1
NESLIHAN SULTAN
Authoress:
Amina Jamil Adam (CHUCHUJAY )✍️
INTRODUCTION
Yaren Rubutu:Hausa
Addini : Muslunci
Ƙasa:Turkiya
Bangare:Sarauta
Author's Note!!
Assalamu alaikum every one,barka da kasancewa dani cikin littafin NESLIHAN SULTAN.
Neslihan :wadda ke kan Jini na sarauta ,Yar sarauta,
Yarinyan Namiji a jinin sarauta:ma'ana Sultan,ta fito daga bangare na maza a cikin Ahalin sarauta.
DISCLAIMER ‼️
Wannan littafin ƙirkirarre ne ,ba labari ne wanda ya faru ba,ban yarda wani ko wata su sauya mun labari ba either electronic or mechanical method ba tare da sahalewa ta ba.
Ba tare da dogon bayani ba mu tafi cikin Neslihan Sultan Kai tsaye🥰
BISMILLAHIR'RAHMANIR RAHIM
CHAPTER 1
DAULAR OTTOMAN
Daula ce wadda akayi ta a ƙasar turkiya wadda ta ɗau tsakanin lokacin 1299 zuwa 1923,daular na zaune a turkiyya kuma tana da iko da gabashi da kudancin ƙasashen dake gefen kogin meditereniya ,cikin mabiyan su akwai Daular Abbasiya wadda aka fi sani da Hamis,da kuma Daular Rumawa.Daular ta samu ne sakamakon cinye ƙasashe da yaƙi,Duk Wani sultan Wanda ya Mulki Daular ba sai ka tambayi karfin mulkin sa ba,Haka take kasancewa akan mulkin Sultan Halil Suleyman.ko Ina kaji ana magana ta ƙwazo da jarumta a cikin masarautar to zaka ji ana ambatar NESLIHAN SULTAN Babbar gimbiya kuma tilo a gurin Sultan Halil Suleyman da Sarauniyar sa Burak Sultan wadda ake wa laƙani da Haseki Sultan ma'ana Matar sarki,laƙanin ta ya samu ne a zamanin Hurrem Sultan wadda take matar ottoman Sultan Suleyman sannan mace mafi karfin tasiri na mulki da ƙarfi a tarihi na Sultanate ma'ana Zamanin da mata ke da ta cewa a harkar da ta Shafi tsarin Mulki.ya kasance bayan Sarauniya Burak Sultan Akwai mata Uku ga Sultan Halil amma duk cikin su Babu wadda ta samu ciki dashi face Amaryar sa ta Karshe Nazli Sultan wadda ta haifa masa yaro ɗaya mai suna Ahmet wanda ke da shekara Goma da haihuwa, Sauran Matan biyu ,Selma da Ayet sun dangan ta rashin haihuwar su da cewa Burak Sultan ta cinye mahaifar su dan bata da ɗa namiji dan haka suka haɗe kai wajen tsanar ta da neman duk wata hanya da zasu bi domin ganin cewa sun ƙawar da ita daga Rayuwar Sultan Halil.bangren Nazli kuwa Baka jin kanta amma cikin kasan zuciyar ta tana mutuƙar kishi da Burak da kuma ɗiyar ta Neslihan wadda Sarkin baya da magana face da tata,sannan ya bata Babban Ƙarfi cikin masarautar,abu guda Nazli ta saka a ranta wanda shine bawa yaranta Training ta yarda a komai zai wuce Neslihan ya kuma zamo ɗa mafi soyuwa a cikin masarautar.Tambayar shine shin Ahmet zai iya maye wannan gurbi da Neslihan take dashi?
Bari muje ga Neslihan domin samun Amsar tambayar mu.
