Chapter 11
Armaan ya karaso presidential villa be wani sha bincike gurin securities ba saboda yana shiga yake nuna identity card (ID card) dinsa,tunda armaan yayi parking motanshi su rahma suka sake tabbatarwa lallai armaan ya cika cikakken butulu kuma mara kunya,ganin rahma ta shiga wani yanayi na damuwa yasa fadila tabota a hankali tace cool down karki damu indai armaan malik ne yana gab da shiga hannunmu meye zaki zauna kina damuwa?sai da rahma tayi ajiyar zuciya tukunna tace i know fadila ina sake mamakin yanda armaan yake marar kunya kenan har ya manta sanda yake zuwa gurina a cikin gidan nan har ya iya dawowa a karo na 2?murmushi fadila tayi tace he's a playboy zeyi abinda yafi hakama,turo kofar yasmin ne yasa gaba daya mayar da hankalinsu wajen kallonta a tare suka hada baki sukace wow what a mind blowing!rigane peach colour sai turban shima peach wanda yayi matukar dacewa da jikinta,babu wani heavy makeup a fuskarta kadan tayi light makeup,ganin yanda suke kallonta yasata jin kunya kadan sannan ta kalli rahma tace yazo yana waje,murmushi rahma tayi wanda kana kallo kasan a dole tayi creating wannan murmushin tace good girl you can go,juyawa tayi ta fita jikinta a sanyaye kadan inda gaba daya matan hankalinsu ya karkata gurin babban window din da ake hango parking space din gidan don ganewa idonsu fitowar armaan malik daga cikin mota
"Range rover 2020 model maroon colour itace motar da armaan malik yayi parking,dark blue shirt da black trouser shine jikin armaan sai wani top colour din rigar da yayi matukar yi masa kyau,tunda ta karaso gabanta yake faduwa ta rasa dalilin da yasa duk sanda ta hada idonta da armaan malik sai gabanta ya fadi,se dai har yanzu ta kasa nuna masa tsantsar tsanar da takeyi masa a cikin zuciyarta,tun ranar dasu rahma sukayi mata bayanin pain dinda armaan malik ya saka musu a zuciyarsu taji ta tsaneshi ta tsani duk wani namiji da zai yaudari ya mace ba tare da wani daliliba,itama kuma tana da tabbacin yana gab da yaudarartane ya gudu ya barta,ajiyar zuciya tayi sannan ta dawo daga dogon tunanin data tafi jikinta sanyaye ta bude motan ta shiga idonta ya sauka akan kyakyawan extra-ordinary hot eyes dinsa sannan ta shaqi hadadden kamshin perfume dinsa,saurin yin murmushi tayi tace hey,kallon yasmin yayi ji yayi gaba daya ya kasa ce mata komai,meyasa yasmin ta zabi rayuwar karya?kuma meyasa rahma ta kasa daukan fansar abinda yayi mata har seta turo masa wata?murmushi yayi wanda ya bawa dimple dinsa damar lomawa sannan yace mata hey,wayanta ta dauko cikin isa da gadara tayi dialing number sunan sweet dad yayi appearing a kyakkyawan screen din wayar,cikin shagwaba tace hey dad,nifa gaskiya na gaji da abinda akeyi min tun yaushe na fada maka i need to talk to you amma har yanzu na kasa samun damar da zamuyi magana,shiru ta danyi alamar tana sauraron abinda ake fada from the other side sannan ta sake ajiyar zuciyar cikin shagwaba tace i know dad amma dai kasan being a president daughter sucks lots of things ko?don kawai ina yar gidan shugaban kasa shikenan kullum bazan samu cikakken time din yin magana da kaiba dad?i told you since yesterday dad.....shiru tayi sannan ta katse wayar bayan tayi tsaki tace fuck up!
"Sosai yasmin ke kokarin bawa armaan dariya sedai babu damar yi a dole ya kalleta cike da kulawa yace what's wrong with the world best cutie face?turo baki tayi cikin shagwaba tace wlh nida dad ne tun jiya fa na fada masa cewar na hadu da guy din dana keso kuma inaso ku gaisa da dad dina amma sam dad bashi da time din kowa sena aikinsa gaskiya ni banason haka yanzu na kirashi yana fadamin zasu shiga meeting da wasu governors ne kenan wasu mutane daban sun fimu a gurinsa?shiru yayi kadan yace it's okay you know you are beautiful right?turo baki tayi alamar rashin yarda sannan yace kuma kinsan beautifuls are always happy banaso inga kina fushi got it?daga mishi kai tayi alamar yeah sannan armaan yayiwa motar key.......
