One
On the authority of Abu Hurairah, who said : The messenger of Allah said : "Part of someone's being a good Muslim is his leaving alone that which does not concern him." fine Hadith narrated by Termithi and others
Abu Hurairah (May Allah be pleased with him) reported: The Prophet (Sallallahu 'alaihi wa sallam) said, "He who believes in Allah and the Last Day, let him show hospitality to his guest; and he who believes in Allah and the Last Day, let him maintain good relation with kins; and he who believes in Allah and the Last Day, let him speak good or remain silent."[Al-Bukhari and Muslim
****************************
Buckingham Palace, City of Westminster...
3 years ago....
A hankali ya bude idanun shi sai kuma ya sake rufewa da sauri. Haka yayita kifkifta ido har idunsa suka kai agogon bango dake cikin karamin Cubical dinsa.
Zumbur!! Ya mike tsaye tareda tangal tangal alamun zai faɗi kasa. Innalillahi wa inna ilayhi rajiun yayita nanatawa, “Shikenan na gama yin latti” ya faɗa tareda wucewa bayi.
A gurguje yayi wanka tareda saka kaya, Dukda bala’in lattin dayayi saida ya sha Coffee saboda baya wasa da breakfast. Acewarsa breakfast is the most important meal of the day.
Haka yayi ta sintiri cikin cubical dinsa har ya gama shirinsa tsaf sai ya rufu kofa ya fita zuwa inda za shi.
“Good Morning Miss Beckinsale?” ya faɗa ma next door neighbour dinshi Wanda zata kai shekara saba’in a duniya amma bata taɓa aure ba.
“Good Morning sunshine, How are you?” ta faɗa tana fari da ido. Dama haka take tsokanar sa wai batayi aure ba saboda dama tana jiransa ne yazo ya aureta.
Tanada bala’in fara’a kuma sau da dama yana rakata irin su cocktail ko Fund raising haka.
“I’m fine” ya faɗa tareda danna elevator ya shiga cikin azama sanadiyar lattin daya riskeshi yau.
Dama yadan kishingida ne bayan yayi sallar asuba domin yayi 5mins sleep to shine bai farka ba sai 8:45am.
Gudu yakeyi akan sidewalk babu k'akk'autawa, yana yi yana bige mutane tareda fadin "Sorry please" haka har ya kai wajen traffic, tsayawa yayi yana ganin yanda motoci ke wucewa da gudu.
Daya lura basuda alamun tsayawa sai kawai ya kutsa dukda ba'a nuna alaman Pedestrian su wuce ba.
Kuuuu kake ji wani mota ya kusan kadeshi, haka yayi kokarin komawa baya amma sai ya zame ya fadi wanwar a kasa, tsaki yayi tareda mikewa, shi kuma mai motan ya fito da sauri don yaga yanayin shi. Sai ya fada ma mai motan, "Sorry please, I'm in a hurry"
shi kuma mai motan yace, "Damn you Man, you can get urself killed with these attitude" sai yayi kwafi ya koma motarshi.
Ko ajikinsa tuni ya cigaba da gudu, yana yi yana duba agogo. "09:24 Insha Allah I won't miss the train" ya fada a fili.
Har ya kai subway yana gudu tareda tsallake stairs uku ko hudu. Ikon Allah train din bai tashi ba mutane sunata shiga tunda tafiya ta Subway yafi idan mutum yayi latti bcs babu traffic yasa baima fita da motarsa ba.
💦💦💦
Sanye take da wani multi coloured long chiffon gown mai guntun hannu, saita hadashi da karamin Blazer Silver mai stones wanda bazai kai cikinta ba, k’afanta kuwa Gucci hightop ne mai spikes kuma yana daukar idanu.
Headphones din Beat By Dre ke kunneta kuma ta rataye dogon Vintage jaka a gefen damanta. Hannunta kuwa wayar handset ne tana latsawa tareda yin murmushi.
A hankali take tafiya zata shiga speed train din, a sanya sanya take komai sai gashi yazo da gudu yana so ya shiga bcs in a minute train zai tashi. "Hello Miss can you hold the door for me please" ya fada mata.
Ita kuma Wanda tuni tana sauraron wani abu daga wayarta bata ma San yana yi ba, koda ta shiga kofa yana kokarin rufewa sai ya hada da jakarta.
Shi yaji dadin abin saboda zai iya kustawa amma bata nuna tana so tayi hanzarin cire jakarta ba balle ya wuce.
A hankali take abinta har ta samu ta cire sai kofan yayi karap ya rufe jirgi ya tashi.
