Nineteen

It was narrated from Aishah that the Messenger of Allah said: "Marriage is part of my sunnah, and whoever does not follow my sunnah has nothing to do with me. Get married, for I will boast of your great numbers before the nations. Whoever has the means, let him get married, and whoever does not, then he should fast for it will diminish his desire." (Hasan)
**********

Hannunta na mak’ale da nawa ta rike tsam, kawai wani iri nakeji. Juyawa nayi bance komai ba kuma ban kwace hannuna ba.

Tsaya nayi dab da ita, ita kuma ta rufe ido tana hawaye. Mamaki kawai take bani yanda bata gajiya da kuka.

Shikuma Doctor yazo ya fara matsa mata kafa, ihu ta tsala tareda mirganawa kamar zata faɗi, da sauri na tarbo ta tareda daka mata harara. "Ni raki ne da rashin juriya ne banso”na faɗa mata.

Narai narai tayi da ido tareda saka hannunta ta matse bakinta. Doctor Yanata complain akan sakacin damu kayi bamu zo da wuri ba.
Afuwan doctor wlh bansan abin zai kai haka bane dana kawota da wuriNaufal ya faɗa mashi

Shidai Doctor baice komai ba illa cigaba da aikinsa, yana kawai kallon Naufal as complete idiot ne bcs gaskiya kafan Fadeela ya lalace.
Ita kuma Fadeela sai matse baki takeyi tana share hawaye, wata sa’in ta faɗa jikina idan an murɗa mata kafan but da sauri take bari idan taji daidai.

Bawai zance bana jin daɗin abin bane idan ta taɓa ni, kawai I’m just neutral. Kafin a gama mata tasha kuka sosai duk ta galabaita.

Daga nan aka bata magunguna da allurai, dole aka kwantar da ita saboda akwai na barci da sauransu.
Toh Alhaji saika je gida ka kawo mata abinci da sauran kayan amfani” Doctor ya faɗa mani.

Toh kawai nace mashi na tafi, motana na wuce kai tsaya, ina ciki nafi 20mins banyi komai ba. Bansan me zanyi ba.

Na farko dai ban iya girki ba, na biyu kuma bazai kyautu na siyo abinci daga restaurant ba tunda bazai taɓa Kamada na gida ba.
Balle yanda Doctor ke mun kallon mugu, yana lura da abincin zai gama concluding banida saura imani.

Kawai wani dabara ya faɗo min akan naje wajen Mommy bcs tana sona, ita kaɗai ne zata mara min baya.
Nan take na tada motar nayi hanyar gidansu, Grand Kadi na gani a parking lot da suit and tie daga gani zashi court case ne.

Har k’asa na ɗuka na gaishe shi kafin na zayyana mashi komai. Salati yayi cikin damuna tareda alkawarin zaije direct bayan ya fito daga kotu. Tun daga lokacin jikina yayi la’asar yanda naga ya razana, tabbas yanzu na fara sanin gatan Fadeela.

K’afa babu kwari na shiga cikin gida, Mommy na riske a falo tana kallon Manara TV. Itama har k’asa na gaisheta which dama ɗabi’a na ne. Tashi tayi wai tana zuwa, dawowanta keda wuya sai gata tareda mai aiki shak’e da kayan breakfast.

Nan take kunya ya fara ɗawainiya dani, wai ace tsakani na da mutanen nan banda mutunci da arziki babu abinda ke shiga tsakanin mu. Ni kuma banda tsiya bana masu komai.
Ga abinci kaci, nasan bazaka rasa guntun yunwa ba” Mommy ta faɗa. Sinna kai nayi bcs kunyar ta nakeji, “Mommy bazan iya ba, dama Fadeela ce ke asibiti

Innalillahi wa inna ilayhi rajiun, meya sameta? Tun yaushe?”
Yanda naga ta ruɗe sai na fara jin nauyin faɗa mata yarinyar ta tafi kwana uku ba lafiya sai yau na kaita asibiti. Ina cikin tunani ashe har Mommy ta zura hijabi tana tsaye kaina.

“Mu tafi koh” tace
Dama abinci nazo karɓa saboda idan ta tashi saita ci
Bata kulani ba kawai ta wuce kitchen, bayan 30 mins haka sai gata ta fito da Katon flask ɗin ruwan zafi dasu kofuna tareda kayan shayi.

