Thirty-four


It was narrated form Anas that the Messenger of Allah said "None of you should wish for death because of some harm that befalls him, rather he should say: 'Allahumma ahini ma kanatil-hayatu khairanli wa tawaffani idha kanatil-wafatu khairanli (O Allah, keep me alive so alive so long as life is good for me, and cause me to die when death is good for me.)"' (Sahih)

***********

Nan take mutane sukayo kan Fadeela tareda kwanon ruwa, watsa mata akayi ana mata fifita.Tana farfaɗowa taga mutane charko-charko akanta tasan cewa ba mafarki takeyi ba da gaske ne.

Nanta sake barkewa da kuka mai tsuma rai, ita kuma Anty Saudah tana chan tana ganin tashin hankali saboda Miemie bata motsi har locacin.

Hadi ne ya sungumeta ya tafi da ita cikin Mota saboda zasu asibiti. Haka Anty tabi sahun shi a ruɗe ko mayafi babu, a hanya ne wajen parking lot wata ta mik’a mata hijabi.

Deela na ganinsu ta mik’e wai zata bi su, anyi anyi a hanata tareda cewa ta zauna a gida kila Babyn an fita da ita unguwa ne.

Nan Deela ta fashe da kuka, zama tayi dirshan a parking lot sai rizgar kuka takeyi. Kana ganinta gwanin ban tausayi, Hajia Rabi tazo ta janyeta daga wajen saboda maraice ne kafin sanyi ya shigeta.

Bilqees ne ta kira Naufal ta faɗa mashi abinda ake ciki, dama locacin yana hanyar layinsu. Juyawa yayi ya nufa hanyar asibiti.

Abinda yasa bai fara zuwa wajen Deela ba yasan cewa she is a strong woman unlike Anty Saudah. Yana isa locacin an shigar da ita ER, Hadi ne yayimasa bayani a gurguje.

Ita lokacin Anty Saudah tana kan kujera tanata kuka a hankali. Tunani ɗaya  yake mata yawo a kai, ya zata yi idan ta rasa yarta ɗaya tilo. Nan ta soma kuka a bayyane, Naufal duk zafin dayake ji a ranshi ya shanye yana bata hakuri.

Itakuma Fadeela tanata kuka kamar ranta zai fita, bata san Wanne yafi mata ciwo ba. K'onewan da Miemie tayi kokuma ɓacewan da Pha’eexah tayi?

Idanta yayi jazur kamar garwashi domin kuka kuma kanta sai sara yakeyi. Ji takeyi  kamar Allah ya dauki ranta ta huta da wannan tashin hankali.

Suma su Mommy sunajin abinda ya faru tazo gidan gona, anan kuma Fadeela ta soma sabon kuka, Mommy bata hanata ba illa tayata.

Haka suka runguma juna sunayi gwanin ban tausayi, kowa a wajen tausaya masu yakeyi. Gashi Fadeela tayi trying wayar Naufal bai dauka ba.
Sabon kuka ta somayi  saboda duk a zaton ta yana wajen Yasmeenah ne. Cema Mommy tayi bari taje asibiti wajen Miemie da Anty tunda anyi ransacking gidan ba’a ga Pha’eexah ba. Zamanta anan baxai fito da ita ba.

Mommy bata hanata ba saboda ita ta tuka ma motar da suka tafi.
Shikuma cikin ruɗewa ya bar wayar a cikin motarsa. Yasa bazai san wanda ke kiran sa ba. Su Grand Kadi da Abba sun tafi police station dasu gidan radio.

A wajen police station ɗinne sukaga IG watau babban Khattab yazo duba abu wajen DPO. Nan take ya saka kwararrun yan sanda akan case ɗin kuma yayi masu alkawarin basu huta ba sai anga duk wanda akwai saka hannunsa a cikin abun.

IG da kanshi ya kira Khattab ya faɗa mashi halinda ake ciki, anan fah Khattab ya ruɗe. Mukullin motarsa ya figa ya soma gudu babu ji ba gani.
Sau biyu yana kusan aukawa ma trailer amma yana kaucewa da wuri.

