Five
Abu Barzah Al-Aslami narrated that the Messenger of Allah (s.a.w) said "The feet of the slave of Allah shall not move [on the Day of Judgement] until he is asked about five things: about his life and what he did with it, about his knowledge and what he did with it, about his wealth and how he earned it and where he spent it on, about his body and for what did he wear it out." (Da'if)
*************
Naufal Hussain Beli matashi ne mai jini a jiki ɗan shekaru Ashirin da tara a duniya, kuma ɗan asalin Bauchi ne a wani gari da ake kira Shira.
RTD Engr Hussain Beli shine mahaifin Naufal kuma yanada mata biyu. Hajia Sarai wanda ake cema ‘Mama’ sai kuma Hajia Saudatu suna ce mata ‘Anty Saudah’.
Mama tanada yara biyar a duniya, Nabil ɗan kimanin shekara 32years kuma yana aiki a Airtel Networks a Abuja. Yanzu haka yana auren Safeena yar garin Katsina ne amma a Abuja take zama, sun haɗu sanadiyar supervising wani promo da akeyi a University of Abuja which a locacin ita student ɗin school dinne. Sunada yaro ɗaya mai suna “Mohammad Eemaad”
Daga nan kuma sai Naufal, sai kuma “Amatullah” yar kimanin 25yrs kuma tana aure a Gombe da yaronta guda daya “Abdulrahman” Amatullah tanada bala’in zafi bata daukan raini at all, kuma itama tanada raini sosai, ga kuma kyaman talaka musamman yanzu data aure mai k’unban susa.
Daga ita sai kuma Abla yar 22 years wanda yanzu take serving a NEPA, itace dai mai sauk’in kan ɗakinsu. Batada matsala at all saboda tanada daɗin sha’ani.
Sai kuma autan mama wato yan matan 100l ‘Bilqees’ itama footstep ɗin Abla take bi amma bata kai Abla kirki ba.
Anty Saudah tanada yarinya guda d’aya mai suna “Laurat” amma suna kiranta “Miemie” saboda sunan maman babane.
Bayan haihuwar Miemie da wasu shekaru sai suka lura tayi developing wasu strange ɗabi’u, an kaita asibiti shine akayi masu confirming tanada ciwon Hauka watau Psychotic disorder.
Ansha wuya wajen neman mata magani, sunyi zirya a Psychiatric Hospital Kakuri, Kaduna. Kuɗaɗe masu ɗunbim yawa ake kashe mata kuma still bata warke ba. Jefi jefi yake yi mata tuburan.
Hajia Sarai watau Mama ta tada bala’I akan bazata zauna gida d’aya da Mahaukaciya ba, dayake locacin Abba yanada k’umba susa, saiya siya wani gidan gona haka mai dan girma.
Duka yaran Mama basu ji daɗin abin ba saboda Miemie yarinya ce mai shiga rai, musamman Naufal da Abla, shi saida ya koma gidan da zama, jefi jefi yake zuwa gurin Mama. Yanzu haka Miemie tanada shekaru goma sha hudu a duniya, kamar yanda bature ke fad’in first impression matters, to haka rayuwar Miemie yake.
Idan kuka hadu for the first time ta nuna bata sanka, toh fa saidai kayi hakuri. Amma idan tayi maka fara’a zaku shirya sosai. Ana cikin yi mata magani sai Abba yayi retire daga wajen aiki.
Ko karatun Naufal bashi ya ɗauki nauyin sa ba, Gwamnatin jihar Bauchi ta bada scholarship ga yara masu hazaka, kuma cikin sa’a Naufal ya samu wannan damar. Shine yaje Oxford University inda ya karanta Architecture kuma yanzu haka yana cikin best Architects a Nigeria.
Kasancewar Naufal ya shaku da Miemie yasa ya dauki nauyin Medical bills dinta. A duniya yanzu bashida wani buri face yaga ta samu sauki bata tuburan ko doke doke, bcs idan lafiya ya ɗan zo mata har special school ana kaita domin tayi karatu.
Yanzu haka duk sati biyu sai an kashe mata 70k, yasa da ya kusan losing deal ɗinshi dasu Mr Sutter ranshi ya bala’in bace bcs baisan ya zaiyi bill din Miemie ba tunda sun samu ta rage hauka tuburan, saidai kawai tayita kyalkyala dariya ba gaira ba dalili.
