Chapter 37
MUZUBA MUGANI🖊
37
Bayan fitar bazla da kyar nayla ta iya karasawa dakin sa hannunta rikevda goshin ta da ya fashe,daga ganinsa daga wanka ya fito sabida only sweat ke jikinsa, sai da ta tabbatar bazla tayi nisa, kuka ta rusa masa hannunta rike da forehead dinta,
Tareda fake concern ya karaso da saurinsa hannunta ya cire tare da ganin ciwon tho ba deep wound bane,
First aid box ya dauko yayi Mata dressing gurin inda Ita kuman sai wani narke masa take tana kuka, saida ya gama dressing gurin sannan ya tambayeta, who did this to you?
Kaman jira take ta wani narke jikin sa tace "honey bazla ne fa, kawai dan naganta da trolley zata fita nace Mata bazata tafi ba I will put a word a gurinka so Ka yafe Mata because ni I already did, shine fa ta buga mun flower base tana cewa wai ni da kai karshen mu ba zai taba kyau ba dan haka zata tafi gurin saurayin tan nan da kataba kamasu tare, har dace mun karuwa honey, wani kuka Ta kara rushe wa da shi,
Gaban sa ne yafadi jin tace bazla ta tafi harda kayanta he wanted taking her home da Kansa amma ta tafi, tsoransa daya kar ta shiga wani banzan Hannu , jin nayla na cigaba da raira kukan yasa wata dariya ta kusa kwace masa, amma haka ya Shanye yana mai rarrashinta yace" kar ki damu taje duk inda zata je late her be!
sharp sharp yayi shirye shiryensa ya fita a gidan, tunanin Wanda zai kira ma yake dan yasan there is no way on earth da bazla zata daga wayan sa and he's very sure gida ta tafi amma tunanin Wanda zai kira yake dan ya tabbatar ta Isa lapia,
Yana kokarin dialing din numbern Amrah kiran mom yashigo masa, gabansa ne yasan fadi kafun ya dauka, Cike da ladabi yace mom Ina wuni, jin yarda ta amsa gaisuwan cheerfully yasaka yayi ajiyan zuciya
"
Matan ka naga kasako a motan haya tun daga kaduna ga ciki kasan tana dashi, fisabilillahi Ai kowane irin aikine kabari ni nazatama wani Abu ya haɗoku,"
Jin mai mom tace baƙaramun kwanciya hankalinsa yayi ba kenan bazla bata fada mai ya haɗasu ba, dan yasan da ta faɗa yanzu sai yaji Kaman ya buga wayan sa sabida faɗan mom, like he Donna ya akai dan tun kwanakin nan take faman tambayansa bazla, lokacin da ya faɗa mata akwai ciki kam Kamar ta zukosu ta wayan haka ta nuna murnan ta,,
Cike da ladabi yace mom Nima Naso hakan amma da ta nuna hakan ba damuwa zata bi transport, nayi nayi da ita amma ta nuna aa shiyasa kawai na hakura na barta ta zo din amma zanzo ba next week Zaa Kawo kudin Amrah ba I will be there insha Allah "
Haka yayi ta tsara ma mom zance da saida yaga ta sauko sannan sukayi sallama,
Wani ajiyan zuciya yayi da ya kashe wayan ya dora Kansa bisa steering, wayansa ne yayi ringing , numbern abokinsa wani police da ya saka yayi masa bincike kan muhseen ya gani!
Bayan sun gaisa ne yake faɗa masa cewa sun gano wasu cases din muhseen na murder da yayi shekara wajen 10 and anyi closing din case din gaba daya, sannan sun gano babban hide drug lord ne,
Wani ajiyan zuciya haysam yayi yace okay ku cigaba da bincike kawai kubarni updated ko menene ya faru call me!
Yau sati guda kenan da zuwan bazla kano, amma ba abunda take tsinta a garin sai so kauna da kulawa da mom inna da daddy suke nuna mata, karma ace mom sosai take tarairayarta idan anyi magana tace Arabu da ita jikanta na fari daga gun haysam da bazla ace bazatayi rawar kafa akai ba.
