Eight

*A LESSON*
The Holy Prophet(SAW) said, "Stop doing everything during the ADHAAN(calling of prayer), even reading the Holy Quran, the person who talks during the Adhan shall be deprived of saying the KALIMATUSH-SHAHADA when he or she is about to die! May Allah guide us...

*********

“Dama na danyi wani  k’aramin hatsari ne” Naufal ya amsa ma Abba still yana ɗuk’e a kasa. Shiru Abba yayi na wajen 5 minutes yana tunani irin halin Naufal. Ajiyar zuciya yayi abin duniya ya isheshi sai yace “Wato sabon alkawarin daka dauka ma kanka kenan koh?’’

“Yanzu bazaka  barni na sha ruwa a garin Bauchi ba koh?  Idan an hanaka mutuwa sai ka suma. Shi kenan yanzu dan na haife ka banida sauran kwanciyar hankali a tareda ni kuma. Kana abu kamar k’aramin yaro.”

“Wai tsakani da Allah Naufal mena rageka dashi da kake so bakin cikin ka ya kasheni. Haba mana! Bafa kai kaɗai na haifa ba balle kamin haka, idan ka gaji ne sai kayi min bayani na yafeka a cikin yarana then we can call it a day”

“Kayi hakuri dan Allah Abba Wallahi bai kai zafin haka ba, tsautsayi ne kawai aka samu. Kuma wanda nayi hatsari a gefen su ko qurjewa basuyi ba” Naufal ya faɗa yana tunanin yayi abin arziki. “Ai bakayi gwaninta ba, daka kashesu ne saina san ka cika namiji” Abba ya amsa.

Ita kuma Bilqees ta tashi karatun TDB saboda tanada test saita ji hayaniya a varenda. A hankali taje taga ta lek’a sai idonta yayi arba dana Abba. “Zo nan” ya faɗa ita kuma ta fara jan k’afa duk takaici tace a hankali “I don dieooo.... Meya kawoni wajen nan” haka taje wajen Abba ta durkusa “Gani Abba”
Kallon sama da kasa yayi mata saiya ce, “kije ki tada Abla da Maman ku sai kuzo ku sameni gabaki ɗayan ku a falo” ya faɗa tareda kallon Naufal alamar harda shi.

20 mins later....

Duk suna zaune a falon Engr, Mama da Naufal ke kan one one seater, su Abla ana k’asa ana turo baki. Mama tana ɗan jijiga kafarta ta cika tayi fam. Ita bata ga dalilin da za’a tasheta cikin tsakar dare ba?  Wani zuciya ya raya mata ai aikin Anty Saudah ne. Tsaki tayi a ranta sannan ta faɗa “Nayi maki nisa mahaifiyar mahaukaciya”

“Abba gamu mun zo” Abla ta sake maimaitawa a karo na biyu. “Ai na ganku since niba makaho bane” shiru ya k’ara yi wanda Fallon baka jin komai sai motsin jaridar dake hannunsa. Kafarsa ɗaya akan ɗaya yana karkaɗasu, shikuma Naufal bai taɓa gajiya kamar na yauba. Kwakwalwarsa sai chaji yake yi a hankali don komai yayi masa zafi.

“Hajia Sarai” Na’am Alhaji ta amsa tana kallon gefe.
“Naufal” Na’am Abba
“Abla” Abba Na’am
“Bilqees” Na’am
Ya kira sunan su ko kallonsu baiyi ba still yana duba jarida. Ajiyar zuciya yayi saiya ajiye akan centre table kafin ya mayar da hankalin shi kansu.

“Wannan gidana ne bana wani ba! Saboda haka dole abi dokoki na. My house my rules”
“Bazai yiwu akawo min raini under my roof ba, akan me? Bari kuji daga yau an daina tozarta ni. Ban ɓata ma iyayena suna ba bazaku ɓata min nawa sunan ba, haba!”

“Hajia Sarai daga yau kin gama Kishi da Hajia Saudah, shekararmu wajen sha shida da aure amma kinki saka ma zuciyar ki salama. Daga yau sai yau bana so na kara jin kin takaleta ko wani abu makamancin haka. You are going to be nice to her and her daughter, Zaki rinka zuwa kina dubasu kuma zaki bar yaranki suje” yana kaiwa nan ya numfasa.

