Thirty
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said that the Messenger of Allah (peace be upon him) said: When Allah decreed the Creation He pledged Himself by writing in His book which is laid down with Him: My mercy prevails over my wrath. It was related by Muslim (also by al-Bukhari, an-Nasa'i and Ibn Majah).
**********
Kwanaki sai wucewa sukeyi babu alamar komawanta, da kanshi ya tafi gidan Grand Kadi ya faɗa masu abinda ke faruwa.
Mommy ta kirata tayi mata faɗa sosai kuma tace she is disappointed in her, duk tarbiyan da sukayi mata saida ta watsa masu kasa a cikin idanu.
Grand Kadi ne yace ayi mata uzuri gwara ajita bakinta. Washe gari suka tafi gidan gona inda Fadeela take, Naufal yaci shadda dakarkiya fari ɗinkin babban riga.
Yana tafe yana raha tareda full confidence yau zai tafi da matarsa. Kowa ya taru a falo, Big Daddy, Grand Kadi, Abba, Mommy, Mama sai kuma Anty Saudah.
Sannan saisu Deela da Naufal. Grand Kadi ya buɗe taro da addu’a sannan ya fara faɗin fa’idojin aure.
Daga nan sai Big Daddy ya fara magana akan batun auren su, Fadeela aka tambaya menene ainihin abinda ya faru tsakanin su.
Bata ɓoye komai ta fayyace musu komai, kowa salati ya rinka jerowa bayan ta gama wanda ita a lokacin kuka takeyi. Mama ce ta soma magana “Amma baki kyauta minba, aida kin faɗa min da ban rinka bashi abinci ba idan yazo”
Big Daddy yace yanzu babu wani sauran magana kawai Fadeela zata koma ɗakinta ta haihu a chan.
Nan take Deela ta barke da kuka tana sheshek’a. Kuka takeyi babu kakkatawa kamar zata haɗiye ranta.
Abba ne yace bai kamata Abi sarai ba, ayi mata hakuri tunda yanzu baifi saura wata ɗaya ta haihu ba.
Dagowa Naufal yayi zaiyi magana sai Anty ta kasteshi akan ya rufe masu baki, dole yayi shiru tunda babu sa’anshi a wajen.
Mommy ranta yayi bala’in baci saboda kawai ana sangartar da Deela ne, sau da dama mazajen wasu suna dukansu amma suke zaune ras, kawai dan an mare Deela za’a ce bazata zauna ba.
Ita tana ganin ana bama Fadeela dama ta raina shi ne. Haka dai aka kyale Fadeela ta cigaba da zama gidan Anty har Allah ya rabata da cikin lafiya.
Naufal ya nuna bacin ranshi a fili saboda ba’a gama magana ba ya fita daga falon ya koma cikin motarsa ya kifa Kanshi.
Kuka ya soma rizga wiwi saboda ya gaji, gashi yanzu Yasmeenah ta sakashi a gaba wai saidai ya aureta kuma bazai soma zancen wani aureba tunda Deela bata gidan.
Ita kuma Deela murna fal ranta ta samu nasara, Mommy magana sama sama take mata bayan abin ya faru saboda takaici. Koda suka kebe a ɗakin Deela karfin jikinta kawai ta tambaya sai sukayi shiru.
Kuka Fadeela ta somayi kana ta soma magana, “Mommy ki yafe min. Nasan na bata maki rai kuma zakice na watsa maki kasa a ido, but I promise you tarbiyan da kika min shiyasa yake kwaɗayin zama dani, please kiyi hakuri harna haihu tukun kafin ku mayar dani”
Mommy kawai kallon Deela takeyi yadda ta kafe, ba k’aramin abu zai mayar da ita haka, duk cikin yaran family itace batada riko ko naci akan abu, tunda ta nace akan haka to gaskiya ita kadai tasan ukuban datake fuskanta.
Murmushi ta sakar ma Deela saita matsa inda take ta soma bubbuga mata baya, babu komai baby, Allah ya sauke ki lafia”
“Amin summa Amin”
Bayan kwana biyu......
Naufal yana kwance a office ɗinshi abin duniya yayi mashi chunkoso, saiga Secretary ɗinshi ya shigo ya bashi wasu takardu.
Nan take ya haushi da faɗa wai baza’a barshi ya huta ba, daga nan yayi tsaki ya dauki jakarsa zai koma gida.
