Chapter 14
MUZUBA MUGANI👣💕
14
Zaune take a balcony ita kadai sai smiling take ta na ayyana abubuwa aranta, yau ya kasance sauran kwana biu kenan ta tafi Kd, so kasancewar akwai bashikan dabata gama biya ba a gidan shiyasa take so ta biya da gaggawa kafun ta wuce Kd, agogon hannunta ta kalla taga karfe 7:30 nasafe Wanda tasan lokacin shine dai dai lokacin da mai binta bashin zata fita school dan haka tun 6:30 ta tashi tagama shirya komai,.
Karan heels taji sunata dukan tiles din da zai sada ka da compound, Kara makalewa tayi sosai yarda bazata ja attention din mai tahowanba, Sabah ce sai wani yauki take tasaka wata baby blue fitted gown dinta wadda duk wani sura da Allah ya mata tagama showing yarda kasan a jikinta a ka dinka kayan,
Daga nesa idan ka hango ta kana kallan yarda fuskan ne ke ta mulka unban sheki sabida make up din datasha kaman wacce zataje party, dan ƙaramun veil tayi rolling tare da Dora shade a Saman ka,
Gashi ta saka wani uban heels mai shegen tsini duk da tsayin da Allah yabata bazaka taba ganinta ba tare da heels ba ko da aka halicceta ansaka aunty heels a goshinta ne oho cewan bazla!
Kasancewar Sabah macece wadda indai tana tafiya hardly ne Kaga fuskan ta ba Akan wayanta ba, so as usual yanzun ma hankalinta nakan wayarta tana ta dane dane plus smiling kana kallan ta kasan cikin nishadi take amma me suddenly sai nishadin ya dauke sakamakon wani santsi dataji ya kwashe ta yayi Sama Sama da ita, lokaci daya karar faduwar wayarta dakuma karar ihunta sakamakon yarda taci kasa suka fito!!
Wata iriyar muguwar Dariya bazla dake labe tasaka tana nuna Sabah sakamakon yarda faduwan Nata ya kasance , fuskan nan kaman anzagi shege, da gudu ta yi cikin gida sakamakon muryan mom dataji tana sallallami!!
Da gudu mom ta karaso tana mai dago Sabah dake kukan wahala, kallan gaban Sabah mom tayi taci Karo da bawan ayaba, salati mom tasaka tace oh ni hasfa wanene kuma yaci ayaba ya'aje b'awan anan,
Cike da shesheka Sabah tace mom wlh bazla ce wlh bazan yarda ba yau sai naci ubanta sai kuma tasake fashewa dawani kukan,
Sosai ran mom ya baci a hankali ta tallafo Sabah tace taso muje inga irin hukuncin da tsohowar can kuma zata dauka yau, riko ta mom tayi dan ta tallafa mata taji tafashe da wani kukan tare da riki Hannu tana cewa mom na karye na karye nashiga uku, cike da tashin hankali mom fita ta kira maigadi ya tallafa mata kana aka je dauko mai dauri!
Tafe mom take kaman zata fashe tana ayyana aranta yau sai ta ma bazla dukan tsiya acikin gidannan, ko knocking bata tsaya yiba ta banka cikin falon, rarraba ido tafara kozata ga wani gurin yarda tazo cike da masifan nan ta sauke sa kansa!
Sallama ta kwada kaman zata fasa ko ina ba kakkautawa,
Da Sauri inna tafito tana cewa lapia lapia mai yafaru, wani Abu yasamu Abubakar dinne,
Wani kakkausan takaicine ya torake ma mom wuya wato sai Abu yafaru da Abubakar ne zatazo da gudunta tsaban munafurci,, ajiyan zuciya tayi tare da sassauta kanta dan in akai rashin saa ta iya zaginta, cike da karfin hali tace inna ina bazla Yau kibani ita Dan Allah na koya mata da'a yanzu ga Sabah chan a karye kuma ba aikin kowa bane inba na bazla ba!!
