Fifteen


On the authority of Abu Malik Al-Harith bin Asim Al-Ashari said that the messenger of Allah said: "Purity is half of faith. alhamdu-lillah [Praise be to Allah] fills the scales, and subhana-Allah [How far is Allah from every imperfection] and alhamdu-lillah [Praise be to Allah] fill that which is between heaven and earth. Prayer is light; charity is a proof; patience is illumination; and the Quran is an argument for or against you. Everyone starts his day and is a vendor of his soul, either freeing it or bringing about its ruin." Related by Muslim.
*******

Naufal ɓarin laɓe ya soma yi ya rasa mai zaice, kawai kallon Fadeela yayi, irin kallon Please help me. But ya tuna da yanda dake da nawa bata abu da jiki, yasan baza tayi saurin taimakon saba.

Ita kuma dayake yar gari ce saita kakalo murmushi tareda faɗin, "Laaaa Abba yaje ɗauko babbar rigarsa ne a hotel ɗin dayake kwana kafin yan room service su kwashe"

"Ai gwara daka je da wuri, nima sun taɓa yimin gaba da agogo na" Alhaji Sulaiman ya chapke.

Dukda Abba yasan karya ne, but irin matan dayake son yaronshi ya zauna da ita kenan, mai rufawa mijinta asiri a koda yaushe itace mace.
"Okay ba matsala dama nazo naga yanda kuka kwana ne, kuma ku sani zuwan bazata zan rinka maku, so ku kiyaye!"

Naufal har k'asa ya ɗuka ya gaishe dasu Abbansa, Fadeela ma haka. Babu yanda basuyi dasu akan su tsaya karin kumallo amma suka k'i.

Bayan tafiyar su Abba, Naufal ya tsaya yana kallon Fadeela. Ita har ta fara murmushi a ranta ta samu lambar sa, shi kuma sai yanzu ya kalleta da kyau a rayuwarshi 'Za'a je da babe ɗin nan fah' wani siririn murya ya a ranshi ya faɗa.

Kawar da tunanin yayi da sauri,taku daya daya ya soma cikin k'asaita rai a bace har yakai wajen matakalan bene inda Fadeela ke tsaye. Bai waiga ba kawai magana yayi a bayyane, "Iska na wahalar da mai kayan kara" sai yayi gaba abinsa.

Ita kuma abin dariya ya bata saboda bata taɓa irin rayuwar nan ba. Zuwa tayi ta fara touring cikin gidan, gaskiya iyayenta sunyi kokari babu abinda zata faɗa sai Allah ya saka masu da alheri.

Shi kuma kai tsaye ya wuce master bedroom a zatonsa nanne ɗakin sa, yanda yaga komai Orange daga jere, curtains and rug Kuma ba color dinsa bane. Haushi ya kamashi wai ace shida gidansa amma bashi ke cikin babban ɗaki ba.

Rufewa yayi ya koma wani ɗaki wanda ke biye da master room din, shikuma purple ne kayan ciki. A fusace ya fito yana masifa "Wai tsakani da Allah ina ne ɗakina?"

Yayi maganar lokacin Fadeela ta gama taka matakalan bene na karshe. Tsayawa tayi tana kallonshi cikin Tuhuma irin me akayi maka saboda taga yana wani zazzare idanu.

"Ke ina ne ɗakina? Infact dan kin rainani watau ke zaki zauna a master bedroom koh?"

Shiru tayi tana kallon ikon Allah, "Kayi hakuri dama ina son Katon daki ne dats y, but bari na koma wancan" sai tayi ciki zata kwashe kayanta.

"Wa zai zauna a cikin ɗakin chan mai kalar yan secret society, salan a cinye min kuruwa na. Yi zaman ki ni saina zauna a falo" taji muryanshi.

Fitowa tayi tana nazarin shi bcs ta rasa meke damunsa, "Ga wani daki chan fari, idan kuma baiyi maka ba saina saka Mommy su kawo color of ur taste" saita nuna wani daki mai girma madaidai ci.

Kwafa yayi sai ya tafi hanyar dakin, kamshin turaren wuta ya fara mashi welcome. Dakin fari sol daga bedsheets, curtains etc. Cire takalmi yayi saiya taka carpet, wani laushi yaji mai daɗin gaske. Lumshe ido yayi yana murmushi wanda bai masan hakan ya faru ba.

