Twenty-seven


On the authority of Al-Numan bin Basheer, who said : I heared the messenger of Allah say : "That which is lawful is plain and that which is unlawful is plain and between the two of them are doubtful matters about which not many people know. Thus he who avoids doubtful matters clears himself in regard to his religion and his honor, but he who falls into doubtful matters falls into that which is unlawful, like the shepherd who pastures around a sanctuary, all but grazing therein. Truly every king has a sanctuary, and truly Allah's sanctuary is His prohibitions. Truly in the body there is a morsel of flesh which, if it be whole, all the body is whole and which, if it be diseased, all of it is diseased. Truly it is the heart." Narrated by Bukhari and Muslim.



*********




Yasmeenah Yusuf(YY) kokuma Meenah yanda friends ɗinta suke ce mata. Ita bafillatana ce yar asalin garin Shandam dake jihar Jos.

Mahaifinta Marigayi Alhaji Yusuf ya rasu tareda matarsa Hajia Jidda à car accident tun tana shekara biyar. Daga nan saita koma zama wajen wan mahaifinta Alhaji Abdulrahman.

Shi yana zaune locacin a Las Vegas da matarshi Hajia Hindu tareda yaransa guda biyar. Babban yaronsu mai suna Huzaifah yanada shekaru 28, sai Hilal 27yrs, Haisam yanada 25yrs, Hashim 23yrs, sai dan auta 20 yrs. Ita kuma Yasmeenah tanada shekaru 22 a duniya.

Shekarar daya gabata suka dawo Nigeria sanadiyar Daddy yayi retire a aikinsa. Yara rainan turai Sam basuda tarbiyya kwata kwata, gaba d'ayansu karka cire kowa duk jakai ne.

Dama dama Hashim, shi duk rinsti yana sallah kuma bai kwana da mace, shisha ne dasu codine. Ko auta Habeeb yana shan Wiwi, balle ayi maganar gwaska Hilal.

Shi wannan tsakanin shi da sallah sai ranar Eid, shima saboda ana taruwa aje baki ɗaya. Ga Cha Chan bala'i, Bin mata kamar bunsuru, shaye shaye kamar salansa. Dab da zasu dawo Nigeria da zama ya koyi shan Hodar iblis.



Sannan yanada bala'in zafi, baya daukan rainin at all. Yanzu saiya tara maka gajiya. Dukkansu babu mai aikin yi daga Huzaifah sai Hashim kasancewar duk sun gama.

Tun suna yara Daddy ya siyan masu Shares mai yawan gaske, kowa da nashi har Yasmeenah yasa suke fachaka babu kama hannun yaro.

A cikin su tarbiyan Yasmeenah ne yafi dama dama, at all bata shaye shaye kuma bata bin maza suyi fasikanci. Kawai dai ka barta da shigan banza saboda takan fita ma babu kallabi.

Sannan takan saka gashin gira, kumba da kuma gashin kanti dukda nata yanada tsawo.


Itace ma taci Prom queen a makaranta saboda tana cikin kin yadda. Gashi tanada kokari babu laifi saboda bata faɗi jarabawa.



Tunda Yasmeenah takai shekara sha shida a duniya kyanta ya fara bayyana a mastayinta na 'Ya mace. Tun daga nan suka fara far mata, tana tafiya yayyinta zasu shafa mata jiki. Tada bala'i tayi sosai saida Mommy ta shiga tsakanin su.

Tun daga nan ta raina su saboda girma ya faɗi, suna ce mata kule zata ce masu chas. Wata rana idan Mommy bata gidan haka zasu zauna suyita hirar yanda suka kwana da mace.

Komai suke faɗi kuma basa damuwa idan Yasmeenah tana wajen. Saidai taji kunya ta tashi, idan kuma ta bar wajen sai su bita da zagi, "Shegiya munafuka kamar bakiyi"

Tasan cewa tarbiyanta akwai gyara sosai amma ita Manzo ne a gaban su. A sanda taji kishin kishin wai za'a haɗata da ɗaya daga cikin yaran gidan, kuka ta kwana tanayi.

