Chapter 5
Hey buddies i'm back
A haka armaan malik yaci gaba da wasa da hankalin kawaye guda 3 rahma,zahra da fadila,cikin lokaci kadan yayi winning zuciyoyinsu ta hanyar sanja sunayensa tare da boye duk wata dukiya da arzikinsa,cikin 2 months armaan ya tura iyayen bogi aka tambayo masa auren dukkanin yammatan inda iyayensu suka amince aka fara shirye shiryen auren nasu gadan gadan.....End of flash back
"Jikin ammi sanyaye ta tura kofar babban katafaren palour din mr president ta shiga zaune yake yayi tagumi,saurin dauke idonta tai daga kallonsa idonta kamar ze zubo da hawaye tace mr president,shiru yayi be ce komaiba sai da ya dauki 2 minutes kafin ya juyo ya kalleta jin ta takura mishi da magana yace what?karasa hadiye apple din data gutsira tayi tace haba mr president tun dazu fa nake maka magana amma kwata kwata hankalinka baya gurina,kallon banza ya bita dashi sannan yace har kina tunanin akwai wani sauran hankali a jikin mutumin da akayi wasa da zuciyar yarsa tilo wacce nafiso fiye da komai a duniya?ajiyar zuciya yayi sannan ya sake kallonta yace wai kamar ni za,a kunyata a idon duniya?ranar da nayi tanadinta tare da kashe makudan kudi wannan ranarce zata zama wulakantacciyar rana a garemu baki daya,wallahi duk wanda ya yaudari rahma idan ya kuskura na ganoshi toh wannan ranar itace ranarsa ta karshe a duniya,mikewa yayi ya nufi dakin rahma ya tura dakin a hankali ya shiga abinda yake tunani shi ya gani domin tun faruwar wannan alamarin kullum rahma cikin kuka take
"Tsayawa yai a kanta zuciyarsa a matukar bace yace princess,sai a lokacin ta dago da kanta ta kalli mahaifinta mr president tace yes dad,sai a lokacin ya zauna a gefen gadon ya kalleta yace stop crying indai kudi da mulki suna aiki a kasar nan nayi miki alkawarin zanyi amfani da kudi da karfin mulkin da nake dashi don na gano wanne yaron ne yayi wasa da hankalinmu ya yaudareki,sake fashewa tai da kuka kamar karamar yarinya tace dad do something please shahid ya cuceni ya cuci rayuwata ya cuci rayuwar duk wani mai kaunata do something please dad.....shima ji yayi kamar hawayen zasu zubo masa a idonsa yace I promise sannan ya fita daga dakin bakinsa na maimaita sunan shahiddddd
"Komawa tayi ta kwanta ta janyo wayarta wadda take yau kwana 2 kenan a kashe ta kunna,text messages sama da 100 ne suka shigo a hankali ta fara bi tana karanta fatan alkhairi daga mutane daban daban masu taya ta jimami nayi masu yi mata Allah shi kara ma sunayi,tsaki tai ta fita daga text message ta bude whatsapp messenger sama da 1000 messages ne suketa shigowa rufe idonta tai tace ohh shit!idontane ya kai kan wani group chat da aka hada wanda aka bashi suna LADIES da sauri ta bude ta shiga ganin fadila ne kawai da zahra sai ita a ciki ya bata mamaki,cikin sauri-sauri ta fara karanta chats din zuciyarta na bugawa da sauri,what ta fada da karfi ta mike daga kwanciyar da tayi tana sake maimaita shahid...jameel...fahad duk mutum dayane but how?
"Contacts ta shiga tai dialling number zahra bayan ta daga ne ta hada musu conference call da Fadeela kamar a mafarki suke tabbatarwa rahma tabbas mutum dayane yayi wasa da hankalinsu kuma ba kowa bane sai armaan malik,wata razananniyar kara tayi cikin tashin hankali tace babes nayi muku alkawarin kafin nan da 10 hours duk inda armaan malik yake zansa dad yasa a kamoshi i promise,murmushi zahra tayi tace easy monkey armaan malik da kanshi yayi wasa da hankalinmu ba tare da yasa kowa cikin aikinsaba,meyasa muma baza muyi amfani da kanmu ba domin mu rama abinda yayi mana......of course jaanu fadila ta fada tana sake amincewa da maganar zahra,itama rahma ajiyar zuciya tayi saboda ta yarda da maganar zahra sedai kuma ta yaya zasuyi wasa da hankalin mutumin da yayi wasa da hankalin mata zafafa har guda 3 it's impossible,,,,,dariya zahra tayi tace it will be possible and simple idan har zaku bani goyon baya 100%,shiru sukai suna sauraren zahra ta nisa kadan tace idan har zamu iya samun kyakkyawar yarinya wacce ta kasance tar talakawa toh zamuyi amfani da kudi mu sata yin soyayyar karya da armaan malik,daga lokacin daya fada tarkon soyayyarta a lokacinne zamu sata tayi breaking heart dinsa kamar yanda yayi broken heart dinmu
"Ihu sukayi sosai don sun yarda da plan din zahra 100% sedai yanzu wacce yarinyar za,a samu wacce har armaan malik zai fada tarkon sonta,samun yarinyar da armaan malik ze karbi soyayyarta abune mai matukar wahala domin bai kasance irin cheap person dinnan ba,sunyi kusan 2 hours suna waya kafin suyi sallama zuwa kwana 2 kowa ya nemo yarinyar daya kamata suyi amfani da ita gurin yin wasa da hankalin armaan