Ya mike tsaye zaiyi wanka sai kuma ya tsaya yana tunani, tsaki yayi tareda naushin iska "Wallahi banso haka ba" shi yaso suyi Jani in jaka da ita ne kuma yaso batada farin daki yayi sanadiyar mata dukan tsiya.

Sai yanzu ya lura batada hayaniya at all Kuma tashin hankali bai dameta ba, Ranshi yayi mummunar baci bcs bazata bashi reason to beat her ba, kuma haka kurum bazai kama dukanta babu gaira babu dalili tunda shiba mahaukaci bane.

Ita kuma sororo ta tsaya tana ganin ikon Allah, wai zaka ga abu muddin kana raye. Ita dama farin ɗakin ta shirya mashi kuma koda aka kawo kayensa nan aka ajiye. Cikin orange room ɗin ta shiga tayi ɗai-ɗai akan gado tareda ajiyar numfashi a hankali, sai kuma tayi zumbur ta tashi da sauri.

Dakin Naufal ta wuce, a hankali ta tura kofa tareda sallama, babu wanda ya amsa Still ta shiga. K'arar ruwa taji a bayi da alamun yana ciki. Shikuma ya fito daga shi sai boxers da hand towel a hannu sai kawai ya ganta tsaye tayi zurfi cikin tunani.

"ke meye haka? Meya kawoki ɗakina?"
Rasa me zatace tayi sai kawai ta kafa mashi ido.
"Badake nake ba? Wayace ki shigo"

"Dama abincin Kane nake so na tambaya inda zan jera maka"

Kallonta yayi baice komai ba ya wuce mirror ya fara shafa man Nivea, yana gamawa fashe spray din same Nivea for men sai ya haɗa da Hugo boss. Yana yi yana takama Still Fadeela tana wajen baice komai ba.

"Ina kayana yake?" ya tambaya amma ko kallonta baiyi ba.
"Yana cikin wardrobe"

Bai kalleta ba yaje ya buɗe, a yatsine ya kalle ciki saiya fito da wani milk jallabiya ya zura. Hawa gado yayi ya dauki wayar shi ya kunna wakar 2pac.
"Ki kawo min abincin nan" ya faɗa yana wasa da wayar shi.
Ita kuma fita tayi waje tareda rufo kofa, "ina da aiki a gabana" ta faɗa yayin datake sauka stairs tayi hanyar dinning area.

Abincine mai rai da lafiya Anty Saudah ta aiko masu dashi. A cikin cooler ɗin farko Appetizer ne na minced chicken wanda yasha kayan lambu kamar su carrots da green beans Sai kuma kayan kamshi da barkono.

A cooler na biyu aka soya dankali da plantain sai kuma wainar kwai. Sai kuma pancakes mai vanilla flavor. Daga nan sai Fruits salad wanda aka kwaba madara a ciki.

Daidai gwargwado ta zuba mashi akan tray saita kai mashi cikin ɗakin. Harta ajiye ta juya ta fara tafiya sai kawai yace, "OMG! I've change my mind. Biyo ni downstairs dashi"

Bai tsaya jin mai zata faɗa ba sai ya wuce abinshi. Wani kololon bakin ciki ya tokareta, tunda take bata taba ganin k'askanci irin wannan ba, wai dan wulakanci up and down Zai rinka mata, hakuri kawai tayi saboda zaman aure takeyi kuma ya jiɓanci haka.

Cikin yanayinta na sanya sanya ta karasa wajen dinning area ta ajiye abincin. Ta fara tafiya saiya kirata, "keh meye haka? Dalla zokiyi serving ɗina"

Cak ta tsaya na wasu seconds kafin ta juya taje tanayi, ranta duk ya jagule. Shi kuma haushi ya kamashi saboda yanda take abu kamar babu jini a jikinta, ji yake kamar ya kwace chukalin yayi da kanshi amma da yake mugunta na cin sa saiya barta da abinta.

Dayake Mommy chef ce, Fadeela tasan yanda ake decorating plate yayi kyan gani. Koshi abin yayi mashi kyau saidai bai nuna ba.

