The Beginning of Beginning
Ta ina zan fara baku labari na.
Haduwa ta da Muhammad Ko kuma rayuwar auren da nayi a gidan sa ko haduwata da Mahmoud? Ko ina fara daga asalina ni kaina.
Sunana Nadeeya Ahmad Alaki,ni yar asalin Rano ce sai dai zama ya mai da baba na sokoto inda acan aka haifa gaba daya yan gidan mu. Matan babana biyu Mamana itace babba ma'ana uwar gida sai step mom din mu mama Hamida wacca ta kasance cousin sister din baban mu ce .
Nice ta 7 a gurin maman mu a gidan gaba daya kuma nice ta 11. Yaran baban mu gaba daya mu 16 ne maman mu nada 8 aunty Fateema itace babba sai aunty Habiba, yah Auwal, aunty fareeda, Yahya, Rufa'i sai ni sai auta Asma'u.
Mama Hamida ma na da 8 aunty Badiyya , ya shafi'i, yah Hafsa, Yah Amina, Waheeda ,sumayya sai auta gaba daya mustapha muna Kiran shi Ameer.
Tabbas gidan mu gidan yawa ne kamar yanda family din mu suke a jeren zuri'a mai yawa a Rano, mun taso cikin son junan mu da qauna gidan mu bamu san wani yan ubanci ba kamar yanda muka tashi muka ga ana zaman lpy da mutunta juna tsakanin iyayen mu toh muma haka muka tashi.
Nayi makaranta tunda nursery har secondary a sokoto sallah ko biki ko idan wani abu ya faru ne kawai ke kaimu Rano amma gaba daya rayuwar mu anan sokoto mukayi.
Banda qawar data wuce min yar uwataWaheeda duk da ta girme ni da watanni 7 sai dai kasan cewar ta mai karamin jiki kuma bata da tsaho, tun muna yara komai iri daya ake siya mana kuma komai tare muke yin sa, idan wani abu ya faru tare muke yinsa kuma mu binne abun mu ba mai ji. Tun muna secondary skl nice mai tarin samari ko a group din mu, da brothers din friends dina biyu nayi dating wanda har haka ya janyo fada a tsakinin mu da su gaba daya. Kowa dai yasan secondary school students basa jin magana especially yan boarding dan haka da yar karamar wayar da yayan Tula mai suna Adnan ya bani (a friend of mine) ranar visiting muke shan soyayyar mu, toh tun daga wannan lokaci da wayar muke waya Wanda har hakan ya fara affecting karatu na duk da kuwa Waheeda na dan tsawatar min da kuma nuna min kuskuren da nake kokarin fara aikatawa. A haka dai muka cigaba da wayar mu kullum cikin soyayya har takai da muka yi wa juna alqawarin aure. Lols could you imagine.
I was 17 years ko da mukayi graduating and alhmdulillah mun fito da sakamako mai kyau sai dai na Ruqayyah yafi nawa kyau sosae hakan bai dame ni ba dan nasan dai zan cigaba da karatu na tunda nayi passing jamb and Ina da good 8 credits so why should I disturb myself. Soyayyar mu da Adnan kam sai abunda ya cigaba dan wata fitinanniyar soyayya muke har takai na furta masa yaushe zai turo gidan mu. A take ya yanke wayar dana kuma kira kuma baiyi picking ba hakan yasa na damu sosae har na fara tunanin toh ko na gaya masa wani abu ne da bai masa dadi ba, har dare dae Adnan bai kuma kirana ba sai washe gari sosae naji dadi kuwa bayan nayi picking yake gaya min ai jiya Abban sa ne ya kirasa shi yasa yayi hanging call din, sosae na yarda da hakan sai muka cigaba da soyayyar mu.
*Haduwata da Muhammad*
Bazan taba manta wannan ranar ba a rayuwata Saturday evening 12/04/2016 wannan itace ranar data zama mafarin komai, itace ranar data zama ranar da ko a cikin kabarina bana tunanin zan manta ta ranar dana fara haduwa da uban yata Yasmeen abun soyuwa a gareni itace ranar data zama silar farin cikina da kuma bakin cikina. Tabbas wannan ranar kamar karfen kafa take a gurina.
A dai dai titin arkilla, mun fito daga gurin karbar dinki ni da Ruqayya muna tafe muna ta zabga uban sauri dan yamma tayi sosae gashi na tabbatar duk inda baba yake yana hanya dama gashi sai da umma tace kar mu fita muka ce aa ba jimawa zamuyi ba, ga uban holdup daya taru saboda mutane dake dawowa daga office da kuma yan kasuwa masu zuwa gida hakan yasa titin ya Kara zama hartsine. A dai dai kwanar da zamu shiga a dai dai nan idona suka fada cikin nasa. Sanye yake da riga da wando half jampha coffee fuskarsa Sanye da siririn farin glass Wanda ya Kara masa kyau. Fari ne cikakken namiji mai tsawo. Wata irin faduwar gaba ce ta ziyarce ni a dai dai wannan lokaci hakan yasa nayi saurin dauke kaina, sae dae I couldn't control myself bayan mun wuce sae da na Kara zura kaina naga shima adaidaitar yake kallo a bazata naga ya dago min hannu da sauri na mai da kaina ina dafe kirjina dake bugawa da sauri. Waheeda da bata san abunda ke faruwa ba na kalla naga idonta na kan wayar ta hakan yasa na lafe jikin kujera tare da lumshe idona ina ambaton sunan Allah dan sosae jikina yayi sanyi kalau ga wani irin tsitstsin kewa da zuciya ta keyi.
A sanyaye na fito daga adaidaitar bayan yayi parking a bakin gate, gaba daya mood dina ya chanza Waheeda ma data tambayi meke damuna nace mata ba komai sai kawai ta tabe baki ta shige ciki abunta. Abunda ya yadan saka naji dadi baba bai dawo ba da alama ya tsaya wani gurine. Koda muka shiga mutanen gidan sun shiga sallah hakan yasa mu ma muka fara shirin gabatar da ita.
A gidan mu gaba daya matan sunyi aure sai ni Waheeda sumayya da Asma'u kawai muka rage sai dai Asma'un ta koma gidan aunty Fareeda saboda cikin ta daya zube hakan yasa dakin mu ya zama mu uku kawai. Bayan munyi sallah aka fara gwada dinkin da muka karbo nan take mama ta fara fada wai dinkin ya matse dama ita umma mace ce mai sanyi hakan yasa murmushi kawai tayi bata ce komai ba duk wannan abun da ake jikina a sanyaye yake daga karshe dai na tashi na shige daki. Missed calls din Adnan na tarar har uku ba bata lokaci na kirasa, murya a sanyaye muka gaisa ya tambaye ni meke damuna nace mishi ba komai yace "ok zuwa anjima zamuyi waya" daga haka na ajiye wayar tare sulalewa na kwanta a gurin kamar wacca ruwa yaci.........
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top