BABBAR BODA
Gari Yayi duhu sannan Haske na wuta wadda aka haɗa da itace shine kawai abunda ke bada Haske tsaƙanin Tentuna da aka kafa masu dama,ko ina shiru sakamakon dare da ya tsala amma fa idan a ace maƙiya zasu kawo farmaki a gurin kafin ka farga Jaruman da aka Tara a gurin zasu miƙe domin kowa bacci ne ake yi da ido ɗáya sannan ga masu tsare gida wanda kamar ma su baccin baya kawo musu ziyra,ƙananun kuka na mace dake tashi cikin tenti guda shine Abun da zai ja hankalin ka kasan cewa akwai Damuwa a gurin,ɗaya daga cikin mayaƙan dake kan tsaran ranar ya kalli gudan da suke tare yace "Hayat kana jin koken da nake ji a ɗakin Janaral Jamal kuwa?
Tsaki Hayat yayi yace"sabon abune wannan gurin ka?ba zai wuce wata baiwar yake haikewa ba tunda kasan halin sa na akuyanci,kai zan so kuwa ace haka ne muga yaya Babbar janaral zata yi dashi". rufe bakin sa ke da wuya sukaji wani matsanancin ihu wanda ke fitowa daga Tentin Janaral Jamal,a tare dukkan su suka tashi domin zuwa suga abinda ke faruwa ,a yarda Ihun ya tsorata su suka nufa gurin dan ganin meke faruwa haka ta kasance ga sauran tentunan domin kuwa kafin kace ƙwabo sadaukai sun fito ɗauke da taƙwabin su.
A bangare guda na Baban Tentin da kana kalla kasan cewa na oga ƙwataƙwata ne kuwa mammallakin gurin bai wani yunƙuri na fitowa dan ganin abinda ke faruwa ba,Baiwar dake ninƙe kayan ce ta kalli Surar dake ƙwance kamar babu wani abu dake faruwa ne tace"Gimbiya Neslihan nasan ba bacci kike ba sannan wannan ƙara da kuma ƙururuwar fitowar mayaƙa bata wuce ƙunnen ki ba,Na san kin gaji,amma baki ganin ya kama ta ki je kiga Abinda ke faruwa,ko wasu suka samu nasarar Tsallakowa ."a hankali Wadda aka kira da Gimbiya Neslihan ta miƙe daga ƙwancen da take ta zauna tana mai yin hamma kana Tace"Serra ,Serra ,Serra,Ki kalle Ni da kyau,tunda na san kaina shekaru 25 na sanki sannan na tabbata kema kin Sanni fiye da kowa domin kuwa ba iya Mataimakiyata kawai kika tsaya ba,ke ɗin Aminiya tace,shin a yawan Baiwar da Allah yayi mun Bayan tsantsan Kyau da Iya yaƙi da sanin Kan takobi nasan kin da cewa ina da baiwar sanin mene ke faruwa a inda nake koda bana gurin,wani mai ɗanyen kan ba zai taɓa ƙokarin Shigowa Babbar BODA wadda Ni Neslihan Nake cikin ta ba na kasa ganewa,Ba Haurowa akayi ba,Matsalar ta cikin gida ce sannan koda ban fita ba yanzu kafin ki ƙifta ido zaki ga masu kawo ƙorafi,"maganar da akayi daga waje ne yasa Neslihan Kallan Serra tace"kinji ba ,je ki tarbi mai magana kiji mene ke faruwa mugani idan cikin sojojina da wanda zai baƙunci lahira ne dan jikina ya bani ko ba'a mutu ba jini zai zuba".