Tara

Da hanzari tabi bayanta tana kwalla mata kira, "Hafsah! Zo nan, dawo karkije ki fadi!" Da dariya take maganar tana bin bayan yarinyar. Tunda take a rayuwarta, tun bayan da Hanan ta rasu Lubnah kuma ta kawota gidansu bata taba irin wannan farin cikin ba. Ita duk aikin da Hafsar ma ta saka ta ba damunta yayi ba, ganinta da tayi, wasan da sukayi tare, rigima da komai da komai ya wadace ta.

Sannan barna irinta Hafsah na dan zaman da sukayi yasa ta bita itama da dan gudunta. Hanyar garden din gidan taga ta nufa, binta take tana kiran sunanta amma Hafsah wasanta kawai takeyi. Koda ta isa garden din ganinta tayi zaune saman cinyar Rayyan, ita gabanta ma har faduwa yayi, dan ta manta yaushe rabon data ganshi cikin gidan.

Ganin Lubnah na wajen itama zaune yasa ta taka ta isa wajen, "Yi hakuri dan Allah, Hafsah tashi muje." Ta mika hannu da niyyar tazo su tafi amma yarinya ta mak'e kafada, dama abu Rayyan yake nuna mata a wayarshi.

"Emma nakeso naga ko taci abinci yau, Ammi. Nasan Abba bai bata abinci ba, kila ma har wanka tanaso tayi kuma bai mata ba." Hafsah ce ke magana ko kallon inda Ramlah take ma batayi, idonta kyam akan Rayyan dake kokarin mata downloading My Emma a wayarshi.

"Su Ramlah fa anyi diya, ban taba ganin dariyarku irin ta yau ba. Yaushe Dr Aliyu zaizo daukarta? Ko sai dare? Kila ma ya bar maki ita ta maki weekends ko?" Lubnah ce ke magana da sigar wasa tana yar dariya, wanda itama Ramlah ta mayar mata da dariyar da takeyi.

"Aa fah, anjima kadan zaizo daukarta. Gidan iyayen mamarta zasu kaita ma wannan short term break din, yace mun ta kwana biyu bataje ba." Abunda ta furta kenan tana murmushi sannan ta koma wajen Hafsah.

"Taso muje Hafsah kinji? Kinga ko ya maki downloading Emma din ba taki bace ba, muje na maki da wayata." Da kamar bazata taso ba sai kuma ta taso a hankali tana kallon Rayyn dake mata murmushi.

"Idan na kara zuwa zan ganka?" Abunda ta tambaya kenan da irin kallon alkawarin nan na yara.

Murmushi yayi ya shafa mata kai, "Eh Hafsah, kafin ki dawo zansa wannan Emma din ta girma sai suyi kawance da taki, kinaso ko?"

"Eh inaso. Bye!" Hannunta da Ramlah ta janyo yasa ta mashi waving da dan murmushinta da haka Ramlah ta jata suka tafi dakinta.

Zama sukayi kan gadonta ta janyo wayarta tana mata downloading my emma ita kuma sai bata labari take. Ji takeyi kamar tare take da Hanan bawai Hafsah ba. Bayan ta gama mata downloading suka zauna suna game din, Hafsah sai korafi take akan wai wannan jaririya ce, ita diyarta ta zama yar budurwa. Saida Ramlah ta mata alkawari cewar zata rikayi har ta maidata yan mata kafin ta kara dawowa.

Har saida sukaci abinci dare a daki tare sannan taga kiran Dr Aliyu ya shigo wayarta. Dauka tayi yace mata yana kofar gida kafin ta tashi ta kimtsa Hafsah da ledar kayan zak'in data kwasa mata gaba daya suka sauka kasa. Saida Hafsah tama Lubnah da Mama kafin tana hannunta suka fita waje.

Hangoshi tayi ya jingina da motarshi yana kallon kofa alamar jiran fitowarsu yakeyi. Da murmushi suka karasa wajen motar. Da gudu Hafsah ta ruga ta rungumeshi tana ihun murnar ganinshi, "Abba nah!"

Dukawa yayi ya kawo daidai tsayinta yana murmushi, "Na'am diyar Abban ta, kinyi kewar Abbanki ko?"

Dariya tayi ta rungume shi, "Na danyi kadan, amma Ammi bata bari nayi da yawa ba." Har zaiyi magana tayi saurin tareshi, "Abba, ina my Emma dita? Ka bata abinci? Ka mata wanka?"

Dariya yayi ya mike tsaye yana ciro wayarshi daga aljihu, "Naga dai tanara magana wai wanka takeso kuma tanajin yunwa, amma Hafsah ban iya ba. Yanzu dai ga wayar ki shiga mota kiyi zanyi magana da Ammin ki, kinji?" Koda yace Ammi saidai yaji maganar wani iri, da hanzari ta karbi wayar ta shiga mota shi kuma ya karasa inda Ramlah tayi tsaye tana kallonsu da murmushi akan fuskarta.

"Ina yini?" Ta fada da murya mai sanyi.

"Lafiya lau, Ramlah. Nasan yau duk ta baki wahala ko?" Ya tambay yana yar dariya, itama dariyar tayi kafin ta girgiza mashi kai.

"Kai haba, na saba ai indai halin yara ne, bata ma da rikici kamar Hanan." Tana fadin haka sai kuma tayi shiruyasan yau zaman da tayi da Hafsah tabbas sai ya tuno mata da Hanan, amma kuma hakan zai kara taimaka mat wajen tabbatar ma kant cewar fa babu maganar Hanan har abada zata samu salama cikin ranta.

