Chapter 3
"Tuni wajen ya rude da hayaniya banda kananun maganganu babu abinda yake tashi a gurin wanda ya sanya irfan da nasreen suman tsaye,cikin fushi ammi ta kalli nadia tace ki kalleni da kyau girma da darajar gidannan ya wuce kizo kiyi mana wannan kalar iskancin ko mahaifinki bai isa yazo ya ci mana mutunci har gida ba ballanta ke kanki...da sauri sauran kawayensu nasreen suka shigar da nadia mota suka fita daga gidan,cikin lokaci kadan gaba daya taron ya watse don nasreen bata kara 30 minutes a wajenba irfan da hisham suka sata a mota suka mayar da ita gida
"Da kyar nasreen ta samu ta lallaba nadia sannan ta hakura domin a yanzu bata da wata kawa wacce ta wuce nadia saboda gaba daya halinsu da rayuwarsu yazo daya,sosai ake event's harda na rashin hankali wanda ake kashe kudade masu yawan gaske wajen yinsu...a gajiye nasreen ta dawo daga freinds eve din nasu wanda a yanzu hotunansu ke ta trending a gari ana sake jinjina #Nasfanwedding
"Kaga irfan ka dena damun kanka akan sha'anin mata kasan su mata kullum halinsu baya sauyawa gara ma ka dena damun kanka akan nasreen tunda kai dai kana sonta itama tana sonka toh ya zama dole kayi hakuri da halinta hisham ya karasa magana yana kallon irfan,tsaki irfan yayi yace nasani hisham amma matsalar nasreen tafi ta kowacce mace saboda ai kai sanda kayi aurenka baka fuskanci wannan matsalar ba sannan ina ganin mutane dayawa duk basa fuskantar kalar wannan abun...honesty speaking na gaji da wannan masifar hisham
"Shiru hisham yayi kadan sannan yace c'mon angon nasreen daga yau fa shikenan gobe zaa kai maka amaryarka kuje chan ku karata ku bar kowa ya huta don wallahi har ramewa nayi saboda matsalar wannan auren naku....cikin tsokana ya hade hannunsa kamar yanda indiayawa ke gaisuwa yace namaste wahala
"Kai masa duka irfan yayi yace kaga mallam kazo mu koma ciki kafin mutane su fuskanci halin da ake ciki
"Toh kasan dai bazamu koma ciki ba tare da dollars din liki ba kamar yanda amaryarka tace hisham yayi magana cikin tsokana
"Sake kai masa duka yayi yace you will never change idiot kawai,kaga duba cikin mota akwai dollars cikin briefcase dina dazu na karbesu daga ZOBAN jewels company sai muyi amfani dashi inyaso sena yiwa dad replacing da wasu kudin,kusan kwana akayi ana dinner party dinsu nasreen yanda aka gayyaci manya manyan artist kamarsu davido,kizz daniel,ckay,burna boy,Asake,rema,oxlade,naira marley,joeboy da korede bello duk sun hallara bangaren mawakan hausa suma ba,a barsu a baya ba domin su Ali jita,hamisu breaker da ado gwanja duk suma sunje wajen...sosai mutane ke video's da pictures don hatta souvenir din da aka raba wajen bikin manya manyan expensive abubuwa ne a ciki
"Karfe 2 na rana aka daura auren irfan da nasreen wanda farin ciki ya kasa boyuwa a fuskar amarya da ango har kawayen amarya ma sosai akaci gaba da shirye shirye,karfe 8 motocin daukar amarya suka zo aka dauki amarya,kawayenta da yan'uwanta zuwa gidan nasreen dake maitama wanda yayi matukar tsaruwa kana gani kasan an kashe manyan kudi wajen hadashi.....
End of flash back
"Hey sweethearts,thank you all for your best wishes and happy marriage life to you all when it comes to your own wedding....shine abinda nasreen ke fada inda tasa Ringlight gaba tana making tiktok videos da instagram reels,ganin nasreen bata da niyyar dena videos din yasa irfan karasowa inda nasreen ke tsaye ya bata peck a cheek dinta cikin shagwaba tace good morning darling yaushe ka tashi?
