Chapter 36

MUZUBA MUGANI🖊
36
Washe gari tunda asuba tayi wanka dama already ta hada kayanta tun daren jiya, Ashe idan ta tsaya jiran ya haysam ya kaita gida bata haifu bane ma, dan bakaramun cin fuskane da wulakaci ba wato yaje yace tayi laipin neman matan sa tareda kokarin zubar masa da ciki shine ya kawota gida kome?
Gari na fara haske ta sauka da trolley dinta luckily bataga kowa ba Kuwa, tana fara tafiya dan nufan hanyan fita taji anjanyo ta, ido biyu tayi da nayla wadda tana ganinta ta fashe da dariya, inta nunata sai ta nuna trolley din, juyawa bazla tayi dan barinta gurin dan tasan Idan ta tsaya to tabbas kashinta zai shafi nayla, dan cikin wani irin bakin ciki mai tiriri take, muryan nayla ne ya Daki kunnenta Inda take cewa "baki san tuguna ba bazla, da ace kina da  wayau lokacin da na Kawo miki bukata ta da bakiyi Watsi da Ita ba kinga Baki alaikum ba maiji ba mai gani amma yarinyan nan sabida Taurin kai kikayi burus da abun yanzu ga irinta nan Ai kina Ji kina gani zaki bar gidan abun kaunar taki, kuma abin bakin cikin da Jan fenti jikinki dan kallan yar iska, watsatsiya yake miki, takarasa zance da dariya!

Bin parlor din bazla ke yi da kallo aikuwa idonta yasauka Kan flower base dake ka center table, batayi wata wata ba ta rarumesa tare da makama nayla a goshi, lokaci daya nayla ta saki wata Kara,
Nuna ta da yatsa bazla tayi tace, kina Tunanin wai kinci nasara ne dan wannan dan Ka rarramin tuggun naki, to ni Wallahi da kika ganni nan ba irin abunda ban iyaba Ina tunawa da Zaa mutu ne, sannan ki rubata ki aje mugu baya taba lasting, kuma in kina ganin karyane muzuba mugani, karya low budget hoe, da haka tafice a gidan tareda barin nayla na bleeding!

Bata zarce KO Ina ba sai tasha, Wanda tareda ita aka bude, motan da ta shiga su suka fara tashi sai kano, karfe 10 suka shiga kano, napep ta shiga ya kaita gida koda ta shiga mommy tagani a parlor tayi baki, ji tayi Kaman ta wuce kawai musamman da Taga idanun ƙawayen mom guda biyu a kanta, amma tunawa da tayi ita ta Haifa Mata haysam duk da abunda take ji aranta gama dashi amma taji bazata iya wucewa batareda girmama mahaifiyarsa ba!
Sallama ta musu, da faraaar da bazla bata san mom na da ita ba ta amsa tareda tasowa gareta, dan yake bazla tayi tana mai cewa mom Ina ƙwana, kokarin tsugunnawa take amma mom ta riketa da faraaar ta tace " haba aa don't stress yourself da abunda ke cikin ki I'm okay, kunsha hanya Ina haysam din ta karasa magan nan tana dan lekawa alamun tsammaninsa take,!

Dan murmushin da bai kai zucia ba bazla tayi dan duk sabon abun ya zamar Mata abunda bata Sabah gani ba amma jin tayi maganan ciki Takara tabbatar Mata cewa da biyu take Mata new mutuncin sabida taji tana da ciki, a ranta tace "wonders ",

Batare muke ba mom",
Dan hade gira mom tayi da confusion tace Kamar Yaya ke dawa kuka Zo kenan,
Ni kadai bazla ta bata amsa cike da kosawa dan bata san wannan new drama din tafi gane ta kyaleta ta Je gun innarta,
Jan hannunta mom tayi tace shigo mushiga daga ciki da murnar ta tayi maganan Kaman ta maida ta ciki, gaisar da bakin mom tayi Inda suka amsa Mata da faraaar su!

Amrah ce ta sauko daga part din mom Kaman ance ta dago idanta Kuwa ta sauke su Kan bazla, da gudu ta karaso tareda rungumeta tightly, duka mom ta kaimata tace kaji mun sakarar wofi sai kin karyatane bakiga tasha hanya bane,
Dariya Amrah tayi tace mom bazaki gane ba ne I fucking missed her, duka mom ta kaima bakinta tace Ina ce I warn you bana san F word a cikin gidan nan,
Rike bakin Amrah tayi tace ooops,
Dan dariya bazla tayi dan gaba daya she's not comfortable da sabon al amarin,

Trolley dinta Amrah ta karba tare da yin part din inna, dan kallon mom bazla tayi tace, mom bari nakarasa ciki,
Oh sure cewan mom im too excited to see you ne na Rike ki duka we will talk anjima then, bara na sallama bakina then Nazo na gana da unborn grand dina, kar inna tace na Rike Mata yar inna,

Dan dariya tayi Wanda a iya wuya yake dan mamakin Kara yawa yake Mata, haka ta nufa part din inna  tana juya lamarin!