"Saura ccoffee" ya faɗa tareda kai spoon din abinci baki.
Ta haɗa mashi cappuccino a Nespresso machine dake kan coffee table ɗin wajen. Ta ɗaura akan saucer tareda teaspoon ta kai mashi.

Tas kake ji alamun cup ɗin ya faɗi ya fashe. Data mika mashi cup ɗin saiyaga cappuccino kuma shi Latte yake so yasa bai amsa ba komai ya zube a jikinta tareda faɗi kasa.

"Kefa bakida hankali! Wannan wani irin busy body ne? Waye ce maki ina shan Cappuccino? I only take latte"

"Yi maza ki haɗa min yanzu kafin na tara maki gajiya...... Mts"

Kananan hawaye suka soma malala a fuskarta sai tayi sauri ta goge, ta lura yanaso ya bakanta mata raine amma bazata bashi damar ba. She will always be happy.

Latte ta mashi a wani cup tunda na farkon ya fashe, little sugar ta saka daidai misali. Koshi sanda ya saka a baki saida yayi mamakin to his own taste ne.

Kitchen ta wuce ta dauko vacuum cleaner saboda wajen yayi kacha kacha, tsaf ta gyara wajen tunda ta iya aiki ba'a sangartar da ita ba.

Bayan nan daki ta wuce ta rufe kanta.
Kwanciya tayi rub da ciki tareda dauko babin kuka, wiwi takeyi mai tsuma rai kamar ranta zai fita, kana ganinta saita baka tausayi. A duniya rainin hankali tafi tsana amma gashi anayi mata kamar pure water.

Datayi kukanta ma ishi saita mirgina tareda rungumo pillow tayi barci abinta.

1:15pm.......

Locacin ne su Bilqees suka kawo lunch, hayaniya dinsu ya tada ta. Da fara'arta ta karramasu kamar kannenta na jini. Tana zuwa wajen dinning taga komai yayi normal saboda sunyi mata wanke wanke Thou tanada dish washer, but still!

Miemie ne taje ɗakin Naufal amma bata riske shiba daga alama ya tafi Masjid ne. Horn sukaji a waje driver yana masu alamar su fito.

"Anty yar gayu mun tafi, sai kuma mun Kawo dinner" Miemie tace tana dariya.
"Sai anjima Anty" Bilqees tace tana murmushi. Har kofa ta rakasu ana raha.

Ta koma daki tayi alwala tareda sallah itama. Bayan nan ta sake gyara make up ɗinta da kyau tareda daurin ture kaga tsiya. Tayi matukar kyau tunda her skin is fluffy Kuma she is fair.

Gashi dama fitted gown ta saka komai nata aziman. Tana tafe tana feleke kamar rashen bishiya, tako daidai yarinya yar kwalisa Amaryar Naufal.

A falo ta riske shi yana kallon CNN inda ake Inauguration ɗin Donald Trump sabon shugaban k'asan USA. Tsaki yayi tareda canza channel daga alamu abin bai kai mashi karo, BBC ya koma still suma abinda suke nunawa kenan. Kwafa yayi tareda rufe idanun sa.

Sai kawa yaji kamshin dake firgitar dashi, "Chanel No 5" ya faɗa saiya bude idonsa.

Nan take suka haɗa ido saiya banka mata harara. Sinna kai kasa tayi saboda idonsa yana firgita ta musamman idan ya zare.

"Yaya ina wuni?"
Bai amsataba kuma bashida niyar amsawa.

"Dama nazo na tambaya ne ina zan kai maka abinci"

Nanma kamar bazai ce komai ba saiya ce, "Set the table, Yanzu zan ci"

"Please idan Kinga dama ki rinka yin busy body idan kina abu, mutum sai shegen nawa kamar kunkuru" Ya faɗa yana wani yatsine fuska.
Tana tafe tana gunguni tareda magana ciki ciki, "Bani bace kunkuro saidai......" kafin ta karasa maganar saiga shi agabanta yana huci kamar mayunwacin zaki.
"Saidai wa?......." ya tambayeta.

#NiDaDiyata


*All Rights Reserved*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top