"Murmushi yayi yace na dade da tashi kina nan kina ta faman sana'ar taki ko?
"Turo baki tayi tace i am just thanking our well wishers,honey kaga yanda blogs da press ke ta magana akan aurenmu?god i am so lucky ta karasa magana tana hugging dinsa
"Love you my nas...nas irfan ya fada a hankali sannan yace yanzu dai tunda na tashi toh wannan tiktok din ya isa haka muje ki hada mana breakfast i am so hungry rabona da cin abinci a nutse tun kafin a fara hidimar aurenmu kinga kenan yau zanci abincin nas.. dina
"It was like kamar banji abinda ka fada daidai ba hun,kana nufin har yanzu babu wata chef a gidannan?
"Cikin mamaki irfan yace chef?as in how?
"Murmushi tayi tace kasan dai i am not good in cooking,and honestly speaking bazan iya girki a cikin gidannan ba irfan saboda haka idan har kanaso muci abinci a gidannan toh sedai a kawo chef am i mean chefs atleast ko guda 2 ne wanda zasu dinga yi mana girki ba tare da sun gaji ba...wai ma in tambayeka meyasa har yanzu banga alamar masu aiki ba a cikin gidannan?
"Shiru irfan yayi kadan yace okay as you wish,yanzu dai muje ko tea ne musha kafin mu samu abinda zamuci,bai jira ta sake magana ba ya ja hannunta suka nufi kitchen,banda kallon tsaruwar kitchen din babu abinda nasreen keyi kamar tayi ihu saboda farin cikin tsaruwar gidan ko ba komai duk sanda tayi pictures ko videos duniya zata ga tsaruwar gidan da take ciki
"Da gudu nasreen tayi hugging su nadia da sauran freinds dinsu wanda suka shiryawa nasreen komai na bikinta kana ganinsu kasan yaran manyan masu kudi ne....omgieeeee nasreen you are so lucky kalli irin gidan da kike ciki babe what a heaven nadia ta fada tana sake hugging nasreen
"Girls i am so happy after all and i really missed you guys,sedai fa kuyi hakuri babu abinda zaku samu a gidannan sai soft drinks don har yanzu ba,a kawo min chef ba nasreen ta fada cikin tsananin isa da gadara
"Murmushi nadia tayi yace dont mind habibtee,wai ni kam nasreen when are you planning for your honeymoon?kinsan fa yanzu ana aure ake wucewa honeymoon ba,a wuce 1 week
"Gaban nasreen ne yayi mummunan faduwa don gaba daya basirarta ma ta dauke ta manta sam da wani abu wai shi honeymoon,cikin damuwa ta kalli nadia tace are you sure nadia yanzu baa dadewa ake tafiya honeymoon ko?
"Daga kai nadia tayi tace of course yes....don kinga ko basma yar former governor da akayi bikinku tare gobe goben nan zasu wuce paris kuma you know what kasashe har guda 5 zasuje
"Wow this is unbelievable....amma gaskiya sunyi matukar birgeni don haka nima babu abinda ze hana cikin satin nan mu tafi paris honeymoon,sun dade suna hira kafin suyi sallama su tafi ganin har magrib yana shirin yi
"Karfe 8 Irfan ya dawo gida a matukar gajiye kamar yanda yayi tunanin ganin gidan haka ya sameshi dama yayi musu take away na abinci,gyara zamanta tayi cikin shagwababbiyar muryar data saba mishi magana tace sweetheart nifa har yanzu banji ka fara maganar honeymoon dinmu ba please dont tell me that you are not planning for anything
"Murmushi irfan yayi yace oh no darling i am planning something special for us amma ba yanzu ba saboda yanzu i have lots of things to do dole sai na zama less busy tukunna zamu iya tafiya honeymoon
"Tureshi tayi daga jikinta tace kamar ya ba yanzu ba?Idan bamu je honeymoon yanzu ba yaushe zamuje?
