Chapter 7



Daren ranar sam yasmin bata rintsaba gaba daya a firgice take har seda taga 3 na dare sannan bacci mai nauyi ya dauketa,ganin yasmin bata da niyyar tashi har 6 na safe yasa anna yin tsaki duk da fushin da take da yasmin ta tsaya akan gadon da yasmin ke kwance ta taba ta kadan,a tsorace yasmin ta farka tace na shiga 3 aunty rahma don Allah kiyi hakuri,tsaki anna tayi tace ai baki ga komai ba tukunna sai anjima idan kinji kira daga mr president indai jurin kaza tone tone toh wataran zata tono wa kanta wukar da za,a yankata,anna na gama fadar haka tai shigewarta kitchen ta bar yasmin tsaye jikinta a matukar sanyaye ta shiga bathroom ta dauro alwala ta shinfida sallaya tayi sallah bayan ta iddar ta dade zaune tana lazimi ita kam anna abin har dariya yasmin ta bata yaushe rabon da yasmin ta dauki carbi tun kafin idonta ya bude da gayu da kuma son abin duniya sai dai anna tana da tabbacin duk son gayunta bazata taba zubarwa kanta mutunciba

"Cikin fushi anna ta kalli yasmin tace sai ki taso mu tafi kitchen din first lady muyi girkin tare kinsan mr president yana gari kuma girkin da ake mishi na masu diabetes yana da wahala dole sai kin tayani,idon yasmin kamar ze zubar da hawaye ta kalli anna tace don Allah anna kije kiyi aikinki kawai ni gaskiya tsoro nakeji kar naje na hadu da aunty rahma,tsakin takaici anna tayi sannan ta kalli yasmin fuskarta babu alamar wasa tace idan baki taso kin biyoni ba wlhy sai ranki yayi mummunan baci,ganin anna da gaske take yasa yasmin daukar babban hijab ta saka tabi bayan anna duk da kuwa gabanta na dukan goma goma......sai da sukayi hour 2 a kitchen kafin su gama kammala breakfast din sannan anna ta jera akan dinning suka koma apartment dinsu na masu aiki kamar yanda suka saba,har yasmin ta fara jin sanyi a ranta ganin har karfe 12 na rana amma rahma bata neme taba,telephhone din kusa da itace ta fara qara da sauri ta dauka duk da gabanta ya fara dukan 3-3,muryar rahma taji tace hey yasmin ki sameni a dakina yanzu bata jira tace komai ba ta kashe waya,ajiye wayar tayi jikinta a matukar sanyaye sannan ta kalli anna da take gefe tana jan carbi,hijabinta ta zira har kasa sannan ta saka takalminta ta kalli anna tace anna aunty rahma ke kirana ki tayani da addua,ko kallon inda yasmin ke tsaye anna bata yiba ta juyar da kanta don sosai anna ke jin haushin yasmin