"Fashion paradise nan ne inda armaan ya kai yasmin ya dinga siya mata kaya har abin ya fara bata tsoro,duk abinda ya kai hannunsa kawai dauka yakeyi tun tana biye masa har ta rabu dashi yaci gaba da siyayyar kayan,sun dade ciki sosai suna siyan kayan kafin su fita,sun dade suna yawo da yasmin ita kam banda kallon armaan babu abinda takeyi cike da mamaki,lallai armaan dole ya sace zuciyarsu rahma saboda ko kallonsa kayi you will feel blessed,komai nashi daban yake sannan komai armaan yanayi ne cike da nutsuwa sam bashi da hayaniya,5:20pm armaan yayi dropping yasmin tare da uban kayan daya siya mata sannan ya wuce gida saboda dad dinsa ya kirashi yanason ganinsa
"Cikin sallama ya karasa inda yake expecting dad din nashi yana nan,zaune yake kamar yanda ya saba yana shan coffee gefe daya da cookies a cikin plate din sai fruits dake ajiye a gefe,sallama ya sakeyi sannan ya zauna cikin ladabi yace dad barka da hutawa,murmushi alhaji malik yayiwa dan nasa bayan ya cire karamin AirPods din dake kunnensa da alama yana recording wani abunne sannan yace armaan an dawo?murmushi armaan yayi yace yes dad na jima da dawowa ma na leqo naga kana aiki da system shiyasa na koma sai da nayi sallah tukunna,girgiza kai yayi yace gaskiyane yau tun dazu inata aiki kasan gobene zamu gama contract dinmu da S&H enterprises,zaro ido armaan yayi yace seriously dad gaskiya aikin yayi sauri sosai best of luck! Bayan sunyi hira kadanne alhaji armaan ya gyara zamansa bayan ya cire medicated glass din idonsa yace armaan dama inaso zamuyi magana ne mai mahimmanci akan zancen aurenkane kamar kullum dai kasan maganata bata wuce kayi aure yanzu babu abinda kake bukata sai aure,murmushi armaan yayi hakan ya bawa alhaji malik mamaki ganin duk sanda zeyiwa armaan maganar aure toh karshe sedai ya fita ransa a bace amma yau cikin murmushi yake kallonsa haka?gyara zama yayi yace dad indai zancen aurenane daga yau ka dena damun kanka you have to stop worrying about it,na samu yarinyar da nakeso idan komai yayi dai-dai zaka jita very soon,murmushi alhaji malik yayi yace serious?daga mishi kai yayi yace yes dad I'm serious,shima dariya yayi yace toh masha Allah yarinyar wanne gidane kuma yar waye?shiru armaan yayi wanda yasa gabansa muguwar faduwa ba tare da yasan dalilin yin hakan ba yace toh gaskiya dai dad bamu dade da haduwa da itaba har yanzu dai ina bincike akanta amma idan na gama bincike zakaji ko wacece dad,cikin mamaki alhaji malik ya kalli armaan yace armaan wannan wacce irin maganace?yanzu fah kake fadamin ka hadu da yarinya har kun daidaita kuma kana fadamin cewar zakayi bincike akanta,kenan ko inda take baka taba zuwaba kenan?shiru armaan yayi wanda hakan yasa dad gano rashin gaskiya sosai a fuskarsa yace tashi ka bani guri armaan ni dama nasan tunda mahaifiyarka ta rasu har yanzu bazan taba samun wanda ze maye min gurbintaba na farin ciki hakan shine dalilin daya hanani yin aure kuma kaima bazan takura makaba you can go,jikin armaan sanyaye ya kalli dad din nasa wanda a yanzu shine kadai ya zamo masa mudubin dubawarsa na farin ciki kuma yana alfahari da mahaifinnasa amma meyasa yake yawan batawa dad din nasa rai?cikin damuwa yace I'm sorry dad baka fahimceni bane....cikin tsananin zafi da bacin rai yace i said get out armaan
"Cikin tsananin mamaki yammatan ke bude kayan da yasmin ta shigo dashi tun suna iya magana har dukansu sukayi shiru banda kallo babu abinda sukeyi,fadila ce tace hey guys,,,,sai lokacin rahma tai dariya tace we are dead...a tare suka yi dariya sukace good job yasmin inda sukaci gaba da daukan labari a gurin yasmin.....sai bayan magrib tukunna ta karasa bangarensu direct wanka tayi sannan ta dauro alwala ta gabatar da sallar magrib,kallon anna tai cikin shagwaba tace anna ina abincina?cikin damuwa anna tace tab ai kuwa babu abinci don yau gidannan anata yin baki shiyasa ma banyi kokarin ajiye miki abinciba sedai yanzu ki tashi ga 500 chan akan fridge ki dauka ki kaiwa babanki a waje kice masa nice banda lafiya ya karbi kudin ya siyo min wainar shinkafa inba hakaba kinsan ba zuwa zeyiba,murmushi yasmin tayi inda tausayin mahaifiyartata ya shiga zuciyarta sedai a zuciyarta wani irin murmushin mugunta yasmin tayi tace anna kenan bakisan level don change ba ai yanzu idan abincin president ko first lady naga dama toh dole su bar min,amma a zahiri kallon anna tayi tace toh bari inje don wlhy kinsan yunwa nakeji sosai kuwa Allah yasa dai inga baba a wajen kinsanshi sarai akwai son yawo,dukanta ta danyi kadan tace kaniyarki baban nakine me yawo
"Driver ta kira cikin isa,da sauri ya bude mata mota ta shiga ya fara driving seda ya fita daga gidan ya kalleta yace ina mukayi?seda ta dauki kusan 3 minutes cikin jin kai da rainin hankali tace mishi 5 star hotel zaka kaini inci abinci
Thank you for reading my story!
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top