Ten


Malik relate from Nafi that when Abdullah ibn Umar sneezed and someone said to him, "May Allah have mercy on you," (Yarhamuka'llah), he said, "May Allah have mercy on us and you, and forgive us and you." (Yarhamuna'llah wa yaghfirlana wa lakum)

***************

17 days later.....


MIEMIE



Tafiya takeyi cikin sauri sauri, kallabinta tamke akan qugun ta. Dayake tanada tsawon gashi haka wasu suka bazu a fuskarta har yana tsone mata ido.


Bata cireba haka ta barshi tana tafiya abinta. Ta kai babban titi near Bauchi club dake kusada makarantar su na Special school. Tana kokarin tsallake titi amma dataga mota ya danno kai koda ta kai rabi ne kuma motar yayi nesa da ita zata pella baya.


Tsaye yake gefen mai gasa masara yana kokarin ya siya, baima lura da wasu halitta ba a wajen balle ita. "Amma anyi wawiya" mai gashin masara ta faɗa. Juyawa yayi tareda cire tabaransa ya kalli abin ake magana akai. Wata yarinya ya gani wanda bazata kai 15 yrs ba tana guje guje a titi. Tsaki yayi ya mayar da tabaransa ido saiya mika ma mai gashin masara dari biyu "Keep change" ya faɗa sai yayi hanyar motarsa.


Ta kara komawa baya da gudu a karo na uku kuma duk a Idonsa. Tsaki ya karayi ya soma danna wayarsa ko ajikin sa. Wasu samari su uku sukaje wajen ta suna mata surutai, Ita kuma bata kula suba. "Bada ke nake magana ba?" ɗaya daga cikinsu ya faɗa tareda chapke mata gashin kanta. Kara ta saka wanda ya mayar da attention ɗin kowa kansu.


Kwafa yayi saiya fito daga motarshi da saurin gaske, "Kai meye haka Mallam, kanwata ce fah" ya faɗa tareda janyo ta zuwa inda motarsa yake. Buɗe kofar gaba yayi saiya turata ciki. Shima ya zagaya ɓangaren driver ya zauna saiya kunna motar tareda fadin "Inane gidan ku na kaiki"


Bata amsa mashi ba illa kuka data keyi, tana jin alamar ciwonta zai tashi ne yasa ta gudu daga school ta fara gantali akan titi. Duk a hargitse take kamar bible din hausa.


Daya lura batada niyar amsashi saiya kira babanshi which shine IG din yan sanda. Bayan wayan da wajen 45mins haka saiga babanshi ya iso tareda escorts dinshi. Kallo ɗaya yayi ma Miemie yasan cewa akwai alamar tambayan hankali a tareda ita.


Tag dinta na suna dake rataye akan Wuyanta wanda shi guy din baima lura ba babanshi ya ɗaga ya karanta. "Bauchi Special School" ya karanta. Sai ya mayar da attention dinshi kan yaronshi tareda faɗin "Khattab ai ga komai a rubuce don ruɗewa shine ka kirani, gashi an rubuta Laurat Hussain Beli" sosa k'eya Khattab yayi tareda dariya saboda yasan he wasn't really paying attention to her.



Nan take IG yasa wasu police suzo su tafi da ita station ayi documenting komai cikin protocol. Nanfa ta soma dambe dasu wai bazata bar motan Khattab ba, shure shure takeyi tana hambarin police din idan kuma fatan ka ya kusa da bakinta saita ganna maka cizo. Haka tayi biji biji dasu tayi masu jina jina, su kuma suna raga mata ne saboda ba lafia ga yarinta. Daddyn Khattab yace su kyaleta.



"Bakyaso ki bisu ne?"


Gyada kai tayi alamar eh


"Ina ne gidan ku?"


"Ni tareda YaNaufal Zan tafi"


"Waye YaNaufal?"


ɗaga idonta tayi saita nuna Khattab. Sai IG yayi murmushi tareda faɗin, "Ai sunan shi ba Naufal ba, bakiji Khattab nake kiransa dashi ba."



"Na sani amma idan mutum yanada kirki toh YaNaufal zan kirashi" tafada tana Sheshek'ar kukanta.


Khattab ne yace mai zai hana aje school dinta tunda gashi rubuce maybe aga family member dinta.



Daga ɗayan bangaren Anty Saudah take zaune dirshan a gaban school din Miemie wai sai an fito mata da ɗiyarta. Tun sanda driver ya koma gida wai babu Miemie babu dalilinta saita saɓa gyale tawuce makarantan tanata kuka. Su kuma school din Naufal suka kira a matsayin Next of kin dinta. Duk an taro hankali a tashe kowa yayi charko charko, Naufal tunanin shi ɗaya ya zaiyi idan ya rasa Lil sister dinshi.


Duk zufa yakeyi ya rasa meke masa dadi, har police station yaje yayi reporting babu wani kyakyawan labari. Su Abla da Bilqees suma sun samu labari hankalin su a tashe, sai Abba yace suje gidan gona incase Miemie ta gane hanyar gida. Ita ma Mama bataji dadin abin ba sanda ta samu labarin, tasan cewa babu daɗi babba yayi ɓatan hanya balle yaro. Kawai addu'a takeyi Allah yasa a ganta.


Su Khattab sun nufa hanyar makaranta Miemie za'a mayar da ita. Shi dai baice komai ba illa tuk'a mota, ita kuma kuka take rusawa. A hankali ya furta "Sunana Khattab ba Naufal ba" ta gefen ido ta kalle shi saita watsar.



