Sha uku
NAHAR
_13_
Kallon shi take yi kamar a tsorace har ya qarasa shigowa parlorn. Sanda ya dago nasa idon sai tayi saurin dauke nata kamar ba kallonsa take ba. A zaune take a takure har ya zauna saman kujerar kusa da ita.
"Maryam." Ya kira sunan ta a hankali. Kamar ba zata dago ba sai ta kalle shi tana jin wani irin abu a kanta kamar zazzabi na shirin kama ta.
"Ke baki san ciwon kan ki ba, abi?" Ya tambaya yana hade hannayensa biyu.
"Amir ba abokin wasan ki bane okay? Kin san mene mahram? Kun zo nan a karatun da kuke yi?"
Girgiza masa kai tayi alamun a'a. "Toh ina so ki sani har ni ma bai kamata kina zama waje daya dani ba muna wasa irin na yara, okay? Bana son rashin kamun kai, bana son shirme. Ba ruwan ki da unnecessary play and stuff like that. Ki kama kan ki. Duk gidan nan babu wani namiji abokin wasan ki! Tashi, just go before you open that river of tears. Maza bace min..." ya nuna mata kofa. Kamar wadda ya zabgawa bulala haka ta tashi har tana nema ta harde ta fice daga parlor din hawayen nata suna tsiyaya.
Wani irin abu take ji a kanta kamar zai rabe gida biyu tunda ya fara magana.
Tana fita ya shafa fuskarsa yana sighing. Da alama ajiye yarinyar nan a gida ba zai taimake ta ba. Zai tabbatar an samo mata mai koyar da ita daga baya sai ta shiga school din don ta dinga hulda da mutane ko hakan ya saka ta san me duniya take ciki.
Da wannan tunanin ya tashi, wayar sa tayi ringing. Yana cirowa yaga Teetee ce wadda a dole an saka su yin waya. Yana gani yasan a gaban mahaifiyarta take so he picked.
"Hello owl I'm busy!" Sai ya kashe. Ko bakomai ya rama tsokanarsa da tayi itama.
Da murmushi mara tushe ya maida wayar sannan ya fice.
*****
Aisha na wanke wanke taji kamar tana jin sallama daga tsakar gida, kallon kanwarta Maimuna tayi dake gefenta tana tsane kwanukan tayi sannan ta tambaye ta.
"Maimoon ba na ce ki dinga rufe mana kofa bane wai?"
"Sorry sis, ina jin Bello almajiri ne fa ya barta a bude."
Tsaki kawai Aishan tayi. Yanzu da ita kadai ce a gidan babu wanda zai saka ta doguwar magana amma Ummah ta hado ta da Maimuna wai ta dinga debe mata kewa especially a satittikan nan da Isma'il din zai dauka bai dawo ba. Wani on site audit din suppliers din su ya tafi daga nan kuma zai je wani training.
Bata so ba dai amma ba yadda ta iya. Tsane hannunta tayi da towel sannan ta cire waterproof apron din da ta saka aka dinka mata takanas. Ita mace ce mai kaifin basira da architectured mind. Yanzu yanzu zata yi designing solution to her challenges. Ta kasance tana jiqa kayan ta idan tana wanke wanke a gaban sink. Ko da kuwa ta dora apron sai ta jike ta taba kayan ta na ciki. Saboda haka sai ta samo wani material aka dinka shi da leather ta saman yadda ba zai taba ratsawa ya jika mata kaya ba.
Fitar ta tsakar gidan yasa tayi turus. Idan har a cikin hankalinta take toh mai kula da Nahar take gani. Hannunta dauke da yar ledar shopping. Gaban Aisha ya fadi amma sai ta daure tayi murmushi sannan tayi mata maraba.
"Sannu da zuwa Hajiya." Ta fadi yayinda ta ajiye mata ruwa da lemo. Yanzu ya zatayi? Me zata ce mata? Ko dai ta sulale ta kira Isma'il ne? Ko kawai ta fada mata gaskiya? Tana wannan tunanin ne Hajiyan ta danyi tari wanda ya saka Aishan firgita har wayar hannunta tana subucewa.
Da ido Hajiyan ta bita amma bata tanka ba. Ba zata manta tarbar farko da Aishan ta mata ba, cikin mutunci da girmamawa shiyasa a yanzu ma bata ji komai ba game da yadda Aishan ta kyale ta sam bata magana balle ta san ran yin doguwar hira. Sai da suka shafe mintuna Hajiya na jira ace mata ga Nahar amma shiru. Da ta gaji da kawaicin sai ta ce,
"Kamar yan albarkan ba sa nan."
