Twenty
*Lesson*
Patience is when you're able to conquer that angry voice in your head which wants to take revenge on others who hurt you or are mean to you!
Mufti Ismail Menk
Ibn Mas'ud (May Allah be pleased with him) said: The Messenger of Allah (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "He who says: 'Astaghfir ullah-alladhi la ilaha illa Huwal-Haiyul-Qayyumu, wa atubu ilaihi (I seek the forgiveness of Allah, there is no true god except Allah, the Ever-Living, the Self- Subsisting, and I turn to Him in repentance),' his sins will be forgiven even if he should have run away from the battlefield (while he was engaged in fighting for the Cause of Allah)."[Abu Dawud, At-Tirmidhi and Al-Hakim
**********
CYPRUS
A East ɗin Mediterranean akwai wani Island da ake kira Cyprus, chan daga wajen Arewan garin akwai wani k'aramin gidan gona wanda ya k'unsa ɗakuna biyu da bayi uku tareda da kitchen daya.
A cikin falon akwai dinning area, drinks cabinet da kuma chimney.
Wani matashi ne wanda bazai kai shekara 25 a duniya ba ya shiga cikin gidan, hannunsa shak'e yake da itatuwa kuma ya nufa hanyar fireplace ɗin falon, yana zuwa wajen saiya dire tareda ajiyar zuciya.
Kayan sanyin dake jikinsa ya fara k'okarin ragewa, safar hannu ya cire sai kuma maufler tareda head warmer.
Yanzu fuskarshi ya bayyana sosai wanda da baka ganin komai sai k'wayar idanu. Jacket ɗinsa ya cire tareda ajiye wa akan couch sai ya rige daga shi sai sweat pants tareda T-shirt.
Kai tsaye dinning area ya wuce ya haɗa ma kanshi shayi a wasu fararen Chinese wears. Yana sha yana lumshe ido,Saida ya zuba ma kansa kofi biyu na ruwan bunu kuma ya shanye tas.
Tsam ya mik'e tsaye ya wuce wajen wani calendar haka wanda yayi kacha kacha da rubutu. "Day 190" ya rubuta a bangon saiya wuce hanyar bedroom ɗinsa ya shiga bayi direct.
Kallon kansa ya tsaya yi a mirror ɗin bayin, duk ya canza kamanni ya susuce. Rabon daya aske gashin kansa kona gemunsa tun yana Nigeria. Yanzu Afro yayi tsawo kamar jirgi ya doso gari ga kuma fuskarshi jaɓa jaɓa da gashi.
Mutane biyu kawai yake tausaya mawa, na farko dai Mahaifiyarsa wanda yasan tana cikin matsananci tashin hankali akan rashinsa.
Na biyu kuma Haskensa Miemie, rashinta yayi sanadiyar gudunsa. Shifa bazai iya zama gari ɗaya babu ita yasa kawai ya tafi.
Wanta yayi making ɗinshi clear bazai taɓa bashi ita ba saboda wasu dalilai nashi. Shikuma idan ba Miemie bazai zauna da wata mace a inuwar aure ba.
Babu makawa idan yana gidansu za'a tursasa shi akan ya aure Lili which bazai iya buɗe idonsa ya ganta ba.
Wanka yayi sannan ya shirya cikin Long sleeve da jens wando, ɗayan ɗakin opposite nashi ya wuce tareda shiga. Maidaidacin ɗaki shake da kayan computer kala kala tareda sauran abubuwa daya jibanci haka.
Zama yayi akan wani kujera dayake gaban babban computer. Kunnawa yayi sai wani rubutu ya fito inda aka rubuta NTI TELECOMMUNICATIONS.
Nan ya saka password ya soma aiki gadan gadan, kana ganin yanda yake aiki cikin kwarewa kasan cewa ba sabon hannun bane.
NIGERIA
"Inspector mun samu leads akan shi" wani Sergent ya Shiga office ɗin IG tareda mashi salute.
Ajiye takarda yayi dake hannunsa sannan ya gyara zama tabaransa.
"A Ina ne wajen?"
"Sir Chan Cyprus ne, akwai wani ICT company dayake ma aiki. Toh wani ɗan department ɗinmu dayayi tracking hotonsa a cikin database ɗinsu"
"Innalillahi, tuntuni muna nemasa amma yana chan Cyprus. How true is this information?" IG ya tambaya.
