2

NESLIHAN SULTAN

Na

Amina Jamil Adam(CHUCHUJAY)✍️

Chapter 2

__ Cike da girmamawa ta ɗuƙa gaban Sultan Halil Suleyman tace"ina miƙo Gaisuwa ga Sultan Halil adalin sarki,sannan ina mai gabatar da kaina matsayin wadda ta sare kan Janaral Jamal Bisa laifi da na kama shi da shi na yiwa Baiwa fyaɗe wanda a iya sanina Daular Usmaniyya tayi Babban Allah wadai da fyaɗe da masu aikata shi,ina fatan Sultan bazai ga laifin hukunci na ba duba da ya aikata ɓarnar ne a ƙarkashin Rumfata wanda hakkina ne na hukunta sa".Babban Minister Esma'el Kizlar ne ya katse ta ta hanyar faɗin"wannan ba ƙaramun zunubi bane kike aikata Neslihan domin kuwa laifin da ya aikata ba hukunci na datse masa rayuwa ne dai dai ba ,sannan mene dan yayi wa baiwa fyaɗe kila ma da goyon bayanta sannan wane ya sani yayi mata ƙwarƙwara kawai raki ne naku irin Na Mata Duk Wani Abu da zaku zama ba zai barku ba".cije Baki NESLIHAN Tayi tana Mai san danne kururuwa da zuciyar ta take mata na San ganin ta soke Babban minister ,kafin tace Wani Abu daya daga cikin ministocin dama waɗan da a kullum a bayan ta suke yace"Ranka ya ɗade Sultan kowa a nan gurin yasan Gimbiya Neslihan mutum ce mai adalci ,tabbas kuwa idan ya zamana ta sare kan janaral Jamal dalilin ba ƙarami bane duk da kuwa sani da tayi na yanayi girman sa,Sarkin mu mutum ne mai Adalci,muna fatan zai Karrama Gimbiya Neslihan saboda Hukuncin da ta ɗauka bisa abinda ya faru"a tare mabiyan Neslihan suka sake maimaita maganar da ta ƙarshe cikin amincewa da cewa a karrama Gimbiya Neslihan saboda hukuncin da ta ɗauka bisa abinda ya faru.

Cike da baccin rai Babban Minista ya kalli Ministan da ya fara wannan magana yace"ina fatan Kasan da sanin wanene Janaral Jamal ,babu koda shakka Dole ne Gimbiya ta karbi hukunci na kashe Babban mayaƙi akan abinda bai taka kara ya karya ba".cike da fushi Neslihan ta mayar da kallan ta gare sa tana mai san saita kanta tace"idan har Babban Minista Esma'el yana da dama na yanke hukunci a cikin wannan masarautar ina neman Alfarma da ya nuna mun wannan Ikon ya kaini cikin Babbar Kurkukun Diyabakir ya kulle"takowa tayi gaban sa tana mai ƙarawa da cewa"Babban Minista ina so ka sani Jamal ya mutu kuma nice nan NESLIHAN na kashe sa ,idan kuma da ace ya kasance kaine a Gurbin da na tarar da shi da tuni kaima yanzu kana ganawa da mahaliccin Ka".take mabiya Babban minista suka fara maganganu akan cewa Neslihan nayin rashin ɗa'a ga Babban Minista yayin da mabiyan ta ke nuna rashin yardar su .Gyaran Murya guda ɗaya da Sultan Halil Suleyman yayi itace ta jawo da hankalin kowa sannan ta haifar da nutsuwa ga duk wani mabiyan sa dake cikin kutun,Kallan Neslihan Yayi cikin yanayi na Alfahari da ita kafin yace"watanni shida kenan Babbar Gimbiyar wannan masarautar bata Gida wanda ba sai na maimaita daga inda ta fito ba,Kowa anan yasan cewa ita ɗin tana chan tana wasa kaifi da kaifi da maƙiyan mu,a yau Gimbiya ta dawo gida Kamata yayi mu tarbeta cike da murna ko mene ke da akwai bazai gagara a duba daga baya ba,ina yiwa Gimbiya maraba da dawowa gida Kuma a daren yau za'a shirya bikin Dawowar ta gida ,ya kamata ace ko wanne minista na ya koma gida domin shiryawa wanann biki na tarbar Sojar mu bayan samo mana Nassara".yana kai aya ya miƙe inda wazirin sa ya gyara masa hanya.