"Da kyar yasmin ta tura kofar dakin rahma ta shiga duk da Ac din dake cikin dakin be hana yasmin goge gumi ba sannan ta zube kasa zuciyarta na bugawa da sauri ta sunkuyar da kanta kasa,cikin isa da gadara rahma ta kalli yasmin tace tashi ki zauna akan kujera,gaban yasmin ne ya sake faduwa cikin kuka tace don Allah aunty rahma ki yafemin don girman Allah kiyi hakuri wallahi bazan sake maimaita irin wannan gangancin ba don Allah kiyi min rai wallahi bazan sake ba don Allah ki rufa mana asiri karki koremu daga gidan nan wlhy bamu san inda zamujeba,murmushi rahma tayi tace yasmin nace ki tashi ki koma kan kujera ki zauna magana nakeso muyi dake mai mahimmanci,da kyar yasmin ta zauna akan daya daga cikin royal chairs din dakin sannan ta dago ta kalli rahma tace ina jinki,chapman din hannunta ta ajiye ta kalli yasmin dake faman zuba gumi fuskarta tayi ja sosai hakan be hana kyau dinta fitowa sosai ba a hankali tace you are so beautiful babe.....shiru ta danyi na 30 seconds sannan tace yasmin kinaso ki zama kamar ni?kinaso ki dinga wasa da kudi kamar yanda nakeyi?kinaso ki dinga tafiya guards na take miki baya kamar ni?kinaso rayuwarki kullum ta kasance cikin farin ciki kamar ni?mamaki ne ya kama yasmin tai saurin daga kanta alamar eh tace hakane aunty rahma inaso hakan ta kasance a rayuwata amma hakan bazai taba faruwa dani ba saboda ni ba kowa bace fache yar aiki......dariya rahma ta danyi kadan bayan tayi liking post din fadila a IG sannan ta ajiye wayar a gefe ta kalli yasmin tace idan har kin amince zakiyi soyayyar wata 2 kachal da armaan malik a matsayin yar shugaban kasa toh nayi miki alkawarin zaki cigaba da rayuwa a matsayin yar shugaban kasa har karshen rayuwarki

"Kamar a mafarki yasmin ke jin rahma,tana nufin yanzu zata hau role din yar shugaba kasa ne?tana nufin zata dinga hawa motan da ranta keso?tana nufin zata dinga kwana a guri mai kyau?tana nufin burinta na zama slay queen zai tabbata?idontane ya sauka akan Iphone 14 pro din hannun rahma da sauri ta fara imagining yanda zatayi zafafan portrait tayi posting dinsu a Snapchat da Instagram,ba tare da tayi shawara da zuciyarta ba ta kalli rahma da zafafan hot eyes dinta tace na yarda na amince zanyi miki kowanne irin aikine idan har zan samu duk abubuwan da kika lissafo min,cikin mamaki rahma ta kalli yasmin tace are you sure?da sauri yasmin ta daga kanta tace da gaske nake aunty rahma,hugging din yasmin tai cikin murna ta dauki wayarta ta kira zarah da fadila ta sanar dasu bayan ta kalli yasmin tace jeki amma inaso hakan ya zama sirri tsakanin nidake kawai banaso kowa yaji labari sannan ki shirya anjima by 4 zan fita dake shopping ki siyo duk abinda kikeso wanda zakiyi amfani dashi wajen sace zuciyan armaan,toh kawai yasmin tace ta nufi apartment dinsu a hankali zuciyarta ke nanata mata sunan armaan malik.....ko yaya wannan armaan malik din yake?murmushi tai tace oho

"Lokacin da yasmin ta koma bangarensu bata tarar da anna ba ta fita gidan biki,kwanciya tai kadan akan gado taci gaba da tunanin shi kuwa wannan armaan malik din ya yake?dabara ce ta fado mata tai saurin janyo wayarta a karkashin pillow ta kunna data sannan ta shiga IG tai searching armaan malik,a firgice ta mike zaune tana cigaba da kallon kyakkyawan picture dinsa wanda yayi posting  10 minutes ago amma sama da 2 millions sunyi liking da comments

A tsorace tace what?saurin girgiza kanta tayi tace gaskiya wannan bashi bane armaan malik din da aunty rahma zata bani aiki akansa inajin dai wanine daban,kallon agogo tayi taga har 3 yayi direct ta shiga tai wanka ta fito ta danyi light makeup ta saka black abaya,karfe 4 ta nufi apartment din rahma tana ta kamshi duk da ba wani perfume me tsada yasmin take amfani dashiba,dukansu bayan mota suka zauna driver yana driving dinsu,sun danyi tafiya kadan rahma ta mikowa yasmin wayarta tace duba nan da kyau wannan shine armaan,ganin exactly picture din da ta gani dazu yasa yasmin kallon rahma a tsorace tace kina nufin wannan shine?

Alhamdulillah i am back🐒😂
Don't forget to vote,share and comment
Thank you for reading my story!!!

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top