ƙarasa maganar tayi tana mai shafa wata sarƙa dake Daga Tsintsiyar hannunta zuwa ɗan yatsanta na tsakiya.Aje kayan Serra Tayi ta nufi ƙofar dan ganin mai san magana da Gimbiya Neslihan,Babban Mataimakinta ne A wajen yaƙi Aley wanda ta bawa yarda matuƙa sannan ta wani bangare Abokai ne domin kuwa tare sukayi Yarinta,karatu da kuma koyan Yarda zasu sarrafa taƙobi,cikin Damuwa ainun ya Kalli Serra yace"ina san magana da Gimbiya Yanzu ,kiyi mata magana".kafin Serra tace wani Abu Gimbiya Neslihan ta fito cikin takun ta mai ɗaukar hankali wanda kallo ɗaya baza kace ta sauke kan maƙiya bila Adadin ba,shafa sarƙar dake hannun ta tayi tana mai Kallan Aley kafun tace"Aley nasan tabbas tunda kazo bakin Tenti na A cikin wannan dare akwai damuwa wadda Ni kaɗai zanyi maganin ta,sannan ina so kai da Serra ku sani a gurin nan Ni ba Gimbiya bace ,Ni mayaƙiya ce mai Jagoranta sojoji Dubu biyu da saba'in,Amma idan muna cikin Daula babu laifi idan kun kira Ni da Gimbiya,maza ka sanar dani abunda ya tada hankalin mutanena kowa yafito a wannan lokaci".cike da Damuwa Aley yace"Akwai damuwa domin kuwa Janaral Jamal ke keta haddin Babbar Baiwa da kika basa a shekaran jiya,sannan duk gurin nan babu wanda ya isa yayi yunƙurin shiga duba da sanin wanene shi sannan.... "Hannu Neslihan ta ɗaga masa tana mai takawa zuwa bangaren da zai sada ta da Tentin Janaral Jamal ranta a mutuƙar bace,ba tare da ta damu da gaisuwar da Suke bata ba tace"ina san kafun na rufe idanuna na buɗe a ƙwashe mun wannan rumfar data katange Jamal da Abunda yake aikatawa a ciki".A yarda ta bada umarnin kamar jira suke suka ɓaɓɓake tantin wanda ya Bayyana Janaral Jamal kan Wannan Baiwa yana sukuwa kamar ya samu doki,saboda tsabar yarda hankalin sa ya bar jikinsa bai ma san an buɗe Tentin ba Aiki kawai yake yayin da Baiwar a wannan lokaci batama cikin hayyacin ta,cikin Matukar baccin rai Neslihan ta nufi taƙobin sa ,kafun kowa ya farga Kan Janaral Jamal ya dawo ƙasa daga kan gangar jikin sa,Alamu tayi da hannu ,babu ɓata lokaci sojoji suka sauke gangar jikin janaral Jamal daga kan Baiwar wadda baki ɗaya ba zata ce ga inda take ba,shafa takobin Neslihan tayi ,jinin da ke jiki ta goga a hannunta ta mirza a hankali kafun tace"ita taƙobi Rashin Amanarta yafi Amanarta yawa domin kuwa bata duba kaine uban gidan ta taƙi sauke kanka daga gangar jikin ka bisa wakilcin wani,Ni Neslihan Bana manta Alheri,mahaifina ya koya min tuna Alheri,sannan bana wasa da hakan saboda haka ku rufe Janaral Jamal ku gyara sa gobe idan an wuce Daular Ottoman zan wuce dashi Domin na kaiwa iyalan sa,domin kuwa yayi mun Alheri Guda ɗaya lokacin da yayi sanadin shiga ta Babban Kurkukun Daular ottoman na sati guda,Ina so ku sani bani da damuwa da tsoma hanci na cikin shirgin wasu amma muddin ka taka doka ta zan taka kanka ko wanene kai,na faɗa a baya zan maimaita ,rundunar Neslihan Sultan Bata yarda da yiwa mace fyaɗe ba koda kuwa mafi ƙasƙantaciyar kuyanga ce ,shi yasa na baku damar ɗaukan matan ku tare da ku,idan baza kubi umarni na ba mafi sauƙin Azaba da zanwa mutum shine na raba kasan da jikin sa,idan kuma Ubangiji na bai ƙaddara mutuwar sa ba a ranar to zan dandaƙe masa gaban da yake keta mata,Allah Yayi wa Janaral Jamal mutuwa a hannun taƙobin sa bisa wakilcin Neslihan Sultan,ina san kafin na isa Masarautar Ottoman labarin nan ya riga Ni shiga gari,Babban likita yazo ya bawa zeynap kulawa".bata Jira maganar kowa ba ta juya ta bar gurin inda tana wuce wa sojojin suka fara kayya kayya tsakanin su.