Yana isa yayi horn sau ɗaya, biyu, uku kafin mai gadi ya buɗe masa. Aiko nan ya soma masa masifa yana mai barazanar kora idan bai dauki hankali ba.
Yanzu yana Missing Fadeela to the extend daya zama very aggressive, kana kallonsa zai iya gaya maka magana san rai, idan kai mai hayaniya ne sai faɗa ta kaure maku.
Dakin Deela ya wuce wanda ya mayar nasa tun kwanaki, kwanciya yayi akan gado yana tunaninta ga kamshin turarenta ta Ko’ina. Abin bai isheshi ba dauko Chanel No 5 yayi ya fesa akan pillow kana ya runguma kamar ita ke wajen.
Turaren da idan ta saka da yakeji kamar ya kasheta yanzu shine abin so wajen shi. Yana kwance sai cikinsa ya fara kiran ciroma alamun yunwa, babu kidan da bayayi daga yori yori sai bumper to bumper.
Murmushi yayi mai kuna a rai kana yace a fili “Allah ya jikan Fadeela badan bata mutu ba, da yanzu tazo tana rok’ona naje naci abinci”
Saida ya huta gajiyarsa yayi sallah tukun kana ya wuce kitchen yana kallon me zai dafa, Indomie ya yanke shawaran ya dafa tunda yafi sauki.
Ya daura Indomie akan gas saiya fara kokarin buɗe Geisha. Cikin Kaudi ya karya karamin handle din abun dole yayi amfani da wuka.
Ya dukufa yana wannan ashe ya mance bai saka seasoning ba, maganar albasa da kayan miya bai taso ba saboda baima yi niyyar sakawa ba.
Kaurin konewa yaji gashi ko Geisha bai gama fafewa ba, yana zuwa da sauri ya taba zai sauke dama wajen electric ne. Nan take wuta ta fizgeshi, da sauri ya bar wajen saboda har cikin zuciyarshi yaji kamar za’a cire mashirai.
Gashi bai cire ba, ga shocking ga kone hannu dayayi, saida yadan huta kafin ya koma gashi yana gani Indomie ɗin yayi kurmus yayi bakin kirin.
Ko’ina kauri kamar ana gobara, kashe socket yayi saiya bar cikin kitchen ɗin bcs shi karin kanshi abin ya dame shi.
Buɗe fridge yayi zai dauki koda lemu ne amma wayam saboda ya cinye komai tas kuma bai siya wani ba, koda yaushe Deela tana hanyar kasuwa idan ta lura abincin su yayi kasa.
Haka ya sake hawa sama yaje bayi ya saka hannusa a cikin ruwa saboda yana masa zugi, gashi masu restaurant ɗin layinsu sun fara mashi sheda har sun daina cewa ‘Welcome Oga’ sai ‘Customer welcome’
Yanda yake sintiri gidan abinci ba kimansa bane a matsayinshi na namijin aure, daidai gwargwado Deela ta kare masa wannan hakkin saidai idan shine bayaso yaci.
Shikuma yanzu baya son yana haduwa da Yasmeenah saboda tana stressing ɗinshi akan ya nuna soyayyarsa yace zai aureta. Shikuma ya bata uzuri akan tabari matarsa ta haihu tukun.
Shi a locacin yanada tabbacin dole Deela ta dawo saboda batada wani excuse, sai yayi aurensa hankali kwance.
Kuma abu na biyu dayasa yake gudun ta face karta gane cewa Fadeela bata gidan a irin cikin zance haka kafin ta raina shi akan ya kasa rike gidansa.
Haka ya hakura yaje ya siyo kayan shayi wanda dama ya kare da bread, yana shiga kitchen zai daura ruwan zafi saiya tuna haɗuwarsu da rana, girgiza kai yayi ya bar wajen.
Bayi ya wuce ya ɗebo ruwan zafi kana ya soma dakan bread ɗinsa. Yaci yafi rabin babban leda amma cikinsa kamar an shafa ne. Wani matsananci yunwa yakeji saboda rabon dasu haɗu da abinci tun jiya da suka fita lunch da Yasmeenah.
Coke yayita sha sai yanzu, mukullin mota ya dauka yace gwara yaje gidansu kafin yunwa ya kashe shi.
Yana isa parking lot yaga Miemie da Khattab suna cikin mota ana dariya.
Haushi ya kamashi ya nufesu gadan gadan, su basu ma sani ba kawai suka ganshi a gabansu yana haki.
