Takwas

nafisatuu I love you❤️ As promised.

Ko kallonshi bata karayi ba ta wuce cikin gida, dan ita abunda yake damunta ma yafita karfi. Rayyan ido kawai ya bita dashi har saida ta bace kafin ya wuce ya tafi bangarenshi. Tunani yake wai ita wannan wace irin mutum ce. Yau zai ganta gata nan dai kamar ko wane mutum, wani lokacin ma cikin kwana biyun nan tunda ta fara zuwa koyan photography ya lura ta dan koma daidai, amma yau kuma zai iya cewa ta koma ruwa.

Ramlah tana shiga falo ta iske Mama zaune kan kujera tana kallo, da guntun murmushin da ya kasance wanda tayi amfani dashi wajen maida hawayenta ta karasa wajen Mama ta zauna. "Ina yini, Mama? Ana hutawa?" Ta furta a hankali tana zama kan kujera.

Juyowa Mama tayi da fara'arta. "Ramlah har kin dawo? Nama dauka tare da Lubnah zaku dawo ai."

Girgiza mata kai tayi, "Bata kammala ba, shine Dr Aliyu ya taho dani gida kawai. Bari inje inyi wanka sai na fito, ko akwai abunda za'ayi maki ne, Mama?" Ta tambaya tana mikewa tsaye, dan halin da take ciki babu abunda take bukata daga wuce ta kebe daga ita sai kanta sannan kuma tasha kukanta san ranta.

"Aa ba abunda zaki man Ramlah. Amma dan Allah ki fito muci abinci tare kinji? Bansan zaman dakin nan naki." Dan murmushi tayi ta amsa Mama kafin ta nufi hanyar benen dan ta wuce dakinta. Har kasan ranta take jin Mama da Lubnah, dan yanda suke mata mutum bazai taba cewa ita ba yar'uwarsu bace ta jini.

Tana shiga daki ta tabbatar a rufe yake kawai ta fashe da kukan da saida kirjinta ya amsa. Yanayin yanda taji lokacin dafa rungumi Hafsah shine ya fado mata a rai. Ji take tamkar ita ta haifi yarinyar nan, kuka take tanajin inama ace Hanan dinta bata rasu ba? Da yanzu bata zo Abuja ba, da tana can ita da diyarta suna rayuwarsu.

Wai shin kowa haka yakeji idan ya rasa wani nashi? Dama haka sauran mutane suke shiga kuncin damuwa idan suka nemi wani nasu suka rasa? Mutuwa ta masu yankar kauna?  Tunani take da ace tana da kudin maganin Hanan da ta mutu kuwa? Saurin kauda wannan tunanin tayi domin gudun sab'ama Allah.

Batasan lokacin data dauka tana kuka ba saidai taji karar kwankwasa kofa, "Aunty Ramlah, Mama tace ku take jira kuci abinci." Al'adar gidance, duk ranar juma'a sukan hadu suci abinci tare. Batasan ko haka sukeyi ba tun kafin tazo, amma ita dai tunda tazo haka sukeyi koda kuwa basu da lokaci a ranar to sai sun k'uk'uta sunzo sunci abinci tare.

"Kice mata gani nan fitowa." Da hanzari ta fada bandaki tayi wanka kafin ta fito ta saka wata doguwar riga mai laushi. Ita har mamakin yawan kayan da Lubnah ta siyo mata takeyi, dan ita wasu kayan ma batasan ranar da zata sakasu ba. Barta dai da doguwar riga, dan cika duk tafi saka dogayen rigunan, su kadai ma ta taba sawa. Satin daya gabata ma sukaje aka karbo mata dinki, amma tunda tama kayan kallon farko ta saka durowa bata kara kallo ba.

Saida tayi sallah kafin ta sauka falon, tana sauka ta iske har Rayyan da Lubnah sun hallara wajen suna dan fira, wanda kullum firar tasu bata wuce ta aiki sai daidaikun lokuta ne suke maganar rayuwa. Dan murmushi tayi kafin ta zauna, wacce kujerarta tana kallon ta Rayyan.

"Lubnah har kin dawo? Banji duriyar ki ba." Ta fada tana kallon Lubnah, amma sai kauda ido takeyi dan kar su lura cewar tayi kuka.

"Nazo shiga dakin naji kina kuka, Ramlah. To me zan maki? Sai na kyaleki kiyi ki gama tukunna." Daga gani ran Lubnah bai mata dadi ba, batasan wannan damuwar da yawan kukan da Ramlah takeyi. Tasan kukan rashin wani naka kusan zaa iya cewa wajibi ne, amma kuma daukar kaddara ma wani abu ne.

"Kiyi hakuri, Lubnah, bazan sake ba."

Kamat daga sama Rayyan ha fara magana, "Wannan therapist dinne ai, banga anfanin shi ba nikam. An taba therapist din da kuma zaisa ka kuka?"

Da hanzari ta dago tana kallonshi ga wata harara da take watsa mashi, "Nafa ce maka ba ruwanshi."

"To in ba ruwanshi meya saki kuka? Naga dai yaushe rabon da kiyi wannan kukan naki?" Hararashi kawai tayi bawai dan tasan abunda zatace ba.

"Ramlah rabu dasu kinji diyata? Ai kukan ma rahama ne, kunfi so kuga tana bakin rai ta rasa ahunda ke mata dadi?" Dariya Lubnah da Rayyan sukayi a tare suna fadin, "Su Mama mai diya."

Kusan duk marecen juma'a tare suke yinshi da Lubnah. Wata ranar zasuje saloon, wata rana kuma spa zasuje gaba daya, amma yau tana da babban uzurin wanda haka yasa Ramlah ta rasa me zatayi da marecen ta. Camerar ta dauko tunowa da tayi an basu assignment. Ta rasa ma ina zataje ta dauki hotunan. Fita tayi taje garden din gidan, ranar dataje taga akwai wasu fulawowi masu kyau sosai.