Yar Dariya inna tasaka kana tace haba Hafsa ina mai hankali zai dauka wannan zancen, naji tayaya bazla zata iya karya Sabah da girmanta!. Wani kololon takaici mom ta hadiye tace inna b'awan ayaba fa tasaka mata a hanya inma ba hakan bane Ai kinfi kowa sanin shedancin bazla ba sai an fada miki ba ''
Sakan baki inna tayi tace LA hafsatu ni kike gayama bazla shedaniya ce to bismillah ga dakinta chan shiga ki koya mata daa,
Bata jira cewan inna ba ta nufa kofan dakin bazla din, knob din ta Kama ta murda tajisa a kulle, batayi wata wata ba tafara knocking,
Bazla da tun shigowan mom take labe tana sauraransu, jin knocking din mom yasaka ta cikin Sauri ta cire kayan data saka ta dauko nighties tasaka gaban mirror taje ta Mayar da gashinta all messy kana ta dauko eye drop tasaka a ido tuni suka chanza yanayi!
Kallan door dinta da mom keta bugawa tayi sannan tayi murmushi tace Yau hajiya mom zakiga sharrin yan zamani,
Clip tasamu ta saka dai dai cikin ta kana ta nufa bakin door din ta bude tareda sakin wata banzar Hamma mai sauti!
Hannu mom tasaka ta finciko ta tace dan ubanki abunda kikayi kin kyauta kenan yanzu da ace ta fasa kai mai zakice,.
Wata iriyar irin I don't get you face bazla ta bata sannan tace subhanallahi mom wane ya karye? Mai ya faru?
Hannu mom ta daga out of frustration zata Mari bazla taji inna ta rike hannunta tace kul ban yarda da Mari ba! yarinyata nuna miki ba tasan zance ba amma kina shirin hukkunta ta, kiji ta bakinta nikuma indai bazla ce ta aikata laipin Zan baki bulala ki zaneta ina cewa ita ma yarkice!
Wani smirking mom tayi kana tace uban wanene yasaka ki Sama Sabah bawan banana a hanya? Do you know abun da kikayi causing hrn!?
Yanzu gata chan kwance how do you explain it,?
Clip din dake bakin cikin tayi pressing wani zafi ya shigeta lokaci daya kuma tasaka wani alhajin munafukin kuka, tace mom fisabalillahi mai zai sa na mata haka, sai kace wata makiyyiyata, ko makiyata Ai bazan mata hakan ba, mom look at my eyes Yau tun da nayi sallan asuba na koma bacci knocking in kine yatashe ni, look at my hair all messy, jikinta ta nuna tace kalla look I'm still on my nighties taya Naje na shirya mata hakan!! Sai takara fashewa da wani kukan harda shesheka tace mom I Donno mai zan miki ki so ni, ni bansan mainene laipina ba!
Da Sauri inna ta karaso tareda hugging dinta tace, share hawayanki yarinyar kirki ni daman nasan za'ayi haka, yanzu fisabillah Hafsa da me kika karu, yarinya yar marainiyar Allah bakisan illar cutar da maraya ba, sai kuma tasaka kuka irin na rikitatun tsofaffin nan tace "Allah sarki Muhammadu Yau da ace da ransa da bamu fuskanci haka ba da tsakanin mu daku sai dai ziyara!
Wani firgici mom tashiga,karema bazla kallo tayi taga tabbas fa bata da alamun tunda garin Allah ya waye ta fita, sosai taga wautar ta kallon inna da ke goge hawaye tayi da Sauri ta karaso gunta aranta tana fadin wannan makirar tsohuwar yanzun nan sai ta kashe mun aure, rike hannun inna tayi tashiga rero hakuri kaman wata sabuwar marokiya,
Dariyace ta kusa kwacewa bazla, da sauri ta shanye Dariya ta Kare wage baki wajen kuka, duk da tsanar da mom ke mata bai hanata jawota jikinta tana lalashinta ba,
Cike da wata munafukar murya bazla tace mom kimata sannu kafun mu shigo ni da inna! A hankali a hankali ta lallaba su ta bar part din!!