Sai da Aishan tayi jim sannan tace, "eh, am sunje isla... oh baban nasu ya kai su hutu ne gidan mahaifiyarsa."
Kamar ba zata ce komai ba sai ta murmusa. "Hakan ma ba lefi. Ga yar siyayyar alawa da na kawo ma Nahar din. Ko zaki iya hada ni dasu a waya?"
Da sauri Aishan tace eh. Ai kuwa ta kira Maman ta fada mata zasu gaisa da Hajiyar Nahar. Cikin nutsuwa da rashin nuna akwai wata matsala Mama tace ai sun fita yawo da kanwar Isma'il din. Harda karashewa da godiyar basu Nahar din amana a matsayin yar aiki.
Bata kara wani mintin ba ta mike jikinta yayi sanyi. Amma ko kadan bata nuna musu komai ba. Har kofa Aishan ta raka ta. Tana ficewa kuwa ta rufo kofar hade da ajiyar zuciya. A take ta fara kiran Isma'il din.
Yana dauka ta rushe da kuka. "Ka gani ko? Ka ga abunda ka jawo mana ko? Ni wallaho ba zan zauna a gidan ka ba har sai ka fito min da yarinyata. Yanzu maganar sati nawa a ke? Anya kana tsoron Allah kuwa Isma'il?"
Ihunta kawai ta cigaba da yi bata san ma ya kashe wayar ba don ya fara gajiya da shirmen ta.
****
Kamar da wasa lokaci yana ta tafiya har su Nahar suka cika wata uku da bacewa bat daga garin Kano. Zuwa yanzu Isma'il din ya sanar da Hajiyar gidan marayun wadda ta fashe da kuka tana cewa wannan wacce irin kaddara ce akan Nahar din. Allah kadai yasan wani hali take ciki. Karshe dai ta hakura ta cigaba da taya su addua kuma ta rufe case din domin ta yarda da iyalin Isma'il din.
Nahar kuwa wadda take amsa sunan Maryam zuwa yanzu tayi wani haske da kumatu alamar hutu. Har zuwa wannan lokacin bata fara fita daga gidan ba. lesson teacher aka samo mata yana koyar da ita, da yake tana son karatun sosai take fahimta. Turanci ma ya zauna a bakinta ba kadan ba because kowa da shi yake mata magana.
Idan Alfa Mubarak wato malamin ta yazo shima ya kanyi kokarin koyar da jta larabcin wanda idan yana yi babu abunda take iyawa sai amsa eh ko a'a.
Tsaye suke da Chef Shola suna girki Nahar din tana taya ta Amir ya shigo. Nahar na ganin shi ta tura baki kamar ko yaushe tun ranar da Othman ya mata fada. Fasa kula ta Amir din yayi. Cike da son tunzura Nahar din ya kalli Chef Shola yace,
"Chef in kin gama ina son grilled fish. Kar ki bawa wata olodo tayi min. I want your signature recipe ba jagwalgwalon yara ba." Daga gefen idonsa yake hango yadda Nahar din ta ajiye wukar hannunta sannan ta shiga yarfa hannu cike shagwaba kamar zata yi kuka.
Chef Shola da ta riga ta fahimci da Nahar din yake tuni ta fara rike dariyarta inda Nahar din ta fice hawaye taf a idonta su kuma suka fashe da dariya.
"Don't mind me Shola." Da ga nan ya fita yana daga kafadarsa alamun he doesn't care.
Tafiya kawai Nahar din take yi, tears blinding her view har ta buge da mutum. Nan take hawayen suka zubo sannan ta zuba idanun ta akan Othman wanda ya daure fuskar nan tam.
Rabon da taga wani sincere smile from him tun ranar da ya mata fada. Ba shiri ta sadda kanta kasa tana kokarin maida hawayen saboda ta san baya so yanzu sai ya fara fada akan kukan da take. Kamar wadda take badawa idon barkono haka hawayen yaki tsayawa.
"Now out of my sight!" Ya fadi, da dan karfi. Ba shiri ta matsa da sauri. Tana zuwa daidai kofar dakin ta sai ga Amir nan tsaye a wajen. Wata harara ta mishi tana neman hanuar wucewa.