Kamar kullum abun da ta saba, kwance take kan 3 seater tana karanta *, pain and prejudice"
Ta dukufa gaba daya kan karatun littafin taji an fisge novel din, Jamal ta gani sai daga novel din Sama yake Yana mata dariya tareda cewa yaya bazla catch me if you can, da Saurin ta tamike tana binsa da gudu whilst shi kuma ya nufa compound da gudu litaffin na hannunsa Yana mata dariya,
Cikeda masifa wadda ta zama sabuwar dabiaar ta tace "wallahi Allah jam jam idan na riƙeka sai kayi bayani,
Basketball little field ɗinsu ya nufa da gudu da tayi missing sight dinsa, gware taji tayi da hard chest din da she's very familiar to, then same familiar cologne din da tayi sati rabunta da jin irinsa, and what hurts shine she's missing all ,komai da komai,
Gudun mene kike yi hakan , after kinsan you ain't the only one baby doll? , "muryan da ta ke masifan san ji ya Daki dodon kunnenta, da sauri ta Janye ta matsa tana masa wani kallo, gani tayi Kaman satin da tayi bata saka shi a ido ba yayi kaman wata, dan wani kyau Taga ya Kara mata ga haskensa da yasake bayyana, hannunsa guda cikin aljihun white jean dinsa,
Wani tsadaddane murmushi dauke a fuskanta Wanda ita yake bawa, idanunta taji suna neman cika da ruwa tunawa da mutumin dake gabanta shine Wanda soyayyarsa tama zuciyanta da duka gangan jikinta yawa, same time kuma shine Wanda tafijin haushi fiye da kowa a duniyan nan, kalaman da yafarfada mata a daren ranan su suka soma dawo mata daya bayan daya a cikin kanta, da sauri ta juya dan barin gurin!
Hard hannunsa taji yasaka tareda azaman kamota, kallon hannunsa tayi kan arm dinta, oh God I miss his touch ta ayyana a ranta, amma lokaci daya ta cire duk wannan desire din ta saka hanunta ta bige nasa, giran Sama da na kasa ta hade tace "don't you ever use those hands on me, and who are you to tell me what to do huh?
Murmushi yayi mai tsada yace baby doll just week amma kin chanza haka like nifa kike tambaya wane ni, well your lovely husband and lokaci daya kuma babydaddy Dinki '
Wani hawayen takaici taji zai zubo mata amma tayi kokarin mayar dashi dan tagama yarda yaga weak spot dinta, bata rai tayi tace my babydaddy? Ya haysam stop deceiving yourself kamanta ne Ai babyn Ka dayake jikina na zubar dashi tuntuni, kar Ka manta Ai kai shaidane da idonka kagani, so idan mafarki kake Ka farka!
Sannan I beg you kadaina shiga harkana please Abu guda daya da zai shiga tsakani na da kai shine karubutan divorce tunda Allah ya kawoka kafun katafi sai Ka bayar a aje mun dan bana shaawan sake saka fuskan Ka ma a idona because the only thing that's succeeding to offend me is your face!
Batare da ta Kara jin wani magana daga garesa ba ta bar gurin!
Sukoko yasaki baki dan baiyi tunanin cewa shawo kan bazla zai masa wahala haka ba, bell ne yayi ringing a Kansa da yatuna a cikin magananta tace ita ba cikinsa a jikinta, a hankali yace " shit God help me 'kar dai zuciya yasa bazla ta zubar masa da cikinsa,, da sauri ya rufa mata baya amma kafun ya cimata muryan mom ya taresa"
Aa mutan kaduna saukan yaushe "
Cije hakoransa yayi tareda dunkulle hannayensa, juyowa yayi yana mai placing best smile dinsa da yakeda yace "Wlh mom yanzu nan fa shigowana kenan,
Tsugunnawa yayi har kasa tareda gaishe ta, Kana suka shiga cikin sashen ta,zama tayi yayin da shima ya zauna a kujeran da ke kusa da inda ta zauna,
Gwanda da kazo da wuri kam dan around 8 iyayen muhiddeen zasujo so!
dan yake yayi yace mom to shi aikin mene yakeyi, "he's a doctor ta basa amsa a takaice tana sipping fresh mango juice dinta, then kuma tace Ai Ina ma zakasan shi yaron Alhaji umaru ne abokin dad dinku, yaron akwai nutsuwa da hankali I think shekaransu na biyu kenan da Amrah bansan abun zai serious hakan ba shiyasa I didn't bother to tell you "
Oh yace naganesa maibin faisal Ai faisal din abokina ne sosai remember Ai Ina tuna lokacin da deen din yaje China God las las Ashe baby sis dina zai zo ya kwace!
Dariya suka saka baki daya then mom tace ehen Ai haka abun yake ina cewa kaima shalelen inna Ka dauke mana baki daya yaushe rabon da tazo Gidan nan ai ta jima inba da Allah yasa da cikin nan ya bayyana ba dan ma ba mai girman cike bace Ai da tuni ko little bump ne ya fara appearing,!
Wani Dadi ne ya ziyarcesa Wanda bai masan daga Ina yake ba, jin dahir din cikinsa Yana nan lapia lau dan sosa keya yayi shi a dole kunya,
Aje cup din mom tayi tace ita kuma waccan shekara nawa sai afkin ci da kashi amma ba ɗa ba ɗan Ɗaki,
Shi dai bai ce komai ba tho shima da fari abun yafara damunsa amma ganin bazla da ciki not the matter of being selfish amma sai yaji abun ya rage damun sa!
