Chapter 3

"A daren armaan malik ya gama magana da doctor Abdallah da sauran duk wani shirye-shiryen da zasuyi don komai ya tafi dai-dai akan basajar da zeyi na likitan bogi

"Ta dade cikin bathtub tana yin wanka sannan ta fito daure da towel a jikinta daya kuma ta daure jikakken gashinta dashi,inda telephone take ta nufa ta fara kiran housemaid din gidan,earpiece ne kunnenta hannunta rike da waya ipad tana rawa tana jin waqa sosai take nishadi don yasmin ma,abociyar jin waqace da duk wani abubuwan more rayuwa,da sauri anna ta karaso dakin da yasmin ke rawa ta fisge earpiece din kunnenta tace ke yasmin,a firgice yasmin ta yarda wayar dake hannunta tace lafiya anna kika shigo da gudu kika ciremin earpiece?

"Tsaki anna tai tace yasmin ina ganin kin kusa yin silar dena aikinmu a cikin gidannan,tun daga kitchen nake jiyo karar telephone din chan a kalla anyi kira ya kai goma amma kina nan kin toshe kunnenki kina jin waqoqin banza da wofi wanda bazasu amfaneki da komaiba sai matsala,murmushi yasmin tayi sannan ta kalli mahaifiyarta tace toh kiyi hakuri anna nasan nayi lefi amma ki dena cewa wakokin banza nakeji wannan fa sabuwar waqar kizz daniel ce kuma tana da dadi sosai,kallon yasmin tai cikin bacin rai tace ke kika sanshi ni bansan shiba yanzu zaki wuce kiran da rahma take miki ko kuma seta karaso da kanta?zaro ido tai tace anna dama aunty rahma ce take kirana ban daukaba?na shiga 3 na lalace.....da gudu ta dauki hijabi ta saka ta nufi apartment din rahma tana matukar haki

"Ta dade tana knocking kafin rahma ta bata damar shiga dakin,zubewa tai a kasa kamar me neman gafara tace aunty rahma kiyi hakuri dazu kinata kiran telephone ban dauka ba sallah nakeyi lokacin,murmushi rahma tai cikin takaici ta kalli yasmin tace tashi kije ki dauko min tsinanniyar wayar da take hanaki yin ayyukan gidan nan,wato ni zaki rainawa hankali kina chan kinajin waqoqin da kika saba ji baki da lokacin da zaki daga min waya shine zakice min sallah kikeyi ko?toh yanzun nan kije ki dauko min wayar

"Gaban yasmin ne ya fadi don idan akwai babban tashin hankalin da take tsoro shine a rabata da farin cikinta wato wayarta,zaro ido tai wanda tuni ya cicciko da hawaye tace don Allah........saukar marin da tajine ya hanata karasa magana cikin masifa rahma tace maza jeki dauko min wayar don't waste my time,jikinta sanyaye ta mike da kyar kafarta ta dauketa zuwa apartment dinsu na masu aiki,ganin hawaye a idonta yasa anna mikewa tsaye a tsorace tace lafiya yasmin?me rahman tai miki har kike zubar da hawaye haka,nasan dai dukanki tai kuma duka da mari ai ba bakon abu bane a wannan jikin naki don tun kina yarinya kika saba da duka kuma baki taba zubar da hawayeba sai yau yasmin?ajiyar zuciya tayi tace anna kema kinfi kowa sanin duka ko wata masifar gidan nan bata isa ta sani cikin damuwaba babban abin damuwata shine a rabani da wayata,,,,ajiyar zuciya anna tayi tace cewa tai ki kai mata wayar ne?daga kanta tayi tace eh sannan ta daga karkashin pillow ta dauki wayar ta fita zuciyarta a matukar bace ta ajiyewa rahma wayar ta fita tana kuka

"Dawowa daki tai ta zuba tagumi taci gaba da kuka,tsaki anna tayi tace ke nifa kin isheni da kuka don kawai an karbi wayarki shine ze zama abin kuka,turo baki tai tace au haka ma zakice anna yanzu shikenan na dena jin waqoqin kizz  daniel dina?yanzu shikenan na dena karanta littafin duniya zamani wanda marubuciya mardy bounce takeyi?sake faskewa tai da kuka kamar wata karamar yarinya duk da dama yasmin karamar yarinyar ce shekarunta basu wuce 15 ba,kwarai da gaske nifa dama yasmin don dai kawai banason rigimar kine  amma banason ki da rike wayar nan ace mutum kullum cikin jin waqoqi ya toshe kunnensa kamar wani dujal yana rawa,inko bakya jin waqa to waya na makale hannunki kina karatun littafin hausa wani lokacin ma duka biyun kike hadawa ina dalili?rayuwarki tanaso ta lalace a banza kin dauki kyale-kyale da gayu kin sawa kanki kina jin kanki kamar kece yar gidan shugaban kasar toh ina kara tuna miki keba kowa bace sai yar aikin gidan shugaban kasa mahaifiyarki ma haka,mahaifinki kuma me bawa shukoki ruwane a gidan shugaban kasa,turo baki ta sakeyi tace anna wai kinji nace wani abune ni don Allah ki barni da takaicin rashin wayar nan kawai....