"Dogon hijab ne har kasa jikinta ash colour wanda yai iri daya dana kawarta wacce suke tafiya tare da alama daga islamiyya suka dawo,mardiyya ce ta taba yasmin cikin fushi tace nifa wlhy bazai yiwu mu dinga tafiya kamar wasu kurame ba,ke kullum idan aka taso daga islamiyya seki toshe kunnenki da earpiece kina jin waqa ki bar mutum yayi shiru kamar kurma,dariya yasmin tai tace kanki akeji nifa wlh indai da waya a hannuna to bani da wata damuwa.....bata karasa magana ba wata hadaddiyar mota tai parking a dai-dai paloma event center,wata kyakkyawar yarinyace ta fito sanye da wata gown royal blue wadda tai fitting jikinta sosai kafarta sanye da wani heel shoe peach colour sai hannunta rike da iphone 14 pro max da alama live video takeyi a instagram,"bura uba"yasmin ta fada ba tare da tasan ta fadi hakan ba sannan ta kalli mardiyya dake gefenta tace Mardy kalli wata hadaddiyar yarinya yanda kwalliyarta tayi mugun birgeni
"Dariya mardy tai tace kanki akeji kedai kinsan ramin kura ba gurin wasan yaro bane,keda ganin wannan kinsan yar gidan babban me kudice kuma kina ganin gurin bikin nan kinsan bikine na manyan mutane,hade rai yasmin tayi tace koma dai wacece ai bata kai yar gidan shugaban kasa ba ko?sake bushewa mardy tai da dariya tace toh nufinki ke yar gidan shugaban kasace wai?harararta tai tace eh mana seki fadamin banbancin yar shugaban kasa da kuma wacce takeyin aiki gidan shugaban kasa,don wlh idan nai niyya zan iya yin kwalliyar da tafi wannan tsada da komai,tsaki mardy tai tace karyar banza ta ina zaki samu kudin da zakiyi wannan kwalliyar?murmushi yasmin tayi tace ina zuwa....matsawa tai kusa da masu gadin paloma event center ta tambayesu gobe wanne event din zaayi,anan ne suka fada mata bridal shower zaayi da karfe 8 na dare......kallon mardy tai tace gobe karfe 8 na dare ki zauna cikin shiri zakisha mamaki,daga nan sukayi sallama yasmin ta shiga presidential villa
"A kwance ta tarar da anna da alama bata jin dadin jikinta,bayan ta cire hijab din jikintane ta kalli anna tace anna ya zazzabin naki?da sauki ta fada a takaice sannan ta kalli yasmin tace maza kije ki gyarawa rahma dakinta yau banajin dadi bazan iyaba,tamkar an zuba mata ruwan sanyi a zuciyarta tace toh anna sannan ta nufi kofar fita zuciyarta cike da zumudi,anna ce ta kira sunanta a hankali tace yasmin,juyowa tai cikin rashin fahimta tace na'am......don Allah yasmin idan kinje gyara mata daki kawai zaki ki fito banaso kice zakiyi wani abu da zesa kija min zagi,turo baki yasmin tai tace toh anna sannan ta fita daga dakin ta nufi apartment din rahma
"Bata tarar da kowa ba a dakin ta fara gyare-gyare sai data gama gyara komai tukunna ta kalli kanta jikin mudubin rahma murmushi tai tace wlhy ni ya kamata na zama yar shugaban kasa ba keba aunty rahma,jikin closet ta nufa ta janyo wata hadaddiyar gown red colour sai wani heel shoe black colour wanda yayi matukar kyau da tsada,sai data gama gwada kayan jikinta sannan ta saka cikin leda.....drawer ta bude taga tarin dollars ciki ita kanta kudin ya bata tsoro sedai rawar kai irinna yasmin ya sata dauki rapper guda daya cikin kudin sannan tai murmushi tace saboda liqi....bata bari anna taga kayanba ta boyesu bayan taci abinci ta kwanta zuciyarta cike da farin ciki
"Washegari tun karfe 6 na yamma yasmin ta bar gida ta nufi gidansu mardy saboda ananne zata shirya cikin kwanciyar hankali ba tare da kowa ya gantaba
"Bayan rahma ta fito daga wankane tai light makeup kadan ta nufi jikin closet,sedai jikinta ne yayi sanyi ganin bata ga kayan data ajiye wanda zatasa da bridal shower din kawarta mufeedah ba,cigaba tai da dubawa tana matsanancin mamaki ganin har 8 ya kusa rahma bata fitoba yasa ammi shiga dakinta ta tarar da ita zaune jiki mirror tana tunani,da sauri ta taba rahma tace lafiya kika zauna rahma kina kallo guards dinki na waje suna jiranki......tsaki rahma tai tace ammi kinsan shekaran jiya nai order din red gown wacce itace ankon bridal shower din a wani babban mall a london da wani shoe wanda a kalla yakai 1000 dollars sune nake ta nema ban ganiba.......itama mamaki ammi tai tace rahma nasan shirmenki may be kin jefasu a wani gurin don haka kawai ki dauki wasu kayan ki saka tunda kinada red gowns dayawa,,,,duk da ba haka rahma taso ba amma dole ta dauki wasu kayan ta saka sannan ta nufi parking space
Hahahahaha dariya ya hanani in kara rubuta komai wlhy........team yasmin there is God oooo🤣
Thank you for reading my story!!!
Don't forget to vote,share and comment
Heroine
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top