Sha Takwas

Koda taga sun kai bakin gate din gidan, dukda batasan gidan waye ba saida gabanta ya fadi. Ji take kamar ta kurma ihu tace masu ta fasa ganinshi ba yau ba. Kila har saita jira ta kara mafarkin Hanan saita tambayeta me zata ce mashi? Da hanzari ta girgiza kai alamar wannan ma ba dabara bace ba. Maigadi ne ya bude masu gate suka shiga har saida Rayyan yayi parking tukunna suka juyo suna kallon yanda tayi sanyi, da alama tsoron abunda zataje ta gani takeyi.

Murmushi Lubnah ta mata daga inda take zaune kafin ta fara magana. "Tsoro kikeji ko?" Ko kokarin musawa batayi ba ta daga mata kanta. "Babu abunda zai faru Ramlah, mu dukkan mu munsan ba'a mutuwa a dawo ai, ko anayi?" A hankali Ramlah ta girgiza mata kai, tunda da ana dawowa ta tabbatar da Hanan dinta ta dawo. "Muje kawai ki ganshi, kuyi magana ya tabbatar maki bashi ne Abban Hanan ba sai ki samu natsuwa." Ganin tayi wani rau ray da ita yasa Lubnah ta juya ta kalli Rayyan da dan murmushinta.

"Rayyan wani lokacin Ramlah tafi jin maganarka a kaina. Bari naje ciki wajen Zainab, ka samu ka lallabo ta, bamu da wani isasshen time." Daga mata kai kawai yayi ta fita motar. A gidan Zainab sukayi mutumin zaizo ya samesu, tunda ita Lubnah bataga dalilin zuwa gidanshi ba haka kawai a hadashi fada da matarshi.

Saida yaga shigewarta cikin gidan kafin ya fito ya zagayo baya inda Ramlah ta zauna jikinta duk ya mutu. Juyawa tayi ta kalleshi a raunane, "Idan bashi bane fa, Rayyan?" Kamar zatayi kuka tayi maganar, hannayenta duk sunyi sanyi rau.

Murmushi ya mata irin mai kwantar da hankalin nan. "Idan bashi bane ba sai mu koma gida ki cigaba da addu'ar Allah ya jikansu gaba daya, kinji?"

Dan daga mashi kai tayi, "Yanzu tashi muje to, kinga bamu da lokaci kar muyi loosing flight dinmu. Daga ni har Lubnah munada aiki gobe, kema zakiyi editing pictures din biki, ko?" Itama sai lokacin ma ta tuna da pictures din biki, a hankali ta daga mashi kai.

Har ta yunkuro zata tashi sai kuma ta koma ta zauna, "To idan shi dinne fah?" Wani kallo ya bita dashi irin 'Ramlah ba mun gama maganar nan ba? Ba'a mutuwa a dawo.' Da sauri ta turbune baki, "Nasan ya mutu kuma ba'a dawowa, to kila ko wani..." dan girgiza mata kai yayi.

"Ramlah dan Allah, wai ko so kike ki saba ma Allah ne?" Girgiza kai tayi kafin da hanzari ta daga fuskarta sama tana fifita idanunta da hannayenta dan kar hawayen da take dannewa su zubo.

Dakyar Rayyan ya samu ta fito motan suka jera a tare. Ita ya jira ta fara shiga sai ga Lubnah ta leko tace mashi ya shigo mana, ai Mukhtar dinma yana nan. Yana shiga ya iske Ramlah tsaye sai kallon Yassar take kamar idanunta zasu fada kasa, kuma basai ya kalleta zai gane cewar gabanta faduwa yake ba haka zalika ta kusa fara wannan kukan nata me daukar rai.

Dan zuwa yayi kuka da ida, "Ramlah, kinga mutumin nan baisan abunda yake damunki ba, ki koma ki dan zauna, kinji?" Kamar wacce aka yanke ma lakka haka ta juyo ta kalleshi ya dan daga mata kai alamar eh kafin ta juya ya mu waje gefen Lubnah ta zauna.

