Six
Narrated 'Abdullah bin 'Umar, Allah's Messenger (pbuh) said, "A Muslim is a brother of another Muslim, so he should not oppress him, nor should he hand him over to an oppressor. Whoever fulfilled the needs of his brother, Allah will fulfill his needs; whoever brought his (Muslim) brother out of a discomfort, Allah will bring him out of the discomforts of the Day of Resurrection, and whoever screened a Muslim, Allah will screen him on the Day of Resurrection . "
********************
Saboda yanda kayana ya matse ni, da ban na shiga hall ɗin batare da zugan amarya ba. Na samu wani seat a gaba na zauna tareda sauran friends ɗina tunda high table is just for bride and groom.
Kowa ya hallara da wanda aka gayyata da wanda ba’a gayyata ba, kowa yazo rangem yaci shinkafa.
Yana isa Zaranda hotel inda za’ayi dinner din, yawan mototin wajen ya bashi mamaki. Hall ya cika sosai kuma rabin gurin yan mata ne “Sunzo tallan kai” ya fada a ransa yana taku cikin k’asaita.
A wani table guda ɗaya dattawa uku ke zaune kuma duka aminan Alhaji Sulaiman ne(Baban ango).
“Ai ina gaya maku na rasa dalilin sa na kin yin aure gashi ba yaro ba” Engr Hussain ya faɗa fuskarshi duk takaici.
Alhaji Musa ya dauki samosa guda ya gatsa saiya buɗe roban Swam ya sha, “Kuma kace ya gama karatu koh?” ya tamabaye su.
“Yaron kirki mai taimakon iyayen shi, wallahi tun sanda Engr Yayi retire ya rinka daukar ɗawainiyan k’anansa, amma sam baya maganar aure” Alhaji Sulaiman ya chapke.
Saiya k’ara da cewa “ko dayake tare suka tashi da Sadeeq duk halinsu ɗaya na rashin san aure amma shi Sadeeq baida aikin yi sai 8 Months ago ya samu. Amma shi kuma gogan ya kusan shekara 3 dafara aiki kuma yanzu yana chaɓawa sosai a garin Bauchi”
Shi dai Alhaji Musa shiru yayi yana sauraron hirar da abokinsa yakeyi da amininsa. Kuma yaji ance yanada da halin rik’e mace ga kuma yaji ance yanada hankali da tausayi.
“wow!!! dude ɗin chan ya hadu, sai dai baki ne” Mansura ta faɗa. Ita kuma Sadiya tace, “wanga green eyes haka, naji ance idan dare ya tsala masu irin idon suna komawa mage” sai gabaki ɗayansu suka kyalkyale da dariya.
Ni ko jin abinda suke banayi saboda ina sana’ata na shan wak’a, Mansura ta fizge earpiece din “wai dalla meye haka? Inace Momy ta hana ki?” juyawa nayi na kalli left and right cikin isgilanci kafin nace, “banga momy anan ba, so bani abuna” saina fizga abina.
“Amma bansan guy ɗin, saboda yasan ya haɗu shine yake wani salo” Sadiya ta faɗa. Ni kuma na juya inda suke kallo naga waye amma naganshi a duke yana gaida wasu.
“Ashe yanada tarbiya” Mansura ta faɗa, har cikin raina ina so naga fuskarshi saboda yanda suke kod’ashi yayi yawa, inaso naga if he is worth kwace min earpiece ɗina.
Naufal ya cika yayi fam, tun shigowarsa yan mata ke kallonsa but nasu yafi bak’anta mashi rai. Mutum ɗaya ta kalleshi tayi magana sai sauran su kwashe da dariya ba karamin haushi ya bashi ba. Fatan shi ɗaya, wata tayi mashi ba daidai ba ya daketa tunda yanada saurin hannu.
Dama yazo wucewa ne yaga Abbanshi da baban Sadeeq, toh shine suke gaisawa while yan matan two table away sunata giggling suna kallon shi “Nifa raini ne banso” ya faɗa a ransa.
Su Mansura kuwa sai magana suke a hankali suna kallon Naufal, ni kuma tuni na fizge earpiece dina na mayar mazauninshi. Daukar Pepsi nayi na buɗe sai abin ya fara zuba. Da sauri na mike ina kokarin juyawa sai na bige mutum.
Shi kuma yazo wucewa ta gefen su sai wata daga cikin su ta bigeshi tareda watsa mashi Pepsi. “D’ankari” ya faɗa a ranshi. Ni kuma Dimples nace abin nema ya samu wai matar makaɗi ta haifi ganga.
