Bakwai
Mikewa yayi tsaye yana kallonta da yar dariya sannan yana kallon kofar, "To Ramlah, tunda nidai yanzu ba'a so na ga Dr Aliyu nan sai ki mishi magana shi." Ko kadan baiji haushi ba, in baccin ba dadin da yaji dan alami sun nuna da taimakon Dr Aliyu akan iya ceto rayuwar Ramlah, tunda har tafi sakin jiki dashi.
Dan dukawa tayi tana wasa da yatsunta tana murmushi irin na kayi hakuri, ta kusa minti sha biyar office din Dr Mahmud amma duk tambayar da zai mata bata ce mashi k'ala. karshe dai yace mata ko a kira mata Dr Aliyu, sai a lokacin ta daga kai ta mashi magana akan eh. Yanzun ma da murmushin jin kunya ta dago tana dan girgiza kanta.
"Allah ba haka bane ba." Ta furta a hankali, shi kuwa Dr Mahmud dariya yayi yana daukar wasu takardu kafin yayi hanyar kofa, jnda sabo ya saba da halin Ramlah yanzu. Tun ranar da suka fara therapy session da Dr Aliyu daga ranar kullum saidai ya kira mata shi, bata taba yarda tayi magana dashi.
"Na saba yanzu nikam, kila ma dai daga yanzu da kinzo zan maki kwatancen office dinshi ba sai kun rika tadani office dina ba." Da yar dariya Dr Aliyu ya dan bugi kafadarshi kafin ya karasa kujerar zamanshi ya zauna. Saida ya jira Dr Mahmud ya rufe kofar kafin ya dago yana kallonta.
"Ramlah, an tashi lafiya?" Abunda ya tambaya kenana ita kuma ta dago ido tana kallonshi tana murmushi a hankali. Dama labari take san bashi.
"Lafiya lau. Ina kwana?" Ta mayar mashi da martani. Shidai baisan dalili ba amma Ramlah tana burgeshi, kuma sosai ba kadan. Dukda cewar tarin damuwar da take ciki yak'i barinta ta kwantar da hankalinka amma daga ganinta sai ta burgeka kuma sai kaji kanasan taimaka mata da dukkan wani iko da Allah zai baka.
Murmushi yayi a hankali, "Ina kwana kuma? Saidai ina yini, dan yanzu babu dadewa sha biyu zatayi yan makaranta su tashi. Kinga yau juma'a ai." Dan kada kai tayi alamar ta tuna, amma a zahirin gaskia idan ba yanzu daya fadi ba ita bata ma gane ranakun mako, kawai dai rayuwa takeyi gata nan dai ita.
"To ina jinki, ya photography class din? Akwai dadi? Kinyi pictures?" Ya tambaya yana kureta da idanu, itama dagowa tayi da fara'arta alamar zatayi maganar abunda takeso.
"Sosai, inajin dadin zuwa class din. Na manta camera din a gida dana nuna maka."
"To yanzu akwai abunda kikeji dama ace kinada ikon maidawa baya ki dauki hotonanshi dan karki manta?" Shi wani lokacin har taka tsantsan yake wajen tambayar da zaiwa Ramlah, dan cikin minti daya tana iya chanzawa baki daya ta koma Ramlar ta tada.
Dan jim tayi da kamar bazata amsashi ba sai can kuma ta daga kai a hankali, "Hanan. Kullum na kalli camerata sai inji dama zan iya komawa baya dukkan rayuwar da mukayi da ita in dauka hoto. Dariyarta, murmushinta, yanda take bacci, rigmarta, kukanta, wasanta, komai nata." Sai kuma tayi shiru, dan tunawa da tayi da lokacin da Hanan tana raye ba karamin fama mata tabon dake zuciyarta yayi ba, wanda a kwanakin nan babu abunda batayi dan taga ta goge shi tayi rayuwa kamar kowa, kamar yanda Lubnah da Mama sukeso suga ta rayu.
Tunda take yau ce rana ta farko data taba yin magana akan rayuwarta ta baya, wanda hakan ba karamin dadi yama Dr Aliyu ba dan kuwa an samu cigaba sosai ma ba kadan ba. "Wacece Hanan din? Tana ina?" Hawayen dayaga sun zubo mata yasa yaji dama bai mata tambayar ba, amma kuma hakan ne kadai zai kara taimakonta.
Da kamar bazatayi magana ba sai can kuma ta fara, "Ta rash, diyata ce, shekararta biyar. Da inada iko dana koma rayuwarmu ta baya, komai nata nayi recording, har yanda ta koma da ciwonta yayi tsanani, yanayin yanda take kallona da zafi da radadin ciwo tana ceman Ammi. Har gawarta dana dauka, dan wataran sai naji kamar Hanan dita bata mutu ba, har muryarta inaji tana kiran sunana." Zuwa yanzu kuka take kamar ranta zai fita, watanni sun shude, amma Ramlah ta rasa yanda zatayi ta rage zafi da radad'in mutuwar Hanan a cikin zuciyarta.
Saida ya barta ta gama kukan kafin ya mika mata hankici, "Sannu, ko na baki ruwa?" Ya tambaya yanayin hanyar firij din dake office din. Dan daga mashi kai tayi, ya bude ya dauko hada da disposable cup ya aje mata. Saida tasha ruwan hankalinta ya dan kwanta kafin shima ya koma ya zauna.
"Allah ya jikanta, Ramlah." Yasan yi mata magana akan ta dauki kaddara kuma ta manta da dukkan wani abu daya faru babu abunda zaija mata face wani kukan. "Inada diya nima, sunanta Hafsah. Shekararsu daya da Hanan." Da hanzari ta dago ta kalleshi.