"Anyi kowane bincike kuma an gane Khattab ne"
"Kuma kun tabbata anan yake aiki ba scam bane?"
"Affirmative Sir"
"Okay ku shirya mana Visa muje Cyprus muga gari"
2 days later....
Khattab ne ke cikin Garden ɗinsa yana gyarawa, dayake Miemie ta koya mashi yanda zaiyi shuka da sauran su so bashida matsala wajen yi yanzu.
Saboda yana Missing Miemie in the first place Yasa ya siya gida mai yanayin gidansu watau na gona. Yana cikin gyara sunflowers da kuma Hydrangeas sai kawai yaji an shigo mashi gida, bai yi kokarin dubawa ba saboda mutum ɗaya ya sani watau makwabcin sa Mr Kareem.
Tafiya yaji ta wajen ɓangaren dayake Kuma yasan Mr Kareem bazai zo wajen ba. A hankali ya ɗaga tareda juyawa, fuskar da bazai taɓa manta wa ya gani. IG ne yake tafiya wajen dayake.
Nan take gabansa yayi mumunar faduwa, da sauri ya mike tsaye tareda da sakin shovel ɗin hannunsa. Jikinsa rawa ya somayi baisan mai zaice ba.
Shikuma Daddy ɗin Khattab zuwa company ɗin Khattab yayi sai akace mashi Khattab a gida yake masu aiki wai baya san cuɗanya da mutane, toh dayake he is good babu Yanda zasuyi.
IG yana nuna masu clearance ɗinshi a matsayin jama'an tsoro kuma ana neman Khattab dead or alive a Nigeria. Nan take suka haɗashi da wani officer domin ya jagoranci shi zuwa gidan.
Yana isa saiya ji motsi ta wajen garden yasa yaje ya duba. Ido cikin ido yake kallon Khattab shi wanda ya maza ya sauke nasa saboda kwarjini.
"Ka kyauta kenan Khattab?" Mahaifinsa yace.
*********
Motar shiru babu abinda ke tashi sai tafsir ɗin Sheik Aminu Ibrahim Daurawa akan aure. Sannu a hankali har suka isa gidansu, horn sau ɗaya yayi Maigadi ya buɗe masu.
Suna cikin parking lot sun fito sai Maigadi Mallam Idi yazo wajen su.
"Ina wuni Hajia ya jiki?"
"Lafia lau ya aiki?
"Alhamdulillah" Daga nan saiya ɗaukan masu jakar su, har cikin falon ya ajiye masu sannan ya masu saida safe.
Fadeela a hankali ta ɗingisa kafarta har ɗakinta domin tayi sallah, shima Naufal ya wuce Masallaci.
Bayan ta idar saita sauka ta sake microwaving kazan saita haɗa mashi da snacks ɗin da suka siya.
Ta ɗeba nata tana kokarin wucewa saiya shigo falon, kallon ta yayi sau ɗaya saiya kawar da fuskarshi. Kan Dinning ya kalla sai yaga komai is set.
Murmushi yayi a ranshi yana tafe fuskarshi kuma babu yabo babu fallasa.
"Saida safe Yaya" ta faɗa sannan ta haye sama.
"Toh" ya amsa mata dashi.
Tana ɓacewa saiya tsaya cak, haushin kanshi ya fara ji sosai bcs yanda ya amsata bai dace ba. Besides shida yake neman sulhu.
Amma zai gyara abin, yayi assuring kansa.
Next Day....
Ya kasance Weekend so Naufal bazashi aiki ba, kuma koba haka ba babu inda zashi bcs ya barma Aminu komai a hannunsa tunda shi yana jinya.
Wajen asuba ta farka tana mitsike idanu, tana cikin bargo tana ajiyar zuciya a hankali. Karar kofan Naufal taji da alamu zashi Masjid ne.
Murmushi tayi mai bayyana hakora saboda Other half ɗinta akwai ibada.
"Allah ya daidaita tsakanin mu" ta faɗa tareda yin mik'a, salati tayi saita wuce bayi.
Shikuma Naufal yaso ya tsaya ɗakinta domin ya tasheta amma wani zuciya yace masa "Meye ruwanka da ita salan raini ya shiga tsakani, halan da kai kake tashin ta?"