“Naufal! Dole ka aure Fadeela, kuma you will treat her nicely. Gobe zakaje kabama iyayenta hakuri da ita kanta. Zakayi auren nan cikin daɗin rai, yar mutunci zaka aura dole ka mutunta ta. Batun Miemie kuma banida abin cewa sai Allah ya saka da alheri” shiru Naufal yayi baice komai ba saboda duk gabobin sa yana mashi ciwo.

“Abla da Bilqees ku fito da mijin aure tun kafin nakai hoton ku masallaci, musamman ke Abla tunda kece babba. Kuma zaku rinka zuwa wajen Miemie kuna dubata”

Yana kaiwa nan ya dauko jaridar sa tareda fadin “Duk wanda yaga bazai iya bin abinda nace ba sai yayi hanyar gate yanzun nan or else kowa yaje ya kwanta”

Naufal ya fara tashi tsaye tareda faɗin “Saida safe Abba” saiyayi hanyar BQ. Sai mama ta tashi tayi hanyar ɗakinta. Su Abla suma saida safe sukace sakayi hanyar ɗakinsu. Murmushi Engr yayi saboda ya fara dawo da tarbiyan gidansa hanya madaidaciya.

“Nifa ban gane me ake nufi da Ya Naufal zai yi aure ba?” Bilqees ta faɗa. “Shine nima naji gashi kin sanshi yanada bala’in taste” Abla ta amsa

Bilqees tayi ajiyar zuciya kafin tace, “Fadeela! Ko wacece ita?”

WACECE FADEELA ?

Marigayi Mallam Bello ya haifa yara biyu tal a duniya. Musa da Abbas, ya rasu babban yaronshi yanada shekara 21 duniya. Dukda k’arancin shekarunsa bai hanashi rike mahaifiyarsa tareda kaninsa ba. Shiyayi jjigilarsa harya zama lawyer gashi yanzu shine Grand Kadi, yanzu Sam bazai iya musa masa ba akan alfarma saboda shine mahaifinshi.

Alhaji Musa wanda ake kira Big Daddy yanada yara biyar, Maimuna, Zainab, Hafsat, Safiya sai auta Mubarak. Sunar matarshi Hajia Rabi.Yanzu haka duka yaranshi mata na zaune lafiya lau gidan mazajen su thou Zainab aurenta na biyu kenan. Jikoki 14 Big Daddy yakeda.

Shikuma Grand Kadi Abbas yanada yara uku, Jawahir, Muhsin sai auta Fadeela. Jawahir tanada yara uku, Yanbiyu Abdulrahman da Abdulrazak sai Fauziya. Shi kuma Muhsin yana Masters a Dubai tareda Mubarak shi kuma degree yakeyi . Ita kuma Fadeela tana 400l a ATBU Bauchi tana karanta fine arts.

Fadeela dai yarinya ce mai natsuwa ga dadin zama, ta san ya kamata saboda ba’a yi masu wasa da tarbiya ba. Fara ce daidai misali, bazaka cemata kyakyawa ba amma babu muni a fuskarta, daidai gwargwado take Tabarakta mashaAllah.

Siririya ce kuma tanada ɗan tsawo. Gashin kanta yanada santsi amma bashida tsawo bai wuce cikin cokali ba. One good about her shine she is very classy, ta haɗu iya haɗuwa. Dressing A1 take ci saboda tasan fashion trends.

A duniya tanada bala’in san yara, domin ko a bus saita murmusa masu. Burinta ɗaya ta haifinata but gashi yanzu an haɗa ta da wanda ya tsaneta. AllahuMusta’an kawai take faɗi.

Matsalarta guda biyu ne.
1.Tana san shan waka kamar ibada.
2.Ta fiye sanya sanya da nawa ko wajen magana.
But dama dan Adam ajizine,  dukda wannan bata san raini at all. Bataga dalilin da bazaku mutunta juna ba.

Wannan kenan!

*********

Daga ɗayen bangaren Fadeela ta koma ɗaki ta shiga cikin bargo ta duk’unkune sai kyarma takeyi, duk zazzabi na farad ɗaya yayi awon gaba da ita. Momy kai tsaye ɗakin Fadeela ta nufa saboda saita cin mata. Tana tura kofa taji abuɗe but wuta a kashe. “Gwara da baki rufe ba” momy ta faɗa da karfi.

“Dan rashin hankali uban waye sa’anki? Muna magana zaki shigo mana da zancen banza” sai Momy ta fizge blanket dinta. Yanayin dataga Fadeela ya bata tausayi sai ta mayar da duk wani abu data je dashi. Dama ita Fadeela bata iya fushi ba, abu kadan sai ta hau zazzabi.