Su kuma abinda suke ma dariya shine Khattab yana bata labarin Lili, yanzu baya ɓoye mata komai tun wani rana da Lili ta kira a gaban Miemie har yayi sanadiyar dena masa magana na kwana biyu.
Yanzu baya ɓoye mata komai, duk shirmen data ke masa yake faɗa mata sai suyita dariya. Ita Miemie murna take ta samu wanda ta fita hauka.
Muryan Naufal sukaji wanda shiya saka suka bar dariya tareda tsayawa cak.
“Bana hanaku zance cikin mota ba?”
Khattab ne ya fito yana kokarin mika ma Naufal hannu su gaisa amma yaki bashi, mayar dasu cikin aljihu yayi kafin ya cigaba da magana cikin faɗa.
“Wannan wani irin abune? Idan kanwarka akema haka zakaji dadi? Koda yake bakada kanwa you wouldn’t know”
Juyawa yayi ya kalle inda Miemie take tsaye tana tura baki, “wuce ciki, ta ɗin an fasa”
Tura baki tayi tareda makale kafada tana bubbuga kafa a kasa, “Haba Yaya yanzu yazo fah!”
“Ni kike gaya ma haka, Karyan iskanci! Ni sa’anki ne ?Wallahi na sameki a wajen saina karya ki”
Saiya cire takalminsa ya nufa inda take, Khattab yana ganin za’a nakasa mashi Haskensa saiya ce mata ta tafi kafin taci dukan banza. Anan ta ruga tana faɗin “saina gaya ma Anty abinda kamin” ta faɗa tana kuka.
Yaji haushin da za’a kai kararsa wajen Deela amma babu yanda zaiyi. Juyawa yayi ya kalle Khattab, da sauri ya shige motarsa kafin Naufal yayi masa magana tareda mashi saida safe.
Shikuma saiya tafi cikin gida, yana shiga tareda sallama ya tarar da kowa a falo, as expected Deela a ciki ta amsa mashi.
Murmushi yayi saboda komai zatayi bai zai koreshi daga rayuwarta ba. Miemie ta soma korafi akan masifan da yayi mata. Anty Saudah ce ta zungureta da kafa akan tayi masu shiru.
Deela na daga gefe tana fere kankana da abarba. Zama yayi akan kujera harda canza masu chanel daga ZeeTv zuwa CNN, “Ya haka Mallam?” Anty Saudah tace.
Itama Deela taji haushin abin amma ta danne, dariya ya soma kafin yace, “news ne fah”
“Maza ka canza mana, kaje gidanka chan amma nan gidana ne”
Baiso ba ya canza masu, yana lura da yadda Deela taki kallonsa, yama mance yaushe rabon dayaga idonta. Kullum tana cikin kallon kasa kafin tabar wajen baki ɗaya.
“Miemie jeki dauko min plate matana ta saka min kankana” ya faɗa yana kallon Deela yaga yanayinta.
Babu musu tayi yadda yace, itama Deela ta zuba masa sosai yasha ya nare. Daga nan ta soma kokarin tashi tsaye, yanda takeyi komai da kyar gata da nawa asalinta.
Gashi ciki komai a hankali zakayi, sannan kafarta sun kumbura sunyi narka narka kamar doyar Benue. Duk tausayinta ya kamashi.
A hankali ta soma tafiya tayi hanyar ɗakinta saboda idanunsa yana takura mata. Bayan ta tashi Anty ta tambaye shi ko a kawo masa abinci, baiyi musu yace mata eh.
“Daka rike matarka da kyau ai bazaka rinka bin gida je kwaɗayi ba” Anty Saudah ta faɗa sai tayi hanyar kitchen.
Wani tunani ya faɗo mashi a rai ko ya auri Yasmeenah kurum koba komai zai rinka samun abinci a sauki.
Wayarsa yayi kara kuma wanda yakeso yayi magana da ita ne.
Yana dauka yaji kukanta sosai daga ɗayan ɓangaren, “da kyar nasha wajen Yaya Huzaifah” taketa nanatawa tana kuka.
“calm down meya faru? Talk to me please”
Cikin kuka ta fayyace masa abinda Huzaifah yayi mata, hankalin Naufal yayi mumunan baci. Hankalinsa ya kasa daukar abinda ya faru, ya kasa saisaita tunanin sa waje ɗaya.
Wai ace wanda zai aura akeso a lalata, gwara yayi gaggawa ya aureta kafin suyi mata mai gaba ɗaya, besides jiran meya keyi!
#NiDaDiyata
*All Rights Reserved*
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top