Haka yaketa yi harya kai asibitin.
Ko rufe motarsa baiyi da kyau ba ya soma gudu ciki, lokacin kuma yayi daidai da isarsu Fadeela.

Suna tsaye a bakin Emergency Room babu wanda ya fito daga ciki, likitoci ne keta aikinsu.
Anty Saudah tana ganin Fadeela saita sake barkewa da wani sabon kuka, nan suka rinka yi su biyu. Duk cikin family suna cikin wanda sukafi shakuwa da ita.

Shima Khattab yana ganin yadda suke kuka saiya kame chan kurya yana kuka. Hankalin Deela ya kwanta dataga Naufal a wajen.

Tsagaita kukanta tayi taje inda yake ya dafa kumatu yana tunani ta zauna, riko masa hannu tayi ta soma magana cikin kuka, “Pha’eexah ta.........” saita barke da kuka, kwantawa tayi akan kafadarsa tana kuka wiwi.

A hankali ta soma magana, “Shikenan an tafi da ita, na shiga uku na lalace” tana kuka sosai wannan karon kamar ranta zai fita daga jikinta.

Lokacin yayi daidai da fitowan wani doctor, da sauri suka tashi kowa yana so yaji me ake ciki. Shikuma Dr din baice komai ba zai ratsa su ya wuce.

Khattab ne finkico shi yana masa masifaMeye haka Doctor kana ganin mu tsaye zaka wani ratsa mu ka wuce

“Mallam sakeni mana” Doctor yace

Basan sake ba ɗin, dan rainin wayoya amsa

Naufal ne ya shiga tsakanin su, shima yaji haushin abinda Dr din yayi kuma yaji daɗin yadda Khattab ya saisaita shi. Kawai baya jin daɗin jikinsa ne da sai yayi ma Doctor ɗin dukan tsiya.

Doctor ɗin ya soma tafiya abinsa tareda nuna Khattab da yatsa yana hararar shi, Mommy tayi magana daga zaune.

“Doctor Haba mana ya zaka wuce mu baka ce mana komai ba”

Kiyi hakuri Mama, jini zani store in daukosaiya tafi.

Yaje ya dauko zai shiga ciki sai Naufal ya tambayeshi “Doctor please ta farfardo kuwa?”

Kuyi hakuri shi muke kokarin yi” nan take Khattab ya fashe da kuka, wai ace kusan awanta uku a ciki amma an kasa tada ta. Shima baya maso ya kawo wani mugun tunani waiko bazata farka ba.

Daddyn shine ya shigo tareda Grand Kadi da sauran jama’a. “Meye haka kake yi kamar mara tawakkali? Maimakon kayi mata addu’a” Daddyn shi ya faɗa.

Mikewa yayi ya tafi kurya inda yake kukanshi babu mai kwaɓansa.

9:30 pm......

Locacin wasu Doctors su huɗu suka fito duk suna zufa, ga kuma leberori suma suna fitowa da Miemie akan gadon da ake turawa.

Da sauri yan uwan Miemie sukayi wajen ta, kana ganinta saita baka tausayi matuka. Duk bandage a jikinta manya manya, daga fuskanta, cikinta haɗe da bayanta, kafar dama da kuma hannun damanta.

Ga wani an zagaye goshinta dashi, sannan an saka mata Oxygen domin shakar numfashi. Da sauri suka rinka bin gadon dakin da aka ware masu.

Daga nan wani Doctor mai suna Abdullahi ya soma magana, “Bincike ya nuna cewa ba bigewa tayi ba, an buga mata kanta da sledgehammer ne. Kafin wutan ya soma ci

Salati kowa ya somayi, masu matse kwalla kuma kamar su Fadeela da Anty suka soma. Kowa Mamaki yakeyi wai da gangan akaso kashe Miemie. Dr ne ya cigaba magana.

Munyi kokari munga munyi stabilizing ɗinta amma gaskiyar magana shine sai anyi addu’a saboda har yanzu jini yana fitowa daga cikin kanta kadan kadan

Kuma hayaki yayi yawa a cikin lungs ɗinta, yanzu dai idonta biyu kuma tana jinku. Amma bansan ko zata iya magana ba ko buɗe idonta

Daga nan sai Naufal ya tambaya asalin meya faru, Fadeela ta labarta masu komai daga zuwan  su Yasmeenah har batan Pha’eexah da kuma konewan Miemie.

