Twenty-four

Narrated Abu Hurairah reported the Prophet (pbuh) as saying "Women may be married for four reasons, for her property, her ranks, her beauty and her religiosity. So get the one who is religious and prosper (lit. may your hands cleave to the dust)."



**********




Haka rayuwar Khattab da Miemie ya kasance, kusan kullum sai yazo yaga Miemie amma a falon su. Idan ta shiga motarsa to Naufal ne da kansa ya kira shi akan ya taimaka masa wajen daukanta daga School bcs bazai samu time ba.


A duniya Khattab yana san irin wannan locacin bcs yana samun daman zance sosai, ya kan biya da ita wajen su Vanilla joints haka da sauran su, ya siyo mata su shawarma da sauran kayan lashe lashe. Shake da Leda take komawa gida idan yazo.

Tsalla soyayya sukeyi mai tsafta, saidai shi kullum zulumin ya zaiyi da maganar auren shi da Lili yakeyi. Bcs an riga an kai baikonsu tun kafin ya gudu.

Yanzu abinta sai girma yakeyi bcs yanzu kayan aure take siya, bata da aiki sai Online shopping gashi kuma ta shiga whatsapp groups na business ɗin kayan aure bila adadin.



Haka take saving hoto ta ajiye mashi idan ya dawo saita rinka nuna masa. "Yaya wannan colour ɗin yayi? Wanne yafi tsakanin wa'annan" haka take damunsa da tambayoyi.

"kiyi abinda kike so" abinda yake amsa mata dashi kenan kuma bazai kara ce mata kala ba. Wata rana tayi zuciya ta tafi wata rana kuma ta zauna tayita tambaryasa a haka dukda baya amsawa.

Shikuma abinda yasa baya amsawa bcs bashi zai zauna da ita ba saidai ya sake guduwa, kuma koda ta aureshi saidai gangar jikinsa amma ba ruhinsa ba yasa gudun ba'a cigaba ba gwara ba'a soma ba.

On the other hand Lili kallonsa kawai takeyi, ana nan ana mata haɗin mata gangariya yar Maiduguri. Duk abinda Khattab ke mata tana ankare dashi, auren nan dole ayishi koda yana suma ne, jira kawai takeyi ya santa a matsayin 'ya mace sannan maganin ta yana aiki.

Idan yayi mata wani abu dariya takeyi a ranta saita ce, "zaka shigo hannu ne, bakasan halina bane" Ni kuma Dimples nace hali na Wanne kuma?



*******



Fadeela tana shan maganinta daidai yanda akayi mata prescribing, gashi idan ta fara shagwaɓan ta na fama tana kuka, Naufal yana gefenta yana petting ɗinta.

At all Baya San yaga hawayenta, duk randa taje school taga yaran samɗa saita mashi jidali, gashi Hadiza matar sadeeq haihuwa yau ko gobe.

Shiyana tunanin hanata zuwa makaranta bcs zuwanta baya kara masa komai sai tashin hankali. Sannu a hankali harta kai 2 months tana shan magani.

Kawai saita tsira shan fanta mai kankara, Itafa ba ma'abociyar shan abin bane, tafi san Coke but kawai saita fara marmarin shan Fanta kuma shima fanta ɗin saiya fara kankara ko alamar haka.

Wata rana idan zata dawo daga School take siyo abinta, wata rana kuma Other half ɗinta zai siyan mata. Haka tayi stuffing ɗinsu a cikin fridge abinta, daganan sai kwaɗayin ya girma.

Daga fanta ta kara da agwaluma da gasharshen masara, Naufal tun baya complain har ya soma yi bcs shike siyowa saboda ta daina zuwa makaranta bcs sunyi exams, rana daya ko biyu take zuwa wajen supervisor dinta.



Abin ya fara damunsa sosai, bata da lalaci bcs tana duk wani aiki daya kamata mata but saidai ta sauya masu yanayin girkinsu. Kwata kwata bata san warin stew so batayi.