Hannu yasa ya dauko tissue a aljihun sa ya bata. "Haba besty, why the tears?"
Kin karba tayi har lokacin a qule take dashi.
"I'm sorry." Ya fadi yana murmushi, sannan ita kuma ta kalle shi sai ya gyada mata kai alamun he truly mean it. Da murmushi kadan a fuskarta ta karba.
"Friends again?" Ya tambaya. Ba tare da tayi wani tunani ba ta gyada mishi kai.
Shigewa dakin tayi shi kuma ya matsa ya bar wajen while Othman dake tsaye yana kallon su ya girgiza kan sa yana qwafa... shi fa bai gane meye a tsakanin wannan yaran ba! Koma meye shi baya so, bai kwanta mishi ba. It's just a no from him. Just no! Babu wani friendship da yake so Nahar din tayi da kowa a gidan.
In that case, yasan yadda zai bullowa lamarin. Tsaki yayi saboda ran shi da yaji yana baci sannan ya nufi nashi side din yana ta saqe saqe a ran shi.
Hajiya Hairah mace ce da bata son shishshigi a lamuran ta saboda haka sai Othman din yaga zai fi dacewa ya nuna mata abunda yake faruwa tsakanin Nahar da Amir din. Ya san zata dauki matakin da ya dace kuma cikin ruwan sanyi. Bata cika son hayaniya ba sannan kuma bata son tashin hankali.
Zaune take kamar ko yaushe da bowl of fruits a gaban ta wanda yake shine silar wani glowing da take ko yaushe. Manyan mata suyi ta tambayar ta meye sirrin kyaun fatarta amma sai dai tayi murmushi kawai tace abun a jininta yake. Kwanaki ma har gani tayi wata blogger tace wai ai tana zuwa tana saka fillers ne a fuskarta, wasu suka ce surgery ake mata, wasu sunce wai glow drip take zuwa ake sa mata. Ko kadan abun bai dame ta ba. Duba da heritage dinta, ta san muhimmancin cin kayan itatuwa a jikin dan adam. These fruits are far better than most cosmetics in dai mutum yana sha yadda ya kamata. Rabon da ta sha lemon roba har ta manta. Just last few weeks ne ma taga wani company da suke son fara natural drinks. Ji take kamar ma taje tayi signing partnership dasu. Bari dai PA dinta ta gama samo mata information akan masu company din.
Olive ta dauka tana kallon sa kamar tana wani tunani. Lallai ba karamin market wannan fruit din zai kawo ba da yake kuma seasonal fruit ne. Ita kadai take ta tunanin ta har Othman ya shigo.
Hannunta yayi kissing sannan ya zauna a kusa da ita. Sai da suka taba hira sannan ya cigaba da magana.
"Amir and Maryam are becoming something else, I'm afraid that love will come in between them. Ko ita Maryam bata da hankali shi Amir ai yana da. Musamman ma da nasan he is single mummy..."
Dan jim tayi sai kuma tayi shrugging. "In ma ya so ta a banza. Na riga nayi mata tanadin yadda rayuwarta zata tafi. Na riga na tsara komai..." ta fadi a hankalo tana mikewa. Tunda ta tashi dinnan ya san abun ya girmama.
"Tun ranar da na dora idona akan ta na gama tsara mata rayuwarta Othman. Kar ka yi tunanin cewa na bar ka ka dauke ta haka ne kawai. Ina da manufa wadda zata kare mu dani da ita... kar ka wani damu, ko sun so juna ba ruwana, zasu wahalar da zukatan su ne. Ba kuma zan dakatar dasu ba saboda hakan zai disa ayar tambaya. Let them live Zinnurain. Na ish marratan wahidah..."
Shocked is an understatement of what he felt a daidai lokacin da ta idar da maganar ta sannan ta zauna. Kan shi a kasa ya mike. Dole ya samo me mummy take kullawa. Zai kira sis Umaimah ta fesa mishi. What if taki? Tsaki yayi for the umpteenth time a ranar sannan ta bar parlorn.
Alarm dinsa ne ya kada alamun yana da appointment a asibiti. A dole ya shiga sharp shower ya fito ya tafi asibitin.
AeshaKabir
Rufaidah Yusuf
****
Readers, me kuke ganin zai faru? Me Hajiya Hairah take tsarawa?
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top