Biyar
Saida ta jira har motar Lubnah ta wuce kafin da ajiyar zuciya ta juya ta shiga asibitin. Yanzu har ta saba zuwa asibitin, duk kuwa da cewar ba wani cigaban azo a gani bane aka samu, amma ba laifi. Cikin natsuwa take takawa har ta karasa office din Dr Mahmud. Saida ta kwankwasa taji an mata alamar ta shigo kafin ta shiga office din idanunta kyam a kasa har saida ta zauna. Dagowa tayi da niyyar gaishe shi amma sai taga wata fuskar ta daban.
Da hanzari ta fara juyawa tana kallon office din dan taga ko mistake din shiga wani office din tayi, amma sai taga shi dindai ne, dan kuwa komai yana nan kamar yanda ta sanshi. "Ina kwana?" Ta furta a hankali tana kallon bakuwar fuskar data cikata da kallo.
"Ina kwana kema? Ramlah ko? Dan yace mun ke kadai yake da session dake yau." A hankali ta daga mashi kai tana wasa da yatsun hannun ta.
"Yana ina?" Ta tambaya tana dan kara kallon wajen kofa koda zataga shigowar Dr Mahmud.
"Yaje wata seminar ne, bazai samu damar zuwa asibiti ba yau. Ni sunana Dr Aliyu, ni zan zama therapist dinki a yau." Da har tana da niyyar mikewa, amma jin maganarshi yasa ta koma ta zauna tana tunanin yau ma wani sabon me san surutun Allah ya hadata dashi.
Duk tambayar daya mata, kamar yanda takewa Dr Mahmud shima haka ta mishi, babu amsa balle ya saka rai cewar zasu samu wani cigaba. Sai can ya danyi baya yana kallonta yana murmushi, "To yanzu Ramlah, me kikeso kiyi a rayuwarki? Kinga kamar ni inasan karance karance, dukda cewar aikin likitanci yanada cin lokaci, amma no matter how ina samun time nayi karatun novels da poems. Ke me kikeso ta wannan fannin?"
Saida tayi jim kamar bazata amsa shi ba can kuma ta dago tana kallonshi. A karo na farko Dr Aliyu yaga alamar rayuwa a idanta, da wani abu da zai iya kiran zagwad'in abu, wanda a turance ake cema enthusiasm. Da dan guntun murmushi kan fuskarta ta dago tana wasa da hannayenta, "Inasan hoto. Bawai a daukeni ba, Aa, ji na dauki mutane. Ba lallai sai mutane ba, komai na duniya. I love photography."
Murmushi yayi ganin ya samu hanya ta farko da zai samu har ya taimaketa. "To yanzu Ramlah kinasan hoto, in yanzu aka baki camera zakiyi?"
Da murmushi me gaggawa ta daga mashi kai, "Zanyi mana. Akwai abubuwa da yawa a rayuwa wanda bayan hoto dan adam sai ya manta dasu, abubuwan da suka faru da mutum musamman ma na farin ciki. I think photography is the greatest gift to mankind, my opinion though." Mamakin kanta ma take, rabon da tayi magana har ta manta, balle turanci, sai taji abun banbarakwai. Amma a lokuta da dama takan gaza yanda zatayi dan tayi magana mutane su fahimce ta. Dukda cewar batayi wani ilimi mai zurfi ba, amma kuma Allah yayi mata kaifin kwakwalwa.
Magana suke a hankali yana jan hankalinta tana kara bude baki tana mashi magana. Ya lura da wani murmushi dayake kwance kan labbanta, da alamar da gasken fa take san daukar hoto kuma har kasan ranta. Bayan sun gama ya daga waya ya kira number din driver da Lubnah ta bata akan idan ta gama ta kirashi kai tsaye kawai, dan ita tanada taron da zata halarta bai zama lallai ta iya daukar waya ba.
Lambar ce bata shiga ya dago ya kalleta, "To Ramlah lambar direban bata shiga, ya za'ayi kenan? Zaki gane gidan ne sai na kaiki?" Ya tambaya. Gani yayi tayi wani kasak'e kamar wacce aka jefa da kankara kafin ta girgiza mashi kai a hankali.
"Ko ka kira Lubnah?" Abunda zata iya furtawa kenan. Amma ita yanzu ko ranta akace zaa dauka in bata nuna gidansu Lubnah ba ai ta gwammace a daukeshi dan bata gane komai. Yaushe ma ta tsaida hankalin nata waje daya?
"Banda number dinta amma bari na kira Mahmud sai ya kirata." Hakan kuwa akayi. Suna nan zaune suna jiran Mahmud ya kira Lubnah sai gashi ya kirashi daga baya. "Tace zata aiko wani ya dauketa, Aliyu. Nagode sosai fah. Zaka iya magana yanzu akan halin da take ciki ko sai na dawo?"
Dan kallonta Dr Aliyu yayi da wutsiyar ido, "Ina ganin anjiman zaifi. Sai ka dawo din." Daga haka sukayi sallama. Sakon Lubnah ya fada ma Ramlah kafin ta mishi godiya ta mike ta fita. Har tazo bakin kofa ta jiyo muryarshi yna fadin, "To Ramlah baki fada man sunanki ba."
Da wani yanayi take kallonshi, irin ba sunan nawa ka kira yanzu ba? Amma sai ta danyi murmushi, "Sunana Ramlah."
Ya girgiza kai a hankali, "Kinga kamar ni Sunana Aliyu Idris Batsari. Ke miye naki sunan."