Fadawa Kan inna tayi cike da murnan ta!
Ya illahi bazla kar Ki karasani nikam cewan inna, dan janyeta tayi sai kuma Taga haawaye a idonta, dago fuskanta inna tayi tace to lapia mey kuma na kukan inna shi haysam din,
Wani Abu ne!?
Share hawayen Bazla tayi tace" aa inna kawai nayi kewarki ne sosai, rugume inna tayi inda ita kuma take shafa Mata bayanta a hankali tace Nima nayi kewarki ki yar inna dan ma ke dince wataran bakiji shiyasa da nake fushi dake,

Emm dan gyaran murya Amrah tayi tace inna gafa wata yar innar Anan KO yau dan ta asalin tazo shine kikayi Kaman baki san da tsayuwa ta a gurinba, inace Zata koma gidan mijin ta kyanema dan tayin kwana,

Hannu inna ta miko Mata tace to taho yar nema, dariya suka sa Baki daya, bayan dan wasan su na tsakanin kaka da jikane Amrah ta tashi da saurin ta tace damn sis Ina da lecture 1 and mutumin nan yanzu zai muku test, I have to go yau idan na dawo tareda ke Zan kwana akwai gist '
Pecking dinta tayi a cheeks Kana ta fita, wani kululun hawaye bazla ta Shanye da ta tuna fa tana da makarantar ta da ta baro a gida, tasan yanzu gaba daya komai Nata zai lalace sabida karya biyu kacal daga bakin nayla, amma hakan baisaka tayi Dana sanin gudowa da tayi ba sabida moment din da haysam yayi choosing matarsa akanta ta kudira ta daina yin auren dan haka duk ranar da yashiga kano sai yabata takaddarta inyaso tabar musu gidan su, tunda itama nata uban ba gida ne bayya dashi ba, yanzu KO kademi akace taje ta zauna Zuwa zatayi burinta daya ta Haifa baby dinta lapia ta bashi /bata kulawa!

Tabata da akayi ne yadawo da ita daga Inda taje, lapiyar ki kuwa inata magana hankaliki na wani waje,
Murmushin ta nemo tareda dorama fuskanta tace" inna kawai Ina Tunanin kademi ne da rayuwanmu nacan amma tunda Nazo yanzu Ai zamuje ko?

Kama hannayenta duka biyu inna tayi tace mene ya hadaki da mijinki yar inna, fadamun, kwace hannunta tayi tareda duk wani kokari dazatayi kar hawaye ya zuba tace" kaji inna sai Abu ya hadani dashi zan nema inje asalina, da gaske nake ba komai tsakaninmu hasalima shiyace Nazo nan din wani aikine ya rikesa shiyasa nabiyo motan haya, wai sabida cikin nan kinsan na farko inna Ana zuwa gida Ai!

Kallo inna ta bita dashi Batare da yardar maganar da ta fada din ba amma sai ta bar maganar tunda har tasan ta boye sirrin mijinta dan haka bataga abunda zaisa ta Sata fada dole ba dan haka tasa aranta kan bari ta zuba musu ido Taga karshen gudun ruwansu!
Shikenan sai musa Rana muje kademi din tunda Ai kina nan Har ki haihu!
Inna ta rufe zancen da haka, da murnar ta taringa ma inna godia "

Dan serious face inna tasaka tace kinkuwa je kin gaida hafsatu?
Gyara zama bazla tayi tace ehen dama Kaman jira take tace "inna dama Ina zuci zucin na tambayeki, lapia Kuwa naga da na shigo gidan nan KO karasowa ban ba naga ta tashi da murnarta ta tarbeni, abun wani bambarakwai ni tsoroma ta Bani kar wani tuggun Zata sake hadawa musamman akan cikin nan ni abun wani irin banyarda da ita ba!

