Ashirin Da Shida
Magana ya fara mata a hankali cikin natsuwa, ita dai Ramlah bata tanka shi ba dan kuka take bil haqqi kamar yau tayi rashin Hanan. Dan numfasawa yayi kafin yayi shiru ya tsaya kawai yana kallonta, jin shirun nashi yayi yawa yasa Ramlah ta juyo tana kallonshi sai taga ai ita yake kallo. "Kayi shiru." Maganar ma dariya ta bashi, sai da yayi yar dariya tukun ya bata amsa, "To Ramlah ya kikeso na miki? Naga ai kamar dadin kukan kikeji ko?"
Da sauri ta turbune fuska tana girgiza kai, "Kawai inaso kaita magana ne, sai inji raina na mu sanyi. Ko har ka gaji?" Zuwa yanzu hawayen nata sun daina zuba, itama juyowa tayi na yanda zasu fuskanci juna. "To inta magana me zance? Hakuri zanta baki ke kuma kina kukan ai ko?"
Hannayenta duka biyu tasa ta goge sauran hawayen dake kwance kan kuncinta, "Na daina kukan yanzu ai. Ka bani labarin Maman Hafsah." Sai bayan tayi magana ta lura fuskanshi ya chanja sai kuma taji dama bata yi ba. Sai a lokacin take jin haushin kanta, kullum itace tasa bawan Allahn nan gaba tana mashi kuka bayan shima fa yayi rashin nan a rayuwarshi. "Yi hakuri, muyi wani maganan na daban."
Murmushin karfin hali ya mata yana girgiza kai, "Nima yau ki zama therapist dita, I'm just realizing ban taba maganar ta da kowa ba tun bayan rasuwarta." Dan daga mashi kai tayi a hankali tana kallonshi. Magana ya fara kamar wanda be san ayi, "Sunanta Fatima, kuma tanada kyau kamar ita tayi kanta. A makaranta muka hadu, itama likita ce amma bangaren mata. Tunda nake ban taba ganin mace kamar Fatima ba, ga sanyin rai, ga fara'a..." saurin tsaida kanshi yayi, dan lura da yayi tunano suffarta da halayyarta zai iya haddasa mashi wani ciwon a zuciya. "Anyways, da kawata ce kawai muan haduwa wajen karatu daga nan muka zama abokai sosai da sosai har naji na fara santa. Koda na fada mata ina santa bata ce bata so na dan itama ta dade tana kaunata. Daga nan muka fara soyayya mai tsanani tsakaninmu amma lura da nayi kullum santa karuwa yake a zuciyata haka zalika kusancinmu yana karuwa, nasan tabbas wata rana dole shedan yayi galaba tsakaninmu, hakan yasa na nemi shawararta akan inaso nawa Baba magana aje gidansu a nema mun aurenta.
"A farko kamar bazata yarda, dakyar na samu nayi concinving dinta ina nuna mata hadarin soyayyar da muke a wata kasa da babu wanda zai fada mana muji kuma kusan ko yaushe muna tare bacci kawai ke raba mu. Koda su Baba sukaje wajen iyayenta basu fito gidan ba saida aka daura aure. Tunda nake ban taba farin ciki irin na ranar ba a rayuwata." Tunda ya fara magana Ramlah bata ga murmushin shi ba sai a lokacin. Wanda daka gani kasan cewar har yanzu farin cikin ranar yana tattare dashi kuma bazai taba mantawa dashi ba.
"Kinsan miye abun dariya?" Girgiza kai tayi, tana mamakin yanda dariya ke san subuce mashi bayan su dukansu sunsan wannan labarin ba'a dadi ya kare ba. "Tunda na fada cewar an daura mana aure itama yan gidansu suka fada na daina ganinta, ko makaranta muka hadu rugawa take idan na tambayi friends dinta sai suce wai kunyata takeji. Tun abun yana bani haushi har yazo yana bani dariya dan ita da gaske kunyar tawa takeji. Ranar dai naje dakinta a hostel nayi sa'a a bude, dan kuwa ko bude bata barinshi tun abun, tana zaune tana cin abinci ga littafi gefenta tana karatu." Shiru yayi daga nan.
