Chapter 8
Murmushi rahma tayi sannan ta daga kanta tace of course wannan shine armaan malik babban player wanda ya kware a wasa da zuciyar yammata ya zama dole ki nutsu kafin kiyi nasarar sace zuciyar armaan,ajiyar zuciya yasmin tayi don a yanzu jikinta ya fara sanyi taya zata iya sace zuciyar armaan?hadadden saurayi son kowa kin wanda ya rasa a matsayinta na wacce iyayenta suka kasance yan aiki
"Cilantro mall driver yayi parking mota yasmin da rahma suka shiga mall din,abaya,gowns,shirt,trousers,skirts da duk wasu sauran kayayyaki rahma ta dinga diba har abun ya fara bawa yasmin tsoro,bangaren watches,earrings da necklaces suka tsaya shima ta dade tana zabarwa yasmin watches masu kyau sannan suka siya shoes,bags,perfumes da cosmetics....Atm card rahma ta mika aka cire 600k aka saka musu kaya a mota suka wuce,basu karasa gida ba sai da suka tsaya a essence plaza rahma ta shiga batayi wani taking much time ba ta fito hannunta rike da leda,tana shiga ta mikawa yasmin ledar,a hankali ta karbi ledar ta bude zaro ido tayi cikin tsananin mamaki tace Iphone 13 pro max......sai after magrib suka koma gida direct apartment dinsu ta wuce hannunta rike da manyan ledoji har seda aka tayata da wasu,kwance ta tarar da anna a palour tana karanta hisnul muslim,bin yasmin tayi da kallo ganin ta shigo jikinta a sanyaye ga kuma kayayyaki ana ta shigowa dasu,sai bayan an gama shigowa da kayanne anna ta kalli yasmin cike da mamaki tace daga ina kike?sannan wannan kayan ina kika samosu?
"Murmushi yasmin tayi duk da ba wani bayyana yayi a fuskarta ba tace lah anna kinga dazu na raka aunty rahma shopping shine nima ta siyamin wannan kayayyakin dubasu kiga harda waya me tsada,cike da nazari anna ta fara bin kayan da kallo sannan ta kalli wayar da yasmin ta mika mata tace yasmin,a hankali yasmin tace na,am,sake daga wayar anna tayi tace wannan ba ita bace wayar da kika nuna min hotonta wancan satin kikace yanzu itace wayar da ta shigo yanzu mai tsada?saurin daga kai yasmin tayi tace eh itace anna Iphone 13 pro max ba,girgiza kai anna tai tace amma shine rahma ta siya miki ita tare da wannan uban kayan haka yasmin?jikin yasmin sanyaye tace wlh anna nima bansaniba kawai dai tace inada kirki shine dazu dana rakata shine ta siyamin nima.......toh kawai anna tace sannan ta dauki hijab dinta tace dama yanzu zanje nayiwa hajiya kunun gyada daga nan zanyiwa rahma magana inji meye dalilin siya miki wannan uban kayan haka,tana gama fadan haka tai waje,anna na fita yasmin ta dauko charger ta saka wayanta a chaji duk da faduwar da gabanta yakeyi
"Sai da anna ta tambayi rahma tukunna hankalin ta ya kwanta don tayi tunanin wani saurayine ya siyawa yasmin wancan uban kayan haka
"Sai da yasmin ta iddar ta sallar ishai tukunna ta mike daga kan dadduma ta koma gado ta kwanta inda anna ke kwance kasa a katifa,wayanta ta ciro daga charge tukunna ta sake komawa kan gadon,Instagram ta bude kamar yanda rahma tai mata umarnin ta turawa armaan DM (direct message)ta dade tana kallon profile dinsa tare da jinjina uban followers dinsa a hankali tace kalli yanda 8 million people's suke following dinsa sai kace wani artist,komawa tai tayi following dinsa duk da tasan armaan bazai taba following back ba ganin 8million peoples ke following dinsa amma shi mutum 20 kawai yake following,bayan tayi following dinsa ne ta koma DM ta tura mishi hey jikinta a matukar sanyaye
"Tunawa tai tun safe rabonta da cin abinci ya sata mikewa ta nufi karamin fridge din dake kusa da gadon ta dauko kunun gyada ta zuba a cup sai da ta shanye duka tukunna ta ajiye cup din ta koma gado ta janyo wayarta,what?????ta fada da karfin gaske idonta na kan wayarta tana kallo cikin mamaki....a firgice anna ta mike zaune tace lafiya kike ihu haka yasmin,saurin yin murmushi tai tace lah yi hakuri anna kinga mardy ce take fada min harda sunana cikin masu yin sauka a wannan shekarar,itama anna murmushi tayi tace masha Allah amma kuma ai ba ihu zakiyi ba addua zakiyi ki godewa Allah,toh kawai yasmin tace don ta kagu anna ta koma bacci
"Armaanmalik started following you" shine abinda ta gani rubuce jikin wayar,wani notification sound dinne ya sake shigowa da sauri ta koma DM ta duba ganin yayi mata reply da Hi ya sata mikewa zaune kamar zata fasa ihu don dadi sedai babu damar haka don ta yiwa rahma alkawarin babu wanda ze san halin da suke ciki,hannunta na rawa ta fara typing
"Yasmin:how are you?