Sai mu siyan mata bread a hanya kuma na saka Husna (Mai aiki) ta dafa abinci, anjima zaka dawo ka karba
Nagode sosai Mommy, Allah ya saka da alheri
Muna tafe a cikin mota zulumi fal raina, kawai yanda Fadeela ta susuce nake tunani. Da akwai yanda zanyi mata makeup karda a gane danayi. Dadin abin su Abba da Anty Saudah basu sani ba aiko cinye nama ɗina zasuyi bcs na lura dis days sunfi Santa akaina.

Mun isa cikin asibiti lokacin Fadeela ta farka, tana ganin Mommy ta barke da kuka. “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel” na rinka nanatawa kafin Fadeela ta tona min asiri.
Kawai Mommy patting bayanta takeyi ciki so da kulawa, “Yi hakuri My baby, Kowa da jarabtan shi. Karki damu an kankare maki zunnuban ki ne... Daddyn ki shima ya kusan zuwa” Haka Mommy ta rinka shafa mata baya tana bata baki.

“Ka kira Hajia Saudatu kuwa dasu Hajia Sarai?” Mommy ta tambaye ni, yak’e nayi kafin nace, “Yanzu zan kira su
A gabansu na kira Anty Saudah da Mama harda Abba akan an kwantar da Fadeela, yanda hankalin su ya tashi yafi na iyayen Fadeela.Nidai bazan iya barin ɗakin ba bcs ina tsoron kada ta fayyace ma Mamanta komai.

1 hr 45 mins later.....

Motar Anty Saudah ya fara isowa cikin haraban asibitin. Tazo tareda cooler ɗin abinci dasu fruits da kayan shayi. Tana shiga tayi ido da Fadeela ba tace komai ba, kawai ajiye kayan tayi suka gaisa da Mommy har tana tambayar ta jikin Miemie shine take cewa gaskiya yanzu yayi sauki sosai.

Bayan nan ta matsa wajen Fadeela tana mata kallon tuhuma, “Sannu kinji! Tun yaushe kikaji ciwon?”
Ita Fadeela bata gane abinda akeyi ba saita faɗa ranar. “Shine dan mugunta yau kaga damar kawo ta asibiti” ta juya tanama Naufal sababi.

“Dan wulakanci an gaya maka jaka aka kai maka, salan ta mutu ko ta nak’asa?” Mommy ne ta chapke, “Yi hakuri  Hajia Aiba laifin shi bane”

Karki ce haka, nasan halinshi sarai kuma nasan abinda zai iya aikatawa
Suna cikin haka ne saiga Mama da Abba da Bilqees. Mama kallona tayi ta juyar da kanta kuma koda na gaisheta bata amsa mani ba.

Shikuma Abba da nace mashiIna kwanada kai ya amsa min. Chan gefe na koma na tsaya kamar bare saboda kowa fuskarshi yana ɗauke da irin kallon da kake ma mugu.

Abba ya soma magana k’asa k’asa, “Yanzu Naufal me muka yi a duniya da kake so ka hana mu sakat?” sai kuma ya kafa min ido. Kunyar duniya ya kamani kamar kasa ta buɗe na shiga. Bance komai ba nayi shiru.

Gwara dai ka tambaye shi sai mu bashi hakuri?” Mama tace. Ita kuma Anty tace, “Ai kuwa dai, saboda wannan ɗebo ruwa dame yayi kama?”

Abba yayi ajiyar zuciya saiya kalle Fadeela sannan ya sake kallona, “Dube yarinyar nan fisabilillahi, halan kana tunanin jaka aka kai maka? Dafa gatan ta da komai ka k’askantar da ita.... Kalleta da kyau kamar an hak’ota a rami

Ai idan rami ne da sauki, ji yanda tayi kamar ita ce k’asan da aka hau sanda ake yin Badar” Mama tace.
Mommy ne tace,”Kuyi hakuri bafa laifin shi bane yasa ta faɗi, ai tsautsayi baya wuce ranar shi”

Toh sai akace kada ya kawo ta asibiti??” Anty Saudah ta faɗa.

Ina dasu Paracetamol a ɗaki yasa nace kada ya damu bari mu gani ko zanji saukiFadeela ta tare min.