Saidai kullum sai sunci tuwo miyan kuka bcs shine yanzu best food ɗinta. Gashi tayi dundumemiya abaya kawai ke shigan ta sai kuma kimono tunda duk kayanta fitted ne. Ita dai kawai ta lura tayi ɓatan wata ne amma bata gaya ma kowa ba har Naufal.



Wata rana taje school suna zaune a garden chairs dasu samɗa da Mansura, kallonta sukeyi cikin tuhuma. Bata ko kallesu ba bcs kananan tsegumi ne bata so. Saiga mai masara dafaffe tazo wucewa.

"mai masara! Kawo mana, ina tsammani akwai canji cikin jakana"

Fadeela ta faɗa tana duba jakarta. Samɗa ne ta jungure Mansura tana mata kyas da ido alaman su kalle Deela.

"Gulma ajali !" Fadeela ta faɗa bata kallesu ba. Mansura ta gyara zama saita dafata sannan tace, "Baki lura kin fiye kiba bane halan? Gashi sai cin tsiya. Idan bakiyi hankali ba sai Naufal ya sake aure"

Dariya Fadeela tayi sosai kafin ta ce, " wai wani Naufal ɗin? Badai nawa ba bcs baki lura yanda muke soyayya bane"

"Mun lura mana gashi ya bayyana a jikin ki" Samɗa ta chapke. Sekeke Fadeela ta kallesu sannan ta juya kai. Da sauri Mansura ta zaga ta duka gabanta, "Bakya jin wani motsi a cikin ki?"

"Banaji Rabu dani"

"Amma kina amai da ganin jiri?"

"ka nace maki babu abinda ke damuna, ah ahn kyaleni mana"

"Mansura tace lafianta lau ki kyaleta mana" Samɗa ta faɗa.

"Malama babu ruwanki, kana ganin Fadeela kasan akwai wani abu cikin jikinta, ga shegen kwaɗayi yanzu bata wuce tayi kwata kwata"

Shiru Fadeela tayi for some minutes Sai ta soma magana kasa kasa "Nima abin ya fara isana, gashi rabon danaga period dina tun kafin na fara shan magani"

"Oya bani kudina" Mansura ta faɗa ma Samɗa tareda mika mata hannu. Sai kawai Samɗa ta zuge cikin jakarta ta fito da 500 naira guda 4 ta bama Mansura.

Itadai Deela bata gane me sukeyi ba, sai bayan sun natsa Mansura ta soma magana, "Dama nace ma Samɗa ciki gareki shine tace wai baki gaman shan maganin kiba. Kawai wai kiba ne bcs kinajin daɗin aure"

"Shine nace idan cikine zata bani dubu biyu idan kuma ba shi bane zan bata dubu biyar"

Dariya suka kwashe dashi su duka suna shewa harda shan hannu, "Kunada kudin banza shine bazaku bani na kara na cin masara ba da fanta" Deela tace.

"Karki damu muje na siyo maki da kuɗin nan" Mansura tace.


"Amma fah kina wuta " Samɗa ta faɗa tareda zungurinta.

"Toh dafa! Nina wasa ne" Deela ta faɗa tana ɗaga kafaɗa.



Haka suka gama hirar suka tashi kowa ya kama hanyar gidansu, yau Deela tayi alkawarin fada ma Other half ɗinta good news.

Gyara gidanta tayi tas ta bishi da turaren wuta dasu room freshener. Rissotto ta kirka wanda yasha Ugwu da albasa mai lawashi. Sai tayi ginger drink mai garlic a ciki.

Tayi setting table gwanin ban sha'awa bcs wasu sabbin coolers peach ta dauko yau. Upstairs ta wuce domin tayi wanka saboda tasan zashi gidansu kafin ya dawo.

Ta lura tunda Miemie tayi saurayi bashida katabus kullum saiya je shi a dole yaya babba.