Karfe sha biyu na ranan ko azahar basu tsaya yi gida ba bazla da Amrah da inna suka dauka hanyan kademi shima sai da sukayi ta Rokan inna Kana ta yarda zataje suyi ko da sati ne, Jamal uban kan kamba Kuwa cewa yayi ba zaije ba, haysam Wanda baisan da tafiyan ba Kuwa ya fita a Gidan bayan gaisawa da inna dan basuyi wani dogon hira bama yafita kan sai ya dawo,
Hour biyu ya kaisu kademi, mamaki bazla take ganin yarda gidansu yakoma dan ba daban nan tayi rayuwanta mai yawaba sai tace ba shi bane, Koda suka shiga Gidan ma komai anyi modernizing dinsa amma basake yarda Gidan yake ba akai amma ansaka furnitures and All luxury da zai shiga,
Bayan sun gama zagaye Gidan ita da Amrah ne suka nufa gun inna wadda tasa driver yashiga da kayayyakin and it seems ita bata yi wani mamaki ba dan ba yau ne ranar da tafara zuwa Gidan ba,
Hannun inna bazla ta rike tace inna amma wannan ba Gidan mu bane ba ko?
Dariya inna tayi tace jaira shine mana maigidanki ne ya maida shi haka a da wai zaasake zanen Gidan na kiya, dan nan Gidan na tarihine cikinsa nayi rayuwa da baffanki da kuma mahaifanki!
Shiru bazla tayi batareda ta kuma cewa komai ba tunda aka sako haysam a zancen! Bayan sun huta sunyi sallah, sannan kowa yanema abinci Wanda dama already sunyi guzirin dafafe da kuma Danye wanda zasuyi amfani dashi!
Koda dare yayi kwance suke da bazla da Amrah kan gadon dake cikin tsohon dakinta Wanda haysam ya mayardashi kaman ba kyauye ba, dan 24 /7solar yasa musu cikin Gidan!
Kallon Amrah bazla tayi tace aikin banzan ace mutum yayi hour Yana waya kaman ku kuka Kawo soyayya duniya, mayar da kanta tayi gurin cigaba da karanta pain and prejudice dinta da saida suka sha drama da Jamal kafun yabata "tunda bata da wani abunyi karatun kadai ke debe mata kewa, maryama tamata introducing novel din "a call to arms for women and their body! (The book is brilliant, blood drenched, page Turner, every girl, woman and man and most particularly every doctor should read it" by Gabriel Jackson)!
Duka taji amrah tadan Dallah mata tace naji tunda k3 da yaya kunga kaman kun tsufa sai kubar mu yara muyi, tsaki bazla tayi tace finally angama Ashe, gwara muyi muyi mutattara ki mu mikamasa" taƙara sa zance tareda mikewa ta shige bathroom gudun kar Amrah ta zurfafa da zancen haysam!
Sosai amrah ta fahimci akwai wani Abu Wanda ko ba dade sai ta tonusa amma for now zatabar abun ya wuce, dan tasani abun fa Kamar wuya ace bazla ta bar karatunta sabida tazo gida goyan ciki!
Washe gari bayan an karba kudin neman auren amrah 100k tareda saka ranan auren wata uku, inna ke fada musu bayan tayi waya da dad!
Siyasiya inna tace zasuje washe gari so bazla tayi deciding ta zagaya da Amrah taga gari, Gidan mai Gari suka fara zuwa, mamaki matan maigari suka ringa yi da sukaga bazla harda mai cewa wai yar innace tayi wannan kilin din jikinta har wani sulbi sulbi yake kaman wata kifanya Allah mai iko,
Dariya suka saka baki daya, sosai bazla ta musu kyauta ciki harda mai gari dan iya zamanta garin tasani mai gari ba karamun cover yake mata ba, bayan hakama ita abunta baya rufe mata ido shiyasa indai tayi Arba da idon Sani saitamasa alkhairi, bayan tafito daga Gidan khadijan kawarta ta primary wadda ta aura yaron mai gari sule, sosai tayi murnan ganin bazla inda sukayi hirar yaushe rabo, yaranta uku da sule,Sosai tamasu alkhairi,
Kicibis taci karo da dan tani Wanda ya manyanta ga kuma rayuwa irinta zaman kyauye, har ya wuce kuma ya dawo da baya yace kai kai kai wanake gani mai Kama da yar inna, dan murmushi tayi ta sunkuyar da kai dan wata kunyarsa ta zo mata musamman da ta tuna bushashar da suka tafka,
"Itace dan tani Ina wuni, wage baki yayi yace lapia lau alhamdulilah, ya burni, kai Ashe rai kan ga rai, jiyan nan muke tuna bayanki da su danlami da Audi ashee kina hanya aikamn dan Allah kizo muje ku gaisa da tine,
Amrah dai zuko zuko take binsu tareda jinjina ma bazla dan duk inda sukaje sai anyi tuna baya wanda yasa taci dariya ta gode ma Allah!
Yo do y'all know I suddenly came across writer block hahaha😂Goddamn that shit , but shuuu I'm back and yoooooooo few more chappy's to goooooooooo
I'm missing the book already❤
Xochuchujay❤
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top