Bayan an Idar da sallah saiya tsaya lazimi kafin gari ya k'ara haske, yanayi sai kuma Fadeela ta faɗo masa a rai. Da sauri yake kawar da tunanin but still ya kasa bari, haushin abin yakeyi matuka but babu yanda zaiyi.
Da gari yayi haske saiya wuce gida abinsa, a hanya ya haɗu da Doctor daga gani asibiti zashi. Sun tsaya sukayi gaisuwan mutunci but still Doctor ɗin Bai wani sake jiki dashi ba kamar da.
Ya tambaye shi lafiyan Fadeela kuma ya jaddada mashi amfanin magani da kuma tayi kokarin taka kafanta.
"Karka damu Doctor" Naufal yayi assuring ɗin sa.
"Toh" yace saboda yana bala'in jin haushin Naufal. So da dama ya saba ganin couples wanda basa shiri amma ba kamar yanda nasu yake ba. Ya lura matar batada matsala kawai mijinta ne mai zafin kai yasa ya dena sake mashi fuska.
Bayan ta idar da sallah saita mirgina gefe ta kama barci, ba ita ta farka ba sai wajen 7:30 am. Wanka ta somayi saita shafa ma kafarta wani magani haka mai suna 'Power Heat'
Zama tayi akan mirror ta rasa wani irin kwalliya zatayi, sai kawai tayi smoking eyes da purple lips. Wardrobe ɗinta ta wuce ta ciro wani bakin dogon pencil gown saita dauki wani peach kimono ta haɗa dashi.
'Daurin turban tayi wanda ya kara k'awata mata fuskarta. Su humra da turaren Chanel No 5 ta fashe kanta dashi. Tayi kyau ainun ita kanta ta yaba balle wani, takalmin soso baki ta saka mai dunlop.
Kitchen ta wuce kai tsaye ta auno wake ta fara wankewa saboda kosai zatayi masu da kunun gyaɗa. Dayake blender ɗinta na zamani ne saita markaɗa abinta.
Shikuma koda ya dawo bai ganta ba sai ya wuce kai tsaye ɗakinsa, baiyi 5mins ba barci mai kyau yayi awon gaba dashi. Wajen 9 am ya tashi kuma kamshin abinci ya cika mai hanci. Shima wankar yayi saiya saka 3 quater camouflage da sleeveless riga fari.
Koda ya shiga falo bai ganta ba kuma babu abinci akan dinning kawai kamshi ne yacika Ko'ina. Zama yayi akan Couch ya fara kallo, Keeping Up with the Kardashian ya gani yana aiki kuma Yasan ita ta Saka bcs koda yaushe abinda yake riskewa kenan, dariya yayi saboda baiga amfanin kallon mutanen da basuda sana'a sai shopping.
JSC sport ya saka ana nuna Basketball kuma favorite player ɗinshi Kobe Byrant ke wasa, nan ya shagala Yanata kallo. Ita kuma ta fito zata ajiye cooler sai taga ya shafa'a yana kallo.
Bayan ta gama jere komai yayi tsaf saita taka sannu a hankali har wajen dayake, wannan Karon babu karap karap ɗin takalmi. Kamshin Chanel No 5 yaji but bai hasala ba kamar da yanda yakeyi, wannan Karon jindaɗin kamshin yayi.
A gefen sa ta tsaya ta rasa me zata ce bcs ya kura mata ido Which baisan ma yanayi ba. "yaya ina kwana?" ta faɗa tana wasa da yatsunta.
"lafia lau, ya jikinki?" ya faɗa fuskarshi babu yabo babu fallasa.
"I'm much better, thanks" sai sukayi Shiru basu ce komai ba, kana ganin su kasan akwai tension a tsakanin su. Da wani siririn murya tace masa, "Dama yaya nazo na faɗa maka na gama abinci ne"
"Okay sai muje kiyi serving ɗina"
Tana tafe yana binta da ido kawai kallon ta yakeyi, tanaji à jikinta ya kafa mata ido saboda duk ta birkice. Dadin abin kayanta bai nuna matsewa saboda Kimono data saka if not tasan Zata kara turguɗewa.
Kamar yadda ta saba ita ke jawo masa kujera saiya zauna, wannan karon yace mata, "Thanks"
Gyada kai kawai tayi saita soma zuba mashi, yanda yake abin har mamaki yake bata bcs he was very polite.
