Chapter 19

MUZUBA MUGANI 🚶
19

Zaune yake a airforce base shi da abokin sa sulaiman suna hira a kan earlier work da su kai, wayan sulaman ne yayi ringing so yayi excusing kansa dan amsawa, ganin Shiru shiru bai dawo ba yasa ya dauka wayan sa ya kunna data da niyyan tura abu ga best frnd dinsa sadeeq daya ke Italy dan wani years course,
Messages suka fara shiga masa,but bai bi takansu ba ya nufa na sadeeq, after sun gama maganan da zasuyi and all buddies time ya fita kaman zai kashe data dinsa sai yafasa ganin message daga nayla Wanda yasan rare abune tamasa magana a WhatsApp indai yana gari,
Hotuna yagani guda uku, kaman yaki budewa dan yasan attimes nayla can be stupid, amma sai yaji wani sudden urge na budewa yazo masa so without thinking twice yayi downloading pics din

Wani tashin hankali da Bacin rai ya ziyarcesa ganin bazla jikin wani namiji Wanda bai sani ba, all he knows cewa a makaranta ne sabida tana cikin uniform dinta, and definitely guy din a makarantan yake,
Wani mugun bacin rai yaji ya taso masa jijiyan kansa duk ya tashi, key dinsa ya fusga ya nufan motan sa,
Allah kadai ne ya kaisa gida sabida yarda yake rough driving ,
Horn kawai yake dannawa a bakin gate din ko gama budewa baayi ba ya fige motan yayi ciki,

Bazla, bazla, bazla kwala Mata kira yake tayi batareda kakkautawa ba , bibbiyu yake tsalake stairs din bai tsaya ko ina ba sai dakin bazla yana murada handle din kuwa ya bude luckily bata kulle ba,

Yana shiga tana fitowa daga bathroom da alaman alwala ta dauro, cike da rashin fahimtan baccin ran nasa tace ya haysam lpia,? rufe bakinta yayi daidai da daga Hannu dayayi ya saukesu kan fuskanta,
Wani ihu tasaka tana neman ma buya dan Ga dukkan alamu ba a saitinsa yake ba,
Bathroom tayi niyyan komawa da Sauri yasaka hannunsa ya jawota baya, Hannu ya dora a lips dinsa yamata alamun da tamasa shiru, haysam din datasani a kademi ne ya dawo mata ba shiri ta hadiye kukan ta, wayansa ya ciro ya nemo pics din yace uban wanene wannan?, wato abunda kike yi kenan a school din right,
Karama dake har kinsan warmth din namiji,

Wani masifa ta hango tattare dashi ga kuma wani mugun mamakin ganin hotonta da sir aydee all curled in him, abunda yafara fado mata shine wanene yamata wannan cin mutunchin and shin me ma zata fadama ya haysam ya gamsar da shi,
Wani tsawa daya buga mata shi yadawo da ita daga duniyar thoughts dinta,
Zakifada mun uban wanene wan nan din and uban menene tsakanin ku, how many times yayi touching dinki ko sai nayi kasa kasa dake a gurin nan tukkuna,

Kar kada kai tafara yi dan bata san tayi involving mutum da yayi comforting dinta lokacin da take bukata, kada masa kai tafara tace ya haysam wlh ba abun da kake tunani bane Allah ba ruwansa, wani tukukin bakin ciki ne ya fado masa jin wai kare wani namiji take gabansa namijin ma wanda a ganinsa advantage dinta ya ke dauka,
Baiyi wata wata ba ya cire USB din charger dinta yafara dukan ta dashi, ba abunda ke tashi sai kuka da Ihun bazla tana kururuwar basa hakuri, sai da ya Zane ta ciki da bai sannan sai ga Nayla ta shigo ciki da sarsarfa, tun shigowansa ta ke labe tana sauraransu Dadi kaman ya kasheta yau haysam na suburbudar Bazla dan haka dadi kaman ya kashe ta dan effort dinta bai tashi a banza ba!

Hannunsa tayi Sauri rikewa tace haba honey bai kamata kasamu karamar yarinya kaman wannan kana dukanta hakaba, munsani duka tayi laipi amma ba haka yakamata ayi settling abunba, kasan abunka da yara da suka kai stage din puberty dole sai anasa musu ido, ban tura maka pics dinnan dan kamata haka ba nima dana gansu narasa tunanin mai zanyi shiyasa na tura maka if to say nasan duka zaka mata we could have settled it ni da ita kafun kadawo,

Wani sharp look bazla ta bata jin cewa itace ta tura ma haysam pics dinnan amma abun tambayan dayake mata yawo akai shine wanene ya mata wannan pics din har ya tura ma nayla, mene tsakanin nyla da wanda ya turo wannan pic's, what was that suppose to mean? Kenan nayla stalking dinta take har a school!