Kuka takeyi sosai saboda tana tunanin yau zata rasa mutane biyu da sukeda mahimmanci a rayuwarta. Duk juriyar da Khattab yake kokarin Nunawa saida wani hawaye na takaici ya gangaro daga idanunsa.

Shiko Naufal abin duniya yayi masa chunkoso, ‘yarsa ta ɓace ga kuma k’anwarsa rai yana hannun Allah. Zuciyar shi sai zafi yakeyi yana tafasa, shiko kuka ya samu yayi ko zaiji sanyi amma ya kasa.

Idanunsa a kafe sai zallan ɓacin rai dake bayyana, tausayin kowa yake a wajen musamman wanda abin yafi shafa kamar Khattab, Anty da kuma Fadeela.

Doctor yace su Abba su biyoshi office zai masu magana, duk sun watse sai Khattab yaje inda Miemie ke kwance.
Rike mata hannu yayi yana rero kuka, ko ajikinsa baya jin kunyarsu Anty ko Deela. Baice komai ba haka ya kafa ma fuskanta da baka ganin komai daga bandage da Oxygen.

Saida yayi ma’ishi sai ya fara magana still hawaye yana malalo mashi daga idanu. Abinda yasa yaketa kuka baifi yadda yau da rana Miemie ke masa maganar mutuwa.

Yaya Khattab idan na mutu ya zakayi?” “Miemie meye haka?” “Please just answer me” “Bazaki mutu ba sai munyi aure kin haifan min yara masu kalanyan  gidan ku” dariya tayi kafin tace “You never know......”

Kuka ya sakeyi sosai daya tuna abinda ya wakana tsakanin shida Miemie da azahar dazu. Cikin kuka yace, “Please Haskena ki tashi karki mutu. Nasan anso a kasheki ne amma ina so ki basu kunya by staying alive”

Kuma i promise you duk wanda yayi ɗanyen aikin nan za’a kamashi duk inda yake.....” saiya cigaba da kuka.
Rike mata hannu yayi yana matsawa a hankali, itama ta rike masa hannu amma idanun ta a rufe. Suna cikin haka sai su Naufal da Abba suka dawo.

Yanda suka ga Khattab jaɓe jaɓe da hawaye gwanin ban tausayi, ita Anty tana tausayin shi saboda yama fita damuwa.

Meye haka kake kuka? Wayace maka mutuwa zatayi?” Naufal ya faɗa a takaice. Mikewa Khattab yayi yana jan manjina saiya bar ɗakin gaba daya.

Motarsa ya koma kai tsaye, sai a lokacin ya lura baima kulle ba. Kifa kai yayi akan steering yana sheshek’ar kuka.

Itakuma Deela zuwa tayi tana shafa mata goshinta wanda akwai bandage akai, hawaye itama takeyi saita soma magana da dishenshen muryanta.

“Please Miemie ki tashi kinji, kinga an tafi da little one. Im sure zaki san wanda yayi wannan abun....” kuka ta barke dashi mai kara, su Mommy da Anty sunata matse kwalla saboda tausayin Deela.

Tabbas zata shiga wani yanayi idan ta rasa Miemie kuma bayan ta rasa ‘yarta. Ciwon Miemie yanzu ya hanata kukan rashin yarta.

Naufal ne ya janyo Kujera ya zauna dab da ita, bubbuga mata baya yayi ya kwantar da ita akan kafaɗarsa.
Kiyi hakuri kinji, in sha Allah komai zai daidaita

“Allah yasa” ta amsa.

Suna haka kowa yana addu’a a ranshi. Abba ne yace masu Fadeela su tafi da Anty. Akwai nurses da aka ware zasu rinka dubata kafin gari ya waye.

Kuka Deela ta barke dashi wai baza’a bar Miemie ta kwana ita kadai da bare ba. Hakuri  aka rinka bata amma taki shiru. Naufal ne yace zaije ya dauko Abla ta kwana  da ita.