"Da gaske kake?" Ta tambaya, saida yayi yar dariya kafin ha gyada mata kai.
"Nayi dan yaro ko? Lokacin nayi aure da wuri, amma wajen haihuwarta mamarta ta rasu, tana wajen Mamata yanzu. Ko kinasan ganinta? Dama yanzu zanje daukarta daga makaranta." Da hanzari Ramlah ta mike daga kujerar da take zaune.
"Allah sarki, Allah ya jikanta. Eh dan Allah, ba matsala in munje?" Ji take duk wata yarinya dake shakaru daya da Hanan tamkar Hanan dinta, zataso taga wannan Hafsar.
Da yar dariya ya mik'e shima yana kallon agogonshi yaga lokacin ma har ya dan gota, tana can kuwa tana bak'in rai in ba'ayi sa'a wani abun ya dauke mata hankali ba. "Babu wata matsala, amma bari na kira Lubnah na fada mata zan maidaki gida, kar hankalinta ya tashi." A gabanta sukayi magana da Lubnah, dan kuwa tunda suka lura Ramlah tafi sakin jiki ta mashi magana suka amshi lambobinshi.
Suna tafiya yana bata dan labarin Hafsah har ya nuna mata hotonta a wayarshi. Kallon yarinyar kawai takeyi, amma lokaci daya santa ya shiga ranta. Koda suka isa makarantar burinta bai wuce taga yarinyar ba. Tana zaune mota bayan ya fita ta hangoshi hannu rike da Hafsah sai tsallen murna take har suka karaso motar. Da gudu ta rugo ta fada jikin Ramlah sai kuma kamar an tsikareta ta dagata tana dariya ta juya tana kallonshi.
"Abba, itace Ammi ta ko?" Cak numfashin Ramlah ya tsaya, anya ba Hanan dinta bace? Amma basu kama ko ta minti daya.
Dagawa tayi ta kalli Dr Aliyu wanda yayi saurin girgiza mata kai alamar Aa, kartayi kuka. Saurin maida hawayenta tayi tana me janyo Hafsah jikinta. "Eh Hafsah, nice Amminki."
Da jin dadi Hafsah ta dago daga jikin Ramlah ta juya tana kallon Aliyu, "Abba! Dan Allah bari naje na kira Farha taga Ammi ta yau, dama kullum sai tace tanaso ta ganta, ita kuma Hajia Mama in nace tazo daukata sai tace kai zakazo daukata." Bata jira cewarshi ba ta ruga sai gata hannu rike dana kawarta Farha.
Magana Ramlah take masu amma kuka takesan yi. A haka dakyar direban su Farha ya samu ta bishi suka tafi gida ita kuma Hafsah ta shiga mota suka tafiya. A hanya babu abunda take sai bama Ramlah labarin makaranta, wani abun ma shi Aliyu ya dauka ta manta ya faru har sukazo kofar gidan.
Fitowa tayi daga motar tana kallonsu da murmushi amma duk wanda ya kalleta yasan kuka takesan yi. "To Hafsah, banda rashin ji kinji? Kuma duk abunda Hajia Mama tace kiyi kiyi. Bye!"
Ai nan da nan Hafsah tace bata san zance ba, kuka ta farayi tana fadin itadai wallahi kodai a barta nan ko kuma Ammi tabish gidan Hajia Mama. Karshe ma duk maganar da Aliyu yake mata fitowa tayi daga motar ta rike kafafun Ramlah. Har zai fara mata fada akan ta fito su tafi sai Ramlah ta girgiza mashi kai kafin ta duka har kasa tana ma Hafsah murmushi.
"Hafsah rashinji fa babu kyau, ko kinaso Allah ya k'ona ki?" Da hanzari yarinyar ta girgiza kanta kafin Ramlah ta cigaba, "To kinga indai bakiso Allah ya k'onaki dole ki riga bin maganar Abbanki, kinji? Yanzu kije gida nasan Hajia Mama tana can tana jiranki. Kiyi wanka, kiyi sallah, kici abinci, yau zakiyi kallon carton da wasa duka, ko Abba?" A tare da ita da Hafsah suka daga suna kallonshi, wanda tunda Ramlah ta fara magana idanunshi kyam a kanta.
Murmushi ya masu a tare kafin ya daga masu kai, "Har garden zan barki kije kiyi shuka, Hafsah."
"To kinji har shuka zakiyi yau. Banda rashin ji, kinji Hafsar Amminta?" Rungumeta Hafsah tayi tana murmushi mai kayatarwa. "To shikenan, Ammi, bazan kara ba." Sak yanda Hanan ke fada mata in tayi mata fadan wani abun. Dakyar ta samu ta daure har motar Dr Aliyu ta bace mata da gani kafin ta sake hawayenta suka zubo.
Shiga tayi cikin gidan amma batasan ta inda zata tsaida hawayenta ba. Kamar daga sama taji ance, "Nikam dadin kuka kikeji ne ko mi?" A razane ta juyo taga Rayyan gefenta yana tafiya shima cikin gidan da alamu yanzu ya dawo, hankalinshi kwance yake bama zaka dauka da ita yayi maganar ba.
Sauri tayi ta share hawayenta, amma tasan tabbas yau sai taci kuka ta gode ma Allah. "Ina yini?"
"Ina yinin ki? How was the therapy? Shi waccan doctor din haka ake therapy ki dawo gida kina kuka kuma?" Yar dariya ta subuce mata.
"Ba ruwanshi." Yasan ba ruwanshi, dukda baida tabbaci akai, yasan yarinyar nan ita tasaka ta kuka. Dan shi koda ya hangosu ya dauka bak'i akayi gidan mata da miji da diyarsu, sai can ya lura ashe Ramlah ce.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top