Chapter 6

"Sai da yasmin ta fara tsayawa gurin tailor ya rage mata rigar saboda rahma ta fita jiki sannan ta wuce gidansu mardy,sosai mardy ke mamaki ganin yasmin da expensive kaya haka anan ta sake tabbatarwa lallai yasmin zata iya abinda yafi haka indai akan kudine,da kyar yasmin ta lallaba mardy ta shirya suka tafi gurin bridal shower din tare bayan sun tsaya anyiwa yasmin makeup,,,,kamar babyn roba haka yasmin ta koma saboda tsananin kyan da tayi kamar yar india dama tana kama da Alia bhatt lol,sai karfe 9 yasmin suka karasa gurin saboda sun bata lokaci gurin makeup,a farfajiyar event center din yasmin ta kalli mardy tace don Allah kawata idan mun shiga cikin hall din zakijene a matsayin yar aikina haka saboda kinga tsayin rigar nan ya dan yimin yawa kinga seki dinga tattare min kar inje in fadi sannan kinga ban iya tafiya da takalmi me tsini sosaiba

"Kallon banza mardy tayiwa yasmin tace amma wlh kin rainamin hankali ki kalleni da kyau kice wai ni zan dinga tattare miki riga wlh baki isaba gara ma ki nemo wata tun dare be mikiba,sake kasa kasa tai da murya tace haba Kawata kinsan dai kece me rufamin asiri duniya yanzu idan ina tafiya na fadi a gurin nan ai kinga tare zamuji kunya kuma kalli jakata cike take da kudi se muyi ciniki a nawa zakimun aikin ta karasa magana tana bude jakar hannunta,zaro ido mardy tayi tace na shiga 3 yasmin ina kika samo kudin nan haka?murmushi yasmin tai har dimple dinta ta lotsa tace ke kiji wata irin tambaya kin taba jin an tambayi Yar gidan shugaban kasa inda ta samu kudi?ai kawai kisa a ranki wannan kudinane halak malak saboda kudin kasarmu ne ake sata don haka ki kwantar da hankalinki zan baki kudi masu yawa

"Sanda su yasmin suka karasa hall din cike yake da yammata wands suka amsa sunansu slay queens,yara yan gayu ya'yan masu kudi kasancewar bridal shower ne babu namiji ko daya a gurin yammata ne kawai suke zazzaune ansa wakar i dont care na ed-sheeran wakar yana tashi cool and romantic,suna shiga idon kowa ya sauka akan yasmin wacce za,a iya kiranta da angel saboda tsabar kyau da shiga rai

"Direct gurin amarya da kawayenta ta wuce ta fara ruwan dollars tana liqi,tuni hankalin kowa ya koma kanta ana tunanin yar wanne me kudince haka,da sauri yammatan suka tashi suka fara yi mata videos da pictures,tuni yasmin ta saki jikinta a gurin ta fara rawa itama anayi mata liqi,basma ce ta karasa inda rahma take zaune a farfajiyar gurin bikin tace hey mrs heart broken har yanzu bazaki dena wannan tunaninba karki manta munzo gurin nan ne don ki samu rage wani tension din dayake kanki

"Tsaki rahma tai tace wlhy basma komai na duniya baya min dadi kawai tashi mu tafi bazan iya jure ganin abubuwan takaiciba,murmushi basma tayi tace naji yanzu zamu tafi amma taso muje kiga wata yarinya nidai tunda nake ban taba ganin yarinyar da ta sace zuciyar yammata ba kamarta,kyakkyawace kamar ita tayi kanta sannan abinda ze baki mamaki yanda take spraying kudi a gurin nan ko ke da kike yar shugaban kasa iya kacin abinda zakiyi kenan shiyasa nakeso kizo muje ki ganta nasan ku slay queens babu wanda baku saniba

"Wani irin kishine ya tokare a zuciyar rahma cikin takaici ta kalli basma tace ashe har akwai yarinyar da ta fini kyau?ashe har akwai yarinyar da ta fini arziki?ashe har akwai yarinyar da zata shiga guri ta zama abin kallo wadda ta wuce ni yar gidan president?this is impossible basma,,,,,,dariya basma tayi tace wlhy rahma i,m not kidding you taso muje ki ganta kinsan Allah ta fiki komai da kike tunani,mikewa rahma tayi yace karyane wlhy muje na ganta

"A tare suka hau upstairs na hall din suka shiga,still yasmin na tsaye ana ta yin pictures da ita masu rububin karbar phone number dinta sunayi,a firgice rahama ta kalli basma tace wannan kike nufi?saurin daga kanta tayi tace of course ko baki yarda da abinda nace miki bane?cigaba da kallon yasmin tai tana liqa dollars cikin tsananin mamaki sanye da kayanta a jiki inda zuciyarta taci gaba da bugawa kamar zata fito saboda tsananin takaici da bacin rai,tabbas wannan yasmin ce maganar basma gaskiyace yasmin ta fini kyau da komai kuma ita ya cancanta ta zama yar gidan president baniba....shine maganar da rahama ke maimatawa a zuciyarta cike da azabar bakin ciki

