The visitor

A kullum da tunanin bawan Allah da ban ko san sunan sa ba nake kwana nake tashi, dana rufe ido na shi nake gani ko waya nake da Adnan dashi nake imagining ina waya. Duk yanda naso yakishe daga cikin raina na kasa. Addu'a na kullum Allah ya Kara nuna min shi ko sau daya ne, waya da Adnan ya fara fita min a rai idan ya kira ni yanzu ji nake kamar na kurma ihu.

Wata ranar Laraba abu biyu suka faru na farko maganar da Adnan yayi na cewa zai turo magabatan sa next week na biyu kuma bakon da mukayi.
Ina kwance bayan mun gama waya da Adnan sai ga ya kabeer ya shigo kasancewar Waheeda taje kitso sumayya kuma na skl umma kuma dama principal ce a wata government skl dake bayan layin mu mama kuma na bacci hakan yasa ni kadai ce na rage a parlo gaba daya tunanin duniya ya dameni maganar ya Auwal ce ta dawo dani daga duniyar tunanin dana fada, "ki hado abinci da ruwa ki kawo parlorn waje ina da bako" daga haka ya fice sanin halinsa ne ya saka ni tashi cike da sanyin jiki na shiga kicin na hado komai na fito na koma daki na dauki veil dina na fice.

Knocking nayi kafin a bani izinin shiga murya a sanyaye na daga labulen na shiga kaina a kasa dan bana son brothers dina su saka ni kawowa friends dinsu abinci abun na mugun bani takaici , dagowar da zanyi idona suka fada caraf cikin nasa wani muguwar bugawa kirjina yayi na tabbatar da za'a gwada jini na maybe ya hau sosae kamar yanda nake kallon sa da mamaki nima ni yake kallo with so much surprise on his face dakyar na tankwashi zuciya ta cike da basarwa ina ajiye tray din da ke hannu na a center table murya ciki ciki na gaida shi ba tare da tunanin ma zaiji ba amma a mamaki na sai jin nayi ya amsa "Lpy kanwar mu ya gda" a takaice nace "Lpy" ina kokarin ficewa daga parlorn.

Da sauri na karasa kasan bishiyar dake nesa da parlorn kadan na zube gurin zaune ina sauke gauron numfashi ban san iya tsayin lokacin dana dauka a gurin ba taba nin da waheeda tayi ne yasa na dago kaina ina zuba mata rinannun idanuna da suka dan canza kala.
  "Allah dai yasa Lpy" murmushi na kirkira ina kokarin Kara gyara yanayina nace mata lpy ba dan ta yarda ba ta kama hannu na muka koma cikin gida.

Bazan iya fada maku a wane irin yanayi na kasance ba a yan kwanakin da suka shude kaina ya kulle damuwa ta fara bayyana a fuskata damuwar da bani da amsar bawa mutanen gidan meke damuna fara'a ta ta ragu na rage ko zaman parlor idan ana hira meke damuna?

Wannan tambayar itace abunda ni kaina bani da amsarta ban san meke min dadi ba ban san meke damuna ba,ko waheeda da bana iya boyewa komai yau na kasa fada mata damuwata dan ban san wace amsa zan bata ba toh ince mata me? Mutumin da har yau ban san sunan sa ba nake tunani safiya zuwa dare kome? Wannan maganar hankali ma bazai dauka ba at first tayi tunanin ko problem muka samu da Adnan shi yasa tayi deciding kiransa taji  sai dai ya shaida mata ba komai ya kuma Kara da korafin sa akan na rage kula shi sosae hakuri ta basa akan hakan kafin suka yi sallama.

Admission ya fito alhmdulillah a nan Dan fodio ne muka samu ni da Ruqayyah sai dai kowa da Course din da zaiyi ita pharmacy ni kuma pure and applied chemistry sai dai bashi naso ba amma duk da haka nayi farin ciki sosae. Murna a gurin yan gidan mu kam sai wanda ya gani kowa ya mana addu'a da fatan alkairi a bangaren Adnan ma ba kadan ya nuna farin cikin sa ba sai gashi da dare duk da yanda nake ji haka na daure na shirya na fita sosae kuwa na sake kamar ba ni ba dan Adnan gwanine gurin barkwanci ba jimawasai ga waheeda daya kira sosae muka sha fira da zai tafi kuma ya ciro wata box fara mai kyau ya miki min waheeda kuma dama yasan ita chocolate ne nata dan haka su ya kwaso mata bayan mun masa godiya ya tafi. Sosae zoben azurfan yamin kyau ba kadan ba kuma dai dai yatsana.

Bayan kwana biyu baba yace mu shirya muje Rano wannan labarin yama kowa dadi haka muka shirya kuwa sai Rano. Sosae kuwa wannan karon zuwan Rano  yamin dadi dan munyi yawo sosae munje gidajen yan uwa sosae kwanan mu biyu baba yace mu koma saboda skl da kuma aikin sa sai aka bar mama da sumayya.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top