Chapter 13
MUZUBA MUGANI💃👣
Kaman dirar mikiyya haka maganan yadaki kowa a dakin, Kar ace mom ma datayi mutuwan Zaune dan batayi tunanin tsohuwar nan ta kai har haka ba, da kyar daddy ya iya bude baki yace inna wani abu ya faru ne?
Juya masu baya inna tayi cikin kakkausar murya tace ni dai nace ka saki hafsatu idan kuma ban isa bane ba to sai naji..
Da sauri yace "aa inna ai kinfi haka ma a gurina kuma Nasan tunda kikace nasaketa da a kwai dalili, kallonsa ya maida kan mom da tagama kidimewa yace ni Abubakar nasake ki Hafsa saki daya,
Wani irin rikitaccen kuka tasaka while duk mutanen dake cikin dakin suka yi mutuwan zaune kaman ruwa ya cinye su kar ma ace nayla Dan bata taba tunanin inna ta kai Har haka ba tsoronta daya kar itama a girgide mata Dan auren da takeji da!!
Ba abunda ke tashi banda sautin kukan mom a dakin, haysam dayasan halin inna sarai Dan Haka mamakin sa bai yawa ba kwai dai bai yi expecting hakan ne ba!
Guri inna tasamu ta zauna Kana tace Abubakar na Kuma umartar ka da ka maida matar ka, dif kukan mom ya dauke mamaki yayi replacing dinsa!
Kaman yarda inna ta umarci dad ya karacewa ni Abubakar na Mayar da matata Hafsat dakinta kuzama sheda,
Gyran murya inna tayi Kana tace Abubakar kasan Mai yasa nasaka kayi hakan? Girgiza kai yayi alamun Aa "yauwa tace kana ta cigaba da magana nayi hakan ne domin na nuna ma kowa anan musamman ke hafsatu Akan cewa ni nan ni na haifa Abubakar kuma ni na isa dashi da duk wani Abu da ya mallaka a duniya, domin kuwa duk cikin kunnan ba wanda yasan yarda na Samu cikinsa da yarda na raina cikin har tsawon wata Tara, dakuma yarda na fuskan ta lokacin haihuwarsa!!
Kallonta takara maidawa Kan dad Kana tace yanzu abunda nake son sani shine shin bazla Akan Hafsa take zaune ko kuwa Akan wannan jairar matar dan ka din,ta nuna nayla, sannan ta kuma nun Sabah tace ko kuma Akan wannan yar d'osane din datake zaman cin arziki, dan bazla tafita matsayi cikin gidan nan sabida bazla Abubakar haifarta ne kawai bai ba kuma yau ko ba raina shi zai riketa, kuma duk duniyar nan bata da uba da ya fisa,
Dan tari tayi Kana tace bari dai na gajarta maka zance Abubakar so nake Hafsa da sauran su fada mun menene bazla ta musu da zasu sameta suma ta shegen duka dan tsabagen rashin mutunci har da mai saka wayar wuta kaman ta haifeta Alan dole sai tafada musu Inda haysam yatafi da ita,
harde Kafa tayi tana jiran amsa, daddy kuwa da ransa yayi mukura wajen baci kasa magana yayi illa nuna mom da yake da dan yatsa jikinsa sai rawa yake, mom na ganin haka tayi saurin Tararsa da ban hakuri dan tasan irin bacin ransan nan rabon da yayi sa har ta manta "
Muryar ta na rawa tace dan girman Allah daddyn haysam kamun rai walh tallahi sharrin shaidan ne wlh namaka alkawarin hakan bazai sake faruwa ba,
Shiru dad yamata amma jikinsa bai bar rawaba, Guri yasamu ya zauna tareda Dora hannunsa a kai,
Haysam ne ya katse mom da cewa mom how could you ranan fa tace mun bata da lapia shiyasa na kaita asibitii, amma ke ya nuna nayla bansan ina kikasami liver in da kika bugar mun yar uwa ba and I will make sure kiyi regretting actions dinki, kuka nayla tasaka Irina gogaggun Yan bariki tace wlh honey bansan mai ya shiga Kaina nayi hakan ba, gurin bazla ta rarrafa tace hava little sis kinsan bazan miki haka da sane na ba, hannun da ta rike na bazla tayi sauri kwacewa tana rarraba ido,.
Daddy ne yace bazla yarinyata zo nan zauna kusa dani, jikinta kaman ba laka haka ta koma kusa dashi ta zauna, Cike da kulawa yace menene ya hadaki dasu tell me kar ki boye min komai!...