Anan ta rage kukanta sai tace yaje ya dawo zata zauna da ita tukun kafin yazo ya mayar da ita gida idan an dauko Abla ɗin. Kowa ya tafi tareda mata addu’a.

Naufal ya tafi ya dauko Abla, yana parking lot dasu Anty da Abba za’a tafi sai suka ga Khattab cikin motarsa yana kuka. Tadashi aka yi ya tafi gida sai yace ba yanzu ba tukun.

Abba ne yace ya shiga ciki ya zauna kafin Naufal yaje ya dawo saiya tafi. Shiga yayi ciki jiki babu kwari duk ya gaji. Ga wani matsananci ciwon kai da kuka da haifar masa.

Zuwa yayi cikin ɗakin saiya tarar da Deela ta shingiɗa, zama daga chan bakin kofa amma ta ciki. Tagumi yayi saiya soma gyangyaɗi saboda gajiya.

Itama barci yana daukarta amma tana buɗe idonta ta. Suna cikin haka sai barci ya dauke su duka. Basu suka farka ba sai sanda Naufal ya dawo da Abla.

Ya akayi wanchan abin ya daina motsi? Naufal ne ya tambaya sanda ya shigo kana ya nufa hanyar ECG da aka haɗa da jikin Miemie.

A firgice suka tashi, Deela tana mitsike ido Shikuma Khattab ya zura da gudu wajen gadon. Saka kunnen shi akan kirjinta yayi amma baya jin alamun bugun zuciya.

“Why is she not breathing?” Deela ta faɗa hankali a tashe.

Da sauri ya mayar da kunnen sa wajen hanncinta tareda cire Oxygen tube ko zaiji alamun shakar numfashi amma wayam.

Innalillahi wa inna ilayhi rajiun ra rinka maimaitawa yana yi yana jijigata amma bata motsa ba, asalima jikinta a kankame.

Fadeela ce ta tsandara ihu saita sulale kasa, da sauri Naufal ya tarbota. Bata hakuri ya somayi yace kila wani abune daban.

Ko ba’a faɗa mashi ba yasan Miemie ta koma gidanta na gaskiya. The worst part shine an kasheta ne bawai hakanan bane, tunanin sa ɗaya how can someone be this cruel?

Abla zuwa tayi ta rungume Deela sunata  kuka  tare, Fadeela ne ke magana cikin kuka a hankali, “Innalillahi wa inna ilayhi rajiun, shikenan Miemie ta tafi barmu

Shikuma Khattab gefe yake ya zauna a kasa zaman dirshan, kwakwalwarsa sai tafasa yakeyi. Shi tunda yaji labarin accident ɗin yasan za’a yi haka.

Yau gaba ɗaya sai maganar mutuwa takeyi da kuma rok’on sa gafara. Har haushi yaji yayi mata magana, ce masa tayi “you never know when you’ll die, gwara ka shirya kafin lokacin ka”

Duk kalamanta yanzu yawo yake masa a kai, saidai yanzu Idonshi ya kafe. Yama kasa kuka, salati kawai yake cikin ransa. Kirjinsa zafi yakeyi ga gudu da sauri kamar zai fashe.

Ji yayi kamar an daura mashi katon dutse cikin kirjinsa, ga kuma miyau na bakinsa ya kafe k'ab. Karkarwa kawai yakeyi kamar yana jin sanyi.

Shikuma Naufal komawa yayi bakin Varenda yayi tagumi, abin daure masa kai yayi wai dazu ya ganta  yanzu kuma ta rasu. Daukar wayarsa yayi domin ya kira ABBA.

Assalamu Alaikum, ya akayi  ne Naufal” Abba yace ta ɗayan ɓangaren. Naufal bai iya amsa sallamar ba, kawai  magana ya soma.

“Abba shikenan Miemie ta tafi ta barmu. Abba Miemie ta rasu, ta koma gidanta na gaskiya

Innalillahi wa inna ilayhi rajiunabinda Abba ya iya faɗi kenan.

Shikuma Naufal wasu zafafan hawaye suka soma gangarowa daga idanunsa, da farko kadan kadan sai kuma suka fara gudu.







#NiDaDiyata





~Yarinya Mai DIMPLΣS~

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top