Kure bazla da ido inna tayi, ganin kallon datake matan yasa bazlan tace ni ni inna bana son wannan kallon kaman kema baki yarda dani din ba! Gaba tayi tabar inna gudun kar ta rafko ta,
Tana shiga dakinta ta haye tsakiyan gado hannunta rike da tube, saitin bakinta ta kaisa kaman mic tafara tsalle da waka "the victory is mine, we party party party, ohhhhhhhh yeaaaaaaaaa""
Haka tagama shirmenta ta koma ta kwanta!!!!
______________________________________________
Tunda suka dauka hanyan kaduna take bacci sakamakon baccin da bata Samu ba dare jiya sabida gaba daya rabbi daren hirace ta wakana tsakaninta da inna da Amrah!
A hankali daddy da shine wanda ya kawota din yafara tashinta, bude ido tayi a agajiye tace daddy har munzo'
Murmushi yayi yace ehen Ai naga kina ta sharara baccinki hankali kwance ko ki tashi ki taya daddy driving,
Dariya tayi tace kai daddy kasan fa ban iyaba, fitowa tayi daga motan tana bin tafkeken gidan da kallo, cars space dinta kalla taga wasu kyawawan motoci guda biyar, gurin da aka sa su kawai abun kallo ne,
Ta shaafa da kallon dukiyar da aka kashe a gun, tama manta tare da daddy take sai da taji yariko hannunta,
A kunyace ta dauke kai tace Allah daddy gidan ya haysam mai kyaune sosai,
Tana rufe bakinta haysam na fitowa fuskansa cike da faraa, har kasa ya tsugunna ya gaida daddy cike da girmamawa da kauna, kana ya kira gateman dinsa yafito da luggage's din bazla,,
Kallonsa ya maida kan ta tukkuna yace ke baki iya gaisuwa ba, dan sunkuyar da kai tayi cike da kunya dan ya kamata ta na kallonsa, dariya daddy yayi yace kai dai kalla yar inna kawai nasan Yau bacci Baa magana,
Dariya sukasa dukasu haysam gaba yana musu jagora cikin gidan,
Koda suka shiga gidan everything is semineat baza dai kace mace na rayuwa cikin gidan ba amma duk da haka kyau da kawatuwar sa bata boyeba,
Table haysam ya nema lami mai aikin nayla ta shirya musu, daddy ne ya taresa da cewa Aa sai dai bazla ni yanzun nan zan tafi sabida ina da abun da zanyi a nan and bana son tafiyan dare,Ina mai dakin naka yakarasa maganan tareda mikewa,,
Dan sosa kai yayi yace wlh daddy ta danyi nisa ne wai suna da bikine haka!
Oh cewan daddy shaanin mata sai a hankali Ai, na tura maka komai na school dinta ta email dinka!!
Bayan tafiyan daddy haysam ya kai bazla masaukinta tare da mata jagora gun cin abinci suna dan hira akai akai.
Lamice tafito da warmers,macece da bazata wuce shekara 23 ba dan da kadan naylan zata tsere mata, kallonta kawai ya saka bazla tayi losing appetite dinta sabida wani karni Da dauda dake tashi jikinta,
Bayan tafiyanta bazla ta kalla haysam tace ya haysam ni wlh bazan iyacin abincin da matarcan ta girka ba look how Dirty she is!
Shiru yayi yana juya maganan bazla dan tabbas shima bawani iya ci yake ba, fadan su kullum da nayla dan ba abunda ta iya dafawaba..
Dan murmushi yayi yace okayy lets eat out side, shiru bazla tayi kana tace what about I cook something light?
Daga gira yayi yace sure!!!
______________________________________________
H3y lovies what about this chappy😁
Bazla finally gidan haysam!
What do y'all will happen idan nayla tadawo¿
Okayyyyyyyyyy
Next chappy
Don't forget to vote, shar3 and comment 💋xx
Chuchujay🖊
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top