Nine
It was narrated from Hakim bin Muawiyah, from his father, that a man asked the Prophet(): "What are the right of the woman over her husband?" He said: "That he should feed her as he feeds himself and clothe her as he clothes himself; he should not strike her on the face nor disfigure her, and he should not abandon her except in the house (as a form of discipline)." (Hassan)
*********
Ina kwance akan sallaya bayan na idar da sallar Asr, lazimi nake tayi harna gaji. Dama ni kaɗai ke gidan Mommy taje supervising wani catering services haka. Anty Husna ce ta shigo wai ana sallama da dani.
Shiru nayi bance komai ba, sai kuma na Mike zaune ina fuskantar ta tareda wani irin kallo. Saboda ni kwata kwata I’m not expecting any male visitor, though I don’t have plenty of them.
“Wanene?”
“Ina ganin yana cikin bak’in jiya” ta amsa mani.
“Oh!”
Na faɗa saina yi kwanciya na, nifa tukura ne banso. Watau shi har yana san auren kenan da har zaizo zance wajena. “mts” naja tsaki mai bala’in k’ara.
Ita kuma Anty Husna har takai stairs sai wani zuciya ya raya mata kamar fah Fadeela bazata fito ba. Juyawa tayi nan take ta koma ɗakin. Inda ta barta nan ta same ta.
“Auta kinyi bak’o shine kike kwance? Babu kyau wulakanci! Kije kiji mai zai ce mana, koba komai su Hajia basu ji dadi ba idan kika raina sa, kuma bakya tsoro kada ya rama idan an kai ki?”
Mai aikin mu Anty Husna ta faɗa, ni kuma shiru nayi sai daga bisani nace,
“Haba Anty wani irin wulakanci kuma! Wallahi bansan me nayi masa ba. Kwata kwata ya tsane ni, kamar ya sanni a wani waje. I just can’t figure it out. Kina ganin Idonshi zakiga tsanata a ciki karara”
Na faɗa idona fal da hawaye, kallona ta tsaya yi saita ce, “Kiyi hakuri, wata rana sai labari. Kinsan cewa mai hakuri yana dafa dutse harya sha romonta” miko min hannunta tayi saina kama tareda mikewa tsaye.
Drawer na wuce na dauki Swiss lace orange mai ratsan purple da silver. Saina dauki purple gyale wanda ake ce masa Aisha Buhari na saka tareda takalmin Zara.
Fuskana payau babu makeup sai pink lip gloss wanda ya kara ma pink lips ɗina armashi kafin yace ina sanshi yasa nayi masa kwalliya.
Shi kuma Naufal bayan yayi parking motarshi sai yaje wajen mai gadi akan yayi mashi iso da mai gidan, to anan ne aka faɗa mashi babu kowa a gidan illa Fadeela. Shiru yayi kafin yace to ayi mashi iso da ita.
“karshen wahala bai fi mutuwa ba, kila yau zata kasheni kowa ma ya huta” ya faɗa a ranshi. Haka yayita zaman jiranta tareda latsa wayarshi tunda shi ma’abocin Instagram ne. Yana cikin motarshi ya shafa’a ya mance da komai sai yaji kamshin turaren da bazai mance dashi ba.
“Chanel No 5” ya faɗa a fili yayin da ya ɗago green eyes dinshi. “Assalamu Alaikum” na faɗa da murya kasa kasa tareda tsayawa gefen motan. “Wa’alaikumus Salam” ya amsa mani sai ya mayar da hankali shi akan wayar shi.
Ni firgitani yayi, bashida maraba da mage. Ga Green eyes ga bakin fata, sunkuyar da kaina kasa nayi ina wasa da yastuna.
Bayan 45 mins……
Haka na cigaba da wasa da yatsuna ina regretting rashin fita da banyi da wayana ba, koba komai zan buga Candy Crush.
Shikuma Naufal kwata kwata ta birkitar dashi da kamshinta, turaren data saka irinshi Ex Gf dinshi Anastacia take sawa. Sunyi soyayya sosai a London sai daga baya ta guje shi wai bazata aure Musulmi ba.
Acewarta Muslims are terrorist. Yayi kokarin wayer mata da kanta about Islam amma ta kafe. Abin ya ɗaga mashi hankali sosai har ya kusan shiga wani hali da bai dace ba. Bayan aukuwan abin da 2 weeks sai yagane ashe Anastacia aure zatayi da Mayor din district dinsu.