Mama ce a hasalce tace, “Idan kika kara saka baki saina mauje ki. Watau ke mai miji koh? Kina tsoron kada ya rama abinda mukayi mashi akan ki koh?” Saita juyo tana fuskantana, “Kana ji na koh?”

Bance komai ba sai Abba yacebada kai ake magana ba, you’re Very stupid” Ba shiri na amsa Mama saboda na lura da girmana sunaso su tara min gajiya.

Ciwon kai naji labarin yarinyar chan tayi sai anjimu a gari, dama ɓata min suna kake so kayi na kasa shiga makwabta, ina tafe ana nunani ga Maman Mugu.” Sai kawai tayi kwafa ta juyar da fuskanta.

Dama Hausawa sunce abinda ka suka shi zaka girba, idan alheri ne to, idan kuma tsiya toh shima haka saboda babu wanda zai shuka shinkafa yaga rake. Tas bayin Allah ɗinnan suka min, wanki babban bargo suka min la’ada waje saboda su uku ba wanda ya raga min.

Mommy babu magiyan duniya da batayi su bari ba amma ina, sai mita sukeyi.Kamar kwallo suka mayar da abin, sai attacking ɗina sukeyi tareda passing ma junar su.

Harda cewa Abba yayi, “Toh Hajia Sarai Kinga abinda yaronki yayi
Da sauri ta chapke, “Ba yarona bane, yaron Saudatu ne

Nima banaso gaskiya, Hajia kinaso?” sai Anty Saudah ta kalli Mommy tana dariya tareda tambayar ta.
Sosai ma kuwa tunda kun haɗe mashi kai”

Dama tun zuwansu Bilqees ta fara ba Fadeela abinci bcs tun tea ɗin da Mommy ta bata babu komai a cikin ta. A baki ake bata ana lallashinta gwanin ban sha’awa.

Anty Saudah ta ɗauki kankana da abarba ta fara ferewa, kallo nayi tareda shiru bcs cikina ya fara kiran ciroma tunda banci abinci kwata kwata yauba.

Mommy daga baya ta zuba min abinci tareda bani Fanta, Motana na wuce naci nayi gyatsa tareda guntun gyangyaɗi bcs na galabaita daga sintiri danayi ɗakin Fadeela jiya.

Bayan kwana uku......

Babu wanda baizo gaishe da Fadeela ba including Miemie, saboda tana jin Anty yar gayu batada lafia sai kan ya fara motsawa. Dole aka kawo ta kuma cikin ikon Allah babu handcuffs kuma batayi anything funny ba.

Ita tayi ɗawainiya bata abinci da ruwa, ita abin dariya ya bata saboda ciwon K’afa takeyi ba na hannu ba, kuma ta fara taka kafan kaɗan kaɗan.
Kana ganin ta cikin kwanakin nan kasan cewa yar so ce kuma ba abin wulakanta wa bane. Hatta Big Daddy da iyalansa Ba’a barsu a baya ba, ko Alhaji Sulaiman baban  Sadeeq  yaje dashi kanshi Sadeeq da matarshi.

Abinci kuwa mai aikin Anty Saudah ke kawo three square meal tareda Mai aikin Mommy. Itama Jawahir duk sanda taje saita kai masu wani abu.
Kwata kwata Naufal baya jin daɗin asibitin idan Anty Saudah da Mama nanan, yafi son idan sun tafi gida ya zauna da Mommy Asha hira.

Bilqees ke kwana da Fadeela thru out. Ni Naufal wajen 6am na isa asibitin kafin su Mama su rigani zuwa asibitin su kama kiranaMugubcs na tsana sunan har cikin raina.

5pm....

An haɗa kayan Fadeela komai da komai ana jiran Doctor ya gama prescribing magani ya sallame su. Itama ta ɗan warware tayi ɗan armashi abinta ba kamar yadda aka kaita ba.

Mama ce tace saidai Fadeela ta wuce wajenta ta k’ara murmurewa saboda tasan halin Wa’e saita kalleshi ta gefen ido. Idan ana sabo da tozarci ya riga ya saba dashi dis past few days saboda sun mayar dashi laughing stuff, mocking ɗinsa anyhow kawai sukeyi.