"Armaan:Actually,good what about you?
"Yasmin:I'm also good
"Armaan:may i know you?
"Yasmin:of course yes,why not?
"Armaan:then?
"Yasmin:I'm yasmin hayat from abuja 19 years of age and I'm studying
"Armaan:awesome!nice to meet you
"Yasmin:thanks!and you?
"Armaan:check my profile
"Yasmin:🙄
"Armaan:Are you ready to meet me?
"Yasmin:yeah!sure
"Armaan:tomorrow,4pm c'est bon cafe
"Yasmin:Alright!i will be there
"Armaan:well,goodnight....see you tomorrow
"A hankali ta ajiye wayar akan bedside drawer,dora hannunta tayi akanta don ta samu saukin ciwon da kanta ke mata,tsaki tai kadan tace meyasa na amince da zamu hadu gobe ba tare da na nemi shawarar rahma ba....ta dade kafin bacci ya dauketa saboda gajiyar da tayi har makara tai batayi sallar asubah ba,bayan ta iddar da sallah tai breakfast karfe 10 ta nufi apartment din rahma gabanta na faduwa tai knocking kofar,,,,jin ana knocking yasa rahma bude idonta cikin bacin rai ta kalli agogo it's 10am ta fada a hankali sannan tayi tsaki a iya saninta duk cikar gidan babu wanda yake tashinta a wannan lokacin koda kuwa mahaifiyarta ce,jin anci gaba da knocking yasa rahma mikewa zaune ranta a matukar bace tace who the hell is this?muryar yasmin na rawa tace aunty rahma nice,mamaki ne ya bayyana a fuskar rahma jin muryar yasmin tasan tabbas it's something special a hankali ta sauka daga kan gadon ta janyo towel jikin hanger ta daura saboda she always sleep half naked......bayan ta bude mata kofa ne yasmin ta zauna akan resting chair hannunta na rawa ta mikawa rahma wayar dake hannunta,da sauri rahma ta karbi wayar ta fara karanta chart din da sukayi da armaan jiya,cikin farin ciki ta mikawa yasmin wayar tace perfect! smart girl with sharp brain hakan yana nufin anjima by 4pm zaku hadu da armaan malik a c'est bon cafe?saurin daga kai yasmin tayi gabanta na faduwa,murmushi rahma tayi tace good i will arrange everything karfe 2:30 kizo ki sameni
"Toh kawai yasmin tace ta nufi hanyar fita daga dakin,tana fita daga dakin rahma ta janyo wayarta ta fara sanar dasu fadila da zahra.....2:30pm yasmin ta shiga apartment din rahma,bathroom ta nuna mata bayan ta zuba mata shower gels masu kamshin gaske ,ta dade cikin bathtub kafin ta fara wankan yau kam yasmin jinta take kamar tafi yar president jin kanta take kamar itace bill gates,bayan ta fito ne jikinta sanye da bath robe ta zauna akan resting chair,rahma ce ta shirya yasmin sosai tuni ta dauki kyau kamar wata balarabiya,jikin dispenser din dakin rahma ta nufa bata dadeba ta dawo hannunta rike da coffee ta mikawa yasmin tace take a sip duk da bakya bukatar practical akan komai amma ya zama dole sai an koya miki wasu abubuwan saboda armaan rayuwarsa gaba daya ta turawa yakeyi kuma nasan tunda yace ku hadu a c'est bon cafe toh lallai zakusha coffee a wajen
"Ganin yanda yasmin ke sipping perfectly yasa rahma sakin baki tana kallonta,wani gown peach colour rahma ta mikawa yasmin tasa sannan ta gyara mata gashi ta feshe mata jiki da perfumes masu kamshi,sosai yasmin tai kyau kamar yar india sedai abinda ke bawa yasmin mamaki shine tun dazu take duba wayarta amma shiru babu message din armaan,jikinta sanyaye ta kalli rahma tace har yanzu banga sakonshi ba ko daya sannan bani da number shi balle in kirashi idan naje,murmushi rahma tai tace karki damu tunda yace miki zaku hadu yau toh bazai kirakiba kuma bazai pinging dinkiba amma kina zuwa wajen zaki ganshi,girgiza kai yasmin tayi tace gaskiya harkan big time yayi a rayuwa ba kamar rayuwar bahaushe ba idan yace maka zaka hadu se kayita bibiyarsa still kayita kiransa a waya at the end ma yace maka ya manta lol 9ja for life
"3:30pm rahma da yasmin suka fito parking space din gidan,wani red bugatti yasmin ta shiga driver ya fara driving,,,,,murmushi tayi fuskarta na kallon window din motan tace YASMIN HAYAT yar gidan Mr president
Thank you for reading my story!!!
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top