Ramlah juyowa tayi tana kallon yanda murmushi ke kwance kan fuskarshi, "Me kake nufi?"
"Bazan ida baki labarin ba ai." Batasan lokacin data banka mashi harara ba. Dan daga ganin murmushin dake fuskarshi da kuma kallon dake idonshi kasan tunano abubuwa yake wanda suke faranta mashi rai. "Yo har ma ka isa? Nan ji nake kamar ina karanta hausa novel sai murmushi nake inaso in ji yanda amaryarmu ta kare. Ai wallahi ci gaba kawai."
Dariya ya farayi ganin ita fa da gaske take dan yasan nan da yan mintuna haushi ma zata fara ji, "To in inajin kunyarki fa?" saida tayi yar dariya tukunna ta daga kai, "Cire kunyar na yafe maka na yau kawai." Dan daga kafada yayi alamar ke kika siya da kudinki. "Idan na fara bazan tsaya ba, kin yarda?" Da zakuwa ta daga mashi kai alamar na yarda, "Nidai fada man koma menene inaji."
"Toh, bazan dai tsaya ba sai na kai aya. Bata lura dani ba dan hankalinta gaba daya yana kan littafin da take karantawa, abincin ma ko kallonshi batayi takeci. Saida nazo na zauna gefenta na janye littafin tukunna ta dago. Ai tana ganina hankalinta ya tashi, dama Fatima bata kaunar manyan kaya, dan ko kafin muyi aure kullum idan nazo zamu tafi makaranta sai na jira waje ta chanza kaya, wani lokacin ko weekends haka nazo fira wajenta kafin na shigo dakin dama sai na kirata nace ina waje, to kafin ta bude kofa sai an kwashi mintuna. Ranar kuwa wata yar fingilar rigace jikanta da wando iya guiwa kanta ko dankwali babu, ban taba ganinta a haka ba, sai naga duk kyanta da nake gani ashe yafi haka. Hankali tashe ta miki tana neman hijabi. 'Innalillahi, me kake yi a nan? Ka fita na chanza kaya yanzu zan fito!' A rude take maganar amma kafin ta karasa inda ta aje kayan data dawo makaranta dasu na janyota jikina. 'Ina sanki, Matata.' Abunda na fara furta mata kenan, dan kuwa ban taba san wata mace kamar ta ba, banma taba soyayyar ba sai kanta.
"Mutsu mutsun kwace kanta take amma na kasa sakinta tunda ban taba rike ta, yau kuma dana riketa naji bana iya sakinta. 'Haidar yanzu in aka shigo fah? Wata friend dita zatazo karban littafi fah.' Dama Haidar take ce mun. Ban saketa ba saima zama da nayi na daurata saman cinyata, in hankali Fatima yayi dubu to ya tashi, 'Na shiga uku, Haidar wai miye haka?' Dariya nakeso nayi ganin yanda ta rude amma naki, dan kara kyau tayi a haka ga gashin kanta daya burgeni. 'Koda tazo Fatima kawo yasan munyi aure school dinnan.' girgiza kai tayi, har yanzu ta kasa juyowa ta kalleni, 'Nidai dan Allah ka sakeni na suturta jikina.' 'Tunda kince Allah, yanzu tashi ki shirya wani waje zan kaiki.'
"Koda ta tashi kasa kallon idona tayi, babu yanda banyi ba amma yarinyar nan gezau, karshe da taga bazan fita ta chanza kayan ba saidai ta shiga toilet, koda ta fito dakyar tace mu tafi. Dama tun bayan daura auren Baba ya kama mana gida a wani estate nan kusa da school dinmu saida muka shiga naga tanata kallon gidan tana murmushi, 'Wannan fah? yayi kyau sosai, off campus ka dawo?' Hugging dinta nayi ta bayam dan nidai har ga Allah ban tabajin inasan na rike wani ba kamarta. 'Eh, amma ni da ke zamu zauna.'