Wani mugun Kallo na kullaci Babban minista ya bawa Neslihan kafun ya juya ya bar gurin inda yana fara takunsa mabiyan sa suka mara masa baya,Murmushi kawai Neslihan tayi domin tasan irin tsanar da tarin mutane dake cikin Wannan Babbar kotu suke mata.kallan akwatin gawar Janaral Jamal Tayi kafun ta bada umarni da akai sa ga iyalan sa,tana kai aya ta juya ta bar cikin Kotun Aley na biye da ita a baya,cike da damuwa baya fitar su Aley yace "Neslihan a lokaci irin wannan Bama buƙatar Ƙiyayyar Babban Minista Esma'el sannan a yarda Sultan ya ɗauki wannan al'amari na tabbata tsanar ki ta sake ruruwa ne cikin zuƙatan su sannan bamu san kuma mene zasu aikata ba".ƴar dariya Neslihan tayi kafun tace"Babu abinda zasu iya yi Aley,duk wanda kuma yace zai ƙulla mun wani tuggun Nima na shirya tsaf domin kuwa babu irin siyasa da ban iya ba bugu da ƙari kuma a yanayi na yarda aka haife Ni duk wani abu da Ba'a so ni shine nake so".bai sake faɗin komai ba illa cigaba da Binta da yayi yana mai nazari,dakatawa tayi da tafiya ta kallesa tana mai matsowa kusa dashi,matsawa baya ya fara yana mai mata kallan tuhuma,cigaba tayi da matsawa daf dashi,fuskar ta takai saitin fuskar sa Wanda hakan yasa ya ɗauke dukkan wani numfashin sa ya kulle idanunsa ,hannunta ta saka ta shafa kan hancinsa kafun ta matsa da baya tana dariya kafin tace"Kana da kyau Aley ,ka buɗe idanun ka ba sumbatar ka zanyi ba Duk da kuwa ni Mai yin abuce da bashi da dalili,ka wuce gida ka daina Bina haka kaje ka shiryawa liyafar da mahaifina zai shirya mana ,kayi shiga mai kyau domin ina san ganinka cikin abu mai kyau bayan kayan yaƙi da na saba ganin ka dasu"juyawa tayi ta bar gurin yayin da Aley ya sauke wata Ajiyar zuciya ,dafe kirjin sa yayi yana mai kallan gefe da gefe domin tabbattar da babu wani wanda ya gansu dan Neslihan babu wani abu da ya dame ta idan na da wanda ya gani ɗin,bai san mene yake ɗamun ta ba wani lokaci,kaɗa kai kawai yayi ya fara tafiya dan wucewa gida.