Zama tayi akan gadon ta jawo ta jikinta, rau taji zafi kamar ana shirin soya kwai. A hankali ta soma magana “Yi hakuri auta, komai ya faru da mutum daga Allah ne. Kwantar da hankalinki. Gobe zani wajen Big Daddy na rok’esa alfarma, but idan bai yarda ba Please im begging you in kina gidansa I want you to show him how well trained you are.”

“Please Karki bani kunya, ki nuna masa ke yar halas ce kuma yar mutunci” haka Momy tayita rarrashinta tana mata nasiha har barci ya kwashe ta.

Washegari, 4:56am…..

Abba ne yake tafiya zuwa ɗakin Naufal domin tadashi su wuce masallaci sallar asuba, dama ɗabi’ansu ne muddin Naufal ya kwana a gidan. Ya mika hannu zai kwankwasa kofa sai ga Naufal ya buɗe zai fito, “Alhamdulillah ai ka hutar sheni” Abba ya faɗa yana murmushi. Shi kuma Naufal murmushi ya mayar masa sai suka jera suka yi hanyar masjid.

Bayan sun idar suna dawowa sai Naufal ya koma ɗakin shi, shi kuma Abba ɗakinsu Abla ya wuce direct yaga yanda suke. Bilqees ya gani tana karatun Al Quran sai Abla tana zura hijab da alamun sallah zatayi, baice komai ba ya wuce ɗakin Mama. Itama tana bayi da alamu alwala takeyi.

Tunani ya soma yi bcs iyalinshi na kokarin kare hakkin addini, kwata kwata baisan idan Naufal ya debo halinshi na jiya ba. “Maybe he is the black sheep of the family” wani zuciya ta raya mai. “Allah dai ya shirya shi” ya fada a fili. TV ya kunna ya kalle sunna TV inda ake hira da Bn Uthman sai wajen 6am ya koma NTA inda zai kalle AM Express.

6:30am…

Locacin ne Fadeela ta tashi, kasancewar bata sallah yasa ta ɗan kara barci. Da kyar take tafiya bata ko ganin gabarta sanadiyar kukan data ci which ya haifar mata da azabataccen ciwon kai mai sara kamar na gatari.
Tana tafe tana tangal tangal kamar yar k’waya, ruwan zafi ta watsa a jikinta saita soma samun kanta. A daddafe ta wuce ta haɗa ma kanta Espresso a PS Gucci Nespresso machine dinta dake dakin tunda ita ma’abociyar shan coffee ne. A yanayinta na sanya sanya ta wuce bedside drawer dinta ta dauki Paracetamol, Boska da Panadol extra duk ta hadiye. Saita jingina akan gado tana ajiyar zuciya.

Hawaye ke gangaro mata data tuna sabon rayuwar da zata shiga, within minutes life dinta yayi shredding into pieces. Dogon ajiyar zuciya ta yi saita ce “Alhamdulillah ala kullu halin” a fili saita mike tsam ta saka kaya. Wani valvet overall ne kuma yana cikin kayan zaman gidanta.

Dakin Daddy ta soma zuwa, a kan couch ta ganshi yana duba Alqur’ani da wasu takardu a gefensa da alamu yanada court case. “Assalamu Alaikum Daddy” ta faɗa a sanyaye tareda da zuwa gefensa ta zauna.
“Wa’alaikumus Salam, Auta kin tashi lafiya”
“lafia lau, hope kaima haka?”
Kallonta ya tsaya yi yanda bata nuna wani damuwa akan batun jiya ba, abinda yasa tafi burgeshi kenan a yaransa saboda batada riko kwata kwata.

“Daddy wat are you working on?” ta fada tareda daukar ɗaya daga cikin papers din kan table.
“kul ki ajiye” ya faɗa yana dariya
“Wannan aikin na manya ne”
Murmushi tayi saita ce, “me zan haɗa maka na breakfast?”
“Na hutarshe ki, matana chef ne so zata yi min gangariya” ya faɗa yana dariya. Ita ma dariya ta soma yi bcs a duniya parents dinta su ne relationship crush dinta. Yanda suke abinsu cikin mutunci da girmamawa yana burgeta sosai.

