3
NESLIHAN SULTAN
Na
CHUCHUJAY
CHAPTER 3
Kai tsaye Neslihan ta wuce sashenta da niyyar idan ta kimtsa za ta je taga mahaifiyar ta, bata yi mamaki ba lokacin da ta shiga sashen ta taga mahaifiyar ta ɗauke da wani ƙaramin Akushi hannun ta tana leƙen zuwan ta, Neslihan na shiga ta faɗaɗa murmushi tace"Mahaifiyata abin Alfahari na,har zan shiga sashen ki jikina ya bani kina nan"ƴar dariya Burak Sultan tayi tace"Abar ƙauna ta Neslihan ki faɗi wani abun banda wannan ,Ni nasan zaki shiga sashen Mahaifinki da kakar ki saboda magana zasu miki wadda kike so ta filin yaƙi ,amma gurina kuwa sai kin gama shawara da zuciyar ki da serra tukunna zaki zo saboda zan miki maganar Aure,sanin Hakan yasa na biyo ki da Akushin sa'a ɗauke da jelebi ɗin da na haɗa da hannuna ɗauke kuma da Addu'ar samun Masoyi daga bakin Babban Malam Fahed Nakir insha Allahu baza ki koma filin yaƙi ba sai dai ɗakin mijin ki,maza zo nan kusa"dariya Neslihan tayi ta taka ga mahaifiyar Tata ta rungume ta kafin ta buɗe baki ta karɓi Alewar da mahaifiyar Tata ta kawo a baki,Sumbatar kumatun ta tayi tace"Kada ki damu Uwata ,wata rana burin ki zai ciki, nayi mutuƙar ƙewarki,Serra maza kawo mayafin da na siyawa Mama a babbar kasuwa a hanyata ta dawowa"Serra dake gefe tana ta fama murmushi ne ta tafi inda ta aje mayafin tana jin nishaɗin Karfin Soyayyar dake tsakanin Neslihan da maman ta..kama Sarauniya Burak Neslihan tayi ta zaunar da ita kana Serra ta kawo gelen ta miƙawa Neslihan cike da ladabi,da fara'a Neslihan ta ƙarba ta yafa ƙaramin gyalen kan kafaɗar Mamanta tana mai cewa"lokacin da na zaɓi gyalen nan cike da soyayya na samo shi ina cike da tunanin ki ",cike da jin daɗin Sarauniya Burak ta rungume ta kafin tace"amma ba shine zai saka na daina maganar Aure ba yarinyar ƙirki",a tare suka saka dariya Harda Serra dake fatan itama yau ace Gimbiya Neslihan ta samu miji,duk da tana da masu san ta amma galibin su suna tsoron Tarar ta da kalmar soyayya saboda tsaurin ta,Bayan wucewar Sarauniya Burak Neslihan ta kalli rigar da mahaifiyar ta tasa aka haɗa mata da kayan ado mafi tsada da wuyar samu,a hankali ta shafa rigar tana mai Kallan Serra tace"Serra Kayan nan sunyi Ado da yawa kin san ban cika san ado yayi hayaniya ba".murmushi Serra tayi tace,"Amma kin san idan baki saka wannan kayan ba baki ɗaya Sarauniya Baza taji daɗi ba ko kaɗan"kaɗa kai tayi tana mai murmushi tace "a samo IREM mai ƙwalliyar Kakata ta mun kwalliya,kila na cika burin Mama na samu miji a daren yau,ya kamata na samu miji yarda kema zan miki Aure,amma idan ma a yanzu kina da wanda kike so kada ki boye mun ki faɗa mun zan saka Sultan yayi muku biki,"gashin ta Serra ta fara cire mata abun kama gashin da ta kama kan dashi tana murmushi tace"Ni bazan rabu dake ba Gimbiya ta ,idan kinga nayi Aure to kin fara yi ne,kinga kenan Aure na yana wuyan ki, sannan ina da wanda nake so Amma shi hankalinsa ba kaina yake ba,bugu da ƙari kuma Ni ɗin ba ajin sa bace"juyowa Neslihan tayi tana mai cewa"Akwai wanda zai ce ke ba ajin sa bace?na farko kina da kyau,Kuma ke ɗin Hadima tace,ki faɗa mun sunan sa ko wane Mahaifin sa a garin nan sai na Aure miki shi"sunkuyar da kai kawai Serra tayi tana mai jin nauyin sanarwa Neslihan cewa Aley take so, ɗaukar Furen da zata haɗa mata ruwan wanka dashi tayi tace"Ruwanki zai haɗu nan da minti Biyar"Binta Neslihan tayi da kallo tana mamakin wai Serra nada wanda take so kuma take kunyar faɗa mata,kaɗa kai tayi tana murmushi tace "idan tayi tsami zanji".