Naufal tun fil azal yanada tausayin ɗan Adam, baya so yaga mutum cikin pain. Ko bai sanka ba ka rokeshi alfarma zaiyi maka koba duka ba. Abinda baya so a rayuwarshi shine “Nawa” da Sanya Sanya saboda a cewarshi “Time is money” He is very swift Idan zaiyi abụ yasa ake ji dashi wajen aiki, kuma idan yanayi bawai rawar kai yakeyi ba.
Bashida surutu sosai musamman idan bai sanka ba toh bazai ce uffan ba, daga eh saidai ah ah Har ku gama magana, gashi yasan addini daidai gwargwado kuma yana kokarin kare hakkin shari’a.
Bak’I ne sosai mara misaltuwa, amma bak’inshi yanada kyau kuma skin dinshi is fluffy. Yanada tsawo daidai misali ba jankala kok’I ba, gashin kansa yayi curly a matsayinshi na Fulde.
Yanada Emerald eyes which is very rare ma yan Africa, kuma idanun are not that bulging, sunje daidai da dogon fuskarshi. Bashida saje ko kaɗan saboda bai taba yiba, fuskarshi haka yake payau.
One good thing about him shine ya iya dressing thou mostly suits and tie ne na week days sai kuma T-shirts haka ma weekends. Idan kuma traditional wears ne toh fah saidai ya saka farin kaya da hula, baya sa wani colour at all. Idan yayi kwalliyar nan kuma Miemie tana daidai tana mishi lak’abi da “Yaya bak’i da fari” wai gashi baki amma yasa farin kaya.
Kuma he is very neat, koda yaushe yana fadin “Al naxafatu shaɗaral iman”
Wannan kenan!!!
1 week later...
Yaune bikin k’awata kuma aminiyata Hadiza, tun jiya muka fara su kunshi, Hajia Sumayya Gaya wanda aka fi sani da “India” tazo tun daga kano domin yi mana, Hadiza ta fito sosai sai san barka, nima ba tayar baya ba.
D’inkin da Isma’il yayi min ya fito da duk wani bangaren jikina har kunya nakeji, “gaskiya saina yafa gyale” na faɗa ma kaina tareda kara kallon madubi.
Haka na tsala ma kaina kwalliya tunda ni ma’abociyar shine kuma ina shiga YouTube da Instagram na kalle videos haka, mune ake kira da “Internet Makeup Artist”
Shi kuma Naufal tun yau yakejin Mood swings, gabanshi faduwa yaketa yi. Innalillahi wa inna ilayhi rajiun ya rinka maimaita wa.
Komai sukuku yakeyi, saiga Miemie ta shigo. Dama bata fiye magana ba tunda yanzu ‘yan maganar basa nan, hawa kan gadansa tayi ta kura mashi ido, “Ya Naufal bakada lafia ne?” shima karin kansa baisan meke damunsa ba.
“Halan baki iya gaisuwa bane?”
“Na iya mana, but please answer me”
Juya kanshi yayi gefe saboda bai san me zaice ba, gashi in an hour zai wuce wani dinner na friend ɗinshi Sadeeq. A hankali ya tashi ya wuce bayi yayi wanka tareda dauro alwala.
Ya gama ya fito kenan saiyaji kamar bai kulle shower da kyau ba, ya koma ciki sai yaga komai lafiya lau, juyawa yayi sai kawai yayi missing steps dinshi yana kokarin faɗuwa.
Sink, bango da k’arfen shower duk yayi kokarin kamawa but still saida ya zube a kasa, “tim” kakeji kawai.
Shiru yayi a k’asa zafin ya gama barin jikinshi, da tangal tangal ya samu ya koma wajen gado. Tsaki yayi kafin ya soma dressing, farar Boyel ya saka as expected.
Saiya murza hular k’ube wanda ake kira kwalba a kanshi. Fashe turaran Christian Dior yayi dana Ralph Lauren ko ina sai kamshi.
Ya juya zai tafi saiya lura Miemie tana kallonsa, “ashe baki tafi ba?”
“Ya Naufal zaka kashe arna yau, yan mata zasu rinka rububinka” ta faɗa tareda zurawa a guje.
Dama haka takeyi idanta faɗa abinda yafi karfin bakinta saita gudu shima ya bita ayita wasa. Amma Sam yau bazai iya ba saboda har yanzu bayan shi yana mashi ciwo.
Baiji haushin abinda ta fada ba saboda it’s true, ya saba yaje biki yan mata suyi masa cha a kai suna k’arairaya, shi kawai yasan cewa bai haɗu da soul mate ɗinshi ba har yanzu. Yanada feeling duk randa ya ganta he will know!
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top