"Nas yanzu inada abubuwa dayawa da suke kaina besides ma akwai ayyukan office dayawa dole sena gama abinda nakeyi tukunna zan samu time din traveling ya fada yana kallonta
"Kaga ba wani zance da zaka fada min na fahimta kowacce mace idan tayi aure babban burin mijinta ya shirya musu honeymoon su tafi saboda nuna mata soyayya amma sam banda kai irfan na rasa wacce irin rayuwace wannan ga basma wacce akayi bikinmu tare gobe zasu tafi paris kanaso duniya ta kalleni tace wanda na aura bashi da halin da zamuje honeymoon?ta karasa magana tana kallonsa kamar me shirin yin kuka
"Wani irin takaicine ya kama irfan saboda ya tsani yaga nasreen tana hada kanta da wasu mutanen daban wanda ko alama basu ma hada hanya ba,shiru yayi kadan yace nas ba wai baza muje honeymoon bane tabbas inada halin da zan kaiki duk kasar da kikeso sedai a yanzu bani da wannan lokacin sedai zuwa nan da 1 month kafin nan komai ya zama normal amma yanzu bazan iya tafiya na bar aikin da yake a office ba i dont think ma dad ze barni gaskiya
"Mikewa tayi ba tare da tace mishi komai ba ta nufi bedroom zuciyarta a matukar bace,kiran wayar da ya shigone ya sanya ta mikewa zaune ganin sunan kilishi,da sauri tayi creating murmushi a fuskarta tace hello manya manya
"Nasreen dafatan kina lafiya?
"Lafiya lau wlhi ya komai?
"Alhamdulillah dama inason fada miki birthday party na ne da zaayi gobe i am so sorry na fada miki late wlhi abubuwan ne dayawa ina fatan dai zakizo ko?
"Murmushi nasreen tayi tace oh no karki damu wlh karfe nawa ne?
"7pm a Transcorp Hilton kilishi ta fada a takaice
"Murmushi nasreen tayi tace karki damu i will be there insha Allah
"Tsaye take jikin babban royal mirror din dakin,ba wani heavy makeup tayi ba a face dinta amma nasreen tayi kyau sosai,wayarta ta dauka da handbag dinta bayan ta feshe jikinta da perfumes masu matukar sanyi ta karaso inda irfan yake zaune a palour yana kallon football...kallonsa tayi tace zan wuce
"Cikin mamaki irfan ke bin nasreen da kallo da sauri ya kalli agogon dake jikin bangon daki yaga har 7:30 na dare shin ina nasreen zata je haka,da kyar ya daga bakinsa yace ina zakije kuma?
"Ohh sorry na manta ashe ban fada maka ba tun jiya naso fada maka inaso zanje birthday din kawata ne
"Birthday?irfan ya fada cikin mamaki
"Eh birthday...nasreen ta fada tana kallonsa itama
"Wanne irin birthday zakije da wannan lokacin nas...karki manta yanzu fa ke matar aurece baze yiwu ki dinga yawo any how ba sannan ki kalli lokaci yanzu baze yiwu ki fita a matsayinki na matar aureba kice wai kin tafi birthday
"Kaga don Allah ya isheni haka taya zaka sani gaba kana min wa,azi kamar wacce tayi ridda,aini kaina nasan cewar ni matar aurece amma aurena be isa ya hanani abinda nakeson yi ba saboda banyi aure don na takura ba don wlh idan aurenka ya nemi ya takurawa rayuwata tsaf zan datse igiyarsa in kama gabana,bata jira ya bata amsaba ta fice daga palour da alama ranta ya baci
"Knocking din da akeyi ne ya karu hakan yasa irfan mikewa jikinsa matukar sanyaye yace who's that?
"Muryar ammi irfan yaji cikin tashin hankali ya kalli agogon dake jikin bangon yana matukar mamakin menene ya kawo ammi gidan da wannan lokacin sannan yanzu ya zeyi da ammi idan ta tambayeshi ina nasreen?
Thank you for reading my story!!
I love you all!!!
Heroine🦋
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top