Four
It was narrated that Abu Usaid, Malik bin Rabi'ah, said "While we were with the Prophet(), a man from the Banu Salamah came to him and said: " O messenger of Allah, is there anyway of honoring my parents that I can still do for them after they die?' He said: "Yes offering the funeral prayer for them, praying for forgiveness for them, fulfilling their promises after their death, honoring their friends and upholding the ties of kinship which you would not have were it nor for them.'" (Hasan)
*****************
Wani na annabi ne ya taimaka ma Fadeela ya samo mata keke napep ta hau bayan Naufal yaje wajen motarshi. Tana tafe tanata kuka, still jikinta bai bar rawa ba, dukta susuce.
Ita abinda yafi ɓata mata rai bai wuce wai ita ce zatayi faɗa da namiji wanda ko mata bata gama yi dasu ba.
Dama daga shagon Ismail, Yelwa zan wuce inda makaranta mu yake watau ATBU, amma yanzu gida zan koma dukda inada test amma bazani ba bcs I'm too angry to write.
Muna isa GRA inda gidan mu yake nayi kuka har murya na ya fara dishewa, “Allah ya isa” na rinka faɗi a raina saboda bazan yafe mashi ba.
A daddafe na fito duk jiri na ɗibana saboda bana ko ganin gabana, “nawa ne kudin?” Ki barshi kawai Hajia ai naga abinda ya faru, Allah ya kiyaye na gaba. "Amin" na faɗa mashi kawai na wuce saboda banida energy ɗin wani magana.
“Assalamu Alaikum” na faɗa saina wuce upstairs, ko tsayawa na gaida Momy banyi ba, which ba d’abiana bane. “Wa'alaikumus Salam” ta amsa sai ta bini da ido tana karantan yanayi na. Har na kusan kaiwa karshen stairs saita ce, “Yaki dawo nan, lafia bakije school ba kuma kin shigo kina wani kumbure kumbure?”
Ban amsata ba saboda hawaye dake fito min, haka na tsaya kuma ban yuja ba. “Bada ke nake magana ba?”
kafin na amsata saiga Daddy ya fito daga ɗakin shi cikin black suit and grey tie daga alamun yanada court case Kasancewarshi na Judge.
“Ni matsa min daga hanya, mahaifiyarki tana miki magana kin wani kyaleta. Uwa dai ba abin wulakantawa bane!” Daddy ya faɗa yayinda yake saukowa. Saura kaɗan daya hankaɗe ni saida naja baya, nan take na fashe da kuka saboda duk laifin azzalumin mutumin nanne wannan abu ya faru dani.
Wucewa ɗaki nayi da gudu na kwanta a gado na dauko wani babin kukan. Sai ga momy ta shigo ta zauna akan gadon, janyoni tayi jikinta saita ce, "Auta waya taɓa min ke? Na hana shi sukuni a garin Bauchi”
Sarai nasan halin Momy kuma tanada connections, k'akalo murmushi nayi saina ce, “ Momy fault dina ne, naje tsallaka titi sai mota ya kusan bigeni” dariya momy tayi sosai kafin tace, “ Ho sarkin shagwaba, ni banga abin kuka ba. Anyway tunda kin dawo zo na aike ki gidan Jawahir kinsan Jiya mijinta ya dawo akwai sak'ona a wajen shi.
Momy kallon Fadeela takeyi saboda sam bata iya fushi ba, most of the time tana abu kamar goyon kaka aside rashin kunyar, “Allah ya bata mijin wanda zai rinka tausayinta”momy ta fada a ranta yayinda take fita.
💦💦💦💦
Shikuma Naufal wani dabara ya fad'o mashi, gwara yabi Mr Sutter Abuja ya basu hakuri. Haka kuwa yayi, zura gudu yakeyi akan titi yayi hanyar Abuja. Dama idan wajen gudu ne to fah ya kware saboda zaka sha drifting din motoci ne.
Yana isa Nicon hotel ya fito daga parking lot, tunani kala kala yakeyi tareda neman mai zai fada masu, yana so ya shiga reception din kenan saiya hango Mr Sutter, Mr Pearson da Mr Targeyan sun fito da kayansu zasu tafi.
Da sauri yaje ya sha gabansu, "Please I'm very sorry for my actions, I take full responsibility, please just consider this merger with my firm and I promise you will never regret it" hannun shi biyu yana rok'on su. Fuskarshi tsantsan nadama ke nunawa.
Mr Pearson yaji tausayinshi amma Mr Targeyan yafi zafin kai, juyar da fuskarshi yayi kamar baima san Naufal na wajen ba, dama tun farko baiso ayi abu da bak'in fata, a cewarsa basuda rike alkawari.
Mr Sutter ya kalle Mr Targeyan which har yanzu yaki murmushi, "since he owned up to his mistakes, I think we should consider him but this time around we will reevaluate the first contract. We will give you 6months trial bfr signing the agreed documents"
Murna mara misaltuwa a wajen Naufal, “wow dats what I’m talking about” ya fada yana shaking hannu su, kwata kwata baisan me zai faru dashi ba idan yayi losing deal din saboda anyi relying dashi a firm dinsu gashi uwa uba shine Bread earner(Mai tallafi) ɗin gidansu...
Okay let’s go inside and talk, Mr Targeyan ya fada wannan karon yana murmushi harda dafa shoulder ɗin Naufal. Bayan sunyi meeting ɗinsu suka had’a da lashe lashe, daga bisani kowa yayi hanyar sa.
Su suka wuce airport inda zasu tafi Newyork, shi kuma ya dauki hanyar Bauchin Yakubu saboda shi baisan kwana a wani waje idan ba gida ba. Daukar wayarsa yayi ya kira Miemie kanwarsa suka sha hira dukda shirme take zuba masa sanadiyar tanada psychotic disorder(Ciwon Hauka) but a duniya bashida kamar Miemie.
Farin cikin sa kenan, kuma duk wani zafin nema dayake yi saboda health dinta ne yasa ma bashida sha’awan aure. Acewarsa baya so mace tayi distracting dinsa while sister dinshi batada lafiya.
Ko yanzu ba maganar kirki sukeyi ba, babbaka dariya takeyi saboda tun shigowar wannan makon yan dariya suka motsa. Dama turn by turn ne, akwai yan dariya, yan shiru, da kuma idan ta samu lafiya kadan.
Jira yake ya koma Bauchi gobe su wuce Psychiatric Hospital na Kaduna. Dama idan deal ɗin baiyi working ba dole su canza mata asibiti. Bayan ya kashe wayan sai ya kira Aminu amma har ya gama k’ara bai dauka ba.
Murmushi yayi saboda yasan fushi yayi dashi. Text ya aika mashi na, “Calm down please, I know na ɓata maka rai but don’t worry everything is going to be alright. Ka mance nine Naufal?” saiya tura mai.
Wanene Naufal?
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top