k’afa. Haka yayita rok’on sa Shi kuma IG yayita sababi yana mita, don kansa yayi shiru saboda Khattab yayi alkawarin binsa gida.

IG a gidan Khattab suka yada zango shida Boys ɗinsa, shi ya kwana a ɗakin Khattab while boys ɗinsa su biyu tareda Khattab suka kwana a falo.

Next day around 10am.......


Khattab ne a airport tareda mahaifinsa tareda escorts suna jiran lokacin tashin su saboda shi IG baya san garin at all.

Saidai Khattab ya kasa sukuni,tun jiya bai rutsa ba, tunani ɗaya ya sark’e masa zuciya. Gashi kuma Daddy dinsa bai sake masa fuska ba balle ya tambaye shi anything about her.

Kawai shiru yayi zuciyar sa yana masa kuna, fatan shi ɗaya ace tana sanshi har yanzu kamar yadda yake son ta.

Amma cikas ɗinshi ɗaya yayanta amma zai nema yanda zaiyi maganinshi. Haka yaketa tunani harya shiga jirgi suka ɗaga zuwa gida.
Jirgin su ya sauka a Murtala Muhammad Airport dake Lagos. Daga nan wani jirgin suka shiga direct sai Bauchin Yakubu. Suna fitowa daga jirgi motoci na tarbasu yana jiransu kuma harda Lili.

Tana ganin shi ta ruga da gudu tareda shigewa cikin jikinsa, babu kunyar idanu balle tsoron Allah.

Yaya Khattab I miss you so much, please don’t ever leave me again” ta faɗa tana wani k’ank’ameshi. A hankali ya zame jikinsa tareda shiga mota ya barta a wajen.

Bata ko damuba illa binsa cikin motar, dayaga ta shiga ɓangaren baya inda yake wani haushi ya kamashi yana dana sanin abinda yasa bai shiga gaba ba.

Kara hawa kan kafadarsa tayi ta kwanta, harda bazai kulata ba sai kuma wani zuciya ya raya masa gwara ya kwaɓeta.

Ke! Wai Meye haka? Baki lura tafiya nayi ba kuma duk na gajiya faɗa a hasalce. A hankali ta ɗago tana shagwaba kamar zatayi kukaHaba yaya nayi missn ɗinka ne, baka san irin kukan danayi sanadiyar rashin ka ba”

Sai kuma ta fara matse karamin kwalla ta cigabada maganaYaya ni na gaji Wallahi, kawai gwara ayi mana aure haka kowa ma huta

Wani haushine ya turnuke shi, gyara zama yayi tareda ingijeta. “Ashe bakida hankali! Na dawo ko hutawa banyi ba, ko gida bankai ba kin kawo min shirmekwafa yayi ya soma kallon window

Yaya Maganar auren mu ne shirme? Ka daina so na ne?” ta watso mashi tambaya.

Juyawa yayi ya kalleta saiya watsar, bashida locacinta balle na cha chan baki da ita.

Sun isa cikin gidansu mutane cike sunzo ganin shi kuma duk yan uwa da abokan arziki ne, duk inda ya ratsa abu ɗaya suke tseguntawa.

Laaa ga Khattab, ya canza kamar bashi ba” Baiko kula suba ya wuce falon Mommy ɗinsa, zaune take kuma gefenta Maman Lili ne.

Har kasa ya duka ya gaishe su, Mommy muryanta duk kuka ta amsa, ita kuma Maman Lili kallon rainin arziki tayi ta watsar tareda amsawa à wulakance. Inda sabo yaci ace ya saba da halinta bcs halinta Lili tayi biyo na empty vessel kyau babu hali.

Rike hannun mahaifiyarsa yayi yana murzawa a hankali, magana ya somayi cikin natsuwa. “Mommy ki yafe min, nasan cewa na sakaki cikin zulumi da fargaba

Bata amsa shiba illa kukanta a hankali, haka ya rinka mata magana sai daga baya ta ɗago tayi murmushi tareda cewa, “Allah ya yafe mana baki daya

Zuwa yayi sai yayi patting bayanta sannan yace, “bari naje na kimtsako kallon Maman Lili baiyi ba ya wuce abinsa dama basa shiri.

Yana shiga ɗaki sai yaga Lili kwance tana jiransa, a fusace yace, “Ke Meye haka? Oya oya zo ki fita kafin raina ya baci

“Ni ban san me nayi maka ba duk ka tsanenisaita fashe da kuka.
Indawani ya yi kukan zaiyi wani iri amma yanzu kamar tana busa sarewa a kunnen bebe ne. Zuwa yayi wajen data ke ya finciketa kamar yar tsana har waje sannan ya banko kofar ɗakinsa.

“Damn!” ya faɗa tareda daura hannu akan waist yana tunanin irin rashin kamun kai nata. Ita kuma as expected ta tsaya tana buga kofar tareda watsa kalamai na rashin kunya.

Mommy ne tazo ta taka mata birki tareda Faɗi, “Meye haka kikeyi kamar wanda zamu kai turu? Gwara ki natsu kisan me kikeyi, shifa namiji yana son space ɗinshi baya son takura. Idan yace ki tafi ai saiki tafi tunda ba’a ma mutum dole. Ace ko 12hrs da dawowa baiyi ba kin soma tada mashi hankali. Nifa kada kisa yarona ya kara gudu

Tana kaiwa nan saita bar Lili à wajen à ruɗe, shi kuma yana daga ɗaki yana jin su.