Da gudu yabi jirgin yana fadin" Nooo no no no no" sai kuma ya tsaya ya soma boxing da iska tareda dukan k’arfen dake wurin da hannunshi, zafi yaji mara misaltuwa saiya soma ihu yana tsalle, daga bisani ya lura kowa kallonshi yakeyi, kwafa yayi sai ya kame a gefe.
"Dama idan za'a hada abu da mata sai rai ya baci" ya fada ma kansa. Abin haushi baiga fuskarta ba saboda tayi wrapping irin na Arabs, at least koba komai zai saka ta a list din mak'iyan sa bcs wannan hassada ce k'arara.
Haka yayita zama har 10mins later inda wani train din yazo suka ware. Victoria Tube Station ya sauka saboda shine nearest station to Palace din Queen Elizabeth II, tafiyan mintuna 7 yayi ya kai main entrance.
Tsaye take a queue din Palace din, dama dream dinta ne taga inda Queen Elizabeth take, Daddy ya fada mata idan CGP dinta yakai 4.80 zai kaita country of her choice for summer kuma ikon Allah ta buga 4.82
Tabi duk wani protocol din security saboda yau akwai wani gagarumin taro dat is significant to yan England, yaune Her Majesty zata bada yabon girmamawa ga best students din kowane University din country dinta.
Tana shiga ciki idonta ya hangi royal standard flag din wajen a sama, murmushi tayi tareda fadin "yes the Queen is around" saita shiga ta fara kalle kallen su statue din wajen masu bala’in kyau.
Shi kuma yana isa ya gyara kayan jikinsa, grey suit ya saka tareda farin riga sai kuma purple tie, yayi adjusting dakyau tareda mak’ala links din hannun rigarsa sai ya soma taku daya daya kamar bashi ke gudu dazu ba.
"Da zuwa da wur wuri gwara zuwa da wuri" ya fada yana murmushi. Sai yaje inda security yafi yawa zaiyi signing in.
Mika masu babban yastan shi yayi suka daura akan na'uran su saiga sunan shi ya fito. NAUFAL HUSSAIN BELI representing Oxford University, "that's correct" ya amsa masu.
Gaba ki daya suka ce "Congratulations Mr Hussain, welcome to the Great Buckingham Palace"
Tun dayake karatu bai taba zuwa wajen ba kuma bai taba tunanin zaije ba, yana tafe yana kare ma wajen kallo sosai. Furanni irin su hydrangeas, tulips, lily da kuma Roses tako ina ga kuma wasu anyi customizing sunar Elizabeth dashi.
Security din wajen sun saka Bearskin hat, riga mai Ja da ratsan blue sai kuma bakin wando. Da MI6 gasu birjik, suma FBI da CIA ba'a barsu a baya ba saboda John Kerry na America da dignitaries din England sun hallara.
💦💦💦
A cikin fadan kowa yana tsaye za'a fara taro, masu karban yabo na daga gefe, kid’a na tashi a hankali mai dadin ji irin na al’adar yan England.
Duke and Duchess sun fara saukowa daga wani katafaren stairs mai dumbin tarihi. Yaransu biyu suma ana saukowa tare. Kida ne ya chanza alamar a natsu Her Majesty zata fito.
Ta sauko an fara taro anata bada awards har an kai turn din Naufal, "For Oxford University we present the brilliant Naufal Hussain Beli from Bauchi State Nigeria"
Raf Raf Raf suka rinka tafa masa, shi kuma cikin natsuwa yaje wajen Her Majesty yayi bowing head dinshi tareda shaking hannunta "Thank you so much your Majesty, I'm really honoured" ya fada ita kuma tace, "The pleasure is mine Mr Hussain" saita yi murmushi wanda ya bayyana mata hokararta.
Ya juya zai koma wajen tsayuwarsa saiga wata yarinya idon shi ya hango mai, ya lura tafi kowa tafi a cikin audience. Murmushi ya soma yi yana tafiya tareda kara kallonta.
Yana wajen tsayuwarsa ne ya lura da headphones din dake wuyanta, a hankali ya rinka ware ido dan yaga ko zai ina gano kayan jikinta.
Zuciyarshi ta soma aiki da sauri sauri tana kokarin kawo mashi wasu tunani marasa amfani, wani siririn murya ta raya mai "kila fah yarinyar dazu ce..." da sauri ya kawar da tunanin tareda korar shedan saiya sake kallon bangaren ta.
Kaddara ta riga fata saboda anan yaga Multi coloured kayanta tareda jacket mai stones wanda keta walkiya.
Anan take bakin cikin mara misaltuwa ya riske shi.
Kwafa yayi tareda juya kansa, "Bad luck! har nan kika biyo ni?" ya tambaya kansa rhetorically.
Masoyan DIMPLΣS me kuke gani? Mu cigaba ko mu tsaya daga nan?
I'm waiting for your reply?
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top