Leggings ta saka baki sai crop top wanda bayan duk an yanka, jiran sa takeyi à falo dukta kagu ta faɗa masa sun kusan zama parents.

8:15pm.....



Locacin na ya dawo daga gidansu, sallama yayi sai ya ganta kwance akan couch tana jiransa. Ga kuma kamshin abinci da turare ta Ko'ina.

Murmushi suke sakar ma juna harya isa wajenta. Shafa mata kai yayi yana kashe mata ido. A hankali yace "How is my baby dis evening?"

"we are fine"

Kallonta yayi bai gane ba, "Me kike nufi da 'We'?"


Dariya tayi saita daura hannunsa akan cikinta tana murmushi, nan take ya ɗago abinda take nufi. Da sauri ya rungume ta don murna. Ita kuma sai dariya takeyi. A hankali ya soma magana, "koba komai na huta da kukan dare"

Dukan wasa takai masa sai ta ce, "Dawa kake yi?"

"Nifa bance dake nakeyi ba Malama"


"Gwara dai" saita kara makale shi. Daga nan kuma ta raka shi yayi wanka tareda shiryawa kana sukaje wajen cin abinci. Yaji daɗi sosai daba tuwo miyan kuka bane bcs ya tsane abincin amma bazai iya magana ba.

Yanzu yasan ba laifin ta bane, cikin ne yake mata haka.


Saidai fatanshi Allah ya rabasu lafia kawai kowa ma ya huta.



3 days later...



Wajen karfe goma na safe ya shirya zashi office, panke tayi mashi wanda yasha ayaba. Saita yi masu oats suka haɗa dashi saida bata saka madara a nata ba.

Sun gamaci saita rike mashi brief case ɗinshi sannan hular sa duk yana hannunta. As usual kofa ta tsaya saboda kayan jikinta. A hankali ta daura masa hulan a kanshi saita kara gyara masa button ɗin dabai gama makala wa ba.

Ta juyo zata koma saiya jawota ya kaima bakinta kiss, da sauri tayi kokarin tureshi amma yafi karfinta, don kanshi ya kyaleta yana ɗaga mata gira. "Idan Kinsan bazaki min proper bankwana ba ki daina raka ni"

Dariya tayi kafin tace, "NI banason mai gadi ya ganni Wallahi" juyawa yayi ya kalle inda maigadi yake amma baya wajen, "Kwantar da hankalinki duba baima wajen"

"Okay" tace saita kara jawoshi sannan ta manna mashi wani, ya shagala kenan ta sake shi sannan ta rufe kofa karab. Dariyar ta kawai yakeji bcs tasan ta nema tsokana.

"Ai zan dawo nayi maganin rashin kunyar ki"

"Eh din ai bana tsoro" ta faɗa ta window.

"Zakiyi bayani ne yarinya"

Saiya tafi motarsa, yana tafe yana tunanin yanda san matarsa yayi tasiri cikin jikinsa, ashe dama haka aure keda dadi idan kanada right spouse.


Yanke shawara yayi gwara yaje ya fara siyan kayan yara kafin ya wuce Office, Mumtaza Stores ya tsaya bcs akwai girma sosai, ya shiga ya siyo kayan yara kala kala daga na maza da mata duk ya haɗa, saida ya siya san ranshi kafin ya biya kudi ya tafi.


Ya gama sakawa a boot yana zaune cikin motarsa, tunanin Fadeela yakeyi da sabon rayuwar da zasu gina. Dayake baiyi winning glass ɗin motarsa ba, yana jin hayaniyan jama'a.

Wata ya gani tana tafiya da sauri sauri ta fito daga store ɗin kuma wani namiji yana mata magana amma bata kulashi ba.

Sanye take da riga pink iya cinya da wando jens wanda aka yayyanka sai tayi daurin turban. Jakarta na bouquin Blue yana gefen hagunta. Tazo inda Naufal yake zata shiga motarta.