Kai tsaye bayan Neslihan ta wuce bata tsaya ko ina ba sai sashen Valide Sultan Safiye wato Mahaifiyar Sultan kuma kaka mafi soyuwa ga Neslihan, Safiye Nada Babban Gurbi a cikin masarautar a matsayin ta na mahaifiyar sarki,cikin Ayyukan ta kuwa akwai Rainon Sultan ɗin da zai zama Sarki nan gaba da kuma kula da abinda ya shafi Harem,ma'ana bangare na mata cikin gidan,lokacin da aka haifi Neslihan taso namiji aka samu amma da taga mace ne hakan bai rage soyayyar Neslihan a zuciyar ta ba, kafatanin Abubuwa da dama gurin ta Neslihan ta koya domin tun tana da shekaru biyar ta dawo da ita sashen ta,Safiye Jaruma ce ta gaske sannan macece mai Izzar mulki wadda bata ɗaukar Abinda ya shafesa da wasa,Kishingiɗe take kan shimfidar ta wadda tasha Ado,yayin da bayin ta guda biyu ke mata fifita,jikinta sanye yake da kayan sarauta na Alfarma ,ƙyaƙyawar fuskar ta kuma ɗauke da ƙwalliyar da ta ƙara fito da tsantsan kyawun ta ,cikin Sanɗa Neslihan ta shigo ,alamu tayiwa bayin dake gurin akan suyi shiru kada su sanar da zuwan ta ,cikin sanɗa ta cigaba da Takawa gurin Safiye tana mai gumtse dariyar ta, Ajiyar zuciya Safiye ta sauke har a lokacin idanun ta a lumshe kafin tace"Yarinya ta Neslihan ,ina so ki sani babu yarda za'ayi ki bayyana inda nake na kasa gane ki".tafi Neslihan tayi ta saka dariya tana mai cewa "Valide Sultan,Babbar Sarauniya ,Mahaifiyar sarki ,Kakar Gimbiya kuma Jaruma Neslihan Sultan ".buɗe ido Safiye tayi tana mai mutuƙar nuna farin cikin ta a fuska da zuciya kafin ta buɗe hannu alamun Neslihan tazo,da gudu Neslihan ta ƙaraso tana mai Cewa "Har yanzu bazan girma gurin ki ba Kaka ta"rungume juna sukayi kafin Safiye ta sumbace ta a kumatun ta tace"Nayi kewar ki Gimbiya ta ai da baki dawo ba da kai na zan zo Boda na kawo miki ziyara"kallonta ta mayar kan Baiwar dake mata fifita guda ɗaya tace "Aje a buɗe ma'adanin Kaya ayi sadaqa dan ina cikin mutuƙar murnar dawowar Neslihan".Bata wani jima ba ta bar sashen kakar ta dan zuwa gurin Mahaifiyar ta kafin ta wuce ta huta saboda Liyafar da Mahaifinta ya haɗa mata dare yau.tana tafiya taji saukar dutse a bayan ta ,juyawa tayi cike mamaki dan ganin wanda yayi mata wannan ɗanyan Aikin,idanun tane suka sauka kan Ahmet hannunsa riƙe da danƙo,da mutuƙar mamaki ta isa gare sa tace"Ahmet naka Barka da zuwan kenan gare Ni?,zo nan ka bawa yayarka haƙuri "haɗe rai yayi yace"bazan zo ba,Ke muguwa ce wadda bata da imanin kashe mara laifi,babu tunanin jini ko Alaƙa,ke mutuniyar banza ce Azzaluma,kuma Ni Mahaifiyata ta Koya mun cin zarafin Azzalumai,yau danƙo na miki gobe takobi ne"da sauri Mai kula dashi da ke aikin neman sa tun ɗazun ta ƙaraso inda yake tana mai cewa"ran ka ya ɗade maza ka bawa Gimbiya Neslihan haƙuri"maƙe kafaɗa yayi yace"bazan bata ba ,Azzaluma ce kuma Ni kafin ta kashe Ni zan kashe ta wata rana".takowa Neslihan tayi da mamakin jin Abunda ƙanin ta Ahmet ke faɗa akan ta wanda ta tabbatar Koya masa faɗa akayi har ya haddace ya saka a kan sa,Hannun sa ta kama wanda yake ɗauke da danƙon ta murɗa ta ƙwace,ba tayi wata wata a ta tsinka,cillar wa tayi a gefe sannan tace"ina maraba da zuwan ranar da zaka kashe Ni Ahmet Amma kafin ranar yanzu ka koma ka cigaba da karɓar darasi"barin gurin tayi tana mai share Mai kula dashi dake aikin bata haƙuri.kuka Ahmet ya saka Yana Kallan danƙon da yafi so fiye da komai,dafa sa Ayca mai kula dashi tayi yace Yarima Ahmet kayi haƙuri muje sai na haɗa maka wani danƙon,bige hannun ta yayi ya ruga da gudu dan zuwa sashen mahaifiyar sa Yana kuka,Nazli dake tsaye tana gyara shuƙa ce tayi saurin Aje Almakashin dake hannunta jin kukan Ahmet wanda taji kamar an datsa mata mashi,duƙawa tayi gaban sa tana mai cewa"Rabin Raina lafiya kake kuka haka?"cikin Kuka yace"Neslihan ce ta tsinka min danƙo na"cike da bacci rai tace "saboda mene,daga dawowar ta zata fara cin zarafin yaro"Ayca dake biye dashi ne ta mayar mata da abin da ya faru,share masa hawayen sa tayi tace"Ayca tafi dashi ki sama masa wani".Almaƙashin ta ɗauka bayan wucewar su ta yanke saman Shuƙar baki ɗaya tana mai dunƙule hannun ta kafin tace"kiyi takun ki yarda kike so Neslihan,a sannu zan yanke miki fikafukan da kike tunanin kina dashi ciki sanyin rai ,Ahmet kuwa shine magajin Sultan Halil ba ke ba,wannan alƙawari ne nayi miki sannan nayiwa kaina koda kuwa zan rasa rayuwa ta ne.

TBC

CHUCHUJAY ✍️

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top