"Sanye take cikin jumpsuit brown colour hade da wanda yai matukar yi mata kyau,guards 2 ne a bayanta suka bude mata mota ta shiga sannan driver ya fara aikinsa,karfe 12 rahma ta karasa asibitin,direct office din doctor Abdallah ta wuce sedai ganin akasin doctor Abdallah ya sata fara tunanin ko tayi kuskuren shiga office din wanine?jin motsinta ya sashi juyo da fuskar kujerarsa fuskarsa dauke da murmushi cikin hadaddiyar farar labcoat yace hey,gabanta ne yai mummunan faduwa taci gaba da kallon kyakkyawar halittar da zata iya cewa tunda tazo duniya bata taba ganin namiji me kyau kamarshi ba duk da irin yawon kasashen duniyar da takeyi......what a miracle!!!ta fada a hankali sannan ta zauna muryarta na rawa tace hey,,,,wayartane ya fara kara a hankali ta kara a kunnenta ganin sunan doctor Abdallah.....ok doctor kawai ta fada sannan ta kashe waya

"Kallonta yayi cike da kwarewa yace i,m doctor shahid nine zanci gaba da kula da lafiyarki a asibitin nan ammafa idan kin amince,toh waima meze hanani amince kyakkyawan saurayi kamarka yaci gaba da yimin check up ta fada a zuciyarta amma a zahiri kallonsa tai cikin basarwa tace zanyi tunani sannan ta mike zata fita,har taje bakin kofa armaan yai saurin rike kofar yace ranki ya dade idan kin amince din ai babu wata hanya da zan gane haka mezai hana ki bani number da zan kiraki don tambayarki idan kin amince,dagowa tai ta kalleshi a zafafe tace ka kiyayi kanka da gangancin shiga rayuwata ba tare da kasan dawa kake tareba,murmushi yayi yace sanin ina tare da rahma hayat bagadaza kyakkyawar yar shugaban kasarmu shiyasa nake sake kiyaye duk wani abinda baza kisoshiba......ganin yana kokarin bata mata lokaci ya sata bashi number sannan ta fita zuciyarta na tunanin kyakkyawan doctor shahid

"Ganin yasmin ta shiga damuwa yasa anna cire simcard dinta daga cikin wayarta tecno ta cillawa yasmin tace gashinan nina hakura saura kuma kici gaba da jin wakokin naki har a sake kwacewa,tsalle tayi ta haye cinyar anna tana ta godiya,sai data tabbatar ta jona wayar a chaji kafin ta shiga tai wanka ta fito ta zauna ta bata lokaci tayi makeup sannan ta dauko shirt da jeansy trouser ta saka,tagumi anna tai tana kallon yasmin,haba anna me kuma nayi kikai tagumi kina kallona yasmin ta fada tana zama a kusa da anna,ajiyar zuciya anna tayi tace yasmin ina mamakin yanda kike da rawar kai sannan ina kallon irin yanda kike da fitinannen kyau me daukan hankali,ihu yasmin tai har tana tsalle tace anna basa banba yau dai kince ina da kyau amma meyasa kike damuwa akaina?ba damuwa nake akanki ba yasmin se ganin yanda kika dauki rayuwarki a cikin gidan nan na fuskanci jin kanki kike kamar yar shugaban kasa,lumshe ido yasmin tai tace toh anna idan banyi abinda nakeso ba me kikeso nayi karki manta fa irin rayuwar takurar da mukai a duniyar nan yanzu kuma mun samu muna aiki a gidan shugaban kasa ai dole mu saki jiki muci arziki,kinga anna yanzu nasan aunty rahma ta kusa dawowa kuma banje na gyara mata dakin ta ba,tana gama fadar haka ta dauki wayar da anna ta bata ta nufi apartment din rahma

"Sosai ta gyarawa rahma daki ta feshe da air freshners masu kyau har taje bakin kofa tai saurin juyawa ta koma,jikin dressing mirror din rahma ta tsaya ta shafa powder sannan ta feshe jikinta da perfumes masu tsada tai murmushi jikin mirror din tace ina matsayin yar aiki a gidan shugaban kasa ya zama dole naci arziki nima kuma dole nai aiki da kaya masu tsada,wardrobe din rahma ta bude ta dauko wata hadaddiyar doguwar riga ta saka tai rolling da mayafinta duk da tsayin rigar da yayi mata yawa....wayarta ta dauko ta haye gadon rahma ta fara yin selfie tana sanja styles kala-kala idan ta dauki hoton sai tayi tsalle tace slay queen

"Har ta bude dakin ta shiga amma yasmin bata kula da hakan ba,bude baki tai tana kallon yasmin sanye da kayanta a tsakiyar gadonta tana selfie pictures hade da videos ba tare da tasan ta shigoba

Thank you for reading my story
Vote,share and comment
Heroine

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top