Saidai ba fault ɗinsu bane, dama komai kayi akwai reckoning ko a duniya ko lahira baki ɗaya. Da bai zubar da girman da Allah ya bashi ba yayi abin tsiya da haka bai faru ba. But he promised to do better.

Nifa ba inda za’a je min da mata” ya faɗa masu.

Mama ta dubeshi a kaikaice, irin duban hadarin kajiToh mara kunya hanamu” ta hayayyakoshi.
Ai dama da bakice haka ba, wajena zata zauna kinsan sun saba da Miemie” Anty Saudah ta faɗa.

Haka suka rinka jani in jaka shi babu wanda zai tafi mashi da matarsa wani wajen.
Fadeela na daga kwance tana jinsu duk rai a jagule, tsakani da Allah tunda yace he will do better gwara a barta ta koma ɗakin ta. Sai wani zuciya yace mata “Karya yakeyi kawai bauta yake so ta koma tana yimashi

Kauda tunanin tayi bcs aure ibada ne kuma ladanta yana sama wajen Allah. Indai da aure tsakanin su gwara tayi masa koma menene muddin bazai kare hakkin addini ba.

Kowa yasani Allah yana tareda masu hakuri Besides Hausawa sunce mai hakuri shike dafa dutse har yasha romonta.
Anty Saudah ta dafa mata kafaɗa “ ‘yata! Zaki bini muje gidan gona?”  Bata ce mata komai ba illa Sinna kai kasa tana wasada hannunta.

Sauraron ki nakeyi

Daga ido tayi saita lura kowa kallonta yakeyi, musamman shi gwaskar ya kafa mata ido babu kiftawa. Sunkuyar da kai tayi tareda cewa, “Anty duk abinda kuka ce shi za’a yi

Kwafa yayi ranshi ya bala’in ɓaci bcs tunda suna Santa idan tace zata zauna dashi babu mai hanata. “Ko kai bazaka zauna da kanka ba idan an barkawani siririn murya ya raya mashi.

Ita kuma koda wasa bazata iya cewa tana son zama da mijinta ba bcs rashin kunyarta bai kai haka ba besides suna kwatan mata yancin tane.

Daidai lokacin su Grand Kadi da Mommy suka shigo, Naufal bai bari sun natsa ba ya fara masu k’orafi akan za’a rabashi da matarsa.

Murmushi Grand Kadi yayi, “ karka damu babu mai hanaka tafiya da matarka, kai ka shigo da ita kuma kai zaka fita da ita

Woooow!” ya faɗa tareda naushin iska. Ko kunyar kowa baiji ba ya nuna murnarsa a fili. Harda shaking hannun Grand Kadi yana godiya.

Dariya yake masu Anty Saudah domin yaci argument ɗin, ita kuma takaimai dukan wasa a kafaɗa sai shikuma ya kauce tareda saurin barin ɗakin.

Fadeela sinna kai tayi ba tace komai ba but murna fal ranta zata koma wajen Other Half ɗinta.

An tarasu su biyu an masu nasiha akan aure mai shiga jiki, idan kayi shi da kyau ka kuɓuta, if not Zai kaika ga hallaka. Aure ba abin wasa bane kuma yana cikon manyan sunnonin Manzan Allah SAW.
Zo mu zauna dama zo mu saɓa ne, kuma mistakes are what makes you human but Yanda Kayi handling ɗinshi makes u a better person.

Wajen 30 mins kowa na tofa albarkacin bakinsa kafin aka shi masu albarka suka wuce.
Dama da safe Bilqees, Abla harda Miemie sunje gidanta sun gyara mata tsap. Ita Miemie tun sanda ta fara fita wajen Anty yar gayu aka fara gane kanta, tana shan magani akai akai kuma bata gardama.

Thou ba’a barinta alone, sun shirya ma Fadeela komai hardasu laundry aka tayata.
Shikuma ya tsaya Vanilla joints ya siyan masu kayan lashe lashe sai kuma ya siyan masu kaji gasarshe na kan titi.

Shi Bawai Santa yakeyi ba but kawai after everything he put her through, tayi deserving something sweet. Ita tana mota tana mamakin yanda yakeyi kamar ba shiba.


#NiDaDiyata



  

#TeamNiDaDiyata

#TeamFadeela
#TeamNaufal
#TeamKhattab
#TeamMiemie

Ni dai Team Naufal ce

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top