Dariya inna tayi tareda bugun bayanta tace yar nema, ke gaba daya rayuwaki bakisan kunyaba, kindage ciki ciki to ni cikina na farko na babanki kenan kunyar asani ma na ringa ji dan akwai lokacin da abokan wasan baffanki suka Sani gaba kanvcikin nan ranar kuka na ringa yima baffanki kan banasan cikin dan abun kunya ne ;

Wata muguwar dariya bazla tasaka harda riƙe ciki, nan koma ta shiga zolayar inna,
Inna ce ta dawo da maganar kan ta mom da suke tace kinga hafsatu to bata da din da kika Sani bace, dan yanzu cikin gidan nan sai kice Ita na Haifa ba Abubakar ba sabida yarda ta dawo ji dani,

Rike baki bazla tayi tace to wata sabuwa, saivkuma tayi dariya tace inna kuma mai ya jawo hakan,
Goro inna ta bantara tace to kwanaki ne bayan wata yar rigima haka nan dai tashiga tsakaninmu kan ke da haysam ne akan itafa saidai Araba auren Wanda Ina tunani ita wai mahaifiyar abokiyar zamanki ta zugota kan lallai sai dai asake ki sabida kin kwace ma yarta miji,
Ni kuma naƙi lamuntan hakan na mata fada mai Kama da nasiha kan lallai itama uwar mijice kuma nan KO ba dade KO ba jima sai matar daya daga cikin yayanta sun dan Dana Mata abunda nake ji, da dai Abu tayi Abu har gida Abubakar ya korata, to nan dai suka Mata nasihohi masu shiga jika, nan Nima na lallaba Abubakar yaje ya Daukota dan shi da cewa yayi yagama zama da ita,
Ni kuma naga darajar ƴaƴa da kuma shekarun da aka debe tare Ai saki bashine mafitaba, to tunda ta dawo din nan ta samu muka daidaita zaman namu kuma na yafe Mata, dama in banda abun yara wake wulakanta uwar miji,
Ni nan da kinka ganni bakicewa ba mahaifiyar baffanki ta haifeni ba!.

Dan shiru bazla tayi bayan inna ta kai aya,
Ajiyar zuciya tayi tace to Allah yasa a daure dama Ai ba maisan rashin zaman lapia, Ina kuwa Sabah naji Amrah rannan tana cewa ta tafi maiduguri bata dawo ba,
Tashi inna tayi tace wannan uwar fitinar rabuda ita kawai Ai gwanda ta je Chan gun dangin babanta din tayi zamanta dan mudin tana cikin gidan nan ba zaman lapia dan kullum kanta shedan ke kida, kije ki huta kiyi sallah Nima ita nakayi lokaci yayi!..

After tayi wanka tayi sallah tana shirin kayanta cikin old closet dinta taji anyi knocking, mamakin Wanda yake knocking dan sabon Abu ne gurinta Indaii cikin Gidan ne, inna tamasan wani knocking kawai tayi sallama in an amsa ta shigo, amrah Kuwa Ina boom munfaso, likewise Jamal thinking of him tafara tunanin Ina yashiga dan bata gansa ba,
Knocking aka kumayi tace yes come in",
Mom ce tashigo like  dont get her wrong bata taba tunanin akwai ranan da Zata shigo dakinta ba "

"KO na komane?muryan mom yavdaki kunnenta da sauri ta Kada kai tace aa mom bismillah, dariya tayi tareda zama kan night stand din dakin, zama bazla tayi bakin gado tace mom Ina wuni, dan tama rasa mai zatace Mata, dan smiling mom tayi irin na manya  tace "mungaisa but I won't mind another, dan yake bazla tayi,
Tasowa mom tayi tareda zama kusa da bazla kan gadon hannunta ta kano tace look bazla nasan this is awkward amma you have to know, I'm sorry duka abunda ya faru from the start, nasan ban miki kirki ba, i treat you like no human amma ban tsaneki ba kawai sharrin shaidan ne, and yanzun nagane kuskurena kiyafeni sai ga hawaye ,

Da sauri bazla ta sauko daga kan bed din tareda rike hannun mom tace mom please banyi worthing hawayenki ba KO kadan and ni ban taaba rikeki ba at least farin cikin da nake Kalla naji dadi daga gareki ne Indan zan kullace kowa bakya ciki And nayafe miki dama tuntuni da abunda kika mun Wanda nasani da Wanda bansani ba na yafe miki,

Taso matso nan cewan mom, tana karasowa mom tayi hugging dinta tareda cewa Allah yamiki Alabarka ya azurtaki da yara masu miki biyayya, Allah jikan mahaifanki,

Talking about ƴaƴa ya kikiji yanzun hope komai Kalau game da cikin, ?
Haka nan taji tanajin kunyar mom, sunkuyarda kanta tayi tace lapia Lau komai!

Kara kallanta mom tayi sosai sannan tace Ina haysam din ne da kika biyo haya ina fatan komai is okay and don't hide me a thing"

Cikeda karesa tace Allah mom ba komai aikine yamasa yawa!



Dull chapter ikr 😫

Xochuchujay

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top