"To nagode, Ramlah. Sai mun hadu ranar litinin ko?" Dan daga kai tayi alamar eh kuma tana dan murmushi, "Zan iya kiranki ko zuwa anjima?" Ya tambaya a hankali, da alamu yana tsoron jin abunda zata amsashi da.

Kamar bazata amsa shi ba sai ta wayince ta dan daga kanta, "Eh, nagode sai anjima." Da hanzari ta koma cikin gida shi kuma ya bita da ido yana murmushi, mamaki ma abun ha bashi to wai hakan na nufin kunya taji ko miye? Wani murmushin ya saki kafin ya koma mota Hafsah na game tana bashi labarin Amminta.

Ramlah tana shiga daki kawai kwantawa tayi kan gado kawai ta fada, wani abu ne ya tunkuro mata a zuciyarta wanda batasan yanda zatayi dashi ba. Kuka takesan tayi amma hawayen nata kamar wani yace karsu kara ziyartarta. Kamar wasa kawai taji bacci ya dauketa.

Kamar a mafarki ta farka ta fara ihu tana wani irin gunjin kuka, dama dakunansu kusa suke da na Lubnah, kuka kawai take tana fizge fizge kamar ranta zai fito. Da hanzari Lubnah ta shigo dakin ta ganta kan gado duk ta fita hayyacinta. Rungume ta tayi tsam a jikinta tana rarrashinta. Dakyar Lubnah ta samu ta lallashi Ramlah amma kuka take kamar ranta ya fito.

"Ramlah miya faru? Mafarki kikayi ne?" Tambayar da take mata kenan bayan ta mika mata kofin ruwa dan ta sanu hankalinta ya dan dawo jikinta.

Girgiza kai take tana wani kuka me taba zuciya, "Hanan, Lubnah. Mafarkinta nayi, tace mun bataga Abbanta ba, sai kuka takeyi wai in nemo mata Abbanta, Lubnah ya zanyi?" Tunda take bata tabajin d'acin zuciya irin wannan ba. Yanzu ta ina zata fara? Sannan me wannan mafarkin nata yake nufi?

"Ni Ramlah ban fahimta ba, dan Allah ki natsu kiman bayani kila Allah ya bani ikon taimaka maki sai nayi." Jikanta duk yayi sanyi, ita tunda take bata tana ganin mutum irin Ramlah ba. Da taga bata amsata ba sai ma wani kukan data cigaba dayi sai ta kara tambayarta, "Shi Abban nata yana ina?"

Nan ne fa ta fashe da wani mugun kuka wanda har sark'ewa numfashinta yakeyi. Babu yanda Lubnah batyi ba amma Ramlah taki yin shiru, data dan tsaya da kukan sai ta kara fashewa da wani kukan. Wayarta ta dauka ta kira Rayyan, dan ita a ganinta saidai su kaita asibiti.

"Hello? Rayyan nasan dare yayi amma dan Allah ka shigo cikin gida, ina tunanin sai mun kai Ramlah asibiti." Daga haka ta fita dan ta bude mashi kofar. Yana shigowa yaga Lubnah duk hankalinta a tashe.

Fara fada mashi tayi cewar batasan abunda yake faruwa ba amma ta kusa bacci taji kukan Ramlah daga dakinta, tana shiga taga tana rizgar kuka kamar an kara yi mata wata rasuwar. Dakinta suka tafi a tare, zuwa yanzu jikinta har wata girgiza yakeyi.

Da hanzari Lubnah ta karasa kan gadon ta rikota hannu biyu, "Ramlah dan Allah ki natsu kiyi mana bayani."

Kan kujera Rayyan ya zauna yana kallon yadda take kukan kamar ranta ya fito, "Me tace maki dazun?"

Da hawaye idon Lubnah ta jiyo tana kallonshi, dan ita gani takeyi kamar ma mutuwa Ramlah zatayi, dan irin wannan rayuwar bata taba ganin irinta ba. Sai tayi kamar ta warware sai kuma ta dawo sabuwa. "Wai Hanan tace bataga Abbanta ba, tace ta nemo mata shi, ni abun ya fara bani tsoro Rayyan."

Ganin itama Lubnah ta fara kukan yasa ya mike ya tako har bakin gadon. Lubnah tashi tayi ta koma kan kujerar ta hade hannayenta waje daya tana jiran ikon Allah. Zama dRayhan yayi kan bedside drawer.

"Ramlah?" Ya kira sunanta a hankali idanunshi kyam kan fuskarta. Da wani sanyin jiki da kuma tausayi yake kallonta.

Kukan ta cigaba dayi sai can ya kara kiran sunanta, "Ramlah, ki natsu kinji kiman bayani. Hanan ce ta miki magana? Gaya man naji me takeso?"

Juyowa tayi da idanunta jajahe tana kallonshi wasu hawayen na kara zarya saman kuncinta, "Tace mun bataga Abbanta ba, in nemo mata Abbanta. Rayyan zaka nemo mata shi?"

Kuka tke irin na tausayi, "Ina Abban nata yake sai muje a nemoshi kinji? Yanzu dai ki daina kuka kinji?" A hankali yke mata magana da murya me cike da tausayi.

"Abbanta?" Ta tambaya sai ta kara fashewa da wani kukan, "Abbanta ya rasu, tace mun kuma bata ganshi ba, Rayyan ya zanyi? Ko kafin ta mutu tana jin dadin zataje taga Abbanta, ya zanyi?"

Ya rasu? Dukansu suma mutuwar tsaye sukayi. Cikin wani gunjin kuka ta juyo gaba daya tana kallon Rayyan, "Dan Allah Rayyan ku nemo man shi, Lubnah..." ta juya kamar wata tababbiya, "Ku nemo man Abban Hanan, ta ganshi."

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top