"Haba Yasmeenah, ji ina maki magana kin wani Share ni" a fusace ta juyo ta yi magana cikin harshen Hausa wanda kafin nan bazaka zata ta iya ba saboda ma yanayin shigarta da siffanta.

"sai me dan kasan sunana?"

"Haba Yasmeenah Nifa dan uwanki ne amma kike wulakanta ni for no reason" Guy ɗin ya faɗa. Harara ta watsa mashi sannan ta zura hannu cikin jakarta ta fito da mukullin mota.


Shi Naufal yana daga cikin mota yana jin su bai fito ba. Ita kuma Yasmeenah ta buɗe motarta zata shiga ciki sai guy ɗin ya jawota waje, "Haba Meenah" bai karasa ba ta sharara mashi kyakkyawan mari.

"are you stupid Yaya Huzaifah? How dare you ka saka kazamin hannunka a jikina? Rainin harya kai haka eyee?

Tana masifa jikinta yana ɓari.


Shikuma Huzaifah idonsa yayi ja sosai saboda bacin rai, "Dan ubanki ni kika mara koh? Don kin samu ina kallon ki har zaki raina ni haka?"

"An mareka Yaya Huzaifah ko bari nace Huzaifah..... Kayi abinda zakayi. Kuma ka sake saka filthy hands ɗinka a jikina saina kara maka" Ta fada tana zare masa ido tareda taunar chewing gum.

Gadan gadan Huzaifah ya nufota saita saka hannu kerere akan kugun ta tana jiransa babu tsoro a tareda ita.

Da sauri Naufal ya fito bcs yaki suke shirin yi. "ya isa mana" ya faɗa tareda janye Huzaifah.

" Karyan iskanci yakeyi, aida ka kyaleshi na koya mashi hankali tunda yana jin kanshi kamar jaki" ta faɗa tana jijiga.

"Ba Kinga an shiga tsakanin muba ai dole kiyi kumfan baki. Banza asarrariya" Huzaifah yace sai ya nufa hanyar motarsa.

"eh ɗin, soko kawai" ta mayar masa. Ikon Allah Naufal ya tsaya gani bcs gaba ɗayansu basuda tarbiya.

Karar wayarsa yaji saiya bar wajen yaje motarsa, ita kuma nan ta bisa da kallo tana yaba kyansa da kuma kamalan sa. "woow dis Guy is so marriage material ta faɗa a ranta"

Shikuma kamar yadda ya saba idan ya dauki business phone ɗinsa saiya faɗi sunar sa, "Hello ! Naufal Hussain Beli speaking, how may I help you"

Anan Yasmeenah taji sunar shi, murmushi ta somayi saita gyara tsayuwanta tana yauki. Bayan Naufal ya gama wayanshi baima koma inda take ba saiya ce "Sai anjima Allah ya kiyaye na gaba"

Nan take ya shiga motarsa ya fice, cizon yatsa Meenah ta soma yi bcs taso ta karba number ɗinsa amma ya tafi. But ta dauki Alwashin saita binciko shi duk inda yaje tunda tayi mai Wuyan tasan sunar shi.

Wayanta ya soma ringing, kawarta Laila ke kiranta a waya. Da fara'arta ta dauka sai tace, "Sorry my dear gani nan zuwa, I just met Mr right. Nanda 3 months Idan banyi aure ba zan baki dubu hamsin"

"Yayi daidai aminiya ta, faran mace hasken tsakar gida. Kura mai kallabin kitse, karya gwafa shahon karfe, Mace daya tamkar dubu, dukan matan duniya a bayanki suke....."

laila tace

Dariya Yasmeenah tayi bcs idan ta kyale Laila zasu kwana ana kirari.


"okay naji tawan, thanks but Ina so daga yau ki rinka kirana Mrs Naufal Hussain saboda tunda na ganshi to fah saina mallake shi"









#NiDaDiyata






*All Rights Reserved*



Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top