Da a tunaninta zata daure bazatayi kuka ba, amma tana zama ta duke kanta ta janyo dankwalinta ta fara kuka a hankali. Irin wanda yake cin zuciyar nan kuma baka iya fiddo sautin kukan fili saboda mutanen da kake tare dasu. Tanaji su Rayyan suka gaisa da kowa amma ita ta kasa koda kwakwaran motsi.

Dan labarin Rayyan ya fara janshi dashi, tasan kuma duk yayi hakan ne dan ta kara tabbatar ma kanta cewar bafa Abban Hanan dinta bane ba. Tambayarshi yake mahaifarshi wanda ya tabbatar mashi dashi dan maiduguri ne, a nan yayi karatu har ya gama komai nashi kuma yana aiki.

Maganarshi kawai take saurara, yanda yake ma murya, yanda haruffa ke fita daga bakinshi, komai. So take ta tashi ta ruga dan ta gama tabbatar ma kanta da lallai shine Abban Hanan, dan ita amsoshin da yake bawa Rayyan ba sune damuwarta ba, muryarshi da yanda yake maganar sune abun dubawa a wajenta.

Lubnah ce ta dan yi gyaran murya kafin ita da Rayyan a tare suka fara mashi bayani a takaice, hada bashi hakurin kiranshi da abokin shi yayi kuma suna fatan zai fahimcesu tunda ganinshi da kuma yi mashi magana shine zai tabbatar ma Ramlah cewar bashi bane mijinta.

Juyawa yayi ya kalli Ramlah da murmushin tausayi kan labbanshi. "Allah sarki. Wata kila ko kama muke ko? Baiwar Allah ya sunanki?" Sun fada mashi, amma so yake yaji tayi magana da kanta, dan daga yanda suka nuna mashi yasan akwai matsala babba.

Kin dagowa tayi, gabanta faduwa yake, so take ta ruga amma bata da karfin hakan. Ance ba'a mutuwa a dawo ko? To ita yau gashi an mutu kuma taga an dawo. Bata bukatar yardar kowa, amintar da zuciyarta da tayi cewar wannan shine Abban Hanan ma kawai ya isa.

Murmushi yayi ganin bata amsa ba sai ya juya ya kalli Lubnah da take kallonshi da idanu cike da damuwa. "Bai zama lallai ta amsa ba, kaga tama ki dago fuskarta, kuka take tun dazu." Sai yaji ta bashi tausayi.

Rayyan ne kura ma Ramlah ido, ji yake kamar ha dauketa ya kaita wajen da har abada bazata kara tuna wani kunci da bakin cikin dake cikin rayuwarta ba. Baya so yaga tana kuka, wannan damuwar tata ce amma a bude tashi zuciyar shima fal take da damuwa.

Yassar alama yama Lubnah zai iya zama nan kujerar kila ta amsa, daga mashi kai tayi ta mike ta koma kujerar da Zainab take zaune, dukansu sunyi zaune kawai suna kallon ikon Allah. Ramlah kuwa tana jin ya zauna gefenta taji komai nata ya tsaya, kamshin turarenshi har yau bai chanza ba, yanayin yanda jikinta yake mata in tana tare da Abban Hanan, kota mutu bazata manta ba, tabbas shine.

"Sunce sunanki Ramlah ko?" A hankali yake maganar da dan murmushin shi. Tausayi ta bashi, gashi daga gani irin mutanen nan ne wanda idan damuwa ta kamasu to kafin su yakice ma kansu ita sai an dade.