Neslihan na shiga tentin ta Aley ya biyo ta cike a damuwa,zama tayi kan kujerar fatar fatar Dila dake aje gurin karatunta tana mai Kallan Aley kafun tace "Abokina Aley shin zaka sha shayi ne ,domin kuwa a yanzu ina cikin yanayi na shan shayi,shin Abokina zai tayi ni?Serra ki haɗo mana shayi mafi daɗi a cikin sindaran Shayi da muke dasu ,idan san samu ne ya kasance mai ƙarfi domin bana tunanin bacci zai samu gare ni..Cike da Kulawa Aley yace"Neslihan wannan abin fa ba ƙaramun abu bane sannan ba ƙaramin cece kuce zai haifar ba ciki kotun Sultan".dariya tayi kafin ta kallesa tace "Aley Aley,Jamal ya mutu ba zai dawo ba sannan idan da ace za'a dawo mun da baya zan sake sare kansa daga gangar jikin sa banji koda ɗigo na dana sani ba,sannan kotu da kake magana duk yan siyasa ne sannan babu ɗaya daga cikin su da zai iya yin wani abu dangane da hukuncin da na yanke,idan baka yarda ba kuma bari kagani".shiru yayi na wani lokaci kafin ya ƙara da cewa "ina fatan bayan wucewar mu Mayaƙan Byzantine bazasu kawo farmakin shammaci ba".ɗaukar ƙaramin kofin shayin da Serra ta kawo mata tayi kafun tace"Abokina Aley sai nake jin kamar gwiwarka ta fara sarewa a al'amari na,idan ka leƙa cikin Kurkukun Anemas jama'arsu ce na tara kuma babu wani abu da zasu iya akan Hakan domin kuwa garin su yanzu yana tafin hannuna ,duk wani abu da na saka gaba kai shaida ne bana ajewa sai na kai,kai dai Aley kasha Shayi ka aje damuwa dakaru na suna nan domin kare wannan boda ,Ni kuma yanzun ya kamata naje nayi katsalandan a cikin Babbar kotu wadda ke ɗauke da munafukan mabiya ,ina fatan kana tare dani?"ba tare da yace mata komai ba yayi murmushi kafin ya ɗauki kofin shayin ya kurɓa,murmushin itama tayi dan tasan komai wuya komai daɗi Aley bazai bar bayan ta ba.
Kamar yarda Neslihan ta buƙata kafin ta isa cikin Babban Birni maganar mutuwar Janaral Jamal ta karaɗe ko ina inda mutanen kotun Sultan suke daƙon isowar Neslihan domin ta basu gamsashen bayani.tunda ta doso Babbar ƙofar Shiga Birnin masoyan ta suka fito suna mata maraba da waƙe da raye raye wanda galibin su mata ne,bugu da ƙari kuma duk abinda Neslihan tayi dai dai ne,hannu take ɗaga musu a kan dokin ta yayin da fuskar ta ke ɗauke da fara'a,Kallan Aley dake gefen ta tayi tana mai cewa"Abokina Aley ina mutuwar san mutanen Daular ottoman sannan nayi alƙawarin basu kulawa Wadda nasan zan iya ba sai wani ya faɗa mun ba".murmushi Aley yayi yace"Ko wanne guri kika taka ki sani cewa Aley yana tare da ke".maida kallan ta tayi kan Mutanen tana mai jin wani irin sanyi a ranta kafun tace"Na sani "a taƙaice...koda suka isa fada kai tsaye Kotun Sultan ta nufa dan tasan a yanzu hakan masu baki da kunu suna nan suna neman sharrin da zasu bita dashi,Gawar Janaral Jamal itace Abinda ya fara sallama cikin kotun,ɗaya daga cikin ministocin Hagu ne yace "wanne la'anan nan ne ya kawo mattace har cikin Kotun mai girma Sultan Halil babu tsoron abinda zai biyo baya"?".Neslihan ce nan Mai girma Babban Minista Esma'el kizlar sannan a iya sani na Ni ba la'antacciya bace ,ban sani ba ko a yanzu ne kake san la'anta ta "Muryar Neslihan ta karaɗe cikin kotun yayin da maganar ta da takunta suka kasance cikin izza da rashin tsoro.
Domin yin karatu cikin kwanciyar hankali ku kasance dani a channel ɗina.
08130229878
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top