Cike da nutsuwa tafara basa labarin abunda yafaru tana cikin maganan kaman ance ta daga kanta taga haysam ya kureta da wasu sleepy eyes, sosai ta tsinci kanta da Kin fadan abunda mom tace a kan inna,
Sosai haysam yaji Dadi dan yasan mudin daddy yaji furucin nan to zaman maifiyarsu gidan yakare,
Bangaren mom kuwa wata muguwar ajiyar zuciya ta sauke jin bazla bata tona mata asiri ba!..
Ta Inda dad ya shiga bata nan yake fita ba har sai da inna ta taaresa tareda musu nasiha, kallon mom tayi tace hafsatu ban tsane ki ba Allah yasani kawai san zuciyar kine ke nuna miki haka kuma indai kikasa aranki Cewar ni muguwar uwar miji ce baki mun adalci ba sabida bantaba saka ido a abunda Dana yamiki ba, sai kiyi kwana Nawa gidan nan amma baifi saudaya kike ganina Arana ba hurumin gidan ki bai dameni ba, nasan cewa zaki fahimta abubuwan da nakeyi nan gaba Kema uwar Yaya mazace har Guda uku!
Ahaka dai aka sasanta abun inda suka bama inna hakuri sosai Akan hakan bazai Kara faruwa ba duk da bai kai zuci ba dan sosai bangaren mom takarajin tsanar inna da bazla inda ta kudiri niyya mummuna akansu, Sabah da nayla kuwa da dan sauki musamman nayla da a ganinta idan suka tattara suka yi gaba ba abunda zai dame ta da wani case din so called inna da bazla!
Da dare daddy yakawo sabbanin iPhone 8+ guda biyu da Mac book's ya bama bazla Amrah kowa dai dai a matsayin kyautar su tagama junior class amma da sharadin bayasan wasa!!
Washe gari nayla da haysam suka tattara suka tafi sabida yana yin aiki da ya kira haysam!!.
______________________________________________
Kwanaki Nata tafiya haka zalika almura masu Dadi da akasin haka a cikin gidansu haysam !
Bazla ne da amrah tefe gudu gudu sauri sauri dan zuwa duba admission list board din dake kafe a NIGERIAN TURKISH INTERNATIONAL SCHOOL KANO(ntisk)
Sunan Amrah kawai suka gani a board din amma babu na bazla, duk da rashin jindadin da bazla taji narashin samun school din bai hanata nuna farin cikin sabida samun Amrah din ba yayin da ita kuma Amrah ta Shanye duka farin cikin ta ta dukufa wajen duba sunan bazla amma still bata gani ba! Haka nan suka koma Gida ransu duka ba dadi,
Koda suka fada ma daddy ba karamin rashin jin Dadi yayi ba so directly yakira PC din school din sabida sanayya yasaka yamasa alkawarin duba wa,
After like 30 min yakira Dadi ya sheda masa cewan bazla tasamu admission a school din amma bana kano ba a Turkish in kaduna admission dinta yafada,
Koda daddy yafada musu sunyi murna although sunso suyi school daya amma kome ne kaga yafaru da mutum haka kaddaransa yake dan haka kowanensu ya rungimi zabinsu!!
Yau yakasance sauran week afara classes kome angama musu fara shiga aji ne kawai yarage,
Bazlace zaune bakin mirror sai gogewa take almost minutes Nawa tana abu daya amma Kana kallan ta kasan she was lost in thoughts,
Ikon Allah yar inna tunanin me kuma kikeyi ace tundazu kina ta Abu daya "muryan inna yayi sauri zakulota daga tunanin data fada,
Aje wipe dintayi tace inna nikam in tambayeki wai idan Naje kaduna dinnan amma a hostel Zan zauna ko?
Zaman inna ma tayi ta fuskaceta tace hostel kuma yar inna Bayan kina da Gida a chan din,
Da wani irin fuskan mamaki bazlan ta kalleta tace Gida kuma inna waya Gina min Gida a kaduna kuma,
Dariya inna tayi tace gidan mijinki mana,
Tashi bazla tayi tana bubuga kafarta tana ni ni ni inna banaso naga kwana biyu Dinan saikina cema haysam mijina ni banaso, Dariya inna tayi, tayi harda kelkeltawa tace zo zo zauna yar inna wasa nake miki to gidan yayan ki zaki zauna nacire mijin, zama ta dawo tayi tace amma inna kinsan wani Abu Nifa bana kaunar gidan ya haysam sabida banasan matarsa Allah,
Kamo hannunta inna tayi tace kwantar da hankalinki ba abunda ta isa tamiki indai haysam na cikin Gidan , inma baya nan ni Ai nayarda da yata bazaki zauna a kwareki ba!!
Haka dai inna tayi ta bata baki har ta shawo kan ta!!
______________________________________________
Vote, share and comment
Xoxo❤
Chuchujay
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top