Tasss ya watsa mata mari, sai ya k’ara dauketa da wani ta ɗaya bangaren, marin daya yanka mata mai sa fitsari a jiki ne kuma dole kaga taurari.
Ni kuma a razane naja da baya dana lura azzalumin mutumin dana haɗu dashi kwanaki ne, “dole a rina wai an sace zanin Mahaukaciya”
Dama suna bashi haushi sai ya lura “Bad Luck” ne a gabansa kuma ga earpiece a kunnenta yasa ko tunani baiyi ba ya watsa mata frustration dinsa.
Tabbas sukuku da mood swings dayake ta samu yau sanadiyar zaiyi gamo da ita ne, bcs duk wanda ya hadu da ita yayi gamo. Idanunshi suka kad’a bcs Bad Luck din dake binta yasa ya fadi ɗazu a bayi.
Karkarwa na somayi bakina sai rawa yakeyi, gumi nake tayi duk na jik’e hawaye sai malalo min yake kamar bakin teku. Baya na rinka ja ina kallon mai zai biyo baya, daɗin abin hankali mutane baya kanmu sabida sunata cin abinci.
“Yanzu dai na tabbatar a jakunan duniya, kinfi kowa jakanci” ya faɗa a hasalce. Tsuru tsuru nayi bance komai ba. Mansura ce tazo da sauri “Kayi hakuri Mallam, Fadeela is very clumsy” “Kambu” na faɗa a raina
Word ɗin clumsy data fada ya bani haushi, bata ganin ya mareni ne? Kuma shine zata bini da zagi “toh saime idan na watsa mashi drink? Yafi karfi ne” Na fada ina turo baki tareda juya idanu duk salon marasa kunya.
“kefa na lura karaman mara kunya ne, kuma samarinki masu fruits basa nan balle su tare maki” ya faɗa sai kuma ya cigaba da sababi “kisan me zaki rinka faɗa kafin ki yaba ma aya zakinta”
Wasu yara suna guje guje sai suka tureni na sake watsa mashi, tasssssss ya sake dauke nida mari saida naja baya. “Dama bakisan ina raga maki bane saboda ke sa’ar k’anwata ce, amma bari na koya maki darasi”
“Daga yau kin gama rashin kunya, ko a mafarki kikaga wasu zasuyi zaki kwaɓe su”
Idanun kowa a kanmu, kafin kace ‘Jack Robinson’ Kowa ya dauki wayar shi anata video. Anata posting a snapchat da Instagram, dama Mallam Bahaushe yace idan ba’a yi faɗa a biki ba baya armashi. Koba komai an samu abin tseguntawa.
Ja da baya na rinka yi hannu na biyu a kunci na, Shi kuma Naufal ya dauki alwashin sai ya shiga jikinta da duka sosai saboda saita yaba ma aya zakin tareda bambance zare da abawa. Abinda yafi bashi haushi ko Ango bai gani ba balle kawai ace ya juya gida.
Damkarta yayi ya k’ara watsa mata mari, “Idan ka kasheta sai ka bani gawarta na mayar ma iyayenta” Abba ya faɗa ranshi a bace.
Sai a locacin ya tuna dasu Abba, sakinta yayi ta faɗi kasa wanwar tana kuka. Hall anata kallonsa ana tsegumi, Sadeeq ya sauko daga high table rai a bace.
Kallon up and down yayi ma Naufal sai yayi nuni ma Amaryarsa da hannu alamar tazo su tafi. Ko k’ara kallon Naufal baiyi ba suke wuce.
Abba hannunshi harɗe akan kirjinsa ya k’ura ma Naufal ido, wannan ɗebo ruwa dame yayi kama. shikuma yana kallon k’asa cikin nadama.
Baban Sadeeq yaketa kallon Fadeela, ajiyar zuciya yayi kafin yace, “Naufal ka ɗebo ruwan dafa kanka saboda if I’m not mistaking wannan yarinyar Grand Kadi ce na Bauchi”
Jikin Engr Hussain yayi la’asar “Dan Kuka mai jawo ma uwarsa jifa” ya ayyana a ransa.
Bashi ba har Naufal cikinsa yanata kaɗawa saboda kowa yasan cewa ba’a taɓa yaran manyan mutane a zauna lafiya, uwa uba yarinyar Grand Kadi gaba ɗaya. Yanzu yanzu within minutes zasu iya mayar da life dinka miserable.
#NiDaDiyata
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top