Gashin kanta ta yane da gyalen jallabiyarta kafin ta nufi hanyar kofa. Takawa take a hankali tana kallon wasu hotuna data dauka da camerar. Koda ta isa garden din fulawowin ta fara dauka tana murmushi. Abu na biyu da takeso shine nature. Duk wani abu daya kunci halittar Allah tana matukar sanshi. Hotunan take dauka tana juyawa tana dauka sannan tana kara shiga cikin garden din, ta saita camerar har ta dauka sannan ta lura da Rayyan da yake zaune da wayarshi a hannunshi shima kuma a lokacin ya juya bayan yaji sautin camerar ta.

Saurin yin kasa tayi da camerar tana niyyar barin garden din yayi sauri ya tako inda take. "Hoto kikeyi?" Dan gyada mashi kai tayi a hankali tana niyyar wucewa. "Aa, tsaya mana, dan nace laifin therapist dinki ne sai yasa kike kuka? Fushi ake dani, Ramlah?"

Wata hararar ta kara zabga mashi, ita sai yanzu ta lira bau wanda take harara face shi. "Oh ni Rayyan, da harara na kisa dana dade da mutuwa. Yanzu dai kiyi hakuri."

Tsayawa tayi ta turbune fuska, ita sai yanzu daya furta ta lura bata san abunda yake bata haushi ba. "To yanzu dai kiyi hakuri, me zanyi ki daina hararata dan Allah?"

Girgiza kai tayi a hankali, "Babu. Sai anjima." Sauri Rayyan yayi yasha gabanta. "Ramlah tsaya mana, nasan wani waje nan garin, zai maki dadin daukar pictures, na kaiki?" Yasan hakan kadai zaisa ta dawo daidai, wanda kuka hakan ne ya faru.

Da hanzari ta juyo tana kallonshi, "Dan Allah? Muje!" Da zumudi ta mika mashi camera din, tsayawa yayi yaga me zatayi. Sai yaga ta kwance dankwalin dake kanta, amma ta hanyar da duk kwakwar shi bazai taba ganin gashin kanta ba. Maida dankwalin tayi ta yana shi saman fuskarta. "Muje?"

Har sunzo zasu shiga mota ta juyo tana kallonshi, "Mama, kar tajini shiru." Da dan hanzarinta shiga cikin gidan dan ta fada mata, ba'a jima ba sai gata ta fito da dan murmushi. "Muje, na fada mata."

Shiga sukayi har suka isa wajen babu wanda yama kowa magana. Tana fitowa mora ta fara murmushi, "Wow! Rayyan wajen nan yayi kyau sosai!" Juyowa tayi tana kallonshi da wani murmushi wanda bai taba ganinshi ba.

Rayyan dariya yayi kafin ya kulle motar yazo inda take, "Ashe dai ansan sunana?"

"Zaka fara ko?" Dariya yayi yana daga hannu alamar na tuba kafin ya mika mata camera dinta. Amsa tayi suka taka har inda fulawowin sukafi yawa. Hotunan take dauka sai dariya takeyi. Wani fure ya dauko maikyau ya tako har inda take tsaye ya soka mata shi ta gefen kunne.

Tsayawa tayi kyam tana kallonshi har ya karbi camera din hannunta, "Ban taba gani kina dariya haka ba. Bari kema na maki picture din." Bata mashi gardama ba sai ma kar fadada murmushin da tayi.

Yana cikin daukar hoton wayarshi tayi kara, "Hello? Wake magana?" Ya tambaya yana mika mata camera din, cigabawa tayi da daukar hoton.

Tana tsaye yazo ya mika mata wayarshi, "Dr Aliyu ne ke nemanki, ya kira Lubnah akace muna tare sai ta bashi number ta." Jiki a sabule ta karba tana tunanin meya faru yake nemanta?

Dan matsawa tayi kadan daga wajen, "Hello Dr Aliyu, ina yini?"

Da dan murmushin jin nauyi ya amsa mata, "Lafiya lau Ramlah. Kiyi hakuri na kiraki please, gashi banida number dinki. Hafsah ce keta kuka mun rasa yanda zamuyi da ita wai sai tayi magana dake. Ina fatan ba damuwa?"

Murmushi tayi a hankali, "Lah, wallahi ba komai. Bata wayar dan Allah." Ba'ayi minti daya ba taji muryar Hafsah tana kuka, "Ammi, shine kika ki dawowa ko?"

Wajen dataga wani benci taje ta zauna, "Kai Hafsah ba kinman alkawari baki karawa ba? Indai kinasan ki kara ganina sai kin daina ma Abba da Hajia Mama kuka, ko so kike ince ban kara ganinki?" Daga haka dakyar ta samu ta lallashi Hafsah akan sati me zuwa zatazo mata yawo ranar juma'a.

Tana gamawa ta mike dan komawa inda Rayyan yake sai taga har ya shiga mota. Saida ta zauna cikin motar kafin ta mika mashi wayarshi, "Ga wayar, nagode."

"Muje dai na sai maki waya, Ramlah. Yanzu saurayin naki wayata ma zai kira tsabar bai iya jira." Ita dariya ma ya bata.

"Wai saurayi, Dr Aliyu ne fah." Murmushi kawai yayi ya kyaleta, amma kamar yarda ya fada, daga nan shagon waya suka nufa. Kuma duk yanda Ramlah tayi dashi cewar batasan wayar bai saurareta ba saida ya siya wayar da sim da duk wani abu da ake bukata.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top