"Juyowa ta nayi tana fuskanta ta, sai a lokacin ta dago ta kalleni na lura idanta cike yake fal da hawaye, a rude na riko fuskarta ina tambayar ko lafiya, 'Fatima lafiya? Ko bakya so mu zauna tare? Sai an gama exams? Ko kuwa sai munyi graduation mun koma gida? In haka kikeso I'll understand...' bata bari na ida magana ba ta rungume ni tsam ta fashe da kuka, har lokacin hankali na tashe yake. 'Kawai tsoro nake ji Haidar, ni nasan san da nake maka yafi naka yawa, kuma I can't believe wai ka dade ma da zama mijina. Idan muka rayu a nan muka koma gida bazaka wulakanta ni ba?' Kuka take bil haqqi, dagota nayi daga kirjina ina kallon cikin idanuwanta. 'Zaki haifa man baby?' abunda na furta mata kenan, dan ni babu abunda yake gabana face inga muna zuwa makaranta tare da Fatima kuma ace tana dauke da d'a na ko y'a ta. Wani irin kallo tamun, 'Serious magana fa na maka.' Zagayo hannayena nayi na kara kusanto ta zuwa jikina, 'Nima ai serious maganar na miki ko? Da gaske, mu haifu kafin mu koma gida, Fatima, kinga saura shekara...' ban ida magana ba ta bugar man kirji tana turbune baki, 'Haidar! Tambayar ka abu nayi.'
Saida nayi dariya, idona cikin nata kafin na amsata, 'Idan na amsaki nima zaki amsani?' daga mun kai kawai tayi, 'Toh, ina maki san da bansan adadinshi ba Fatima, kuma har na komawa Allah bazan taba wulakanta ki ba saboda ina mugun sanki kamar na fiddo zuciyata na baki. Zamu haihu kafin mu koma gida?' Neman zillewa take nayi hanzarin rikota, 'Baki amsaba ba tukunna...' tunda nake ban taba farin ciki ba irin na ranar, 'Sai mun koma gida, a raba daki kowa da nashi...' bata ida magana ba na..."
Kafin ya ida magana Ramlah ta callara ihu tana toshe kunnuwa, "To bansan ji! Haba ya isa haka." Wata irin muguwar dariya Dr Aliyu ya fashe da ita, kallonta kawai yake hada wani runtse ido. "Ai kuma baki isa ba yarinya. Ya muka yi dake? Cewa fa kikaji in fadi duk abunda nake san fadi kin yafe, bamuyi haka dake ba?" Dariya kawai yake har kasan ranshi yana ganin yanda ta runtse ido tana girgiza kai.
Juyowa tayi tana kallonshi, "Yi hakuri nidai amma wallahi na hakura da labarin."
Da wasa ya cigaba da magana, "Ayi haka kuwa Ramlatu? Ki tsaya kiji abunda na mata daga nan mana."
"Wayyo Allah na, yau Allah ya hadani. Nidai bansan ji, wannan abu..."
"Me nayi toh? Ba matata bace ba?" Shi tunda yake bai taba ganin dramatic mutum irin Ramlah ba, ita fa bil haqqi wai bata san ji.
"Ai saboda matar take ce yasa bansan ji."
"To yanzu ace ba matar tawa bace ba, zakiji? Na..."
"Kanama Allah Dr kayi hakuri, wallahi na yafe har sauran labarin."
Dariya yayi yana daga hannu, "To sarakan kunya, dake da ita bansan wanda yafi wani kunyar ba ai. Nayi shiru, sai me kuma?"
Juyowa tayi tana kallonshi, "Sai in shiga ciki, nasan Hafsah na can na jira na." Fita tayi daga motar shima ya fita amma bai zagayo inda take ba. "Baki tambaya ko mun haihun?" da dariyar mugunta yayi maganar, wani zaro idanu tayi tana kallonshi. "Wai kai baka jin kunya? Nace ban san ji, na bani." Bata jira amsarshi ba ta ruga da guda tayi cikin gida, sai a lokacin Rayyan wanda idonshi yake kansu ya dauke ya koma kan kujerar motar ya lafe, wani irin madaci ne ya darsu a zuciyarshi ganin yanda yake dariya daga gani yana tsokanarta. Wai shin me Dr Aliyu ne yake nufi da Ramlah?
Badai ku comments ko? Zan tafi hutu kowa ya huta.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top