"Na sani amma banga dama bane" ta faɗa tana fyace magina da kwallar riganta. Nan take abin yaba Khattab kyama saida yayi kakarin amai, dama shi abu kadan saiya saka shi amai. Waigawa yayi don yayimata magana sai ya hange tasono mak'ale a hancinta, da sauri ya buɗe window ya tsida miyau.


Ita kuma Fadeela tana cikin kitchen ta dafa abinci, Danbun shinkafa tayi wanda yasha zogale da gyada ga kuma nama k'anana a ciki. Sai kuma tayi juice ɗin garin kuka wanda yasha pineapple da cucumbers sai ta haɗashi da Sambousah. Ta jera a wasu fararen Italian coolers komai yayi tsaf sai san barka.


Bayi ta wuce tayi wanka tareda jero alwala, tayi nafilfilon ta saita haɗa da sallar Asr. Ita kadai tasan meke damunta saboda a duniya rainin wayau ne ta tsana. Tsaki ta doka tareda faɗin "Karma kazo mana tunda dama ban gayyace kaba" tana cikin haka ne saiga Mommy tazo, "Har yanzu Naufal ɗin bai zoba?"


"Eh shine nima na gani"


"To kira wayansa mana kiji ko lafiya"


Shiru Fadeela tayi bata san mezata ce ba, saboda rabonta da shi tun ranar daya watsa mata kudi, itama Mommy a Pharmacy suka haɗu shine sukayi exchanging number. Toh a bakinta ne Fadeela taji zaizo sai Mommy ta tursasa ta akan saita mashi girki.


Maza ki saka wannan kafin yazo baki shirya ba Kinga babu daɗi, ita kawai kallon Mommy takeyi yanda take rawar kai akan Naufal, "Da kinsan true colors dinshi da kin daina haka" ta faɗa a ranta. Tsam ta mike ta dauki kayan, Sky blue cord lace da akayi mashi ɗinkin kimono. Batayi makeup ba saboda acewarta kanayi ne wajen burge mutum kuma ita tsakani da Allah bata sanshi kawai tasan cewa dole ta mutunta shi.




Su Khattab sannu a hankali suka isa school din Miemie, suna gaba su IG da escorts na baya. Kashe engines dinshi yayi saiya ce, "Okay sauka muje wajen Principal" bata kulashiba kuma bata nuna tanada alamar motsawa ba. Sauka yayi saiya zaga ta ɗayen bangaren. Dayake motarsa Range rover ne kuma it's somehow high sai Khattab ya mika mata hannun sa ta kama ta sauko.



Aiko a idan Naufal akayi haka, da sauri ya karasa tareda cin kwallarsa "Ubanwa ya baka dama ka dauki k'anwata? Da harzaka sakata a cikin akwalan motar ka salan whitlow ya kamata"

Kafin Khattab ya amsa Abba yace, "Meye haka kake yi sai kace dage? Dalla sake shi" bai so ba saiya sake shi. Ita kuma Miemie kallon kowa tayi saita ruga motar Khattab ta dauke Masara a ciki ta fara gabza. Naufal ranshi yayi bala'in baci, "Zo nan Mallama bana hanaki barin school ba? Hawan jini kike so ya kamani na mutu koh? Shikenan na tafi naje na mutu" sai yayi hanyar motarshi. A guje taje tana bashi hakuri saboda a duniya ta tsani wasan mutuwa.


Su kuma su Abban Khattab yayi Introducing kanshi a matsayin Inspector General Hamza Aminu Danbatta. Anan sukayi gaisuwan mutunci shine ya zayyana masu yanda Khattab ya tsinci Miemie. Nan take Abba yasa Naufal ya ba Khattab hakuri, musabaka sukayi sai yace,
"I'm sorry man, I don't know what my life will be Idan babu ita"

"Dont worry komai ya wuce bcs I don't hold grudges." Ita Anty Saudah saida ta rankwashe Miemie akai, ita kuma Miemie tayi dariya wai da gangan ta gudu wai saboda YaNaufal yace bazashi wajen amaryar sa da ita shine tace gwara kowa ya rasa.


Sai a lokacin ya tunada zancen wani Bad Luck, gefe yayi ya kira Mommy tareda bata hakuri akan rashin zuwan shi, yayi mata explaining Miemie ta ɓata ne but yanzu an ganta, in sha Allah within the week Zai duba ta. Jaje tayi masa tareda aika regards dinta wajen Miemie da Mamanta.


Wata sabuwa wai inji yan cha cha! Miemie ta kafe bazata shiga motar kowa ba saina Khattab, shi kuma Naufal yace bata isa ba, nan aka rinka Jani in jaka da ita saida Khattab ya durkusa gabanta yayi mata magana cikin raɗa kafin ta tashi ta shiga motar Naufal.



"Everything yayi daidai yanzu" ya faɗa saiya nufa hanyar motarsa. Naufal dabai iya boye abin mamaki ba saida yayi magana "Mai kace mata data hakura?"


Murmushi yayi tareda faɗin "It's our secret"



Nikuma Dimples nace Iyye su Miemie yan mata.



Ita kuma Fadeela ana gaya mata bazai zoba tayi kwafa saita kwashe abincin kaf takai ma mai gadi tace masa yaci sauran ya bama almajirai.



"Daga yau na gama maka girki" ta faɗa yayin da take hayewa upstairs.








*All Rights Reserved*

💥∂ιмρℓεs💥

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top