******************************************
"Sadauki na UMER yau fa Babbar rana ce ,ya kama ta ace e yanzu mun samu Babban tarko daza mu ɗanawa Neslihan a wannan daren da take ganin daren nasarar ta ne, nayi rantsuwa da ubangijina akan bazan taɓa barin Neslihan ba har sai na ɗauki fansar Shugaba na da ta kashe"wata kyakkyawar budurwa ta faɗa ga Saurayin dake tsaye hannun sa riƙe da mandula ya juya mata baya.tasowa tayi da rangwaɗa cikin wata rigarta wadda taji Duwatsu inda bangaren rufa tsiraicin ta kuwa abu kaɗan ta rufe,fuskar nan kuwa tasha muguwar kwalliya kamar wata mayya amma hakan bai ƙoƙari wajen boye ƙyanta ba,dai dai bayan UMER ta tsaya kafin ta ɗora kanta bisa kafaɗarsa ,hannayen ta kuma ta zagaye su kan cikin sa dake buɗe tana mai shafa shafaffan cikin sa cikin sigar ɗaukar hankali,saitin kunnen sa ta saka harshenta ta lasa kafin tace"amma kafin nan mene zai hana jarumina ya ɗauke Ni ya cilla kan gadon nan, ya ɗaga hannaye na sama ,ya saka masu anƙwa jikin gadon nan ,ya lalata Ni ta yarda yake so,kasan da cewa jikina da komai nawa sadaukar wace gare ka ,na sallama maka komai nawa". murmushi UMER yayi yana mai Kai madularsa baki ya zuga, hannu ɗaya yasa ya juyo da budurwar yana mata wani irin shu'umin murmushi kafin ya kama leɓɓanta da nasa cikin sumba Wadda yasan tana mutuƙar gigita ta,kafin yace ƙwabo ta ɗanesa ta saka ƙafafunta ta zagaye ƙungunsa tana mai mayar masa da sumbarsa lokaci guda tana mai tura jikinta yarda Kirji ta zai taɓa nasa yarda take so..da ƙyar ya samu ya raba bakin sa da nata kafin ya ɗalli goshinta da yatsuna kafin ya miƙa Mata mandular dake hannun sa yace"kina mutuwar san Jima'a abar ƙaunata SIYAH,Ni nasan baza ki iya rayuwa namiji bai kusance ki ba,ina fatan a kaina ya tsaya domin kuwa nima gwarzo ne wajen ɗauke miki nauyin buƙatar ki, idan nasan kina bin wani kinsan zan sare masa kai na soke a Babban Ƙofar shiga Birnin MAMLUK,ke ɗin tawa ce ni kaɗai".cike da jin daɗi SIYAH tace"kaima kasan babu wanda zai kalle Ni sanin cewa Ni ɗin taka ce,sannan duk cikin Birnin Ottoman banga wani jarumi da zai iya bani gamsuwa fiye da kai ba ,yanzu dai mene kace wa tayi na?".ture ta yayi daga jikin sa Yana mai ɗaukar rigar sa yasa kafin yace"yanzu ba maganar biya wa kai buƙatar ƙasa ake ba,magana Ake ta maganar Biyan buƙatar bashin da Neslihan ke ɗauke dashi akai,lokacin biyan sa yayi,yanzu ina so ki tura saƙo gurin Babban minista na cewa maganar dakaruna na boye guda ɗari shida da zan basa tana nan bata sauya ba muddin bai sauya daga alƙawarin mu ba yau Neslihan zata mutu".takowa Siyah tayi tace"umarnin ka shine rayuwa ta masoyina,amma kasa a ranka bashin kaini ƙasan ka yana nan bayan mu kawar da Neslihan,ka bani shi matsayin tukuicin murna".da wata irin tafiya dake ɗaukar masa hankali ta fita domin aikawa Babban minista saƙon UMER,zama yayi bayan fitar ta yana mai tunanin ta inda zai fara wajen ganin ya kawar da Neslihan.