Kukan da takeyi ma ta tsaya, zuciyarta kadai ke bugawa a jikinta itama din tana iya jiyo kararta cikin kunnenta. Cak komai nata ya tsaya. Ganin tayi shiru kusan minti biyar yasa Yassar dan dukawa wajen fuskarta da yar dariya, "Malama Ramlah ba magana? To ko dai gawa ce?" Yanda kasan electric shock ya saka mata a jiki, wani irin zumbur tana jan gyalenta har saida ta bude fuskarta jikinta babu inda baya rawa.

Tunda take a rayuwarta babu wanda yake ce mata haka face shi. Ba ita kadai ba, kowa ma Abban Hanan yana ce mashi haka, saidai baiga kayi shiru ko kana tunani ba, maganar shi kenan, to kodai gawa ce? Girgiza kai takeyi hankali tashi, da hanzari Rayyan da Lubnah suma suka mike tsaye, dan sunsan tsab tana zumburawa da gudu.

Wani sababbin hawaye ne suka fara gangarowa saman kuncinta. Girgiza kai kawai take idanunta kuwa kyam saman fuskarta. "Wallahi kaine, kaine ko, Yaasir? Na fada masu kaine..." sai kuma ta saki wannan maganar ta koma kan kujerar gefenshi kamar wacce zata shige jikinshi. "Baka sani ba ko? Hanan ta rasu. Eh, Hanan dinmu, Hanan dinka. Maganarta kullum Abba, ko kafin ta mutu saida ta tambayeni wai idan ta mutu zata ganka?" Kuka take babu kyaftawa gashi sai magana take zar zar zar bata jira ko numfashi taja.

Daka ganta kasan a kidime take, tsoro da fargaba ne kwance kam fuskarta amma kuma bakinta sai zuba yake ba tsayawa, maganar Hanan kawai takeyi kamar wace tababbiya. "Ramlah, bani ne mijinki ba. Sunana Yassar ba Yaasir ba. Kuma ni bani da danuwa balle nace shine mijinki. Inda yayye da kanne maza amma gaba dayansu muna tare babu wanda ya rasu kuma babu wanda ya bace."

Girgiza kai ta farayi hawayenta suna kara zuba yar yar yar. Hannu ta kai kan fuskarshi kamar wacce aka yanke ma yanda ake rayuwa. Rufe ido tayi dan a tunaninta idan taji fuskarshi dimun dimun zata kara tabbatar ma kanta shine Yaasir dinta, namiji na farko data taba so a rayuwarta. Ta taba fuskar nan ranar daya mutu, banbancinsu daya ne. Fuskar data taba a Katsina tana da sanyin fitar rai a jikinta, wannan kuma a dumin rayuwa tattare da ita.

Ganin har yanzu dai tana da kokwanto yasa ta tuna akwai tabo a hannunshi, idan bata gane komai ba ai zata gane tabon ko? Da hanzari kamar wacce ta zaufe ta bude idanunta da sukayi jajir da hawaye ta saukesu kan fuskarshi. "Tabon hannunka, yana nan ko? So nake na nuna masu su yardai kaine Yaasir!" Hannunta ta kamo zata duba gashi riga me dagon hannu yasa yayi maza ya janye hannunshi yana mikewa tsayen tayi duk ta gama fita hayyacinta.

Kokarin riko hannun nashi take Rayyan ya janyota baya. Juyawa tayi ta kalleshi a kidime, "Rayyan, shine, kace ya bari na duba!"

Hannunta ya rige gam yanda ba zata iya zillewa ba, "Ramlah bashi bane ba, ya fada maki da kanshi. A tunaninki idan shine wani uba ne zaiji danshi ya mutu kuma hankalinshi kwance? Ramlah ba muharraminki bane ba, da matar shi ta kusa haihuwa, is it okay ya baki hannunshi ki duba tabo? Ba'a..." bai ida magana ba ta sulale ta suma, da kyar ya tallabota jikinshi kafin ta ida faduwa kasa.

Anfa koma makaranta, sai dai kawai kuyi hakuri dani sai kuma ranar da kuka jini. Ga exams, ina bukatar addu'arku.

Nagode.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top