"aure take sone kasan yaran zamanin nan are into premarital sex I'm very sure bazla ba virgin bace so why not kawai a katse so called school dinnan shi wannan particular guy din ya aureta, karta jamana abun kunya "maganan nayla ne ya fito da bazla daga deep thoughts din data shiga bata san lokacin datace "uwarkice ba virgin ba shegiya, shedaniya in Allah ya yarda sai kin lalace duk da dukan da haysam ya kai mata bayaji zatayi shiru cikeda tsiwa tace wlh ya haysam yau nagama zaman gidanka,ke kuma nayla wlh sai na zamar miki ciwan kai, wani Mari haysam ya kara bata ganin baza tayi shiru ba yace dan ubanki matata kike Zagi agabana saarkice, ?

Wani kukan munafurci nayla tasa tace honey kajiba makarantan nan ba abunda yake koya mata sai rashin daa da tarbiyyan ni agani na cireta shi yafi ni bama futsarar nake gudu ba kar ta yabo mana cutan zamanin nan.
"Keeee wani tsawa haysam yadaka mata dayasa ta shanye duk wani magana datayi niyya, you're crossing your limit "yafada da wani sauti na daban, Kallonsa ya maida kan bazla yace and ke kuma we are going to the school together goben Naji shi din uban wane, har ya kai bakin kofa ya juyo ya kalli nayla yace ke kuma we need to talk kibiyo ni" bam yayi banging kofan da karfi!

Wani kallo nayla tabi bazla dashi tace kin dauka ke kadai kika iya sharri in atafe kike ni chan na kwana, bugu da gari nidin na Riga ki shan iskan duniya,  so kinga yanzu in duniya yamiki zafi a gidannan sai ki koma na kanin ubanki da ake cin arziki,

Kofa bazla ta nuna mata tace fita dan Allah, nagaji da musayar yawo da mahaukaciya irinki sakara mai warin baki,
Gurinta nayla tanufa a fusace daniyan ta damketa, da sauri bazla ta yunkura duk da tsamin da jinkinta yayi ta dauko love stool tace wlh tallahi kina matsowa nan sai na buga miki shi yayi tartsatsa jikinki,
Ganin glass din da nayla tayi yasaka ta  Dakata tareda cewa wlh namiki alkawarin maganinki a gidan nan shegiya mai kamada aljannu,
Buguzum buguzum tajuya tabar dakin whilst bazla ta fashe da kuka, a lokacin da yake dukanta tagama ayyana ta gudu a gidan, amma da taji cewa komai shirin nayla ne ta kudiri niyyan bazata tafi ba idan har ba gama makaranta tayi ba, bugu da kari bazata taba bama nayla daman cin galaba akanta ba, for sure sai ta gano spy din da nayla tasaka mata a school!
Wata zuciyarce ta raya mata ko sir aydee ne, da sauri kuma ta Kwabi zuciya ta Akan bazai taba going so low dan yayi setting dinta ba!
Da sakesake a ranta Haka tayi warm bath tareda gaggasa jikinta!

Bangaren nayla kuwa kai tsaye dakin haysam ta nufa dan ita gani take kaman ranan take sallah a gurin ta, tsaye tagansa yana facing bango, karasawa tayi cikeda kwarkwasa tayi hugging Dinsa ta baya, kaman jira yake ya fancha kallar da hannun tareda juyowa yana fuskantar ta, cike da bacin rai yace uban wanene yatura miki wayannan pics din and don't you dare lie to me wlh kinsan halina fiyeda kowa,
Wani sarsarfa hannun munafurci tafara tace wlh honey bansan ya akai bafa kawai tura mun naga anyi bansan wanene ba i swear,

Hade rai yasake yi yace bani numbern, gabantane yafadi batasan lokacin da tace I deleted it wlh,
Wani mugun kallo yabita dashi tareda cewa be careful nayla be careful kinsanni bani da kyau, kisan limit dinki, you're my wife whilst bazla is my sister so bakida wani space nashiga irin wannan abun, yau kin wuce inda yakamata kishiga, darajar ke din matata ce shiyasa na daga miki Kafa, I know you best, so know your limit, kina kallo dai yarda kika bari tafara rainaki, how could you be even exchanging words da Bazla kanwanki for God sake,
Hannu yasa ya caressing saman hancinsa yace Banasan haka yakara repeating kansa please,

Wani tukuki da jin haushin bazla taji ya kara taso mata, bude baki tayi da niyyan gardama dashi tace amma honey I was doing all this for her own sake not for selfish interest kasani ba?
Dafe kansa yayi cikeda damuwa yace nayla please da hannunsa ya nuna mata kofa tareda cewa here is the exist please just go I want to be alone,.
Kaman zatayi magana kuma sai ta fasa tafita a dakin tana jadada ma kanta ko yau Kasuwa ta tashi dan koli yaci riba!