Woooow! Allah ya barmin ke Mommy” ya faɗa saiya shiga bayi.



*******

Bayan 3 days....

Haka rayuwa ya cigaba da kasance ma Naufal da Fadeela cikin tsantsar so da kulawa. Koda yaushe ana tare ana hira, girki ko cin abinci.

Sam Sam yaki zuwa aiki yabarma Aminu komai, abu ɗaya ke fitar dashi daga cikin gidan watau sallah. Sai kuma sau ɗaya dayaje stores domin ya siyo masu kayan abinci da ba’a rasa ba.

Tun jiya Aminu ke kiran Naufal akan ana bukatarsa cikin office bcs su Mr Sutter sunyi zuwan bazata. Ranshi yayi mumunan baci bcs baya son abinda zai nisance shida da ita.

Tun da daddare yaketa mita, “Haba banda bakin ciki karara wannan dame yayi kama? Shikenan ba’a bari mutum ya zauna da matarsa lafiya

Fadeela na daga kwance tana murmushin k’eta, sai kawai ya ganta. Daga gira yayi kafin yace, “Au you will not sympathise with me shine kike min dariya koh

“No Other half ba haka baneba, I want to be with you but kasan cewa nima zani school”

Saita mike daga kwance tana kokarin tashi, “Bari naje na haɗa mana breakfast kafin ka makara

Harta kai wajen kofa saita ji muryanshi “A me zaki

“A me na saba zuwa? Motar haya mana” ta amsa bata ko juya ba.

Shiru yayi yana jin haushin kanshi akan duk abubuwan dayayi mata, bcs ya kaskantar da ita ba kadan ba. Dadin abin bata dauki duniya da zafi ba.

Ita kuma taje kitchen ta fara fere masu doya zatayi yam balls, tagama ta daura akan gas kenan sai kawai taji ya riketa ta baya. Bata ce komai ba shima haka kawai shiru sukayi for some minutes.

Itace tayi masa magana cikin raɗa “Other half”

Bai amsata ba illa kara kamkameta kamar wani zai kwace mashi ita.

“Other half please kasan zamu fita yau koh?”

“Na sani mana” Daga nan saiya saketa.

“Okay wat can I help you wit?” ya tambayeta

Murmushi tayi tareda jan masa kumatu cikin wasa saita ce, “Dont worry dear, na hutarshe ka”

Lagwaɓe kai yayi waishi bai yarda ba, da sauri ta rike masa hannu sannan ta matsa dab dashi har suna shakar numfashin juna.

Bana son ka wahala ne, but If you insist dauko min sardine a cikin shelf. Daga nan saika fasa min kwai

Ita kuma ta dauko kayan miya tayi jajjage saboda yafi tunda babu ruwa ko kadan. Haka suka rinka abinsu gwanin ban sha’awa.

Koda doyan ya nuna tare sukayi mulmula. Dama tun yau yake mata salon shagwaba kala kala, indai wannan ne ta saba da halinshi dis past few days Kuma yana burgeta ainun.

Latte ta haɗa mashi ita kuma ta haɗa ma kanta cappuccino. Zaune take akan kujera dab dashi tana bashi. Yaci sosai a matsayinshi na ma’abocin doya.

Daga nan daki sukaje ya shiga wanka ita tana wajen drawer ɗinshi zata ciro masa kaya. Blue suit ta dauko mashi tareda grey tie da kuma farin riga.

Bayan ya gama shiri ita tayi mashi knotting tie, to his surprise ta kuma iya sosai. Ta lura yana mamaki saita ce, “nike ma Daddy knotting idan zai fita

Daga gira yayi alaman ya gane, ita ta rike masa jakarsa sannan tana makale dashi har suka kai kofar falo, bata rakashi mota ba saboda kayan jikinta bai kyautu maigadi ya ganta.

Yatsunta biyu ta saka akan bakinta sannan ta daura akan nasa. Da sauri ta koma cikin gida tana dariya bcs tasan me tayi. Shikuma cikin dariya yaceZanyi maganin ki ai

Saiya juya ya tafi, yana cikin tafiya yaji maganar ta, “eh din” juyawa yayi sai ya ganta a window tana murguɗa masa baki. Dariya yayi yana nuna mata yatsa saiya tafi bcs idan ya biye mata babu inda za shi.

Ita kuma ɗakinsa taje zata gyara, rigan daya cire ta dauka ta rungume, ji takeyi kamar shine ke wajen. Kawai ta rufe idonta tana shakar kamshin.

Tunawa tayi zata fita saita tashi da sauri ta gama aikinta, har lunch saida tayi kafin ta bar gidan.

Ta rufe kofa tareda faɗin
Bismillaahi, tawakkaltu 'alallaahi, wa laa hawla wa laa quwwataillaa billaah.”
tafe tana nishaɗi bcs she is in her perfect neighborhood, with her perfect husband, tanayin rayuwar data ke sha’awa.... Wat could possibly go wrong?




#NiDaDiyata

  


  *All Rights Reserved*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top