Ta ɗanji dama dama da taji Huzaifah ne saboda shi solobiyo ne, juyashi zata yi kamar waina. Amma dai dukda haka bata so, sam bazata iya haɗa zuri'a da yaran gidan ba.

Yasa tun dataga Naufal ta birkice akansa, duk wani aji data ke dashi a matsayinta na 'ya mace ta ajiye gefe. Dama Hausawa sunce da zafi zafi akan daki karfe, ta dauki alwashin bazata hakura dashi ba harta sameshi.

Zatabi kowane hanya daya dace daga kissa, yauki, iyayi kai har Malaman zaure zata iya bi domin Naufal.


Abinda yake mata daɗi shine tun kafin aje Ko'ina ta fara samun lambar zuciyarshi dukda bawai sun wani sake bane yanda takeso amma tana kyautata zaton cewa ya kusan zama nata baki daya.



********



A kwana a tashi babu wuya wajen Allah, yanzu a kalla cikin Fadeela ya kai wata biyar a duniya. Tayi katuwa sosai kuma kafanta ya soma kumbura, komai a wahalce takeyi amma bata fasa aikin gida ba.

Ko Defence na project tayi kawai yanzu zaman gida takeyi tana rainon cikinta. Saidai bata jin daɗin yanda aiki ya kacame ma Naufal, tun safe idan ya fita sai goman dare yake komawa gida.

Tun tana complain akan abin saboda yana damunta sosai gashi ko waya sau ɗaya sukeyi shima sai idan ta kirashi. Flimsy excuse yake bata koda yaushe akan yana conference call da su Mr Sutter, wata rana kuma yace yana construction site ne.

Hakuri takeyi koda yaushe tayi masa uzuri, koba ta faɗa ba tasan Allah yana tareda mai hakuri. Sam bata nuna masa ɓacin ranta saboda tasan cewa duk zafin neman dayake yi akan itane da abinda zasu haifa.

Shikuma yana zuwa aiki karfe 2 yake tashi daga nan zai tafi yawo da Yasmeenah. Basu Ice cream joints Ko wajen shawarma duk dai wurare marasa kan gado kuma baya komawa sai sunci dinner tukun.



Shakuwa mara misaltuwa ke tsakin su, soyayya mai karfi ya shiga tsakanin su. Tun yana ɗari ɗari da ita har yake sake sosai.

Weekends kawai Fadeela ke ganin sa sosai saboda shima bazai iya karyan aiki ba, amma wata rana idan Yasmeenah ta nace dole yace zashi dauko wasu takardu office.

Yanzu jin kansa yakeyi kamar tubabban sarki don karya, tun yana ɗari ɗari idan yanayi kuma yana jin wani iri ajikinsa har yazo ya saba.

Yin karya yakeyi kamar yana faɗin gaskiya. Akwai wani rana haka da asuban fari Abba ya kirashi akan yana san ganinsa.


Yana isa ya rufe shi da faɗa akan dalilin da bai siyan ma matarsa mota ba, nan take yi charap yace ai Birthday ɗinta ya kusa ya kuma order akawo mata.

Kuma alhali karya yakeyi, dayake baya zaman gidan ya mance Fadeela Keke Napep take hawa duk kuɗin mijinta. Shi yanzu duk girman mutum zai iya mashi karya yasa ko tunani baiyi ba yayi ma mahaifinsa.

Babu mamaki idan aka bashi ministan kula da lafiyar karya. Yanzu ne zaisa akaima Fadeela Mota. Koda yake ya ɗanji tausayinta, ga ciki ga kuma rashin abin hawa but he promised to do better.

Last week ya kashema Yasmeenah dubu dari da hamsin akan motarta, ita bawai ta tambayeshi bane saboda tanada kudinta. Shine don raayinsa ya bada wai 'Meye amfanin zama tare'


Tun daga nan bata sake masa musu ba wajen kudi, haka yake siyan mata su designer bags dasu takalma. Sauda dama yakan mance daya kamata ya siyan ma Fadeela.