"Basma ce ta taba ta tace tunanin me kikeyi haka?ajiyar zuciya rahama tayi tace basma waccan da kike gani yasmin ce yarinyar wannan dattijuwar buzuwar matar da takeyi mana aiki a gidanmu,kayan da kike gani jikinta kayanane wanda na siyesu a london zan saka yau shine ta dauki kayan ta saka sannan kudin da kike ganin tana spray dasu kudinane ta dauka,a firgice basma ta kalli rahama cikin mamaki tace kutmar..........wallahi yau yarinyar nan setaci uwarta seta gane kuskurenta shegiya tsinanniya yar matsiyata wlhy.......saurin riko hannun basma rahma tayi tace easy basma,easy please kinfi kowa sanin wacece rahma,kinfi kowa sanin babu wanda ya isa ya takani amma inaso ki kwantar da hankalinki zakisha mamaki

"Janyo hannun basma tai suka karasa inda yasmin take tsaya tana rawa da amarya,a hankali rahma ta tabo yasmin fuskarta dauke da murmushi tace can we have a selfie please?a razane yasmin ke kallon rahama dake tsaye gabanta tana yi mata wani irin kallo me dauke da tuhuma,tuni gaban yasmin ya fara dukan goma goma inda idonta ya ciko da hawaye,da sauri ta nufi hanyar fita daga hall din a upstairs ta karasa cire takalmin dake kafarta inda ta fara gudu a titi kamar mahaukaciya takalminta a hannu daya hannun kuma ta tattare gown dinda tai mata yawa saboda taji dadin gudu,gudu take kamar mahaukaciya da kyar ta samu napep ya karasa da ita villa,gudu taci gaba dayi harta karasa apartment dinsu na masu aiki,a palour ta tarar da anna tana shara da gudu ta bangajeta tabi ta gefenta ta shige daki ta fara cire kaya cikin tsananin tsoro da tashin hankali,da gudu anna ta karasa dakin tace yasmin lfy menene ya sameki?kuma kayan waye a jikinki?yasmin daga ina kike?cikin kuka yasmin tace anna babu tambayar da zan iya amsa miki yanzu don Allah anna ki taimakeni karki bar aunty rahma ta kasheni don Allah anna kice mata bani ta ganiba don Allah kice mata bacci nakeyi yau babu inda naje

"Cikin tsawa anna tace keee saurara min yasmin banason iskanci da fitsara,ki fada min daga ina kike tun dazu nake nemanki sai yanzu karfe goma zaki shigo min gida kina wani kukan banza da wofi,jikin yasmin sanyaye tace anna wlh gidan biki mukaje nida mardiya,cikin mamaki tace wannan kayan jikinki kuma na uban waye?cikin tsoro yasmin tace kayan,,,kaya.....kayan aunty rahma ne kuma yanzu ta ganni da kayanta a gurin bikin

"Cikin tsananin tashin hankali da tsoro anna ta jefar da tsintsiyar hannunta sannan ta dora hannunta a kanta tace na shiga 3 na lalace yasmin kin kasheni,yasmin kin jawo min masifa da bala,i itama ta fashe da kuka

"Amma wlh rahama kin bani mamaki yanzu har yarinyar yar aiki ace wai ta dauki kayanki ta saka kuma ki kasa tona mata asiri cikin jama,a gaskiya se yanzu na sake tabbatarwa rako mata duniya kikayi basma ta karasa maganar cikin takaici,murmushi rahma tayi tace karki damu basma sam sam raina be baciba sai farin ciki da nayi wlh basma yasmin ta birgeni fiye da yanda kike tunani saboda inason yara marasa tsoro kamar yasmin don haka maganar dana fada miki dazu zamuyi amfani da yasmin gurin armaan malik

"A tsorace basma tace how?taya armaan malik zai so yarinyar da ba yar me kudiba?taya armaan malik zeyi soyayya da yar aiki?murmushi rahma tayi tace daga yau yasmin ta zama yar shugaban kasa saboda duk wani gata da nake samu yasmin zata dinga samu har se ranar da wasan ya qare

"Girgiza kai basma tayi tace amma kuma rahama karki manta akwai game din da baya karewa fah,akwai game din da bashi da level din karshe karfa kizo kiyi abinda zakiyi dana sani,murmushi rahma tai tace karki damu yasmin tana son kudi fiye da komai na tabbata akan kudi zata iya aikata kisan kai,don haka zanyi ciniki da ita don tayi soyayya da armaan malik ta 2 months kawai da zarar wata 2 ya cika toh zata rabu dashi

Don't forget to vote,share and comment

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top