Dakyar ta kakalo murmushi kafin ta amsashi a hankali, "Sunana Ramlah Kabir Ibrahim." Bata jira cewarshi ba ta fice daga office din. Da fadin sunanta yaso tado mata da dukkanin damuwar da take kokarin dannewa.
Amma tunowa da daya kuma tilon abunda takeso a rayuwa wato daukar hoto, sai ta saki dan karamin murmushi. Tana hango kanta a matsayin me daukar hoto, har ta isa harabar asibitin. Bata jima a zaune ba sai taga mutum tsaye gabanta.
Ta dago ta kalleshi amma baisan abunda zai fada mata ba, yama manta sunanta da Lubnah ta fada mashi. "Kece?" Abunda ya tambay kenan, yasan yadda yayi maganar kamar wani sakarai, amma da gaske yake bazai iya tuna sunan ba.
Hada fuska tayi waje daya, "Nice wa?" Ita ta gane shi, amma bata taba tunanin Lubnah zata iya aikoshi ya dauketa ba sai bayan daya furta hakan.
"Lubnah tace nazo na dauki wata, na manta sunanta kuma sai na ganki. So I thought maybe bake bace ba." Bai jira amsarta ba ya dauko wayarshi ya danna ma Lubnah kira. "Hello, Lubnah. Yama kikace sunanta?"
Saida tayi yar dariya kafin ta amsashi, "Dan Allah kayi hakuri Rayyan na tasoka kana aiki, ba yanda zan barta ta hau taxi ne kuma direban wayarshi bata shiga. Ramlah mana, ko ka manta tane?"
"Ba komai karki damu. Yauwa thank you." Daga haka ya kashe wayar ya maida hankalinshi akan Ramlah wacce tunda ya fara wayar take kallonshi tana mamaki. Wai me yake nufi? Eh tasan bata cika fitowa ba, haduwarsu ma zata iya cewa wannan ce ta ukku, amma nufinshi bai ganeta ba ko mi? Dan guntun tsaki ta saki can kasan ranta, ba kasafai abubuwa ke bata haushi ba, damuwar dake ranta ma ta isheta.
"Ramlah ko?" Da kamar bazata mashi magana ba sai can kuma ta daga mashi kai alamar eh, Ramlah. "Yauwa, muje, Lubnah tace mun na mayar dake gida." Babu musu Ramlah ta mike suka taka har inda ya aje motarshi kafin suka fita daga asibitin gaba daya.
Abun mamaki yau bata fada duniyar tunani ba, tsayawa tayi tana kallon titi kyam da idanunta tana tunanin inda ace ta dauki wancan wurin hoto wane irin kyau zaiyi. Ita kadai sai dan murmushi takeyi can ta tsinkayi muryar shi yana mata magana.
"Kina jin yunwa? Zan tsaya restaurant na karbi abinci." Juyowa tayi taga magana yayi amma titi yake kallo. "Aa, nagode."
Daga haka suka cigaba da tafiya sai kuma taga sun shiga gidan mai, daga saitin window dinta akwai wasu mabarata. Matar ce zaune ita da yaranta biyu duk mata, wanda Ramlah tanada tabbacin yar karamar zatayi sa'ar Hanan dinta.
"Hajia dan Allah ki taimaka mana, bamh da kowa kuma banda abun basu." Ta fada tana riko yar karamar wacce basai ta fada ba kana ganinta kasan yunwa tayi mazauni a tattare da ita.
Runtse ido tayi a hankali kafin ta juya taga Rayyan ya fita ana saka mashi mai. Sai bayan daya dawo motar har ya zauna yaga tana kallonshi idanunta sunyi rau rau dasu. "Ramlah lafiya?"
"Dan Allah ka bani kudi naba matar nan." Batasan roko, amma yanzu dan dole ta roki Rayyan dan babu yanda za'ayi ta bar matar nan haka nan. Batayi bara ba, amma tana da tabbacin yanda zafi da radadin rashi yake. Ga yara tattare dakai amma baka da abun basu.
Dan lekawa yayi yaga matar tana kallonsu, ko baka da imani sai matar ta baka tausayi. Kudi ya ciro cikin aljihun shi ya mika ma Ramlah ba tare daya tsaya kirgawa ba. Karba tayi ta fita motar baki daya. Har kasa ta dan durkusa tasa hannu ta shafi fuskar yarinya sannan ta dago ta kalli matar.
"Nasan ko nawa zan baki bazasu taba maki maganin matsalar ki ba. Amma ina rokon Allah ya magance maki matsalarki." Godiya kawai matar keyi hada kukanta, yaran kau daga ganin kallon da suke mata kasan basu taba samun wanda ya masu irin wannan kyautar ba. Sallama ta masu ta koma cikin mota ta zauna, Rayyan kuma ya tada motar suka fita daga gidan man gaba daya.
Saida yayi yar tafiya kafin ta juyo, "Nagode sosai. Zan mayar maka duk ranar da Allah ya bani iko."
Da dan murmushi wasa, ganin yadda take ta kokarin maida hawayenta yasa ya mayar da maganar dayaso yi mata. "To ai ni kaina bansan nawane ba. Saidai ki maida mun da wani abun, badai kudi ba."
"To ai kudi ka bani. Amma me kakeso?"
Dan jim yayi kafin ya kalleta, lokacin yayi daidai da zubar hawayenta. "Yanzu a bar maganar bashin nan, goge hawayenki tukunna." Batayi mashi musu ba tasa hannayenta duka tana gogewa, amma kamar ma cewa take su kara zubowa.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top