Sai daga baya ya tuna, daga nan saiya rinka siyan komai guda biyu. Leda ɗaya Yasmeenah ɗayan kuma Fadeela.


Idan yakai gida wajen Deela, ta rinka shi masa da albarka kenan tana jindadi. Shi karin kansa yana jindadin addu'o'inta unlike Yasmeenah dake cewa 'Thanks' sai a wuce wurin.

Gashi kuma wayarsa ya saka password, shima idan ka bude akwai wani a Whatsap, msg, phone book etc.

Kuma idan ya dawo goman dare zaita danna waya, idan Deela tayi masa complain zai ce tayi hakuri Email yake aika masu Mr Targeyen.

Wata rana tana jiransa wata rana kuma tana kwanciya ta kyalesa, kawai daɗin abin su Miemie da Bilqees sukanje sukai har Magrib sai Khattab yaje ya daukesu.



Wani alhamis haka bayan sun gama karin kumallo kafin ya fita, saita tambayeshi izinin tafiya kasuwan Muda lawal domin tayi masu cefane.

Ya bata izinin ta tafi tareda cika mata jakarta da kudi. As expected shi masa da albarka tayi sannan ta rakashi wajen motarsa saiya tafi...



11 am.......



Locacin ta gama aikace-aikace daya kamata tayi sai tayi wanka domin ta tafi kasuwa. Tana gaban mirror saita lura da gashin kanta yayi datti ya chukurkuɗe, anan ta yanke shawaran gwara taje saloon tunda duk hanyar ne.

Ita kuma Yasmeenah jindadi takeyi sosai saboda zata fita date da Mine ɗinta. Zumuɗi Kawai takeyi, wani bakin leather wando na Victoria Beckham ta saka saita haɗashi da riga na chiffon white and black Mai guntun hannu.

Takalmin Jimmy Choo silver ta saka saita dauki Bouquin din Marc Jacobs. Fuskanta shake da makeup kamar mannequin. Sai kuma wani munafikin gyale data dauka.

Tafe take cikin motarta zata salon ayi mata gyaran gashi dasu kafa kafin yamma yayi. Taje har an fara mata sai ta kira Laila kawarta akan tazo ta tafi da motarta saboda Naufal zata kira banyan nan.

Suna zaune a cikin dryer suna hira saiga Fadeela ta shiga itama, kafin a gama wanke ma Fadeela ayi mata setting har nasu yayi sai suka fito suna yauki kana suka zauna dab da ita.

Kana ganin Fadeela kasan babban mace ce, iPhone 7 ke hannunta ga kuma tasha qwala qwalai daga kunnenta har yatsun ta. Sannan atamphan Super wax ke jikinta kuma anyi mashi ɗinkin masu hannu da shuni.

Gashi dama jikinta ya murmure, dole ta birge ka. Su Yasmeenah saida suka kasa hakuri sukayi mata magana. "Halan ke amarya ce?" Yasmeenah ta tambaya Deela.

Murmushi Deela ta sakar mata saita amsa da eh.


"Wallahi kin burgeni ne kawai, ina so nayi kama dake idan nayi aure"

dariya Deela tayi bata cekomai ba.


"Ki tayani addu'a, inada wanda nakeso na aura da fatan Allah ya tabbatar da alheri"

"Aminsumma Amin" Deela ta amsa. Daga nan ta tashi zata shiga dryer, anan ne sukaga tanada ciki. Laila ce tace 'Lahhhh ciki gareta! Wallahi ina son yara sosai kamar raina"

"Kai nayi maki murna, Allah ya saukeki lafiya" Yasmeenah ta ce.

"Amin summa Amin" ta amsa mata dashi.

Daga nan sukayi sallama saboda anzo daukar su. Ita Deela kawai tana amsasu ne amma sam basu burgeta ba. Duk sunyi shigar arna ga gashin Kanti da kuma gashin ido.