Kullum fatan ta itama ta samu koda rabine, idanunta suka ciko da kwalla data tuna Naufal, da sauri ta mike kada Daddy yaga yana yinta. “Daddy ayi aiki lafia, bari na duba Mommy” bata bari ya amsa ba tayi gaba abinta.

Share k’aramin kwalla daya soma gangaro mata tayi, ɗakin Mommy ta shiga which is adjacent to na Daddy. Tana tura ɗakin sai taga duhu alamun momy ta koma barci, itama zuwa tayi ta shiga bargon ta kwanta. Ido ta kafa ma Mommy kur, “kaza mai ‘ya’ya bata mai” Mommy tace tareda murmushi.

“watau baza’a barni nayi barci hankali kwance ba?”
“Mommy ina kwana?”
“lafia lau auta ya hakuri damu?”
Dariya Fadeela tayi sosai saita canza topic din, “Daddy yace zakiyi masa gangariya”
“Na sani Malama ba sai kin faɗa ba” sai Mommy ta kalle silver and black agogon bangon dake manne. “Innalillahi bari na tashi kaɗa na makara, today I’ve a lot of things da zanyi”

Ita Fadeela tana so ta tambaya Mommy ko abubuwan data keso tayi ya jiɓance zuwa gurin Big Daddy but ta kasa magana.
“Mommy please kada Kije wajen big Daddy kafin yace mun raina shi” ta faɗa idonta fal da hawaye. Kallonta Mommy tayi tana nazarinta kafin tace, “akan me Auta?  Kin taba ganin inda mutum ya bude gyaɗa ya tsinci mota?”

“marinki fa yayi shine za’a aura miki shi ya kashe ki gaba daya”

“Mommy ba abinda nake nufi ba kenan, idan Allah ya kaddara auren babu abinda zamu iya and vice versa. Kawai bana so muyi forcing komai ne muyi ma  Allah shishigi kafin muji kunya”

“Besides dan ya mareni is not the worst scenario that people meet their spouse, Wasu fah a social media suke haɗuwa”

Mommy shiru tayi tana kallon ɗiyarta, “Gaskiya hankali baiwa ne kuma idan Allah ya baka sai kawai ka gode masa” jawota tayi jikinta tana jin dumin ta. A hankali tace, “Nagode Fadeela” which is rare ake kiranta, anfi ce mata Auta har masu gadi da makwabta.

4:38pm…

Jallabiya ya dauko sabuwa fara sol ya saka, sai ya haɗa da bakin wando tareda bakin hula. Fashe kanshi yayi da turaren Yes Saint Laurent yana tafe yana shan kamshi, gashi kuma rana ya fara sauka so emerald eyes dinshi yana ɗan glimmering.

“wannan wanka haka? Ya Naufal sai ina?” Bilqees ta faɗa daga gani ta dawo daga School ne.
“Kinsan niba sa’anki bane?” abinda yasa yayi mata magana in a rude way baifi haushin zuwa wajen Bad Luck da zai yi, wanda har yanzu bai taba faɗin sunanta ba.

“Yi hakuri but please jirani na dauko kayana saika ajiye ni wajen Anty Saudah anan zan kwana yau”
Kallonta yayi baice komai ba, mamaki karara a fuskarshi sai kuma ya tuna Bilqees batada matsala probably Mama ke zugata, mai zafin kan gidansu bai wuce Amatullah ba kuma tana chan ta karata da mijinta.

“Karki bata min locaci” ya faɗa yayi hanyar motan Abba tunda ya kai nashi gyara.

Ya ajiye Bilqees a gidan gona saiga Miemie tazo da gudu, “Ya Naufal wai da gaske zakayi aure?” ta faɗa tana haki. Shi kuma yace “bakya so ne?”
“Ina so mana sosai ma kuwa, na gaji da Mommy kaga sai na dawo wajenta” ta faɗa tana waige waige. Shi yaso tace Ah ah amma ta bashi haushi kawai. Kwafa yayi “dama wayace na tambaya mahaukaciya abu?” ya faɗa a ransa.

Tun kafin ya kai gidansu Fadeela yake addu’o’I, shifa ya riga ya chamfa duk randa ya ganta sai wani mugun abu ya same shi. “La ila inna anta subhanaka inni kuntu minnal zalumin” yaketa maimaitawa while driving har ya isa cikin gidan…..

#NiDaDiyata


I'm  really sorry for my silence, buki mukayi. Uncle Usman Allah ya baka zaman lafiya da amaryar ka Rahama.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top