Zuciyar shi ya fara mai zafi sanadiyar tuna Anastacia daya yi, duk wani assignments shi ke mata kuma har exams yayi mata amma ta guje shi. “Birds of the same feathers” ya faɗa tareda kwafa.
Shi yanzu tsanar Fadeela ya karu a zuciyar shi, dukda tanada kyau kuma she is hot but tana firgita shi gata kuma da bala’in nawa. Deep down yasan champi haramun ne a musulunci but he can’t help himself to blame her for all the bad stuff in his life. Yasa ya basar da ita baice mata komai ba thou yana ankare da every move dinta, ya lura sai kwafa takeyi tana girgiza kafanta.
“kaɗan ma kika gani” ya faɗa yana kallonta ta gefen ido. Haushi ya kamani sosai amma nayi kokarin controlling kaina. Insha Allah bazan nuna mashi I’m weak ba, saidai yayi ya gaji. Muna cikin haka ne saiga Daddy yazo.
Da sauri Naufal ya fito daga motarshi, nima naje wajen Daddy ina shagwaba. “Ashe Daddy’s gal ce…. Tabdi!” ya fada a ranshi. Mikama Daddy hannu yayi suka gaisa tareda risinawa.
Daddy da fara’arsa ya amsa. “wannan wani irin mutane ne da ake masu abu basa nunawa” Naufal ya sake faɗa a ransa.
“Ah ah Mallam Naufal kaine tafe haka?” sai kuma ya mayar da fuskarshi kan Fadeela “ya baki kai shi cikin ɗaki ba”
“Daddy tun fa dazu yazo yanzu ma tafiya zaiyi sai gaka ka dawo”
“oh! Allah sarki toh mu shiga mu kara gaisawa” haka suka wuce cikin falon Grand Kadi suka zauna. Naufal sai inda inda yakeyi.
Grand Kadi ya lura akwai magana bakinshi, saiya canza topic din tareda mashi tambayoyi akan aiki da sauran al’amura. Daidai gwargwado Naufal ya bashi amsa saboda ya lura audition Daddy yake yi akan auren ‘yarsa, shi kuma Daddy ya yaba da ɗabi’un sa, murna fal ransa saboda koba komai in sha Allah ba zasuyi zaɓen tumun dare ba, wannan shi Mallam Bahaushe ke cewa ‘wai faɗuwa ne yazo daidai da zama’. Har wajen 30 mins sunata zantawa sai Naufal ya mike zai tafi.
“okay sai Fadeela ta raka ka mota”Daddy ya faɗa. Daga Deela har Naufal babu wanda yaji dadin abin amma haka suka hakura. Rakiyar da nayi ma Naufal was the longest journey of my life, shuru mukayi bamu ce uffan ba har muka kai parking lot.
Motar mommy ya danno kai, tsayawa yayi da fara’arsa na munafunci yana jiran ta iso. Bayan ta fito daga motar ta saiya risina ya gaishe ta yana wani kunya kunya. Sai kuma yace, “Mommy nazo bada hakuri jiya, nasan ban kyauta ba”
“Allah sarki ai babu komai, dama zo mu zauna zo mu saɓa ne” numfasawa tayi kafin ta ce “Allah yayi maka albarka”
“Amin Mommy” ya amsa dashi. Sai Mommy ta wuce cikin gida tana yabawa da halin surikin ta. Shi kuma motarshi ya shiga saiya mika ma Fadeela bandir din 500 naira. “ka bar abin ka bana so” na amsa mashi.
Kallon up and down yayi min, duk ya firgitani saboda Magrib yayi gashi idansa yana glimmering. Ban ankara ba sai naji ya tada motarshi, har ya fara tafiya saiya cilla min kudin a fuskata. Saiya faɗa “Kece matsiyaci ya amma badai niba”
Sororo na tsaya kallonshi har ya ɓace daga haraban gidan mu. Tunda nake ban taɓa ganin makirci irin nasa ba. Oh ni Fadeela ! Meke shirin Faruwa dani? Dukawa kasa nayi na dauke kudin tareda wucewa daki. Akan mirror na ajiye sai na kwanta akan gado na dauko sabuwar babin kuka.
#NiDaDiyata
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top