Washe gari cikeda rashin walwala da fargaba ta tashi tunaninta daya kar haysam yacima aarif mutunci, a ranta ta kudiri niyyan dole ta sauke duk wani pride dinta ta rokesa,
Half cup tasha na custard shima din dan kar takisha ta taro wani laipin dan tabbas ba dan arif ba yau ya haysam sai yasan yadaketa,
Da fari silent drive ne ke wakana kafun ta katse shirun tareda cewa "ya Haysam dan Allah ba sai kaje makarantan ba ni dan Allah kayi hakuri!nasan nayi laipi im sorry!

Da fari banza yamata sai daga baya yace mata" who was the guy dole sai nayi suing dinsa for taking advantage of wawiyan yarinya irinki!
Wani kukan tabara ta barke dashi tafara cewa ya haysam you get it all wrong fa wannan mutum class master dinmu ne and beside he helps me get away from bullies rannan I was humiliated, kara fashewa da wani kukan tayi tace innnnaaaaaa innata inakewanki nasan da tana kusa zata yarda dani, ni gurinta nakesan zuwa!

Kukan Natane wanda ke rikitamasa lissafi tacigaba dayi, Baisan lokacin da ya gangara gefen titi tareda bugun steering din cikin ransa ya furta innalillahi what's wrong with me and mai yariyan nan ke min ne,
Hannunta yakama yana murzawa a hankali yace okay you tell me about i!

Zanzan tafara narrating masa abunda yafaru duka har wanda tayi hugging arif duk bata boye masaba, Sosai ya nuna bacin rai kan abunda su yasmen suka mata and cikeda fusata yace muje school din dole they will pay for it!
Koda sukaje NTIC kinfita tayi a motan, ya yunkura zai fita takamo hannunsa wanda ita kanta batasan inda tasami karfin gwiwan yin hakan ba,
Juyo wa yayi da Kallonsa gareta yana bata kallon alamun what's wrong, batajira amsaba tasa wani kukan tace Allah ya haysam ba ruwansa sir  aydee taimako na kawai yayi please ya haysam dont make a scene,

Dan kallo yabita da shi dan ji yake kaman yayi taking dinta a very moment din, kiss the hell out her yarda bazata iya kara rokan ma wani ba, saurin kawar da dirty tunaninsa yayi ya cire hannunsa a nata yafita dan hes not sure ko zai iya controlling dinkansa!

Sosai ya nuna ma dean din baccin ransa whilst shikuma yamasa alkawRin abu irin haka ba zai sake tashi ba, daya zo tafiya hankalinsa na wani gu daban sai ji yayi yai gware da wani, da niyyan basa hakuri yadago amma ganin arif ne yasa yafasa, inda shikuma arif na shaidasa yabasa Hannu cikeda faraaa dan yaga pics dinsa dayawa gun bazla, wani kallon  banza haysam yabi hannunsa dashi kana yawuc3 batareda basa hannu ba, kaman ma ba mutum ne gabansaba,
Bazla dake biye dashi a bayane tama arif alamun tana zuwa,

Sosai taji dadi da haysam bai hada wani fitina ba akan arif, har bakin mota Tarakasa wani cold kallo yabata sannan yace be careful and I mean it, I'm warning you for the last time, gada masa kai tayi kaman wata kadangaruwa a ranta tace kaji dashi tunda baka bani kunyaba ai shikenan!

Zanzo daukaki da kaina wait for me "shine last word daya  bata kafun yaja motansa yatafi!

Tsaye ta Tarar da arif yana jiranta, tundaga nesa take sakan masa wani warm murmushi, Good morning sir tafada da faraanta, dan pouting yayi  playfully yace kar mufara, a hankali suka nufa hanyan classes, muryansa ta tsinta yana tambayata ya haysam baya sansaba,
At every mean ta nuna masa mood swings ne tho he wasn't satisfied amma ya nuna mata ya yarda!

After class data fadama sahal da khadie about all incidents din zafi suka dauka Sosai, Alan dole sai sunfito da culprit din, kada kai tayi cikeda rashin gamsuwa tace no lets Focus kan exams dinmu tukunna!!!

Chuchujay xx🔐

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top