Ta gama zuba masa kunun saita saka masa madara a ciki yanda akeyi, ashe shi bai taɓa gani ba. "Toh fah!" ya faɗa a ranshi bcs da bfr ne saiya watsa mata a jiki koya haska mata mari bcs baya san shishigi.
Ita kuma ta shafa'a cikin tunani ta mance kofinshi ne saita saka madara, koda ta ankara salati kawai takeyi bcs tasan shi. Tayi mamaki sosai da baiyi magana ba.
Hanyar ɗaki ta nufa saita ji muryan shi, "Ke bazaki ci abinci bane?"
Cak ta tsaya saita juyo a hankali, bata yarda sun haɗa ido ba bcs idanunsa yana making ɗinta uncomfortable sosai.
"Banajin yunwa" ta faɗa tana murza ido tareda tura baki. Kawar da fuskarshi yayi saiya ce, "Maganin fah?"
Bata ce komai ba illa wasa da yan yatsun hannunta, tanayi tana kallon kasa.
"Please kici abinci saboda Kisha magani" ya faɗa kasa kasa. Babu yanda zata yi dole ta hakura ta koma, komai a hankali takeyi bcs duk ya takura mata da Idonshi.
Da a kaikaice yakeyi amma daga baya saiya fito ɓaro ɓaro yana kallon ta, ko sun haɗa ido saidai taji kunya ta cire nata amma bazai cire nashi ba.
Shi kawai yanda take yin komai yake mashi kyau, komai a hankali kamar batada jini. Gashi ta tsantsara kwalliya kamar yanmatan TV.
Haka suka gama cin abincin ta kwashe komai ta gyara tas. Ita tunda take zaman gidan bata taɓa takura ba kamar yau, duk inda taje kanshi yana kanta. Ya mayar da ita abin kallo dukta tsargu.
Tunanin yanda zai nemo sulhu tsakanin su yakeyi amma ya rasa. Gashi ko number ɗinta bashida shi balle ya aika mata text.
Kiran Bilqees yayi a waya akan ta tura mashi number ɗin Fadeela, within Minutes tayi mashi sending. Murna yayi sosai kuma yayi mata alkawarin waya dama tuntuni tana rok'on sa amma yaki sai yanzu.
Komawa ɗakinsa yayi bcs tuntuni Fadeela ta barshi shi kadai. Zama yayi akan bedside drawer ya daura kafa ɗaya kan ɗaya fuskarshi dauke da annuri. A hankali ya soma composing mata msg ya tura mata.
Yayi rubutu sosai saiya tsaya kafin ya cikata da surutu kuma still wani zuciya yana raya mashi zata raina shi amma wannan karon ko ajikin sa, indai zata amsa batunsa bai damu ba.
Ita kuma data koma ɗaki hawa kan gado tayi ta rungume pillow, kawai yanda Naufal yakeyi ke bata mamaki bcs farad ɗaya ya canza from the mean husband ɗinta to someone sweet and gentle.
Blushing Kawai takeyi bcs idan ya fara santa batasan irin daɗin da zataji ba. Tana kwance tana tunani tareda kallon ceiling, wani msg ya shigo mata, ta karanta yafi sau uku tana mitsike idanu amma still abu ɗaya tagani.
"Nasan cewa we didn't start on the right foot, but fate ya kawo mu tare. I feel wrong but I'm human Kuma dan Adam ajizine, I Can't help it but you reflect in my heart. You blossom in my heart and I'm going to cherish it till my last breath.
You are my sound of redemption, the faith that I've lost, the answer that I'm seeking no matter the cost. You taught me forgiveness by giving your love back to me even when I don't deserve it.
I see truth somewhere in your eyes, I can't ever change without you bcs you reflect Me and I love that about you.
No matter how I dodge trying to be careful, going round in circles still my feelings grew more for you.
What I'm trying to say is that, I just wish for us to be like other couples."
Kallon msg ɗin take wai ita Fadeela ya tura ma wannan abu, gyara zamanta tayi saita kalle kanta ta madubi ta kalle waya bakinta a buɗe tana mamaki.
#NiDaDiyata
#TeamNiDaDiyata
Awwwn I'm so sad, Wai yanzu ace TEAM FADEELA su suka lashe gasar. Ya akayi kuka zabeta bayan idon Naufal yana glimmering.
*All Rights Reserved*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top