Da basuyi hausa ba bazata zata musulmai bane, kawai tana tunanin wanda zai auresu a haka. Wayanta ya soma ruri saita tashi taje ta dauka.

Ta window ta hange shigan motar Naufal yana barin parking lots, bayan tagani kuma yayi nesa da ita. Kauda tunanin tayi ta koma aka gyara mata gashin kanta.

Bayan ta gama sai tayi chatan Napep taje kasuwa tayi Siyayyanta. Data koma gida ta daura masu dinner saboda Naufal ya daina cin lunch a gida, ko office ta tura masa bata samunsa kila ya tafi construction site.


Tuwan alkama tayi da miyan karkashi, saita fasa kwakwa da pineapple ta markaɗa masu. As usual ta kanyi kwalliyar tarban miji, yau kawai daɗi takeji saita saka wani bakin guntun free gown.

Gashi kanta yasha gyara so bata daura kallabi ba, dama wajen goma yake dawowa amma wannan Karon har wajen minti arba'in da biyar.

Sam batayi fushi ba saboda hakuri shine zaman aure, koba komai saboda ita yake neman kuɗi. Yana shiga falo ta tashi da sauri ta karasa wajensa tayi hugging ɗinsa.

"My Other half, Finally ka dawo.... Yau na rasa dalilin dayasa nayi missn dinka sosai"

Manna mata kiss yayi sai yace, "Toh gani me kika ajiye min"

"Muje kayi wanka sai kazo kaci abinci, yau favorite dinka na girka"

Daga kanshi yayi sannan ya soma magana kasa kasa, "Afuwan babyna Wallahi Aminu ya isheni da yana jin yunwa shi ne na kaishi daga nan saina ci"

Shiru tayi batace komai saboda ta bala'in shaka, gashi har konewa tayi wajen wrapping tuwon. Idanta Saida ya canza kala saboda bacin rai, ba wannan karon bane take abinci yaki ci, yayi yafi a girga amma na yau ya ɓakanta mata rai.

"other half Ko drink ɗin bazaka shaba" ta faɗa cikin muryan kuka.

Shafa bayanta yayi saiya ce, "Ki ajiye min a fridge gobe sai na sha"


"Allah ya kaimu lafiya"


"Amin babyna"

Sun tafi ɗaki har yayi wanka tana goge jikinsa da hand towel, "Other half yau Kaje wannan sabon plaza ɗin ne wanda ke kusa da Apple clinic?"

Datana kallon fuskarshi dataga rashin gaskiya karara ya bayyana. Dakewa yayi saiya amsa mata da, 'Ah ah, menene ?"

"Babu komai kawai naga kamar motarka ne a wajen"

"NI dama yanzu zan faɗa maki a Gombe na wuni, Zaayi renovating Government house shine mukaje meeting" tabbas akwai zance kamar haka amma meeting ɗin saura sati biyu.

"Oh Allah sarki other half dina nayi maka murna sosai, Allah ya sanya alheri"

"Amin, amma kema meya kaiki wajen? Inace kasuwa zaki amma shine kika biya wani wajen? A duniya karya yana cikin abinda na tsana Wallahi. Idan kika tambayeni ai bazan hanaki ba, amma dan nuna ban isa ba shi ne kikayi abinda kikaga dama koh?"

Nan take ta firgice yanda taga karamar magana ya zama babba, saukowa gabansa tayi ta rike masa hannu, "Other half Kayi hakuri dan Allah, ka mance na saba biyawa saloon idan zani kasuwa saboda banso nayi fita biyu"

"Toh donkin saba sai akace banajin haushi ko me? Ni dai Karki saki saboda bana san karya"

"In sha Allah Other half bazan kara ba" Daga nan ta hau gado tana shafa masa bayan shi tana watsa mashi kalamai masu dadi.

Dolenshi ya sauko ya biye mata suka fara soyayyar su, suna haka har barci ya kwashe su.







#NiDaDiyata

#TeamFadeela
#TeamNaufal
#TeamYasmeenah


I'm proudly Team Fadeela this time around.



*All Rights Reserved*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top