UMER Babban Sadauki ne daga Birnin MAMLUK,Ma'abota bautar Dodon tarihin na Simdas ,ƙasa wadda ke da babban dabi da Ottoman,Mahaifin UMER Babban wazirin Sarkin ƙasar ne sannan babban Mayaƙi da Sarkin su zai iya bada dukkan rayuwar sa amana gare sa sanin tana hannu mai kyau,ciki yaƙin da suka kara tsakanin su da fadar Sultan Halil suleyman, Neslihan tayi sa'a wajen Kashe Wazirin Sarkin MAMLUK ,duk da UMER bai taɓa ganin Neslihan ba amma labarin ta bai bar sa ba sannan zafin fansar dake zuciyarsa ma haka ,yayi alƙawari akan sai ya kashe NESLIHAN ya bawa Babban abun bautar su kanta matsayin Sadaukar wa,a binciken sa ya gane Babban minista shine mafi girman cikin maƙiyan Neslihan dan haka ya ziyarce sa da tayin sa wanda baiyyi tunani biyu ba ya amsa.. Siyah Babbar Hadimar UMER ce kuma mai biya masa dukkan wata buƙatar sa a ka gado da kuma waje, makirci babu wanda Siyah bata iya ba ,sannan ta iya wasa da Guba wanda ke jikin farcen ta ,abun gado ne,tsakanin ta kuwa da Mahaifin UMER raino ne yayi mata bayan ya kwace ta daga hannun masu kashe Mayu,dan a cewar su Siyah mayya ce,bayan ya ceto ta ya Kaita gidan sa ya raine ta sannan ya koya mata faɗa da takobin,bangare guda a waje Siyah Hadimar UMER ce amma a bayan fage abin yafi haka.
Duk da taron a ranar Sultan Halil ya ƙirƙire sa amma fa haka bai saka an tsara sa cikin rashin kyau da ƙawa ba,zaune Neslihan take kan kujera yayin da IREM ke aikin tsantsaro mata ƙyanta,bayan gama ƙwalliyar Neslihan ta kalli kanta a mudubi kafin ta kalli IREM tace"yanzu na fahimci mai yasa Valide Sultan ta dage ke zakina mata ƙwalliya,Ni kaina ban gane kaina ba saboda tsabar ƙyau da nayi,ina ga na waje"murmushi IREM tayi tace"Ai Ranƙi ya daɗe kece kika yiwa ƙwalliyar kyau ba ƙwalliyar ba"ƴar Dariya Neslihan tayi tace"kin san hanyar ki da kalamai,idan na dawo zan ganki"godiya IREM tayi kafu ta bar ɗakin,Kallan Serra dake ta faman Binta da kallo tayi kafin tace"Serra shin Ban cika ƙwallliya ba duba da cewa taro ne iya ƴan gida da kuma abokan arziƙi?"gyara mata gashin ta da ya sauko Serra tayi tace"baki cika ƙwalliya ba,rabon da naganki da ƙwalliya na manta ,amma kinyi mutuƙar kyau nasan idanun kowa yau akan ki yake"murmushi tayi tana mai sake kalla rigar da mahaifiyarta ta kawo mata,ajiyar zuciya tayi tace"yau bari mu fita a mace".
Bangare guda kuwa a sashen Ayet matar sarkin ta uku ,Selma ce matar sarki ta biyu zaune tana ta jijjiga ƙafa cike da ɗauki,zama Ayet tayi ta dafa ta tace"selma ki ƙwantar da hankalin ki yau fa Neslihan kamar ta mutu ne sai dai idan uwarta zata iya ɗaukan ciki ta haifi wata,kina kallo saboda bata ɗauke mu da daraja ba inda muke bata zo ta gaida mu ba matsayin matan sarki saboda bata ɗauke mu da muhimmanci ba"kafun selma tayi magana Hadimar Ayet ta shigo bayanta biye da wani mutum sanye da baƙaƙen kaya irin waɗanda Masu kisan boye suke sakawa,murmushi Selma tayi tana mai faɗin"kasan aikin ka ba sai na sake maimaita wa ba,Neslihan kada ta bar wannan gurin yau a raye,idan ka aikata hakan mahaifiyar ka zata rayu,idan kuma aka samu kuskure ina Mai tabbatar maka da hannu na zan kashe ta".cike da ladabi da tsoro ya Amsa kafin suka sallame sa,wata irin dariya Ayet tayi tace ma Selma"fatan Nasara" yayin da ita ma ta mayar mata.
A/N
Tofa wannan liyafa dai babu alamun zata zo da daɗi domin kuwa mutum biyu ke farautar Neslihan?
Idan kana jin daɗin littafin kayi sharing ma yan uwa da Abokan arziƙi.
TBC
08130229878
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top